UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 11 to 20

Fateema tana shiga cikin gida ta mik’owa Umma kud’in tace ” gashi Umma wai yace in kawo miki”Fad’a Umma ta hauta dashi kan ta mayar mata da kud’in shi tun kan ranta ya b’aci.

Ba musu ta juya ta fita mayar mishi da kud’in shi kaman yanda Umma ta umarce ta.

Sai dai me tana fita taga wayam ba Al’ameen ba motan su,cikin sanyin jiki ta koma gida.

Tana shiga ta tarar har yanzu Umma bata daina fad’a ba.

Zama tayi kusa da Amira tace kiyi hak’uri Umma dana fita bangan su ba sun tafi.

Amira ra saci kallon Umma da ta kasa magana saboda takaici tace ” mesa kika karb’a Fateema nima ya bani kin karb’a nayi”.

Girgiza kai Umma tayi cikin takaici tace ” kinsan hankali bai ishe ta ba inba haka ba me yasa kika karb’i kud’in shi me zancewa Abban ku in ya dawo?”

“Umma ki rik’e kawai tunda ya riga ya baki kawai mu sayi abin karyawa dashi tunda tun safe bamu ci komai ba”.

Duka Umma ta kai mata a cinya tace ” taya zamu tab’a kud’in da bamu san daga ina ya fito ba,duniyan yanzu ba abin yarda bane bamu san daga ina yake ba dan haka ajiyewa zanyi mujira zuwan Abban ku ya yanke hukunci.kuma ina son ku kasance masu hak’uri a duk yanda kuka sami kanku a ciki dan ba yau kuka saba zama ba abinci ba,dafatan kun fahimce ni”.

” eh Umma ” suka ce a tare.

Al’ameen kuwa tunda yaje office ya kasa tab’uka aikin kirki gaba d’aya tunanin Amira nan ya addabe, shi wani special feelings yake ji akanta wanda bai tab’a ji a kan ko wace mace ba.ji yake kaman ya koma ya k’ara kallonta ko zaiji d’an ji relief.

A daddafe yayi sallahn la’asar yana idarwa ya fad’a mota ko ta kan musa driver bai bi ba sai tudun wada gidansu Amira.

Abba ne yayi sallama ya shigo cikin gidan shi.

Fateema ce ta tashi cikin sauri ta karb’i ‘yar ledan da ya shigo da ita ta mik’awa Umma tare da kawo mishi ruwa a randa mai sanyi a kofin silver.

Sannu da zuwa Umma ta mishi,sai da ya sha ruwan da Fateema ta kawo mishi sannan ya amsa.

“Ya kasuwan Mallam” tace tana bud”e ledan da ya shigo dashi.

” kasuwa alhmdllilah kin ganni sai yanzu ko,ina Amira take?”

“Amira ta tafi islamiya” Umma ta bashi amsa.

” haba ya zaki barta ta tafi bata ci komai ba ” Abba yace cikin damuwa.

Umma tana juye garin rogo da suger da ya kawo a k’wano tace ” toh ya zanyi?nace ta hak’ura da zuwa makarantan amma tace dole taje dan yau zasu bada hadda shiyasa na k’yaleta ta tafi”.

“Allah sarki Amira akwai kok’ari Allah ya musu albarka” Abba yace .

“Ameen ” Umma tace sannan tacigaba da cewa ” bayan ftanka Mallam wannan mutumin da ya taimaki Amira jiya ya dawo ya nemi su gaisa,bayan sun gaisa ya bata kudi da taki karb’a shine yayi wannan mai rawan kan dabara wai ta kawo min inna k’i karb’a ta mayar mishi da kayan shi.tana shigowa na hauta da fad’a nace ta mayar mishi da kud’in shi,tana fita taga sun tafi shine na ajiye nace idan ka dawo sai kasan yanda za’ayi dasu.ke tashi ki kawo yagani” tace tana hararan Fateema.

Tashi Fateema tayi jiki a sanyaye ta kawo kud’in ta mik”awa Abba.

Cike da mamaki Abba yake jujjuya kud’in a hannu,ya bud’i baki da niyan magana sallaman wani yaro ya katse shi.

” wai ana sallama da Mallam inji wani a waje” yace bayan sun amsa mishi sallaman.

Tabarma Abba yace a bawa yaron ya shimfid’a a zaure kuma yace yana zuwa saboda ya d’auka cikin irin mutanen nane masu zuwa neman sani.

” karb’i ki ajiye ina zuwa ” yace tare da fita zuwa zaure.

Had’e rai yayi sosai ganin Al’ameen zaune kan tabarman da yaron ya shimfid’a.

” d’an samari lafiya,me kake buk’ata me yasa kake bibitan gidana?”Abba ya jero mishi wa’yanan tambayoyin.

