DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA COMPLETE HAUSA NOVEL

DANGIN SA

  By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 

Marubuciyar, tawa kaddarar da uwata ????????????

  Page :1????    


   Bismillahir rahmanir rahim, WA sallallahu ala nabiyyir Kareem 



   Saurin nake tayi in  ƙarasa wanke2n da nake yi don inje in ɗebo ruwa nasan yanzu mama ta kusan  dawowa daga yawon ta kuma duk irin hidimar nan da nayi mata a gidan ta ba lallai ne ta gani, 



 Khadija ce ƙanwata  wacce take bina suka fito daga ɗakin mu ita da maryam cikin uniform ɗin islamiyya,

“yaya haryanzu baki gama ba, zaki makara ma yau kinga jiya sai da aka miki dukan latti”
“hmmm kudai tunda kun shirya ku wuce ku tafi karku makara ni ba lallai bane inje” alamar tausayi na gani a fuskar ƙannan nawa
“me yasa” suka haɗa baki

   Tashi nayi ina goge hannu na da riga ta ina kaɗa su don in ba korar su nayi ba ba lallai ne su tafi ba sai suma su makara, wucewa sukayi dukkanin su rai a jagule ni kuma na dawo na ƙarasa aiki na 




  ko dana gama na ɗau botiki na fara ɗebo ruwa sai da cikawa mama robobin ta tas sannan na samu na huta, ba ita ta dawo gidan ba sai karfe 5:30 yadda ba yadda za ayi nace zanje mkrnt don lkcn tashi ya kusa




   tana shigowa sai ga ƴaƴanta sun biyo ta ko da yaushe suka fita oho ni dai nasan lkcn da suka dawo daga schl ita kuma ta daɗe da ficewa 

“sannu da zuwa mama” ko kallo na batayi ta hankaɗa labulen ɗakin mu tai shigewar ta

   A ƙofar ɗakin dai na cigaba da zama don banga alamar sakin fuska a tattare da ita, *zainab* naji an ƙwala min kira da manyan harufa 

“na’am”

cikin ɗakin na shiga asukwane ta cire kayan jikinta daga ita sai zani ga ƴaƴanta nan a zaune a ƙasa suna cin gyaɗa, ɗakin da na gama shan wahalar gyaransa
 "to uwar munafunci baki ga alamar na dawo bane baza kizo ki karɓi abinda zaku dafa bane don tsabar kinibibi kina zaune kina kallo na ko ni zan dafa muku" ta faɗa a hasale 




 Bance komai ba "ɗauki garin kwakin can kije ki tuƙa eba sai kije kasuwa ki siyo ewedu kiyi miya tunda muna da dage dage" too kawai nace na ɗauka na fice 




    sai da na tuƙa ebar na kwashe sannan na shiga ta bani kuɗin ewedun da daddawar, ina fitowa na ci karo da su khadija har sun taso,a tsatsatsaye nayi musu magana sannan na wuce don kasuwar ba laifi da ɗan nisa 



   kasuwar agege naje kasancewar tafi kusa da mu na siyo, inda magariba ce ta shigo dani gida ina shigowa sai da na ɗaura miyar sannan nayi alwala na shiga ɗakin mu, bayan naa idar na ƙarasa miyar ewedu ta na sauke ɗakin mu na shigar da abinci inda na tarar da mama da yaran ko shirin tashi sallah basu ba saboda suna kallo kai Allah ya kyauta baga uwar ba baga ƴaƴan ba




 ana sallar isha muka ci abinci su khadija suakyi wanke wanke mukayi shinfiɗa a nan falon mu muka kwanta  gajiyar da ke jikina baisa ma naji dawowar bbn mu.    





      ************


  sunana zainab mahaifina ɗan gezawa ne dake garin kano, mahaifiyata wadda muke ce mata iya Allah yayi mata rasuwa shekara tara kenan da suka wuce mu uku ta mutu ta bari, ni sai ƙannena biyu khadija da kuma maryam, sannan baba ya auro wata bazarawa me wacce muke ce mata mama ita kuma ta haifa masa yara huɗu maza uku sai auta mace



    a agege muke da zama a unguwar ruwa haya muke yi a gida me ɗakuna barkatai inda muke cikin ciki da falo, mama ta hana mu shiga ɗakin ta ko da wasa yasa muma iyakacin mu falo ba abu namu da ke cikin ɗakin, baban mu mutun ne mara zuciya ko kaɗan be damu da harkar mu balle ya kula da rayuwar sana'ar kayan gwari yakeyi a kasuwar gatan kowa, amma sai ya shafe sati be kawo komai gida ba don muci sai yace wai ba kasuwa, ita kuma mama a nata ɓangaren Allah yai ta masifaffiyace don in ƴen abinta suka motsa har wajen gidan mu ana iya jiyo su da baban mu barin ma in ta tashi bata da ko sisi kuma babu abinda zamu sa a bakin saƙatin ranar baba yana da bomb ɗin kamawa da hannunsa 



  ko kaɗan bana jin haushin abinɗa mama take yi mana da ƙannena don nasan cewar ko me tayi mana laifin babanmu, kuma duk jarabar mama bata taɓa barin mu da yunwa ko baba bai kawo ita sai tasan yadda ytayi muka ci muka ƙoshi wannan dalilin ne yasa nake ɗaga mata kafa




  mama Allah yayi ta me shige shige ce gidajen mutane don haka kullum sai ta fita ko babanmu ya sani ko be sani ba ita dai oho shima baya damuwa idan ya dawo be ganta be wani nuna damuwa ko kaɗan 


