KWARATA 29

???? —— 29
Bai ɗauka wayar ba ya fito daga cikin gidan , ina cikin mota zaune nima ban fito ba , shine yazo har wurin mota ya buɗe gidan baya ya zauna amma bai rufe ƙofar ba , juyawa nayi ina kallonshi tare da cewa dana kira naji baka ɗauka ba nayi tunani ko baku tashi bacci ba !
Gyara maɓallin rigarshi yayi tare da cewa ai ina ganin kiranki nasan kina ƙofar gida shi yasa nace kawai bara na fito basai na wani tsaya ɗaukan waya ba , murmushi nayi na juyowa ina kallon gabana wato na juya daga kallon Alaji nace muje ciki to…
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘160 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Tou muje amma bata nan ta shiga maƙota , ɗan zaro ido nayi amma banyi magana ba , a zuciyata nace maƙota tun wannan safiyar ? Lallai akwai ƙatuwar matsala , sauka nayi daga cikin motar tare da cewa muje Wane Yaro ɗan daban da nazo dashi ,
Rufe mota ta nayi muka nufi cikin gidan dukanmu , a ƙaton palon matarshi ya saukemu gafa kujeru har kujeru amma datti yasa sun tashi aiki , bakajin wani ƙamshi ko na tsitsiyar ƙamshi bare kayi tunanin zaka samu turaren wuta banda zarnin fitsari palon kaca ² a firgice babu abinda ke tashi sai wani ƙanni² a palon….
Saman hannun kujera Alaji ya zauna ni kuma kallabin kaina na ciro na shimfiɗa a matakalar da zata gangaro dakai cikin palon dan wannan kujerun idan har na hau su yau babu abinda zai hana ƙurajen ƙyama su fito jikina….
Fira muka farayi da Alaji ya ɗan fara karanto min matsalolin da yake fuskata , yace ga ƙazanta ga rashin ragowa ga fita babu gaira babu dalili , ga rashin godiya ko zai kashe kanshi ya bata bata taɓa masa godiya ba , wallahi idan har zai kwanta da ita sai ankai ruwa rana sannan kuma babu wanka bare yayi tunanin zai ji wani ƙamshi da zaisa mishi yaji wani shauƙi yayin da yake kwanciya da ita…
Uhum har ga Allah ba sasanci ya kawoni gidan Alaji ba a wannan lokaci , ina da wani ƙudiri nawa na daban , ina so inga yanayin yadda yake hidima da gidanshi , surutar da matarshi take amfani da ita kuma har store insu yau sai naje dan inga idan naci gaba da tarayya da Alaji zai iya ɗaukemin duk wasu buƙatu na ? Dan nima in samu wanda zai tayani kula da tawa rayuwar , zan kuma bigi cikin matarshi ta faɗamin komai nasu da wasu sirrika na Alaji daga nan ni kuma zan ɗaukeshi sai tayi da gaske ma zata sake ganinshi…
Babu ko sallama ta faɗo cikin ɗakin daga ita sai ɗaurin gaba hijabinta riƙe a hannunta , Abbu Afsar ka tashi kenan ? Bai kalleta ba yace na tashi daga ina kike ne ? Kallona tayi sannan tace wallahi gidan Naja naje tace zata shigo bata samu damar shigowa ba kusan kwana biyu mijinta ya hanata fita shine nace ta bari ni nazo , kallonta Alaji yayi tare da cewa ita da bata raina mijinta ba ! Ya hanata ta hanu ke kuma da kika raina naki sai kika fita babu izini na.
