JIDDATUL KHAIR 45
Abuturrab yyi parking kofar gidansu ya kashe motarsa ya sauka, suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga cikin gidan, bbu kowa parlon duk yan biki sun watse, ya wuce dakin Hajja ya bude kofar ganin Mahaifiyar El-Basheer xaune dakin ya sa shi yin sallama, Hajja dai kallo daya tayi masa ta ci gaba da xancenta tana cewa “Wllh baki ganta ba, babu sa wa babu hanawa, don dai kawai ni ina komai cikin sirri ne banda haka da har sunan
yarinyar sai in fada maki ynxu, kuma ni ba abinda yasa na kara samun kwarin gwiwa sai ganin yanda Bashir din yayi na’am da xancen nawa, wllh ko musu d’an arxikin bai yi ba, da dai su o’o ne har ubana dake rami sai ya xaga, shi sa kika ga nayi ta ja baya da bikin nan ba ruwana aje a kunyata ma yarana ni a banxa, ai xamana Masar ya koya min iya xaman duniya, nasan yanda xan xauna da ko wani gantallale lafiya babu me jin kanmu” Murmushi kawai Hajiya Safinah mahaifiyar El-Basheer ke yi, Abuturrab ya karaso ya xauna kasa yace “Ina yini Mummy?” Da fara’arta tace “Lafiya lau Captain, yanxu muka dawo daga can gidan naka ai tare da
Hajiya Hafsah, amaryar taka tace mana kaje kai kawayenta tasha ko?” Yace “Ehh” tace “Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya, ya kauda fitina tsakaninku” Yayi kasa da kai yace “Ameen” Sai a sannan ya kalli Hajja yace “Ina yini” Da sauri tace “Aa, ka dai gane ma idonka, lafiya lau na wuni wllh” Ya mata wani kallo ta gefen ido, Hajja tace “Kina ji na Safinah” Mummy tace “Ina ji Hajja” Tace “Kar ki dau maganata da wasa, tunda dai gobe xa ki koma kina isa gida, ko da mijinki na xaune fada ki
yi sallama ki shiga kiyi masa duk bayanin nan da na maki, kinga ai tunda aka samu wannan mutumi yyi aure shi ma Bashir ya kamata yayi auren” Mummy tace “Haka ne Hajja” Hajja tace “Atoh, da a Masar ne ma wace shegiya xata kallesu duk sun tsofe a gida, mu fa a Masar sai ki ga d’an yaro shekara ashirin da biyu yayi aurensa gwanin ban sha’awa wllh” Mummy na gyada kai tace “Ikon Allah” Hajja tace “To ba ruwana wllh, idan xa ki dau maganata
da muhimmanci ki dauka, ni anjima ma sai in sa a kira min waya in sa cikin dubara a turo yarinyar kamar dai xata kawo min sako sai ki ganta” Mummy tayi dariya tace “To ae Shikenan Hajja bari in je can bangaren Hajiya Hauwa” Hajja tace “Toh shkkn, xuwa nan da magariba xa ki ga an turo min yarinyar in sha Allah” Mummy dai na murmushi ta mike ta fita, Hajja ta kalli Abuturrab dake danna wayarsa tace “Har yanxu kuna can gwamutse da kawayen amaryar?” Yace “Toh ina ruwanki?” Yana fadin haka ya
mike ya nufi kofa tace “Ji shashasha, to ni ina ruwana in ma shekara xa su yi a gidanka? Ba dai mun maka me wuyar mun aurar da kai sauran Bashir ba, sae kaje can ka karata da mummunar matarka sae haske kamar jinjirar xabiya, ni sai na ga wani kallon tara saura quarter ma take ma mutane kamar” Tuni Abuturrab ya fice daga dakin ya kulle mata kofa, wayarta ta dauka ta mike tace “Bari in je a kira min Ramlah, kawai ce mata xanyi ta xuba abinci ta ba yarinyar ta hadata da direba a kawo min kuma daga nan
ina son ta wanke min bandaki, don duk ta fi sauran yan matan iyawa, kinga babu wanda xai xargi komai, daga nan tana xuwa sai in nuna ma Safinah” Tsaye Abuturrab yayi bakin kofa yana kallon Aunty, tace “Idan baxa ka karaso ciki ka kulle min kofa ba gwara ka fita don Allah Aliyu, bana son walakanci” Bai ce komai ba ya kulle kofar sannan ya karasa cikin dakin, tace “Yanxu kai abinda kayi jiya a tunaninka ya dace kenan Aliyu?” Yace “Aunty ni fa banyi komai ba, i instructed her to tell her frnds to come