   ***********


     Tun kiran farko na asuba na tashi kasancewar yau mune da wankin vandakin gidan kuma ni nake wankewa in turn ɗin mu ya zagayo tun mutanen gidan suna ƙorafin mama bata wankewa saini har suka haƙura tunda mama ba mutum bace da zaka taɓa ta ta kyale, da sauri na zundimi ruwa nayi banɗaki na fara wankewa amma ikon Allah kafin in gama har a cika a ƙoafar banɗakin a a layin shiga



haka na gama na futo wasu ma har sun ƙagara sun fara mita, ni dana wanke komawa nayi gefe na zauna don banga ranar shigana ba, sai da gari yai shaaa sannan aka ragi ya rage sauran iya temitope ce kawai a layi sai ni komawa nayi ɗaki na taso kannena suka fito 




 Sai da tabbatar da sunyi wanka sannan nima na shiga nayi wankan nawa muka zo muka shirya mama haryanzu bata buɗe kƙfar cikin ɗaki ba ragowar ebar nan na dumama mana muka ci sannan na jaa kƙoar falo muka kama hanyar schl Wacce ta kasance ta gwamnati ce dake unguwar dopemu a ƙafa muke zuwa kullum sannan in an tashi ma mu dawo a ƙafar 



  k

[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

  By mmn walid nd walida(mrs aliyu)



 Page: 2????





   Shekara tana ta tafiya muna ƙara zama ƴan mata lamarin baban mu ba sauƙi don kuwa haryanzu be canza sai ma ƙara taɓarɓarewa da yayi, don yanzu sai yai wata be kawo komai gidan ba wai don muci  mama ma on d other hand lamarinta na nan, amma ita tana ƙoƙari sosai damu in dai banda zagi da gorin da muke sha a wajen ta to gaskiya bata da matsala 



 A yanzu nayi graduating daga secondary amma babu maganar ci gaba yo ina ci gaban abinda har yanzu banje na karbo result ɗin da ya dade da fitowa ba saboda tsabar babun da baban mu ya ɗorawa kansa, don haka ne ma na kama sana'ar taimakawa wata maƙociyar mu sai da abinci 



  Iyan amina muke ce mata yar ghana ce da ke zaune a lagos ita da mijinta da kuma ƴaƴanta biyu shapi'u da kuma amina, tana saida wance (abincin ƴen ghana wake da shinkafa wadda ake ci da tankwa, zaku ga wance din baƙi amma sai daɗi) 



 Da kuma dukunu shima kamar tuwo ne na ghana wanda ake yinshi da masara sannan a naɗe shi cikin ɓawon masara, kullum take biyana wannan ba ƙaramin taimaka mana yayi duk wasu ƴen ƙananan matsololin mu ni da ƙannena ina iya biya mana, mama ma wani lkcn in abin yai mata yawa takan sakar min ciyar da mu nida ƙannena, haka rayuwa take ta ci gaba sai godiya Allah 




   Kullum ni nake zuwa kasuwa inyo cefanen girkin da muke siyar wa, sannan inna dawo in haɗa girkin in ɗora, duk wannan abinda nake yi bai hanani aikin mu haka zan haɗa aiki kamar wata jaka, in su khadija suna nan sukan taya ni amma idan basa nan sai godiyar Allah



  ************


  Bayan shekara biyu

   Rayuwar dai bata canza ba ɗan cangin da aka samu shine yanzu baba yana kawo kayan abin sai dai kuɗin cefane sai ankai ruwa rana da shi, shima kayan abincin bai fara kawowa ba har sai da mama ta gaji tayi yaji da yaga abin ba daɗi sai ya dawo da ita tare da alƙawarin zai dinga kawo kayan abinci haka kuwa ake yi har yanzu 



   Su khadija a yanzu suma sunyi candy tunda dama shekara ɗaya ne tsakani na da khadijar, mun zo mun haɗu mu ukun muna zaman gida su suna yin aikin gidan ni kuma ina sana'ar sai da abinci, wanda yanzu ba laifi nima ina samu sosai 




 Baban mu ya tara mu yace dukkan mu mu fito d miji aure zai mana, abinda nake gudu kenan don ni tunda nake zan iya cewa ban taɓa yin saurayi ba, gwanda ma khadija akwai wani hadi shine yake son ta amma yana da mata don dai matar tasa bata taɓa haihuwa ba ne 




   Bayan mun keɓe ne nake cewa khadija "kiyi wa hadi magana ya fito mana tunda naga da gaske yake" ta kalle ni ido rau rau kamar zatayi kuka