Tsoki tayi tare da zama saman kujera tana cewa baka gajiya da tsegumi haba da Allah dan naje tou miye ? Murmushi nayi ina mai kallonta , gaskiya kyakkyawa ce sosai , ga kyawu har kyawu amma an kashe kyawun da ƙazanta , yarinyar mace kamar wannan tana zama da ɗaurin gaba , gashin hamatar ta kanshi idan kika kamashi zaki iya kitsashi saboda yawanshi , tana da haƙora masu kyau amma ta kashesu da rashin wankewa , kanta kuwa ƙaramar ƙarya kila yayi shekara rabonshi da a kwance , kitsone saman kan amma baka isa ka gane ta ina aka ɗauko tsagar kitson ba ,
Tou bamu dai gama maganarmu ba da Abbu Afsar Ummu Afsar ta shigo gidan , tsokin da tayi masa yasashi tashi ya fita daga ɗakin , ina kwana na gaisheta , ansawa tayi tare da fyace majina da gefen zaninta , sannan tace ban gane ki ba ,
Uhum ai baki sanni ba na faɗa ina sadda kai ƙasa cikin nuna mata ni ta gaskiya ce tunda nasha hijabi daga sama har ƙasa , kallona tayi sannan tace Allah sarki sannu da zuwa , ki dawo saman kujera mana !
Nan ma yayi na bata amsa , bara na kawo miki ruwa , tou na faɗa yayin data miƙe tabar palon , babu wani ɓata lokaci ta dawo da wasu irin haɗaɗɗin kulololi masu matuƙar kyau da tsada , ta wuce taje ta ajiyesu a saman tebirin cin abinci ,
Saida ta ajiye sannan tace bisimillah mana , ta faɗi maganar cikin sakin fuska , banyi magana ba na tashi na nufi tebirin cin abinci yayin da Wane Yaro ya zauna a wurin dana tashi ,
Kujera taja itama ta zauna kusa dani sannan muka sake gaisawa, ɗora hannuna nayi saman kular da take ƙoƙarin buɗewa nace suna na Sultana ɗiya ga Aliyu Muhammad Binna , Babana sananne ne kuma ya shahara a harkar caca , dani da Babana da kowa nawa muna zama a gidanmu cikin kwanciyar hankali , nazo wurinke dan gyara miki wani kuskure Allah dai yasa banyi shishshigi da yawa ba…..
“Yar gajeriyar dariya tayi sannan tace ke kuma me yace miki nayi masa ne ? Kallonta nayi sosai dan na fahimci yanayin rayuwar tata , bata da babbar ciwon dake damunta wanda ya wuce rashin ɗaukar shawara , tana da taurin kai sannan kuma abinda taga dama shi takeyi babu wanda ya isa ya sa tayi ko ta bari sai ciwon rashin wayau dake ɗawainiya da rayuwarta…
Kauda kaina nayi daga kallonta sannan nace ni bai faɗamin komai ba , gyara zama tayi tare da cewa baya da aiki sai kai ƙarata bana san wanka bana shara bana goge ɗaki ban iya girki ba , ban iya kwanciyar aure ba , cikin hayani tace yaje ya nemo wacce ta iya duk wannan abun dana lissafo ban iyaba ta ƙarasa maganar da dukan tebirin data ajiye kulolin da ƙarfi…
Cikin tsoro nace saurara kiyi haƙuri ba hayani ta kawoni ba , shin ko kina fama da matsalar rashin abinci ne ? Ko rashin sutura sabun wanka ko na wanki ? Rashin turare ko man wanke baki ? Cikin ɓacin rai tace babu abinda na nema na rasa dalili dai bazai yuwu ba kullum namiji yayi ta sussukata ni ba gero ba ,
Dariyar mugunta nayi mata tare dayi mata kallon wawiya , data riƙe mijinta ram a hannu da bai kallo matan waje ba , wannan ba matsalar Alaji bace itace ta kai mijinta ga halaka , na rasa abinda yake damun matan ƙarshen zamani , babu biyayyar aure ba ladabi mace ta mayar da mijinta kamar almajirin gidanta baida wani mutunci ko daraja a idonta….
Yake “yar uwata ki sani aure yana da babbar matsayi haka kuma namiji yake da babbar daraja , mijinki shine sirrinki suturarki aljannarki sai kin gyara rayuwar aurenki sannan zaki samu rayuwa mai daɗi a gidan duniya da ƙiyama dan miji ba abin wasa bane , mijinki ba abin wulaƙantawa ba ne sannan kuma mijinki ba abokin gabarki bane , abin ƙauna ne abun tausayawa ne a gareki , ki kwantar masa da hankalinsa sai Allah ya kwantar miki da naki , ki bashi natsuwa sai Allah yasa kema ki samu natsuwa , kisa mishi farin ciki sai Allah yasa kiyi farin ciki a gidan duniya da lahira….
