Labaran Kannywood

Kamani da Akayi da Hukuncin da Kotu ta Yanke Min Ya jawo Min Babban Tabo a Rayuwa ta Cewar Mubarak UniquePikin

Kamani da Akayi da Hukuncin da Kotu ta Yanke Min Ya jawo Min Babban Tabo a Rayuwa ta Cewar Mubarak UniquePikin

Acikin Makon daya gabata ne Labari ya karade Shafukan sada zumunta cewa Gwamnatin Jahar Kano ta kama Mubarak UniquePikin Shida Na’ibinsa Akan wata faifan vedio daya wallafa a Shafinsa na Tiktok inda acikin barkwanci Vedion Suka ambaci Sunan Gwamna Ganduje hade da Iyalanshi.

Kalli Cikakken vedion anan

 

Sai dai hakan ya batawa Gwamnan rai matuka inda yasa aka kamasu Kuma aka gurfanar dasu a gaban Kotu, aka Yanke masu Hukunci inda akayi masu bulala ashirin ashirin tare dashi da Na’ibinsa, sannan akaci kowanensu tara ta naira dubu Shirin ashirin, Da kuma Sharar harabar kotun na tsawon wata guda.

Bayan Hukuncin Kotu akan Mubarak shida Na’ibinsa, Mubarak ya bayyana cewa Kamasa da akayi da kuma Hukuncin da Kotu ta Yanke masa yayi masa babban tabo a rayuwar shi.

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button