” yaya ke fa” murmushi nayi na dafa ta nace “khadija kowa lkcn sa na aure idan yayi zai yi, kinga ke yanzu Alƙah ya haɗa ki da wanda yake sonki ki yi auren ki kawai kin huta da wannan rayuwar da muke ciki mara tabbas”

 ba irin lallami da ban bakin da banyiwa khadija ba amma ƙiri2 tace fafur bata yadda ba ita dai in ban riga ta ba to sai dai muyi tare ba yadda na iya da ita don na san inna na matsa mata sai ta sa min kuka 




   sai da bari dare yayi hadi ya zo zance sun daddage suka zuba soyayya na je nayi musu sallama suka amsa khadija tana ganina ta sha jinin jikinta sai naga ta haɗe rai, ban kula ta ba na koma wajen hadi nai mai bayanin komai da ake ciki, ya nuna jin daɗinsa sosai sannan ya ce in shaa Allah yana komawa zai yiwa magabatansa magana akawo kuɗi ina ganin khadija sai zumɓurar baki take tayi ni dai na bar su na koma gida abina su ƙarata 




       hadi kuwa kamar yadda yai alƙawari haka kuwa ya aiko da magabatansa suka kawo kuɗi inda aka sa ranar wata biyar, kuɗin hannuna da nake tarawa wanda nake samu a wajen siyar da abinci shi na ba khadija muka je tare ta siyo  ƴen kayan kitchen wanda muka ɓoye a ɗakin iyan amina don in mama ta gani ba lallai bane ta bari baba yayi mata wasu ba




  Bikin khadija yana gabatowa inda ni kuma a ɗayan ɓangaren nake shan habaici a wajen mama wai nayi kwantai na rasa mijin aure, shima a ɓangaren baban mu ba sauƙi sai kace nice zan bawa kaina miji, wannan hali da na shiga yakan ɗaga wa khadija hankali don wani lkcn har kuka zaka tsince ta tana yi, na kan ɗige da bata haƙuri, ince mata kowace mace da irin yadda rayuwar auren ta yake farawa






    ************
 Da bikin khadija ya zo Allah ya taimake mu baba yai mata gado dama auren lagos mace gado kawai zata tare da shi sai kayan kitchen duk ragowar hidimar gida su gyaran falo da komai duk na miji ne, munyi shagalin biki lfy mun gama ƙalau sai dai fatan Allah ya basu zaman lfy, flat aka kai khadija duk da dai ba ita kaɗai bace akwai kishiyar ta kowacce ta ɗauki ɗaya shima mijin ya ɗau ɗaya,



   Da bikin khadija Allah ya haɗa jinin maryam ɗin mu da wani cousin ɗin hadi mai suna sadiq, shima kamar yawancin matasan agege ɗan chanji ne, haka shima mijin khadija chanji yake yi 



    Soyayya suka dinga zubawa sun so ma suyi aure kasancewar maryam akwai rawar kai amma baba yace har yanzu be huta daga auren khadija ba gani ni ma har yanzu ba wani motsi, 




    haka ta haƙura, suka zubawa sarautar Allah ido nidai in don ta nine ban ƙi a aurar da maryam ɗin ba amma baba ya ƙi, khadija bata daɗe ba ta fara laulayi, kafin kace me sai haihuwa, ta haifi ɗan ta namiji kyakkyawa kamar ubansa, 



  Ansha shagalin suna inda hadi ya ɗauko ƙanwar mmnsa daga kwatano tana kula da mai jego, hadi ya kashe kuɗi sosai a wajen sunan khadija inda ɗanta yaci sunan baba sa ibrahim ana ce masa khalil, haihuwar khadija ce ta taso da zancen auren maryam, inda iyayen sadiq suka samu baba da zancen har da kuɗin zancen su da na sa rana baba baiyi wata wata ba ya karɓa aka sa musu rana 




   kawo kuɗin maryam ya sa na kuma takura a gidan ba wanda yake tausaya min sai ma wulaƙanci da musgunawa danake fuskanta daga kowane ɓangare na naƙi kawo miji nayi kwantai,



ni dai ba abinda nakeyi sai miƙawa Allah kuka na akan ya zaɓa min na gari, sallah dare nake tashi nayi amma randa mama ta ganni inayi har safiya tana mitar wai ina tashi ina son in asirce mijin wata da daddare, haka ina ji ina gani na daina ko kuma inyi a ɓoye,



  da bikin maryam ya gabato sai aka haɗa da na ƴaƴan mama wanɗanda ta haifa a gidan ta na fari su uku duka mata dama ƴaƴa huɗu ta haifa acan ta aurar da ta farin ta, kuma duk kayan ɗakin da aka kai su da shi babanmu ne yayi musu gaba ɗaya da maryam ɗin 





         na so harga Allah in samu miji ko da bikin maryam ne amma hakan be yuba haka na dawo na cigaba da ruwata ina ta miƙa roƙona ga Allah ubangiji (swt) akan ya dubeni da lamarina 