Matan bariki suna da illa kuma suna tattare da masifun dasu ma kansu basu san suna dasu ba , bariki wuta ce mai azabar raɗaɗi da wahala , zina halakace kuma babbar cutace , me matan barike suke dashi wanda baku dashi ne ? Komai iri ɗaya ne abu ɗaya suke dashi wanda matan aure suka rasa , kuma suma matan auren suna da abu ɗaya wanda matan bariki basu da irinshi !
Wannan abu ba komai bane sai sakaci , shine abinda matan aure garesu , matan bariki kuma basu dashi , matan bariki basu da sakaci abinda matan aure suka rasa kenan…
Ummu Afsar ta saki baki ga wacce bata sani ba taci gaba da buɗemin sirrin mijinta wanda haka ba daidai bane ga duk macen data san abinda takeyi , ɗakinta da tsore inta babu inda bata kaini ba dan in gani da idona tana da komai na rayuwa tsaftarce da haƙƙin Alaji bazata bayar ba , tunzura ta nayi tare da cewa Eyy ki barshi gaskiya gaki ma yadda kike kyakkyawarki ko kun rabu sai kin samu wanda yafi shi , murmushin jin daɗi tayi tare da cewa ai cewa ma akeyi nafi ƙarfin shi , kallonta nayi tare da cewa gaskiya keɗin duniya ce da matsayin gidan sarauta…
Sallama mukayi da ita tayomin rakiya har ƙofar gida inda nayi parking in motana , saida na fara tafiya sannan nasa Wane Yaro ya kiramin wayar Alaji , bayan ya ɗauka nace masa ina san ganinshi amma ya faɗamin sirrintaccen wurin da zamu haɗu , bayani yamin sannan nace masa na gode tare da kashe wayata…
Kai tsaye gida muka nufa a bakin hanya na ajiye Wane Yaro ni kuma na wuce gida , a ƙofar gida nayi parking in mota ta na shige ciki , sallama nayi kamar yadda na saba na wuce ɗakina , ruwa na zubo a boket naje na watsa sannan na dawo ɗaki nayi kwanciyata dan hutama rayuwata….
Bayan sati biyu , abubuwa da dama sun faru , ga lamarin iskanci na kuma yanzu na zuƙa hannu na , Babana kuma ya samu mage kamar yadda malam yace kuma ya aiwatar da aikin kamar yadda akace yayi ,
Na samu Alaji munyi magana dashi kuma ya faɗamin cewa yana san wayayyar mace “yar gayu wacce zata biya masa buƙatarshi a duk lokacin daya so , ba laifi yana da wanka kuma yana gayu kuɗinshi a sake yake ga mata , dan haka na ɗaura dashi cewa ya saurareni ina san na haɗa gidanmu sannan naci gaba da harkar bariki na,
Da alkairi na nake shiga cikin ahalinmu , nakan basu kwance kaya , in siya musu kayan kwalliya idan na samu kuɗi , ina aika musu da kayan abinci kuma ina zuwa lokaci ² ina basu sha’awa kuma cikin hikima na fara musu tallar bariki ,
Duk wata hidimata yanzu Alaji shike ɗauke da ita , babu abinda na nema na rasa fanni abinci kuɗin kashewa da kuma suturu ya kwacemin duk wani abinda zaizo ya dameni , yauma ƙaton rago ya kawomin dan haka na sakashi a napep na tura Wane Yaro yakai gidan Baba ƙarani da 100k nace ya sayi icce…
Babana kenan , ɗan duniya abin alfahirin uwar ɗakin kwarata , cikakken namiji mai dogon zamani , namijin duniya gatan mata , ka gansu ka ƙyasa ko ba sisinka su bika , baka gada ba haye kayi Sultana tai gado ɗan gado kuma saiya zarta…..
