JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 45

karamin towel din a hannunsa, Aneesah ta bi sa da kallo sae kuma ta mike ta nufesa ta rungumesa ta kwanta bayansa kamar me rada tace “In maka shafan cream din ne?” Ya dakatar da goge gashin nasa yace “I am not rubbing anything Aneesah” ta xagayo gabansa still holding onto him cike da kissa tana masa wani irin kallon so tace “Sai me Babynah?” Yana kallonta kafin yace komai ta lumshe ido ta fara sumbatar bakinsa, daukarta yayi bai direta ko ina ba sae saman gado, cikin cool voice dinsa yace “I’m not in the mood Aneesah, ni ma gajiyar biki bai sakeni ba har yanxu….” yana fadin haka ya lakaci hancinta ya mike daga kan gadon ya tafi ya dau pajamas dinsa ya fara sakawa, Aneesah ta bi sa da kallon

mamaki har sannan tana kwance, can side din gadon ya tafi ya xauna bayan ya saka pajamas dinsa, ya juya ya kalleta yace “I need hot tea” Ta masa wani kallo ta mike tace “Baxan iya ba…” tana fadin haka ta fice daga dakin, a parlor ta dau wayarta ta fita ta koma wani daki ta kulle ta

shiga kiran Aunty, Aunty na dagawa tace “Lafiya Aneesah????” Cikin rawar murya tace “Aunty wllh fa kawai walakanci Aliyu ke ji, kinga yau ma ba shi da niyya” Aunty ta bude baki tace “Ke kuma sae kace ba mace ba

Aneesah, ae sae abun ya lalace ya gantale idan ya wuce yau” Aneesah ta marairaice tace “Toh ni ya xan yi masa Aunty, ji fa kudin da mutum ya kashe ma” Aunty tace “Xuwa xakiyi kiyi duk yanda xaki yi komai ya kankama, koma meye kiyi ni dai, sae da safe ni ba a bangarena nake ba” Daga haka Aunty ta katse wayar, Aneesah ta fi minti uku tsaye tana naxari sannan tayi wani murmushi ta fita dakin ta nufi bangarensa.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button