  Mijin maryam sadiq irin mutanen ne masu sakin hannu, don kullum in dai yaga ƴen gidan mu a gidan sa to da saƙo na musamman da zai ba akawo mana, don haka mama take kiran shi da ɗan albarka, bata sati cikakke sai ta je gidan shi kuwa baya gajiya da hidima saɓanin miji khadija, itama maryam ɗin in ta tashi zuwa haka zata zo da kaya ciye ciye lodi lodi, baba kuwa yai ta sa mata albarka hmmm iyayen zamani




 ko da lkcn da maryam ta haihu mama ce da kanta take zuwa har gidan maryan ɗin don kula da jariri da kuma mai jego, nidai tunda naje barka sau ɗaya ban koma ba, sai ƴar autar mu amina da aka kaima ta wai ta taya ta aiki don anga mijinta da ɗan maiƙo 



    ana gobe suna mama ta koma gidan wai saboda aikin miya, ban yi niyyar zuwa sai da khadija ta biyo min sannan ta sani a gaba muka je, wai don kar ace inayi wa maryam ɗin baƙin ciki 




a gida aikin miyar maryam na sha habaice habaice kusan agege da sa ido tun ina danne wa ina nuna ban san dani ake har abin ya dame ni na koma uwar ɗakin ta nai ta kuka na khadija ce kawai ta san halin da na shiga har ta iya lallashina ita kuwa me jego ba abinda ya dame ta hidimar ta kawai take yi

[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

     By mmn walid nd walida (mrs aliyu)




  Page :3????




   Ranar suna ƴa taci sunan kakarta mmn sadiq hafsat wdda za a dina ce mata farhana, sa da rago sadiq ya yanka  banda iyayen kuɗin da ya kashe na hidimar suna, ban so na tsoma kaina a harkar sunan maryam ba don yadda naga mama komai idon ta na kai amma da khadija ta ja ni gefe ta min magana sai na zage na fara rabon abinci nima 



   An sha hidima sosai da sunan mama bata koma gida ba ranar ma ni kaɗai na koma da kayan suna wanda na kaiwa bbn mu saƙon mama,


 Kashegarin suna ina kwance har goma kasnacewar gajiyar da yi a gidan suna yasa nace yau ba inda zani wajen ƙarfe sha ɗaya na safe ina ta juyi ina shirin tashi in san abinyi sa ga khadija 

“kai yaya kar kice baki shirya ba” gira na ɗaga mata alamar ban gane me take nufi ba,

" yanzu yaya si yaushe zamuje gidan suyan naman"  ohhhh yooo ni ba na manta da wani suyan nama ba,

azalzala ta khadija tayi muka shirya muka fita gidan suyan nama amma ga mamakin mu kafin mu je gida ya cika danƙam kamar yau ne sunan mama ta gayyoto mutane bila adadin wai a taya ta suyan sa da rago sai kace shanaye ya yanka, ba wacce kalle mu itama knta me jegon si wani shash shan ƙamshi take yi wai bamu zo da wuri ba, a zuciyata na ce maryam ni ban ma yi niyyar zuwa ba da badan khadija ba ma da bazaki ganni ba

    Mu dai ni da khadija ba wani abin arziƙi muka yi a gidan suyan nan ba don mutanen mama sun yi kane kane da naman sai muka zama kawai ƴen kallo kar dai ace bamu zo ba 




  ranar suyar ma  mama bata koma gida sai kashe garin suyar nama da daddare sai gata da kayan nama, nidai aka bani nawa a farar leda na karɓa nace Allah ya raya na cinye a take, 




    na mama nama ne botiki guda har wani cewa take yi ƴata ce tace in ajiye in taci a hankali, mama ta ci gaba da zuwa gidan maryam tana yi mata wanka ita da jaririyar ta,




   randa maryam ta cika kwana 30 cif da haihuwa su mama an shirya kenan za a tafi gidan ƴar albarka sai ga ƙanwar mijin ƴarta nan ta zo 



  Bayan sun gaisa take cewa mama ai iyami ta haihu, toooo inji mama yaushe 

“yau da asuba”
“a gida ko asibiti”
“a gida nurse aka ɗauko mata”
“ai kinji irinta nan ba za akai yaeinya asibiti ba likita ya duba ta sosai sai ace wata nurse tooo Allah ya raya, nidai yanzu da kike ganinan na shirya ne zan tafi gidan maryam in mata wanka ita iyamin sai kije gidan bbn ta ki faɗa sai a samu me yi mata hidima daga can” mama ta ƙare zancen ta tana gyara mayafin ta

  "ai naje shine suka ce inzo in faɗa miki ba me zama a wajenta" juyiwa tayi "ban gane ba ni ba ƴar mijina bace nake mata hidima don kara amma ni a rasa me karanta min akan tawa ƴar" 



  Ita dai ƴar aike tai tsuru tsuru, "to ku a dingin naku shi ɗan uwan nakin ba zai nemo me zama masa da matar sa ba har sai ni uwar ƴa naje" nan ma shiru tayi ba amsa 

