JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki

Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566
Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde

Oum Hairan
[8/1, 11:13 AM] Oum Hairan: JH0024 Tabe baki suka rinqayi suna miqewa suna sulalewa da daidai ya rage saura iyakar yan dakinsu Rasheed Aunty Hamida Ya’isha Muntaz da Mom iyakar shaqiyancin Muntaz wannan cin mutumcin da akayiwa matar yayansa Saida yasashi hawaye shima. A wahalce ya miqe ya iso garesu sunata aikin rarrashinta kamar suna qara mata qaimin kuka yace “ni dama Mom saboda tsoron irin wannan abubuwan da ka iya tasowa naso kibarma Big Cele matarsa a inda ya barta Amma kika dage Saida kika dawo da ita yanzun ga irinta nan.
Hamida ce ta quta tace “wlh nima Raina baiso dawowar Aminah cikin gdannan ba so abune dai da bakada yanda zakayi dashi Mom gsky a dauki mataki akan lamarin nan wlh idan aka barsu a gdannan zasu dorawa baiwar Allah hawan jini a banza ita gata mijinta ba mazauni ba balle yake rarrashinta” miqar da ita Mom tayi ta kama hannunta suka fito wani abun mamaki duk inda sukabi sai suga bayin gidanma suna darewa suna barmusu gurin lamarin daya qara tashin hankalin su.

Zama tayi a parlour tanaci gaba da kukanta da iyakar rarrrashin mutum bataji a ranta zai iya fada mata kalmar da zata iya kwantar mata da hankali ba, sai yanzu mom ta magantu da cewa “duk wani abu da zai faru ko Kuma yake faruwa Aminatuh kiyi watsi dashi ki durfafi rayuwarki ta gaba kisa mijinki da yayan da zaki Haifa masa a gaba shine komai zaizamo miki me sauqi Amma indai kika sake mutane suka jefa miki qulli a ranki to zaki samu matsala kinsani babu wani abu daya gagari Allah wlh Meenah banida ikon hana wannan mgnr fita da tun farko ban Bari ta fita ba balle tazo ta damemu hqrn dai shine zakici gaba dayi domin shine ya kamaki tsarin gdannan mijinki ya taka shiyasa komai ya dada lalacewa Kuma nasan komai akanki zai kware”
Har Mom ta gama mgnrta Meenah kallonta kawai takeyi daidai lkcn wayar Mom din ta dauki ruri ta duba taga number Rasheed ce gabanta ya fadi tayi kamar bazata dagaba ya sake Kira tadai sanyawa kanta nutsuwa ta daga suka gaisa yace “meye yake faruwa da Meenah ne na Kira wayarta yakai sau goma bata dagaba” cikin daburcewa tace “eh wlh batajin dadine tunda muka iso kasan yanayi na me qaramin ciki dan gwajab² din hanyar nan yasa mata zazzabi Amma dai Alhmdllh yanzu ta samu bacci, ya aikin?”

Aje numfashi yayi yace “alhmdllh hankalina yaqi kwanciya ne da zaman Meenah a gidannan Mom inajin tsoron kada a Dora mata damuwa ba iya ramawa zatayi ba sanyinta yayi yawa ni kadai ne Meenah bata bari Amma Urwat ma idan yayi mata qyaleshi zatayi” “nasan da hakan Rasheed babu abinda zai faru insha Allahu ka kwantar da hankalinka ai bama dadewa zakayi ba ko?” Gyara kwanciyarsa yayi yace “wata uku zanyi saidai fah banjin zan iyashi ni kadai tun jiya nasa a gyaramin gda a barreck idan naga yanayin garin Daltan Babu matsala zanzo ko na turo a tafi da ita”
Fatan Alkhairi Mom tayi masa sukayi sallama ta dubi Meenah tace “ko ya Kira kada ki daga kinsan halinsa idan yasan abinda ya faru bazatai kyau ba ki taimaka wajen boye koma mene daqyar nasamu na dsidaitashi da Mai Martaba mijinki akwai kafiya kamar kafirin farko don Allah Meenah kiyi hqr ga yar’uwarki nan ko kowa yaqiki naji a jikina jinina bazasu gujeki ba su kansu yayyenku sun gamu da kaidin matane musamman Arman saidai addu’a”
Juyawa Mom tayi ta fice Ya’isha ta zauna tana qara bata baki harsaida ta Dan saki jikinta suka qara gyara abinda baiyi musu ba tayi hamma Ya’isha tace “yadai da miqa ko a Kira Big Cele ne?” Murmushi tayi tana shafa cikinta tace “nazama jaka wlh bana jure yunwa Kuma da naci zanji an yasheni kamar wacce mukeci da wani kiga fah jikina har rawa yakeyi” dariya Ya’isha tayi tace “tab kice Big Cele ya qara daure dammara da saqale bindiga” duka takai mata sukayi dariya tace “hankali ne baa kwance ba bari na Kira Mom ta turo a kawo Mana abinci” sallama tayi tace “unborn din danki ne yakejin yunwa Yana neman wahalarmin da yar’uwa” dadi sosai Mom taji dajin ta saki jikinta tace “ok Bari na turo kausar ta kawo muku abinci tun dazu na hada wani abune ya daukemin hankali”