Uhum Baba kenan , Amisty ce kwance a saman Baban Sultana suna ɓalgacewa bayan sun gama ɓalɓalewa yake tambayarta ya Uwar masu gida ? Tace tana nan cikin ƙoshin lafiya , Amisty itace take kaiwa Baban Sultana labarin halin da Sultana take ciki , kuma shine ya tirsasawa Amisty ta kwashe kayanta ta dawo zamani dan kawai ya riƙa jin halin da nake ciki , abin kunya Baba ka rasa macen da zaka huta da ita sai abokiyar “yar ka , dakai da Amisty duk ranar da Sultana ta gano ku zaku fuskanci babbar matsala….
Lokacin da Baba ƙarami yaga rago abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba dan babu biki ba suna kuma ba sallah kawai an bashi kyautar rago , yaji daɗi sosai a lokacin da Wane Yaro yaje kai rago ya samu Zainab da Farida a gidan dan haka daya tashi zai dawo suka biyoshi zuwa wurina…
Nayi farin ciki da ganin “yan uwana , muka rungume juna cikin soyayya irin ta “yan uwan da suka daɗe basu haɗu ba , sannan muka shiga jajantawa juna yaushe rabo ? Bayan an gama suka tambayeni ko na fara kasuwanci ne ? Dariya nayi tare da ce musu sosai ma , me kike siyarwa ne ? Suka tambayeni kai tsaye nace Karuwanci shine sana’ar da nakeyi…
Zasu fara wani mamaki nace karku wani damu kuma kar kuyi mamaki nayi amfani da huɗubar da Baba yake baku ku tashi ku nemi kuɗi domin ku kare mutunci kanku , huɗubar ce na ɗauka kuma da ita zanyi amfani kuma ma babu laifi an samu nasara tunda na siya gida ga mota kuma ina da “yan canjina , ku kun samu gida da mota ne ? Na tambayesu , shiru sukayi , murmushi nayi tare da cewa karku damu ƙanwarku ta kasa kuma ta samu masu siya nayi ciniki sosai dan haka kawai ku dawo nan muci gaba da zama dan tunda na siyi gidan na fitar da ɗakunan matan Baba shima Baban zan dawo dashi dan kasuwa bata yuwuwa babu shugaban ƙungiya….
Gaba ɗaya wutarsu ta ɗauke musu basu da zaɓin daya wuce su dawo zama tare dani tunda inda suke a raɓe suke , koda suka tashi tafiya na basu kuɗi na basu kayan sakawa , sunyi godiya sosai tare dacemin insha Allah zuwa jibi zasu dawo , rakiya nayi musu suka tafi…
Baba ƙarami da jama’ar dake da sauran mutunci a idon Babana sune suka sameshi suka bashi magana cewa ƙauracemin bashi ne zaisa nayi halayen kirki ba , ya dawo kusa dani wani abun ma a gaban idonshi bazanyi ba , Baba yace shi ba wani abu yakeji ba kawai kunyata yakeji ya zama sokon uban daya kasa ceton “yarshi daga shiga wata baƙuwar rayuwa !
Magana suka ba Baba harya amince zai dawo gidana , kuma yaje wurin Maman Fa’iza suka ce zasu dawo suma jibi idan Allah ya kaimu dan haka gida zai dawo kamar yanda yake da , su Nana Karima da suke zaune a gidan kuma bazan tada su ba saidai idan sune suka tashi da kansu…
Da marece ina kwance Amisty ta shigo ɗaki babu sallama , jakarta ta ajiye ta ɗauki buta ta nufi bayan gida , tana fita na tashi da sauri naje na ɗauko jakarta na buɗe , kuɗine masu yawan gaske a ciki dan haka na tattarasu gaba ɗaya na kwashe su na ɓoye sannan na koma saman katifa nayi kwanciyata kamar yanda nake daga farko…
Ban daɗe da kwanciya ba ta shigo tare da cewa tashi gidansu Hafsa zamuje bata da lafiya , subahanallah na faɗa tare da tashi zaune nace meya sameta haka ?