Tausayi mama ta bani yasani tsoma musu baki “mama ki barshi da zuwa gidan maryam ɗin kaeai ni naje ke kije ki ga iyamin”
” a a ke kije gidan iyamin ni na tafi gidan maryam” tana faɗin haka ta juyawarta tayi tafiyar ta

     mamakine ya kama ni, wai mama wace irin macece ne, barin tunanin nayi na jawo ƙofar ɗakin mu na kama hanyar gidan iyamin don inga abinda zan iyayi 





    ko da naje na tarar me jego batayi wanka ba haka zalika itama ƴar ba wanka na rasa abinda zan musu dole na fito daga gidan na kama hanyar gidan maryam don inje on tattago mama don bansan abinda zan musu ba 




    a zaune na tadda ta ta harɗe ƙafa tana kwasar farfesun kayan ciki da bread da shayin ta me kaurin gaske, ko da ta ganni sai ta haɗe ranta "lafiya" ta tambaye ni 




   bayani nayi mata sosai halin da me jego take ciki nayi amma ga mamakina sai ta ja wani dogon tsaki 

“ƴar iskar yarinyar sai da nace mata kar ta auri yaron nana amma gashina nan abinda nake gude mata, yaro da shegiyar tsiyar kamar ɓeran masallaci ace matar ka ma ta haihu amma an rasa me kula da ita don kowa yasan cewar sai dai shi ya saka nasa aljihun a harkar gidan ka ba kai a more ka ba, tunda ta auri yaron nan ƙwandaƙar ta ban taɓa gani sai dai ma intazo wajena in bata kullum shi cikin babu, kamar shi ya yankewa tsiya cibiya, Allah dai ya kyauta bari in gama sai muje tare”

      to kawai na bita da shi maryam tai mun tayin abinci amma sai nace na ƙoshi ko da mama ta gama da muka tashi tafiya sai da ta cewa maryam wai tayi abincin rana da ita don zata dawo 

ita kima maryam ɗin sai tace ai mama ba sai kin dawo ba yunda yanzu na iya wankan kuma na iya yiwa farhana gashi iyami ya haihu hidimar ai sai tayi miki yawa ƙiri ƙiri mama tace bata yadda ai tayi wa bbnmu alƙawarin sai maryam tayi arba’in sannan zata daina zuwa

  daga ganin fuskar maryam ba haka ta so ba amma sai tayi shiru, tun a gidan maryam mama take zagin mijin iyami tana mitar auren nasu har muka je gidan, inda cikin ikon Allah muka tarar da yayar mijin na tan ta zo tayi komai ko da mama ta ga haka ko zama batayi ta koma wai ta baro maryam ita kaɗai, ido kawai muka bita nida iyami ko yaushe mama ta zama haka ohooo





Ni na dinga jigiƙar zuwa gidan iyami taya ta aiki sai yar mijin ta da take zuwa safe da dare tana yi mata wanka da ɗan babyn ta, gaskiyar mama ne lamarin mijin iyami sai a hankali sam bai damu da ita ba balle abinda aka haifa wataran haka zai fita bai bata komai ba sai dai in naje da kuɗin da yake hannuna da shi zamuyi abinda zamu ci 




    nima yanzun samun nawa sai ahankali don iyan amina tana masu taimaka sosai ƙannanta ne suka zo daga ghana don haka yanzu gaskiya ina shiga cikin matsalar kuɗi sosai khadija kawai tasan halin da nake ciki kuma itace kawai take taimaka min da ɗan abin da zan kashe, kuma itama ba kasaifai ta fiya aikomin da shi ba, wataran kuma idan ta aiko min sai ince ɗan aiken ya maida mata da abinrmta don itama nasan halin da take ciki hadi ba wani basu kuɗi yake ba, shi komai na fnfanin gidan sa yake siya ya ajiye don hka ɗan kuɗin da yake basi ba wani abin ya taka kara ya karya bane

[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

  By Mmn Walida nd Walid(mrs aliyu) 



  Page:4????




     Mun shiga sunan iyami lfy lau inda ko  ƙeyar mama bamu gani tun randa ta zo, na ci gaba da zuwa taya iyami aiki har sai da ta yi sati uku sannan na daina, 


Rayuwa taci gaba da tfy muna ƙara girma yanzu ina da saurayi me suna salisu irin ƴen ci ranin nan ne ɗan sokoto, yan zuwa zance duk da dai ba wani son shi nake yi ba amma kuma yafi ka zauna ba aure, baba ya tare shi akan ya turo magabatansa, ba ƙaramin daɗi yaji ba 





 Tun ina lissafin dawowa salisu daga sokoto don zuwa ya sanar da magabatansa har na hakƙura don yanzu kusan watan shi ba lbrnsa, kamar an aiki bawa garinsu




    Ko da ya dawo yazo gidan mu diraect yace wa bbn mu wai shi bbn shi yace wai ba zai auri ƴar bariki ba wayyo Allah na ranar na sha zagi wurin bbn mu kamar me harda kwaɗeni wai dama iskanci muke yi da salisun shiyasa bbn sa yace bazai aure ni ba, shi kuma salisu a nasa ɓangaren yana nufin lagos ai kamar bariki ce shiyasa ban wani ƙullace shi ba 




     Yau da sassafe khadija ta aiko wai don Allah inje, ban san ko menene ba amma ban fita ba sai da naga komai sannan na kama hanyar gidan ta, ko da naje akwance na same ta ba lfy, "ohhhh khadija jikin ne" ya mutse fuskar ta tayi ta kasa magana kasancewar miyan da ya cika mata bakinta, wan ya tabbatar min ciki ne da ita




 Ohhh Allah ƙanwata zata yi na biyu ni ban ma yi auren ba Allah ka dubi lamarina, khalil yana ta rigima ɗaukar shi nayi nai masa wanka na shirya shi na goya sannan na dawo ɗakin nata bacci takeyi don haka sai ban tashe ta sai na hau gyara mata ɗakin nata 




   sharar da nakeyi ce ta tada ta, "sannu yaya"  mmm kawai nace na ƙarasa, tashi tayi zaune 

“yaya dama yaye shi zanyi shine nace bari inkira ki ki tafi da shi idan yaso bayan kwana biyu kya dawo shi”
“kin gayawa bbn sa”
“shi ma yace in kira ki in ce ki ɗauke shi na kwana biyu, amma ni so nake ya kwana uku kinga kafin nan na huta”

  "to shike nan bari in tafi da shi ɗin bana son ina daɗewa a gidan ki kinsan halin mama" to shike nan dubu biyar ta bani wai inyi masa siyayya ƙin karɓa nayi sai da ta rantse min da Allah cewar hadi ne ya bayar a bani sannan na karɓa, na haɗa masa kayan sa na fito kenan muka ci karo da maryam ko daga ina take ohooo





    " a a a awata sabon gani yaya dama ba a ganin ki a ko ina sai gidan khadija, ni kun ware ni kamar ba ƴar uwar ku komai sai dai kuyi tare ba ni" 

“haba dasooo” na bata ansa dayake haka nake ce mata idan ina cikin nishaɗi

"wallahi khadija ce ba lfy tace min inzo in ɗauki khalil in yaye shi, shine fa kika ganni yanzu ma na zo kuma kin ganshi nan a baya na zan juya don bana son ƙananan maganganun mama" 

"yaya khadija" ta faɗa ta karfi tana dafe kirjin ta "ciki na biyu, bari inje inyi mata tsiya ita me cewar sai nan da shekara uku" ta faɗa tana shigewa tare da jan hannu na zuwa cikin gidan "yaya yaushe rabon da mu haɗu tare har muyi hira yaudai Allah ya bamu dama baki isa ki koma gida da wuri ba sai munyi hirar zumunci"    ba yadda na iya haka na bita zungwi zungwi




mun sha hira sosai da ƴen ƙannena sai yau nasan cewar nayi kewar su sosai har sai bayan la'asr sannan mu tashi muna shirin tafiya ne maryam tace 




  "yauwa dama sunday me zuwa ne bikin cika shekara 10 da auren uban gidan bbn farhana don haka za ai celebrating a beach shine nace bari in gaya muku ko za ku mara min baya don kune kaɗai ƴen uwana"  kallon kallo muka tsaya yi ni da khadija, har maryam ɗin ta tsargu bama son zuwa 






    "gaskiya maryam nidan ina fama da kaina bana tuanin zan iya zuwa wani hayaniyar party" inji khadija 

“ni ma gaskiya baba bazai barni zuwa beach ba, yanzu ma ya aka cika yana cewa na zama ƴar iska balle yaji naje beach” rau rau maryam tayi da idon ta

 "yanzu ace ni bani da wanda zai karanta min ku da nake ganinku a matsayin ƴen uwana amma bazaku rufa min asiri ba shike nan Allah ya bamu alkhairi" tana faɗin haka ta sunkuci jakar ta azuciye



"a haba abar sooo   me yayi zafi da zaki tafi" na kamota ina faɗin haka

“to me kuke so in muku tunda yanzu kun tsane niiiiii” ta karashe zancen nata da kuka

"to yanzu ya kiko so muyi abar soo" na faɗa da sigar lallashi 

“ba komai daga ke har khadijar baku da lkcn da zaku rufa min baya alkcn da na gama yiwa mijina kurin zan gayyato ƴen uwana su taya ni aiki kuma muje gurin partyn tare”

“to shike nan karki damu zamu zo mu taya ki, ita khadija sai ta gayawa hadi sai su tafi guri partyn tare ni kin ganni nan idan kika gayyace ni wurin party yanzu kunya zaki ji don ko kayan da zan sa inje banni da shi”

Sai alkcn khadija tai magana “indai kayana ne zan baki, dama akwai wata, doguwar rigata ƴar dubai da na siya tai min tsayi sosai sai ki sako” harara na banka mata wacce ita maryan ɗin bata lura ba

“to kinji yaya don Allah ku zo muje,ƙila acan ma Allah ya haɗa ki da nagari” ta faɗa a zolaye amin thumma amin inji khadija, muka gama tsara yadda tafiyar tamu zuwa partyn zai kasan ce amma maryam ta roke ni da kar in gayawa mama don ta san halin ta sai tace zata je

dariya miua dinga yi mata nida khadija don soyayyar nan da ta ƙullu tsakanin mama da maryam sai Allah, bamu muka bar gidan khadija ba sai da mukayi magariba bayan mun gama tsara komai 



ko dana je gida haka natarar da mama ta cika tayi fam wi naje na zauna a gidan khadija banzo na ɗaura abinci ganin khalil a bayana yasa ta tambayin daliln zuwana da yaron, na faɗa mata maryam ce ba lfy shiyasa tace mi in yaye shi

