JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda ya fara mgnr zuciyarta ta karye hakanan taji tafiyar bata kwanta mata ba Amma jin yace gdansu saita dan samu nutsuwa ta juya ta shige bathroom din ta sakarma kanta ruwa tayi brush tayi sallah suka dauki hanyar Katsinan Dikko tunda suka taho babu me cewa wani qala kowa da abinda yake saqawa a ransa baitaba kawo cewa masomin faruwar komai zai fara ne daga zuwanta Masarautar Daura ba tunaninsa baitaba bashi zuwan nata zai zamo makullin kullewar duk wata nutsuwarsa ba.
Balle ita da batasan komai itadai kawai taji jikinta yayi sanyi ne da tafiyar ba sanin ko Ina tayi ba don haka batasan iya lkcn da suka dauka ba kafin su shiga cikin garin Daura itadai taga sun nufi wani shararren titi yanata maka gudu har suka shiga qwaryar birnin Daura ya nufi wata hanya da zata sadashi da gdan nasu babban gidane ginin sarautar zamani da aka qawatashi da fentika na daukar hankalin me kallo tun daga qofar farko ta shiga gdan taga ana zubewa ana gaishesa Yana daga mawa mutane hannu itadai bin bangarorin gidan takeyi da kallo tana mamakin girma da tsaruwar gdan har sukakai harabar asalin gdan sarautar yayi parking ya bude ya fita ta saman bene Ya’isha ta hangosu ta sauko a guje tana “ga Yaya ga Yaya” da gudu Amrah ta fito itama suka fito Yana ganinsu ya daure fuska duk sai sukaja suka tsaya daqyar Ya’isha tayi qarfin halin matsawa ta kama hannun Juhud tace.

“Masha Allah Yaya babyn kyakkyawa jiya har mafarki nayi da Mai Martaba ya kiramu ya fada Mana zamu qara yawa munyi sabuwar sister”
Sakin fuskarsa yayi da yaji kalamanta Amrah ta kama dayan hanun tace “ki saki jikinki a gdannan rayuwar yanci akeyi babu me takura miki saidai in ke kika takurawa kanki” shidai bai kulasu ba yasa aka dauki kayan suka rankaya ciki Addah Abulle ce ta miqe ta tari Juhud da fara’arta tana cewa “lale lale sannu da zuwa Aminatu barka da zuwa Sarki Waziri Fam” sunkuyar dakai tayi tare da rusunawa ta gaisheta, Dagowar da zatayi idonta ya sauka kan Mom hakanan taji wata faduwar gaba ta musamman tayi qasa da kanta murmushi Mom tayi tace “masha Allah kamar sarauniyar Aljanu wannan ya taka Rasheed dakyau take” shafa sumarsa yayi lkcn da yake zama yace “wlh Mom kinganta nan sai wahalar dani takeyi daughter ga Mom dina ki dauketa matsayin kakarki kinji?” Dariya sukayi dukkansu Mai Martaba dake saukowa daga sama yace “Iyee kai Ina jikar tawa take zo ki bani kudin goro” rufe fuskarta tayi tana dariya ta fada jikin Rasheed ya shafa kanta yace “kunga fah matsalarku zaku tsoratamin ya da maganarku”momy ce ta sakar masa ranqwashi tace “qaryan banza wai yarsa ko kunya baiji baba babu mata kekam Amina kinyi sa’ar uba aure sai inda hali yayi Kuma an shiga kwale² yo uba baiyi ba ya isa ya takurawa yarsa tayi ne” kafin wani yayi mgn Kareem da Muntaz suka shigo Muntaz yayi wani ihu yace “hyeee My Bro ashe kan…na…..han….ya…..” Mgnr a rarrabe ta qarasa fita idanunsa nakan Juhud inda Kareem yayi murmushinsa me tsada yace “ Barakallahu ahsanal Khaliqin, tabbas ubangiji ya kyautata halittarsa” Bro wannan babyn fah?” Cewar Muntaz wani mugun kallo Rasheed ya watsa masa zaiyi mgn Ya’isha ta cafe da cewa “kayy kama kanka wannan babbar kadara ce yar Big boss ce wlh kanayin wargi harsashi zaiyi nutso a kwanyarka”…………

Hmmm akwai kwantacciyar qura cikin wannan gda ga Juhud a tsakiyar zakuna uku fah kowa zuciyarsa na aika masa da saqo akanta????

 *THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300  VIP 600 VIA BANK ACCOUNT  0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER  09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*

DON ALLAH IDAN KIN/KA TURA KUDINKA BANA BUQATAR DOGUWAR GAISUWA KAWAI EVIDENCE OF PAYMENT DA SUNAN LITTAFIN DA KIKESO NAKE BUQATAR GANI KO BANA ONLINE KIBARMIN IN NA HAU ZAN GANI KUMA ZANYI ADD NAKI A GROUP DINA COURSE MUTANEN DA YAWA.

Shares Please

Oum Hairan
[7/17, 5:59 PM] Oum Hairan: JUHUD

(OUM HAIRAN)

(Pure love sex nd romantic story)

LAST FREE PAGE TEN 10

Qarshen Free page na labarin nan kenan idan baki biya ba kiyi sauri ki hanzarta biya ta wannan hanyoyin dake qasa
Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566

DON ALLAH IDAN KIN/KA TURA KUDINKA BANA BUQATAR DOGUWAR GAISUWA KAWAI EVIDENCE OF PAYMENT DA SUNAN LITTAFIN DA KIKESO NAKE BUQATAR GANI KO BANA ONLINE KIBARMIN IN NA HAU ZAN GANI KUMA ZANYI ADD NAKI A GROUP DINA COURSE MUTANEN DA YAWA.

