KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yanayin yadda fararan idanuwan sa suka koma yasa ta tsorata.
Idanun ta suka ciko da ‘kwalla, domin a duniya RAHAMA ta tsani abinda zai ta’ba mata d’an ‘kanin ta.
Lumshe idanuwan nasa yayi na wani lokaci, domin ganin yanayin ta ya sani sarai yanzu sai ta tada hankali ta ciwon ta yazo ya tashi.
Shiyasa ya lumshe idon don idanun su dai daita.
“Meye Auwal? meke damun ka? mai ya ‘bata maka rai?” ta jero masa tambayoyin nan a lokaci d’aya, kuma cikin kuka.
Jin kukan ta damun sa ta ‘karu, amma sai ya danne damuwa nasa tare da bud’e idanuwan nasa akan ta.
Ya sakin mata ‘kayataccen murmushi, ya ri’ko fuskan ta yace “babu komai my love, bar kukan haka” kallon cikin ‘kwayan idanun sa take don tabbatar da zancen sa.
Kauda kai yayi tare da cewa “da gaske babu komai Anty na”.
Jan hanci tayi tare cewa ” Auwal zaka fad’an gaskiya ko sai ranka ya ‘baci?”.
Turo baki yayi irin yadda yara keyi yace “kice su fita to” hararan sa ikilima tayi tare da cewa tana mi’kewa “nayi nan tun kafin a koren”.
Itama Momyn su Akram ta bita tana murmushi.
” Sun fita ina sauraron ka” kwanciya a cinyan ta yayi tare da ri’ko hannu ta d’aya ya dam’ke a nasa.
Zuciyar sa na bugawa, “ina jira fah Auwal” tace gaban ta na fad’i domin da gani ba’karamin abu bane ke damun sa.
Kuma bai ta’ba ‘boye mata damuwar saba.
Jin shirun nasa yayi yawa yasa tace “idan ‘karya kake son fad’a min ba gaskiya ba to kari’ke kayan ka”.
Ganin kaman tayi fishi yasa tashi a jikin ta tare da janyo akwatin da tace wa matar sa ta sayo.
Ya bud’e tare da kallon tulin kayan dake ciki yana nazarin su yana murmushi.
Waigo wa gare ta yayi idon ta na kansa, yace ” Anty duka nata ne?” banza dashi tayi .
Bai damu ba ya fara ciro kayan d’aya bayan d’aya yana kallo tare da murmushi a fuskan sa.
“Anty zasu matu’kar yin mata kyau amma ban son ta yanzu” yace cikin ransa na ‘kuna.
Matsowa tayi kusa dashi tace “ban gane ba?” kallon ta yayi tare cewa “abinda kikajin nan shine kawai” idanun sa sun ‘kara rinewa fiye da dah.
Ganin halin da ‘kanin nata keson jefa Kansa yasa tace tana murmushi ya’ke tare da ri’ko hannu sa.
Kwantar dashi tayi a cinyan ta tare da shafa masa gashin kansa, ta d’au lokaci tana haka shi kuma yana ta wani irin numfashi.
Zuwa can yayi barci, jin yayi barci yasa ta sauke ajiyan zuciya tare da hamdala.
Tana ro’kon ubangiji a zuciyar ta tace “ya Allah ka San yaya mishi zuciya, idan ba alkhairi a tsakanin sa da yarinyan ya Allah kaman tar dashi ita, Allah kasa ya farka bashi da damuwar komai”.
Tace tana kallon fuskan sa mai cike da haiba da zati.
” Mai kika masa haka? nasan ba ‘karamin abu bane ya ‘bata wa Auwal rai”.
“Ina kike? ina zan ganki ? inason sanin ki da sanin mai kikawa my ‘kani na?” numfashi taje tare da d’aura kanta a jikina sa.
Nan itama barci ya kwashe ta.
Damuwa yayi wa Joy yawa kullum kwana nan duniya baza ido take tana kallon hanyan da Auwal zai dawo, tunanin ya zame mata jiki, kuka ko shine abinci ta a halin yanzu, tun maman na lallashi har ta kai ga yanzu ta zuba mata ido, makaranta kuwa yanzu ta sauke sa saboda bata son Auwal ya dawo bata.
Yadda take son mai da kanta da rayuwar ta na matu'kar damun 'kawar ta da mahaifiyar ta.
Kuma saboda zurfi ciki har yau kusan satin Auwal d'aya da kwana biyu Aisha bata san meke damun 'kawar taba.
Tayi tayi ta sanar mata ta'ki , tayi fushi akan haka har takai ga ta sakko domin tasan waye 'kawar ta akan zurfin ciki.