“haka dai za a kare sai dai aita ganin ƙannen suna haihuwa ke kuwa kin zama uwar mata sai in sun kuma samin ciki a kira ki abaki yaye ke kin fasa auren ke nan si dai ki ta rainon ƴaƴa to Allah ya bada sa a” tai ta mita nida ɗakin mu kawai na shige na ɗauko kayan girki na zo na ɗaura na dare ina mamakin abinda nayiwa mama haka da yawa da yasa ta tsaneni

    ko dana gama da wuri muka kwanta nida ɗan yaye na amma abin baƙin ciki, cikin dare yari ya tashi yai ta tsala kuka kamar me na rasa abinda zan masa baba ne ya fito yai ta min bala'i a kaina ga kukan yarioga bala'in bbn mu har gorin nayi kwantai sai da yai min wai nima kaina na zame masa jaraba gashi na je na ɗauko yaro ya zo ya ishe su da shegen kuka sai kace ba jikan sa ba

ya ƙaraci bala’in sa ya koma cikin ɗaki mama dai bata ce komai ba sai dai uban tsaki da take ta ja kamar tsaka ahaka muka kwana da sassafe baba ya tashe ni alkcn na ɗfaa gyangyaɗi ya nan ya tasa min kwandon bala’il ba irin zagin da bansha wai na hana shi bacci,in fito da miji inyi aure naƙi sai yawon gidan ƙanne ko kunya bana ji ranar nayi wan iabu wai shi kuka har na gode wa mai duka
[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

By mmn walid nd walida (mrs aliyu) 


???? *Nasibi writers association*????   

In dedication to all nasibi writers ????

    Page:5????


  Da ƙyar baba ya yadda khalil yai kwana biyu sannan ya jaaa min kunne akan kar ya dawo ya same shi, sai da na gama duk wani abinda nake yi da la'asar sannan na mayar da shi, 


Mun ƙara tsara yadda zamu haɗu a gidan maryam ran lahadin don taya ta aikin da kuma partyn sai magariba sannan na fito na koma gida, munyi da khadija akan zata zo ranar sunday da niyyar zan raka ta asibiti daga nan zamu kasuwa, indan kuma na fice sai baba ta gani yo wayasan lkcn tashi daga wurin partyn 



  Ban gaya wa mama akan partyn ba don nasan halinta sai tace zata, ranar sunday ƙarfe bakwai sai ga khadija a ƙofar ɗakin mu tana mana knocking, 



  ni na buɗe mata sai ga baba ya fito daga ɗakin "waye wannan da safen nan" ganin khadija ya sa shi wangale bakinsa 

khadija lfy kika zo mana da sassafen nan” ya faɗa yana zare ido, jin sunan khadija ya sa mama fitowa daga ɗakin ta da zanin a hannun ta ytana ƙoƙarin ɗaurawa “lfy” itama ta tambaye ta, nima tashi nayi ina zare idin ƙarya kamar bansan komai ba

 "ba fa komai baba dama bani da lfy ne, shine hadi yace min inje general hospital na cikin lagos in ga likita sosai shine na biyo yaya ta rakani ko ta riƙe min khalil inna ta tashi shiga" ta faɗa kamar gaske




 Tsaki mama taja tayi wucewarta ɗaki shi kuma baba sai ya hau mita "da ba sai ki kirata taje can ta same ki ku tafi ba,amma kin tashi kin doko mana sammako sai kace wani abinne ya faru" 


 Kallon inda nake yayi "sai ki tashi tunda kin zama sai in ƙannen ki ba su da lfy su dinga futowa daga gidan mazajensu kina raka asibiti, Allah ya bada lfy" ya faɗa wa khadija 



 Tashi nayi jiki ba ƙwari banji daɗin abinda baba ya faɗa min amma ya zanyi, "bari inyi wanka"

” a a yaya ba sai kinyi wanka ba wanke fuskar ki kawai, ai daga asibitin kasuwar ikko zaki rakani” ta faɗa da ƙarfi don baba yaji ilai kuwa
“kuce yau kawai yawo zakuyi,to ki tabbatar na dawo na same ki a gida” ya faɗa yana shigewa ɗakin

 fuskata kawai na ɗauraye na saka hijabi na ja musu ƙofar falon muka kama hanna, ni na karɓi khalil na goya don naga khadija ƙarfin hali kawai take yi 




 Gidan maryam a A p yake don haka sai muka hau keke napep don da yar tafiya, bakwai da kwata muka isa inda muka tarar madam ɗin an tashi ana ta hidima, mmmmm wayaga su maryam 




   "sai yanzu kuka zo" ta faɗa tana zunɓurar baki 

“au sai yanzu nema, da asuba kike son mu zo ko me”
“ni dai ku zo mu fara don tun bakwai na aiki bbn farhana kasuwa yayo mana siyayyan abinda zamuyi amfani da su” binta mukayi inda ta lissafa mana abinda da zamuyi, springrolls, meat pie, doughnut, sai cup cakes kowanne 300 pieces ,