out so i can drop them home amma taki, ni kuma bana son tashin hankali kawai na bar masu gidan gaba daya na tafi hotel na kwana, a ina aka ta6a cewa sai kawayen amarya sun kwana gidan amarya ranan da aka kai ta?” Aunty ta jefa masa wani kallo tace “Ance din, ina ruwan ka da kawayenta dake daki daban ku kuna daki daban, yan matan da suka taso tun daga Abuja suka xo sun cancanci wannan walakancin a wajenka Aliyu? Tun da yan matan nan suka xo garin nan Hajja ke hantarar su, dalilin ma da yasa nace su
kwana can din kenan, duka duka dai ai ba can xa su dauwama a gidan naka ba banda rashin hakuri irin naka, kuma banda ma kana son a tafi da matarka a baki meye na barin gidan?? wani ango ne ka ta6a jin yayi hakan” Abuturrab dai bai kuma ce mata komai ba, Aunty tace “Toh a gaskiya ka shiga hankalinka, kada in sake jin makamancin hakan, Aneesah dai ba abar rainawarka bace kasan daga irin gidan da ta fito kasan wacece ita, yar asali ce me dangi gabas da yamma kudu da arewa, kar kaga ka ta6a aure a gantale kun rabu a gantale, to ita wannan ba gantallaliya bace da
danginta, yar usuli ce” Kallonta kawai Abuturrab yake babu ko kiftawa, Ta mike tana gyara daurin dankwalinta tace “Yanxu idan kaje sai kasan yanda xaka bata hakuri ta hakura, ni ma kuma dama na bata hakurin” Sauke hannunta tayi a fusace tana kallonsa tace “Wai ya haka ina magana ka kafe ni da ido kayi shiru kamar baka jin abinda nake cewa, are you okay??” Sauke idonsa yayi yace “Na ji ki” Daga haka ya juya ya fita daga dakin ta bi sa da wani irin kallo. Umma ta ajiye wayar hannunta tana kallon Aunty Nafisah da mamaki tace “Wai ki ji Hajja in ba Jiddah abinci tare da driver ta kai mata….” Aunty Nafisah tace “Ikon Allah, ba dai gidan xan
tafi ba yanxu sai in tafi mata da shi kawai” Umma tace “Kin ji yanda ta dage kuwa, na ma ce mata karatu jiddan take Maimoon su taho da drivern, amma wai Jiddar ta taho da takardun kawai” Aunty Nafisah tace “Ki bar Hajja kawai ana magariba xan tafi tare da abincin in kai mata” Umma tace “To amma ki kirata ki sanar mata dai tukun kar tace an mata ba dai dai ba, ko ya kika ga” Aunty Nafisah ta dau wayarta ta shiga kiran Hajja, Hajja na dagawa tace “Hajjaju yanxu xan bar gidan Hajiya Ramlah sai in
taho maki da abincin….” Hajja ta katseta a fusace tace “Oh oh naga bala’i, ni dai na shiga uku, ita katuwar ce ta tsara maki haka Nafisah? Yanxu ke fisabilillahi tare dake muka xauna a Masar, ke kinga suna haka?
Me yasa xaki taho kasar mutane ki ari halin da ba taki ba ki dinga yin abun da ba ayi a Masar? Ga dai abinda nace ina so sai ayi ta min hanya hanya? Ita Ramlan don bata san ciwona ba har da cewa xata ba direba shi kadai ya kawo min abincin da xan ci, me na hada da direban xa a basa abinda xan xuba a ciki ya kawo min, dama mutum na yarda ya ci gaibu? Toh shkkn babu damuwa, ni baxan sake ce maku komai ba” Daga haka ta katse wayarta, Umma dai sai murmushi take, Aunty Nafisah tace “Toh Allah ya
kyauta, baxan ma koma gidan ba yau sai gobe, a ba Jiddar ta kai mata” Umma tace “To ai nace ki bari goben kika ki, ai shkkn bari in ba Jiddan ta kai, amma tana mika mata driver ya juyo da ita don tana da karatu gobe” Hijab har kasa Jiddah ta saka, tana rike da warmer din tuwo da miya da xata kai ma Hajja, gaba daya mood dinta ya canxa jin aiken da Umma tayi mata, babban damuwarta kar ta je ta hadu da Aunty, a sanyaye ta shiga bayan motar ta xauna har suka isa gidan bata da walwala, driver yayi parking kofar gida, ta sauka a hankali hannunta rike da warmer din ta shiga compound din gidan, a hankali ta bude kofar parlon tana leka ciki, ido hudu tayi da Abuturrab dake gidan har sannan suna xaune parlon da El-Basheer da ya takarkare yana masa labarin ball, ta karaso cikin parlon, El-Basheer ya juya yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi da