JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

Kama hannunta yayi suka shiga cikin gdan ya janyota jikinsa yana sunsunar qamshin gashinta yace “kin wahalar da zuciyata yau” dagowa tayi ta kalleshi yayi mata murmushi yace “kiyi komai ba komai ya lfyr babyna” ajiyar zuciya tayi tace “nima nasani” dariya yayi yace “kuma kina tare dashi?” Kautar da kanta tayi sukaji ana buga qofar suka kalli qofar tare ji sukayi anyi sallama gabanta ya Fadi ta janye yace “ina zaki?” Kallonsa tayi tace “Baffa’am ne ke buga qofar nan fah….” Janyota yayi yace “to me zaki bashi?” Tsayawa tayi tayi sororo sai Kuma ta juya da sauri tace “zan bashi hqr ne yace yau bazaici abincin kowa ba sai nawa”
Zama yayi ta bude qofar tana budewa ya shigo yace “ina abincin nawa?” Yana mgnr yana kalle kalle ta kalli Kareem tace “yanzu zan girka maka me kakeson ci?” Kallon kitchen din yayi yace “nima fah na iya girki muje na tayaki nawa ma sai yafi naki dadi” zaro ido tayi tayi dariya tace “habadai aiko Ya Kareem bazan sa girki ba balle kai da girmanka da matsayinka” nuna mata hanya yayi yace “ok aje abani abincina naci na kwanta sallar ma yau bazanyi ba” kitchen din ta nufa Kareem ya tashi yabi bayanta taliya ta dauka ta girkata fara ta tace ta dauko kayan miya ta soya ta zuba kifinta bushasshe data gyara ta dauki hantarta ta zuba ta soya sannan ta zuba kayan dandano ta juye taliyarta ta cakuda a cikin man nan da kayan miya ta barsu suka dahu daidai buqatarta ta sauke.

Bata tsaya hada lemo ba ta dauko na kwali ta dora akai ta zuba mawa Baffa’am dinta nasa sannan ta zuba nasu ta fita yana zaune har yanzu Yana karkada qafa ta ajiye masa a gabansa ya dauka ya miqe yace “yawwa na gde” ficewa yayi ta girgiza kai ta dauko nasu ta jera a dinning ta nufi dakinta tayi wanka ta fito ba kwalliya take ba ita dama doguwar riga kawai tasa ta fito ta qwanqwasa dakin na Kareem tajishi yana karatun qur’ani ta bude ta shiga, Saida yakai simuni sannan ya juyo ya dubeta yaja ajiyar zuciya tace “barka da hutawa” jinjina mata kai yayi tace “na kammala” murmushi yayi yace “kin bawa Ya Rasheed din?” Dagansa kai tayi yace “ya tafi?” Ta qara daga masa kai yace “ok sannu da qoqari”
Tashi yayi suka fita suka zauna a dinning din ta hada masa abincin ta miqa masa itama ta zuba yaja yayi Bismillah ya faraci itakam juya cokalin kawai takeyi gabadaya zuciyarta kwanakin nan a karye take akan lamarin rayuwarta ta dago tace “Ya Kareem” dagowa yayi ya zubanta ido tayi qasa da nata yace “fadi Mana” zuciya taja tace “ina tunanin wani abu fah zuciyata tana saqamin abubuwa da yawa nikam don Allah Ina neman alfarmar kabani damar kula da Baffa’am dina kamar yanda ya kula dani a baya” zubanta idanunsa yayi da suka fara canza kala ya aje cokalin hannunsa ya furzar da iska ya miqe ya juya zaibar gurin, yakai bakin qofar dakinsa tace “itace alfarma ta farko dana fara nema a gurinka idan kaqi yimin ita to tabbas zanci gaba da ji a Raina na rasa damata na rasa yancina tun shekara goma baya lkcn da Ina matsayin ya a gurin Baffa’am dina da shekaru shidda shudaddu da na kasance mata a gurinsa Kareem meye kake zargi don nace zan kula da Abu mafi muhimmaci a sashina?”…………..

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/13, 9:07 PM] Oum Hairan: Juyowa yayi ya zubanta idanunsa da suka jima da canza launi yanayi mata kallon sakarya ya sake juyawa zai shige ciki tace “idan kaqi aminta hakan ba Yana nufin zan barshi ya wofinta bane gareni shine qarshen…..” Daganta hannu yayi yace “ya isa dalla kada ki tarwatsamin zuciya da wadannan shashashun kalaman naki da bazasu taba yuwuwa ba ke a qaramar qwaqwalwarki kin taba ganin inda wani sashi ya kula da sashi a halin wancan sashin ya kasance abin farautar dayan to ki nutsu ki dawo hayyacinki wannan shirmen bazaa yisa Dani ba Ni nasan kaina Kuma nasan ciwon iyalina”
Zabga masa harara tayi tamai da hankalinta kan flat din gabanta zuciyarta na angizota ta fada masa ba sugar shima wata na hanata tana cewa da ita tayi hqr ta qyaleshi hakanan ta miqe a gajiye ta shige dakinta tayi sallar magrib ta zauna tana addu’arta har Isha tayi ta aikata sannan ta miqe tayi Shirin kwanciya tayi hayewarta gado taja bargo tana me miqa lamuranta ga Allah baccin me dadi kuwa ya dauketa Wanda ta jima bata samu irinsa ba cikin baccin taji an bude qofar an shigo tanaji ya mayar da qofar ya rufe yazo ya kwanta kusa da ita ya janyota jikinsa ta janye tace “ko likita yace ake dagamin qafa don Allah ya Kareem ka rabu dani…” Rufe mata baki yayi da qirjinsa yaci gaba da luguiguitata bataso dole don Babu yacce zatayi dashi ta hqr ta gyaleshi itakam zuwa yanzun bajin dadin komi takeyi ba saboda cikinta ya tsufa sosai.

Da safe data tashi ta gama abinda takeyi tayi wanka ta nufi sashin su Mom a lilo ta tarar da Rasheed kamar wani cikakken mutum yaci wanka harda su agogo su glass yana duba wata magazine tayi masa sallama ya dago ya zubanta idanunsa Yana wani lumshesu tace “barka da sfy Baffa’am” daga mata hannu yayi tayi murmushi tace “dama kacemin duk ranar death date din Meenah kana azumin mgn so yau ma azumin mgnr kakeyi kenan” zare glass dinsa yayi yace “kuma ma tace na gaisheki tace tanasonki kadan” murmushi tayi tace “amma kam na gde duk kishin Meenah da kake bani lbr harta soni nikam inada saa” bai kulata ba yaci gaba da karatunsa ta juya tace “shikenan tunda kaqi kulani na daina qawancen” tafiya tayi batasan ya biyota ba tana shiga ta zauna sun fara gaisawa da Mom kenan ya shigo Yana sharar hawaye kamar yaro qarami Mom tace “subhana meye yayi zafi?” Nuna Meenah yayi yace “ba itace tace ta daina qawancen ba” murmushi Mom tayi tace “to Banda abinka Rasheed qawance da matar aure ta Ina zai yuwu?”
Saurin katseta Juhud tayi da cewa “tsokanarsa ma nakeyi ni ban daina qawancen ba” tsalle yayi zai rungumeta Mom tayi saurin tareshi tace “kayy kada ka illatata Mana bakaga yanda take bane” guri ya samu ya zauna Meenah ta miqe ta nufi dakin Addah Abulle ta tura qofar ta shiga da sallama Addah nakan sallaya da alama walaha ta idar ta samu guri ta zauna tace “ina kwana Addah” dibanta tayi ta watsar sukayi shiru na tsayin lkc kafin tace “EDD dinki yaushe ne?” Shiru tayi tana tunani can tace “17 January” qwafa tayi tace “nasa malam Musa da yake yima yaran gdannan rubutu ya rinqa yo miki qila ki samu sauqin naqudar”

Gabanta ne ya fadi hakana taji zuciyarta batayi na’am ba a fili Kuma sai tayi murmushi tace “na gde Allah ya dada girma” daga haka sukaci gaba da shiru har Fadila tazo ta ishesu a haka ta kallesu ta watsar itakam aikin da Addah ta bata batajin zata iya da fari ma ta yaya zata shiga jikin Meenah bayan tun farko basa jituwa balle har tayi nasarar bata gubar da zatasha ta kashe dan dake cikinta? Wannan tunanin ne ya Hana zuciyar Fadila sakat har Juhud ta miqe tana cewa dasu sai anjima dukka suka bita da kallo kowa da saqarsa a zucci.
Sashin Mom ta koma ta zauna tayi tagumi tana tunanin wannan al’amari Mom ce ta fahimci da matsala tace mata “yadai Aminatuh?” Dagowa tayi tace “mom Addah ce tace wai kullum zata rinqa karbar rubutu gurin Malam Musa tana kawomin inasha” da sauri Mom ta kalleta tace “akan me?”
Sunkuyar da kanta tayi tace “wai zan samu sauqin naquda” shiru Mom tayi can tace “miqon wayar nan” miqa mata tayi ta Kira lambar Malam Musa bugu biyu ya daga suka gaisa tace masa “Hajiya Abu tayi maka mgnr rubutun naquda ne?” Shiru yayi can yace “gsky ban tuna ba Ina tunanin ta sha’afene?” Murmushi Mom tayi tace “shikenan Meenah ta ce takeda ciki wata takwas ka fara yo mata rubutun kana kawomin” gdy yayi sukayi sallama ta kalli Meenah tace “to kinji dai sai kiyi takatsantsan koda wasa kada ki yarda su baki kisha wadannan mutanen babu Allah a ransu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button