Kasa da kai Al’ameen yayi yace ” Mallam kayi hak’uri bakomai a raina sai alkhairi,ammmm dama……nace Amira nagani nake…in ba’ayi mata miji ba”ya karasa cikin ladabi.

Kallon shi Abba yayi da k’yau sannan yace ” waye kai kuma daga ina kake?”

Gyara zama Al’ameen yayi yace ” suna na Al’ameen mudassir kuma ni d’ane ga Alhaji mudassir Inuwa”.

Nan da nan fuskan Abba ya washe fara’a ya cika fuskan shi saboda ba wanda bai san shi ba a cikin garin k.d saboda halayyarsa masu k’yau ga taimakon talakawa ” Alhaji Mudassir da sani ?”

Murmushi kawai Al’ameen yayi ya sunkuyar da kai.

Abba yace ” kasan san samarin yanzu ne basu da tabbas sai ka d’auki shekaru kana bawa ‘ya’yanka tarbiya wani yazo lokaci d’aya ya rusa maka shiyasa kaga nak’i baka fuska tun farko amma yanzu tunda naji daga inda kake ba komai sai ka nemi amincewanta dan banyi mata miji ba Allah ya zab’a abinda yafi alkhairi”

Godiya Al’ameen yake ta zabgawa kaman wanda aka mishi albishir da gidan aljanna. cike da farin ciki ya tashi ya fad’a mitan shi sai gida.

Abba yana shigowa yacewa Umma ” ke mik’o min kud’in nan inje bakin kasuwa in sayo mana balangu”

Umma tace ” haba Mallam yanzu kaima cewa zakayi ma tab’a kud’in nan?bayan bamu san daga inda ya fito ba”.

“Waya fad’a miki ba’asan daga inda ya fito ba?”nan Abba ya k’washe yanda sukayi da Al’ameen ya fad’a mata.

Shiru Umma tayi dan ita maganan bai mata ba ina au ina gidan Alhaji Mudassir.

Fateema kuwa dad’i kaman ya kashe ta ‘yar uwarta ta samu mijin nunawa sa’a.

Sallama Amira tayi ta shigo tayiwa Abba da Ummanta sannu da gida ta wuce d’akinsu ran cire unifirm.

Kaman wacce aka tsikara haka fateema ta mike tabi bayanta da gulsa mata abinda ya faru

[3/24, 6:47 AM] Ummee Yusuf: . ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

  *~UKUBAR KISHIYATA~*

????????????????????????

  ( its all about love and betrayal)

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

Story by *~UMMEE YUSUF~*

   (Maman Yusuf)

✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITER’S ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍

Sis zara Allah ya raya mana baby samha Allah ya albarkace ta da sauran zuri’an mu baki daya ameen.

*~part twelve*~

“Sis ya k’ara zuwa”.Fateema tace cike da zumud’i.

Kallonta Amira tayi tace “waye yazo kuma?”

“Al’ameen “.

Zuciyarta sai da ya buga jin sunan amma ta dake tace ” waye kuma Al’meen kuma?”

Matsowa Fateema tayi kusa da ita tana washe baki tace ” wanda yazo wanki d’azu da safe”.

Dafe kirji tayi tana zaro ido tace ” Allah yasa Abba bai ganshi ba”.

” na nawa kuma Abba ya ganshi har sunyi magana”.

“Innalillahi wa inna ilahi rajiun!! Na shiga uku me Abba yace?”ta tambaya a rud’e.

Dariya Fateema tayi ganin yanda Amira ta rud’e tace ” k’wantar da hankalinki sis bcos Abba ya amince dashi 100% dan yanzu ma kud’in da ya bayar.yana hannun shi wai zaije bakin kasuwa ya sayo mana balangu”.

Dariya itama Amira tayi tace ” ke Fateema bakin nan naki akwai son cin dad’i”.

K’asan ranta kuwa fap farin ciki dan itama tun da ta had’a ido dashi ta kasa daina tunanin shi a ranta.

********************

Bayan 2 days Al’ameen ne zaune a palourn gidansu suna hira da parent d’in shi sai dai hajiya hankalinta gaba1 yana kan wani program na larabawa da take kallo.

Al’ameen ya gyra zaman shi kusan yafi a k’irga dan baisan mesa ba yake jin nauyin maganan da yazo dashi kaman wani sabon shiga.

Alhaji yana ankare dashi yace ” yaya dai kaman kana da magana ko?”

Murmushi yayi ya sunkuyar da kai yace ” eh toh kusan hakane nazo neman shawara ne akan wata yarinya da muka had’u da ita 2days ago and da ikon Allah tun daga lokacin sha’awan k’ara aure ya shiga raina”.

” masha Allah!!”Alhaji yake ta makmaitawa.

Hajiya kuma cikin farin ciki ta juyo tace ” Alhamdullilah naji dad’in maganan nan Allah ya sanya alkhairi yasa muga jikokinmu”.

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button