Kwance take da wurin 'karfe 11:00pm idon ta kuri kamar kowacce dare tun bayan barin Auwal garin.
Tana abinda ta saba wato kuka.
"Shin yanzu idan kabar ni ina zan sa raina?, yaushe zaka dawo? ji yadda na rame dama ba akauki ne dani ba. Tunani da fargana bazaka dawo ba yana mugun d'agamin hankali, yanzu ne nagane irin tsanani son da nake maka, inaga kuma shine ajalina mudin baka dawo gare niba . ka aminta dani don Allah shine burina . Kada kabarni doctor kada ka gujeni kasoni kada ka'kini".
" Idan kabar ni bansan inda zansa raina ba, yaushe zaka zo gare ni kace ina soki Joy? " tace tana 'kan'kame filo tare da fashewa da kuka.
Kuna ta tambaya to gashi na daur nayi, yadda na faran ta muku inason nima Ku sani farin ciki.
Comments d'in Ku shine 'kwarin guwar mu mu writer's.
Sai naji Ku, idan ba haka ba kuji shiru.
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
????????????????????????????
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
*????DA BAZAR MU WRITER'S ASS????*
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*My fan's godiya marar adadi, Allah bar 'kauna*
*Dedicated to Heart beat????*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
????2⃣5⃣to2⃣6⃣
Auwal ya riga RAHAMA tashi, jin motsin sane yasa ta farka tare da d'aga sa, kallon sa tayi shima ita yake kallon bayan ya tashi a jikin ta, murmushi ta sakin masa shima ya mayar mata.
"Anty kema barcin kikayi?, eh d'an 'kanina" tace tana jan mai kuma tu.
"Har kun tashi?" a tare suka wai ga, mami ce ke tambayan su, "eh mami munsha barci, ko ban ninyan barcin ba ga wanda ya sani nan" cewan RAHAMA tana kai masa dungurin wasa.
Dariya mami tayi tare da cewa "ai kun saba dama ba yau bane farko, maza tashi kije sashin ku tun d'azu mijin ki ke mana safa da marwa".
Turo baki tayi tare da cewa " kai amma gaskiya Salisu nada neman magana, meye kuma na sintiri?, toni gaskiya ina tare da 'kanina ban gaji da ganin sa ba".
"Banson shashanci maza tashi kije" ba don taso ba ta mi'ke tare da kama hannu Auwal.
Kallon ta mami tayi tare da cewa "ina zaki kuma dashi?" .
"'Bangaren mu mana" janye hannu sa yayi tare da cewa "Anty ni bazani ba gaskiya, saboda mai?".
"Kawai" yace da ita tare da koma wa gadon 'yan matamcin ta ya kwanta tare da lumshe ido.
Kallon sa tayi tare da cewa tana mai maida idon ta kan mami "mami kice masa ya tashi muje, yaje ina? ina tunda kika dawo kuke tare? maza bar nan banson shashanci".
Fita tayi ba don ranta yaso ba, tana fita mami ta nufo wurin d'an nata.
Zama tayi gefen gadon tare da cewa " meye damuwar ka yaro na?" shiru yayi kamar mai barci amma tasani sarai ba barcin yake ba.
"Da kai fa nake kanaji na ina magana kai banza dani" bud'e idanun sa da sukai masa yaji-yaji saboda hawayen dake cikin sa.
Sunyi ja jazur dasu yana kallon ta dasu "lafia Auwal?" tace tana mai d'ago sa.
Bai shiryawa zuban hawaye ba kawai sai gashi sun zubo masa.
"Mami na" yace cikin in ina, "ya akayi ne d'an mami ? fad'a kada kai shiru zaka samu sau'ki kaji?".
" Mami inason ta ina 'kinta, mami ki nake kamar zan mutu na kuma manta da ita, amma zancen Anty yasa na tuno ta, don barcin nan da nai har mafarkin ta nai".
"Mami zan koma gobe" daga haka yayi shiru yana mai dafe 'kirjin sa yarasa taka mai man maike damun sa.
"Auwal ban gane zancen kaba, ban gane inda maganan ka ta dosa ba, mai kake nufi?".
" Fad'a min wacecce kake so, kuma wacecce kake 'ki".
"Duk itace" yace yana mai kallon mamin.
"Fahimtar dani, yaro na ya fara soyayya? kome?".
Ganin ta kafesa da ido yasashi kauda kai tare da sanar mata da labarin komai na dangane dashi da Joy.
Amma koda yazo zancen fyad'e ya kasa fad'a kuma hakan ya'kara masa zafi a zuciya fiye dada.