Suna nan sunata hirarsu gabadaya hirar akan bikinsu Ya’isha ne Kausar ta shigo ta aje musu abincin ta fice Ya’isha ta dauko abincin ta zubansu abincin sunaci suna hirarsu ya sake Kiran wayarta ta dauka ta manna a kunnenta tace “girman kujerarka duniyata” ajiyar zuciya yayi yace “har naji dadi nakasa aikata komai banji lfyr rayuwata da babyna ba hope dai qalau kuke?”
Murmushi tayi tace “ni qalau nake saidai ko kai naji yanayinka a kasalce” qasa yayi da murya yace “meye yake faruwa a gdannan ne jikina na bani ba lfy ba kamar akwai abinda ya faru” shiru tayi tanajin bugun zuciyarta na qaruwa Ya’isha ta zungureta tayi firgigit kamar wacce ta tashi a bacci yace “akwai abinda yake faruwa din kenan ko?” Saurin girgiza kai tayi tace “babu komai kawai dai naji Babu dadine dazun Amma yanzun na warke” bawai yarda yayi ba domin a muryarta kadai ya fahimci akwai damuwa so baison takurawa da tambayar hakan yasa yace “shikenan lkcn la’asar yayi ki huta My Meenah Baffa’am dinki Yana kewa dama shekaran jiya baki baniba Kinga sai kumburamin wando qawanki takeyi” dariya tayi shikam baijin kunyar kalaminsa tace “idan ka zaneta zata nutsu fah…..” “Wht?” Ya furta da qarfi tasa dariya shima yayi dariya suka aje wayar tare ta juya zatayima Ya’isha mgn batanan ta miqe ta kulle barayinta tayi sallah ta qara gyaggyarawa shiru tana jiran Ya’isha har dare tama hqr tayi kwanciyarta a falon tana kallon wani Korian series tana latsa wayarta lkc zuwa lkc tana duba agogo sai goma ta miqe ta bude sashin da dakunan baccinsu suke ta shiga ta watsa ruwa ta haye gado ta qudundune yanayinta yasa batada wuyar bacci nandanan bacci ya dauketa sai asuba ta farka shima tashinta yayi a waya tayi sallah ta shiga harkokin gyaran gdanta duk da akwai masu gyarawa tafiji a ranta tayi abinta domin ta fahimci mijinta ba Maison a rinqa dafdala a sashinsa bane.

Goma ta gama tayi karinta ta sako hijjab dinta har qas ta fito tare da kulle sashin ta nufi cikin gdan domin gaishe da surukanta abin mamaki yau dinma duk inda tabi sai taga jama’ar gurin sun miqe zunbur sun watse wani sanyin jiki ya kamata itan da a baya idan ta fito kowa yakeson yaga tayi masa mgn yanzu itace wai bayin gidan ma suke gudarwa hawaye ya ciko idanunta tayi qarfin halin shanyewa taci gaba da tafiyarta harta Isa qofar shiga bangaren matan gidan ta murda qofar ta shiga falon tare da sallama Mom Addah Amrah sai Urwat sune kadai a falon sai Mai Martaba dake duba jarida a gefe.
Ta nemi guri a qasa nesa da Mom cikin ladabinta da alkunya ta fara gaishe da Mai Martaba ya amsa da sakin fuska yace “Aminatuh baiwar Allah an fito to ya nauyin jikin?” Kunyace ta kamata yayi murmushi yace “kunyar nanan dai to madallah Allah yayi albarka” amsawa Mom tayi da Amin suka gaisa da Mom itama cikin kulawa take amsawa ta juya ga Addah Abulle ta gaisheta ta amsa mata Babu yabo Babu fallasa bata damu ba domin tayi alqawarin jure komai domin mijinta ta dubi Amrah dake kwance tana latsa waya tace “sister ba mgn….” Da sauri tayi jifa da wayar tace “wace sister taki ta ina muka hadu Allah ya kiyaye irin gidannan Babu yanlasan wlh saidai a kwasosu a kwashe² kamar yanda aka kwaso Mana ke ak……”
Wata qara ta saki tare da dagowa ga mamakinta sai taga Kareem ne ya sake kai mata duka Addah ta janyeta yace “na dade Ina fada miki ki rinqa saita kalamanki banason ku rinqa shigar da kanku abinda babu ruwanku kunqi ko to waima Ina ruwanku da lamarin Aminah ne kuke neman hana masa mata sakat a gidannan nine dai zakuce kuna tayawa jin haushi Kuma bada ita kuke ba da ubangiji kuke domin shine yayi alqawarin bazai taba bayar da rabon wani ga wani ba Aminatuh bata yaudareni ba tasoni tabani kulawa ta shirya rayuwarta dani qaddarar baa kaina take ba akan Ya Rasheed take matarsa ce rabonsa ce da iya wuya saita isa gareshi ni na yarda waman qaddarallahu haqqan qadarihi Babu wani ruwa dazai kwaranye zanen qaddararmu ta son Abu daya nida dan uwana Kuma dama duk inda mutum biyu sukayi tarayya akan son Abu day to dolene daya yayi nasara daya ya fadi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button