Sorry fans dazu an samu kuskuren editing a wancan page 10 din wani bangare na labarin ya yanke ga cikakken nan

CIGABA
Zama yayi kusa da Rasheed Yana shafa kansa yace “Big Boss Ina kasamo wannan ba’indiyar yarinyar……” Mgnr ce ta maqale saboda kallon da yaga Yana watsa masa yasan tsaf zai fashe masa baki, miqewa yayi sumsum yabar gurin ya nufi dakinsa Yana saqa abubuwa a ransa, baitaba ganin kyawawar halitta irin wannan yarinya ba tabbas zaa huta da ita saidai idan mugunta tasa ta hanashi sakewa.
Addah Abulle ce ta janyeta daga jikin Rasheed ta dubi Amrah tace “ku kaita dakinku ku bata ruwa tayi wanka kuzo ku hada mata abinci idan taci ta huta don Allah kada ku dameta da surutunkun nan kubarta tayi bacci ko na awa daya ne miqewa sukayi su biyun suka riqe mata hannu sunyi nisa ta juyo da sauri idanunta akan Rasheed tace “ayyah Baffa’am Amma ba tafiya zakayi ba ko?” Dagowa yayi daga kallon wayarsa ya dubeta sosai yace “bakison na tafi ne?” Dagansa kai tayi cikin karyewar zuciya tace “idan ka tafi waye zaike bani abinci waye zaike koyamin karatu sannan waye zaike daukana Yana zagawa dani gari Kuma waye zaike rarrashina?”

Dukkansu ta Sanyaya musu jiki Kareem dake zaune yace “na dauki wannan nauyin zanke koya mata karatun qur’ani Dana bokon zanke daukarta Ina kaita tana ganin garin duk inda takeso zuwa a garin Katsina na dauki wannan alqawarin…..” Dagansa hannu yayi yace “na riga na bawa su Ya’isha wannan damar sune zasuke daukarta suna zagawa da ita kai aikinka koya mata karatun qur’ani da tajweed tunda kai balarabe ne shikuma wancan mashiriricin ka fada masa ya zama malaminta na turanci bayan wannan Kuma banson wata alaqa tsakaninsu” jinjina kai Kareem yayi yana tuntunin alaqar Muntaz da wannan baquwa gabadaya Muntaz ba mutum ne me alqibla ba Amma hakanan zai qyaleshi kowa yayi aikinsa,
Miqewa yayi ya fice ya nufi bangarensa ya bude ya shiga an gyara masa shi tsaf ya cire kayansa ya shiga wanka ya fito ya zauna yana duba wasu abubuwa a wayarsa wata baiwa ta shigo ta gaisheshi ta aje masa abinci ta fita bude abincin yayi ya lumshe idonsa Addah Abulle tanaji dashi abinda yafi qauna ne tayi masa tuwon shinkafa miyar danyan kubewa ya kuwa ci abincin sosai ya kwanta ya huta bai fito ba sai yamma da shirinsa tsaf ya fito cikin shirinsa na tafiya Illorin zuciyarsa gabadaya babu dadi sai yanzu yakejin kewar tafiya yabar yartasa.

Cikin gidan ya shiga Momy ya tarar a falo suka qara gaisawa yana rarraba ido bai hango koji motsin yammatan ba ya dubeta yace mom Ina su Ya’isha” murmushi Mom tayi tace “sun shiga gari ya qamshin bararraken daddawa” da sauri ya dago yace “harda daughter?” Yagar apple dinta tayi tace “itama ai akarada ce sunanan suna hirarsu wancan mashiriricin yace su tashi suje kallon ruwa tace itama zata carton biyu sun zama uku dama sai abinda ya qaru ai Mai Martaba da daurewa qarya gindi dubu hamsin yabasu wai ko zasuga wani abun suyi sha’awa a hanya”
Zuciyarsa ce ta karya ya taho da qwarin gwiwarsa yace “banason yawon nan Mom don Allah asa ido kanta Kinga itadin amanace riqon maraya yanada wahala abu kadan zaka karkace ka fada hallaka” tabe baki tayi tace “to Isah Wazirin Kano zaa kiyaye” yasan gatsali tayi masa ya juya idanunsa ya ciko da qwallah ya miqawa Addah Abulle dake saukowa daga sama wata takarda yace “ki bawa daughter Addah naso muyi sallama da ita hakan bata samu ba don Allah Adda ki kulamin da ita Amana nabarta gareku” dariya abin yabawa Addah Abulle tace “oh Ni Zainabu Abu Abdulrasheed abunnaka azimun ne wannan ya taka da matsayi take saboda rabuwa da ita kake kuka to kayi hqr guda ka bari guda zakazo ka tarar insha Allahu”
Murmushin jin dadi yayi ya juya ya fice driver yajashi sai Kano daga Kano jirginsa ya daga sai Illorin zuciyarsa gabadaya babu dadi ji yake kamar yaje ya dauko yarsa suci gaba da rayuwarsu tare, daqyar yake cusawa zuciyarsa dangana saboda yasan wannan matakin shine kawai gatan da zaiyima Meenah kenan yabarta a Daura a cikin ahlinsa ko ba komai zatayi karatu koda baya gari Kuma zata samu kulawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button