 Zaro ido nayi "maryam jakai ne mu"

“akwai masu taya mu ai” ohhho
“yauwa sai kuma kunun gyaɗar nan da kike yi me farar shinkafa, kinga har na jiƙa gƴadar da shinkafar, ya siyo robobi na yoghurt in mun gama sai mu ɗura a ciki ko ya kikace”
” eeeeeeh hakan ma ya bada ma’ana, muga gyaɗar” nuna min gyaɗar tayi dayawan ta, sannan muka je ta nuna min farar shinkafar da ta jiƙa wuuuuuuu nace ina zare

 "maryam me za ai da dawannan uban shinkafar ke da ake sa ƴar kaɗan don ta ɗaure kunun, amma ba komai ayi waina da ragowar" 

” waina kuma yaya partyn ƴen gayu kin taɓa ganin waina”
“ko ma partyn uban waye bazan bari ai asarar uban shinkafar nan, ina masu taimaka nan su zo suje suyo mana cefanan waina”

  Maryam bata soo yin waknar nan ba amma ba yadda ta iya ni kuma gani nake yi in aka bar shinkafar lalace wa zatai don cikin botikin penti ne ta cika shi dam da jiƙaƙƙiyar shinkafa, masu taya mu aikin suka zo muka basu sautjn sannan muka fara hidimar aikin 




   ƙarfe 2:00 dai dai mun gama komai hatta da wanka jira kawai muke yi sadiq yazo mu tafi, shima ko da yazo yaga wainar nan sai da yayi ta mitar abin ƴen gayu me ya kai waina, sai da nace musu in ba za aje da waina ba ni ma bazan je ba sannan ya Haƙura aka zuba kaya a boot ɗin mita muka shiga  



sabuwar doguwar rigar da khadija ta bani ita na saka ajikina, irin rigunan ƴen india ne me buɗewa sosai daga ƙasan, rigar tai kyau sosai samanta a tsuke yake inda ƙasan ya buɗe sosai don sai inayi ina tattaro ta indai zan hauwuri me tudu ko zan sauka, sai yaba min kwalƙiyar suke yi ni ko kunya ce ma ta kama ni don duk kyan nan nawa na rasa me taya ni ohhhh ni abu 





   lekki beach muka wuce direct tunda anan ake partyn ko da muka je ƙin ɗauko min waina ta suka yi sai ni na koma da kaina na ɗauko abata da miyar ta da ta sha bogo (ƙashi me taunuwa ????????) da kuma pkomo sai nama, na je inada ake jere abincin na ajiye, har anfara shagali kowa yana ta son ya nuna bajintarsa awajen celebrants ɗin ta fannin ko abinda aka kawo na ci ko na sha kona kyauta wato gift, sun yi kyau suma celebrants ɗin  wato alh musa sosai inda suka ci kayan su iri ɗaya su da ƴaƴnsu guda huɗu




    ganin lkcn sallah yayi yasa na ɗan yi nisa daga wurin partyn don in samu in gabatar da farilla, na ɗau lkc me tsawo ina addua sannan na naɗe sallayata na koma gurin partyn tun daga nesa nake jiyo hayaniyar ƴen partyn, nace lallai duniyar tayi wasu daɗi

Y
ƙaraswa nayi don inga menene yake sa mutane wannan hayaniyar ashe akan waina ta da maryam da mijinta suka ce kauyancine ake ta wannan wasoson, ana so can na hangon babba abokin alh musan da kuƙar wainae a hannun sa ya ɗora ta a sama nkansa mutane suna ta binshi ta basu, dariya nm abin ya bani sosai

 sai ga kuma sadiq shima yana ta wani washe baki suna magana shi da alh musan daga gani zuba santi yake yi, matar aƙh musan ce ta matso kusa da mijin nata ta masa magana, sai naga ya juyar da plate ɗin da wainar take ciki a lkcn da ita ta kai hannun ta, ban san lkcn da tintsire da dariya wato yau wainar ta ma tasa masoya faɗa 

bayan an gama wasoson wainar sai kuma aka ci gaba da hidimar partyn, abin nasu ya ƙawatar sosai da sosai, sai da la’asar tayi sannan na kuma fita na gabatar da tawa ni ko me akeyi bana barin sallah ta wuce ni haka nake, bayan na dawo naga salon partyn ya canza wai couples dance toooo

couples za a zaɓa su zo su danceee a filin wurin bayan sun gama sai su ma su zaɓo wasu an ɗan jima ana haka sai kuma akea ce ance dance dance dance, sai naga kowane ɗan miji yana jan matar sa suyi rawa saurayi yaja budurwar sa ƴar iska khadija itace har da kawo min khalilkarɓar shi kawai nayi na bar wurin don inna tsaya sai zuciyata ta buga

[7:42PM, 12/7/2017] ‪+234 806 803 7117‬: ????????????????????????????????????
DANGIN SA
????????????????????
????????

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Leave a Reply

Back to top button