Ƙonewa tayi ta faɗi maganar tare da ɗaukar jakarta , nima tashi nayi banko ɗauki gyale ba makullin mota kawai na ɗauka tare da cewa muje , tunda nake ban taɓa zuwa gidansu Hafsa ba sai yau zan fara , a tsakar gida nayiwa su Nana saina dawo sannan mukayi waje dani da Amisty…
Daga ni sai Amisty muka tafi ni naja motar har muka isa gidansu Hafsa , har zanyi parking a waje Amisty tace inyi horn za’a buɗe , banyi musu ba na dannan horn mai gadi ya kwashe mana get muka shige , kusa da motar Hafsa anan nayi parking in mota ta sannan muka shige ciki…
Har muka isa ɗakin Hafsa bamu haɗu da kowa ba , palon ɗakinta ma ba kowa dan haka bedroom muka shiga kai tsaye , Hafsa tana kwance a saman gado an naɗe ƙafarta da farin bandeji , idonta a rufe kila tanayin bacci ne , zanyi mata magana Amisty tace karki tasheta bacci takeyi , banyi magana ba na samu gefen gado na zauna , palo Amisty ta koma babu jimawa ta dawo ɗauke da wata ƙatuwar roba bansan ko miye a ciki ba , wurin ƙoƙarin ta hawo saman gado ta ɓareminshi kaf a jikina , tsakiyar idonta kaɗai na kalla na gane wannan abun shiri ne ,
Kallon kokon data makomin a jiki nayi sannan na sake kallonta , kiyi haƙuri Amisty ta faɗa , ba koma nace cikin sanyi jiki dan Amisty tsoro take bani , cikin sigar lallashi tace ki shiga toilet saiki wanke , banyi magana ba na miƙe na nufi inda Amisty ta nunamin da ɗan yatsanta , kokon gaskiya baya wankuwa gefe² dole sai na cire kayan nayi wanka gaba ɗaya dan babu inda bai kai ba ,
Cire kayana nayi nai wanka , bayan na gama na wanke kayana na ɗauro towel na fito da kayan a hannuna da niyar ince a ina zan shanya ? Ina fitowa naga Hafsa tana rufe ƙofa da makulli bayan ta gama ta tillashi can saman waldrop , bayan ta tilla ta warware bandejin sannan tace hausawa sunce mai haƙuri mawadaci nasha haƙuri kuma na daɗe ina dakon yunwa da ƙishirwa , yau zanci insha zan kore duk wata tsohuwar yunwar dake cikin hanjina… Dariya sukayi tare da tafawa ita da Amisty….
Amisty ta ansa da cewa lallai zamuga wasan kura ga uwar kwarata gata lesbian , Hafsa tace tabbas yau zan koya mata irin namu salon tunda muma ta koya mana irin nata , a’uziyya naja tare da ƙara riƙe towel in jikina gam , murmushi Hafsa tayi tare da cire rigar jikinta tace kinga sheɗan baya tafiya gashi ma ya fara cire rigar jikina , kin gani ta faɗa yayin da ta ɓalle bireziyarta , ja baya na farayi da niyar komawa toilet ina ihu a kawo min ɗauki kwarata sun rufeni a ɗaki ,
Dariya Hafsa tayi tare da shan gabana tace ina zakije ne ? Kuma babu mai cetonki dan gidan ma babu kowa , shi yasa nace Amisty ta kawomin ke kwana biyu zakiyi kawai kafin nan nasan kema kin zama “yar hannu…
A saman bedsite naga kwalbar mai mai gurguwa dan haka da sauri na yada kayana na ɗauka na kwaɗawa Hafsa a kai harsai da jini ya fita , ajiyar zuciya ta sauke tare da fizgoni tace nagode ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin haɗa bakina da nata , da ƙarfi na tureta naci gaba daba da ihu ina kai mata duka , kwata ² bataji dan haka ta janye towel in jikina , ita da Amisty suka kamani mukaci gaba da kokowa da ƙarfin bala’e suka ɗorani saman gado…..