" Yaka tsaya? inajin ka, shikenan ai mami" bai fad'a wa mami cewan ba musulma bace.
"To meyasa baka fad'a mata ba?" shiru na wasu d'aki'ka yayi sannan yace "yarinya ce sosai mami shiyyasa ban sanar mata ba".
" Yarinya kamar ya? bata isa aure bane?. tukunna dai mami bata wuce 16 years ba fah, yanzu haka ina tunanin JS3 take".
"Ai ta isa aure kam, sai dai kace kawai baka son ka auri yarinya, to mai zai hana a d'aura aure ta ta dawo nan da zama? idan yaso daga baya sai ayi biki bayan ta gama secondary d'in ta".
Turo baki yayi tare da cewa " kai mami to meye ma'anar haka? baki tunanin ta'ki maida hankali a karatun ta?".
"Kuma mani a'a sai ta girma, don bazan bari ayi taje kuma.....kawai.......umm ni dai a'a kawai".
" Shikenan tunda hakan yafi maka, amma shawara ta ka sanar mata tunda wuri ".
" Humm" yace kawai tashi tayi ta fita ta barsa, shi kuma kwanciya yayi yana tunani.
°°°°°°°°°°
Washe gari samakon tashi Auwal yayi, da shirin sa tsaf na tafiya ya fito, lokacin da ya fito babu wanda ya fito sai masu aiki dake kara kanya.
Don duka daga sallan asuba kowa ya koma barci amma banda shi.
'Dakin mami ya nufa duk da yasan ba lalai ya same ta irin wannan lokacin a d'aki ba.
Koda ya shiga babu kowa a ciki, kiran layin ta yayi sai da yakira yafi a 'kirga kuma yana ringing ba'a d'aga ba.
Ganin time na tafiya yasa ya zari key d'in motar sa da kayan sa ya fita a d'akin.
Wurin ma'a danar motocin gidan ya nufa, motar sa ya bud'e tare da jefa kayan sa yayi ciki.
Tada motar yayi ya bar gidan ba tare da sanin kowa ba sai dai masu aiki tsiraru da mai gadi suka gansa.
Sai muce Auwal Allah tsare hanya........
~~
“Joy ki tashi haka mana, barcin ya isa haka” tashi nayi ina tura baki had’e da mi’ka.
“Mama Allah kin cuceni ina cikin barci na mai dad’in gaske kin katseni” nace a cikin zuciya ta.
“Tashi kinji yau bikin Bola, tashi kishirya muje, ba inda zani” nace ina ninyan koma wa na kwanta.
“Tashi ki karya to, ba yanzu zan karya ba, kinsan ko ‘karfe nawa ne yanzu kuwa?”.
” Um’um, 12:30pm ne yanzu, maza tashi ki karya saiki wanka ki kwanta ni Narasa wani tsiya kika tsiro yanzu, da dare baza’a barci ba sai safe yayi akama barci”.
“Kibarni please mama ki tafi abunki” nace tare da gyara kwanciya na.
Girgiza kai kawai tayi tare da cewa “sai na dawo, ah” nace ko wai gawa banyi ba.
11:00am yayi wa Auwal a ‘kofar gidan sa na ‘YAR KADDE, parking yayi a jikin gidan fito wa yayi a motan tare da rufewa bayan ya ciro kayan sa.
Bud’e gidan sa yayi ya shiga tare da tura ‘kofar yayi ciki, kallon gidan yake duk yayi datti.
Bud’e ‘kofar shiga d’akin yayi jefa jakar kayan sa yayi tare da tu’bewa ya fara gyara gidan.
Tsaf ya gyara ko’ina gida ya fito shar dashi, lallai yaron mami yayi ‘ko’kari.
Bayan ya kamala gyaran gidan yayi wanka, shiryawa yayi cikin ‘kananun kaya , kayan sun kar’besa sosai, a lokacin ne yaji anfara kiran sallan azahar don haka sai yayi alwallah tare da fita don zuwa masallaci.
Bayan an idah salla ne ya fara tunanin mai zaici, fito wa yayi daga masallacin yayo gida.
Joy ta fito daga cikin gida da nufin shiga gidan su Aisha sai taga mota a jikin gidan Auwal.
Kallon motan take kamar shine a ciki, a zahirin gaskiya bata ta’ba ganin mota irin wannan a cikin ‘KAUYEN ba.
Motan ta bala’in d’aukan hankalin ta, zuciyar ta na raya mata cewa Auwal d’in ta ya dawo.
Farin cikin da na dad’e bangani ba a fuskan ta shine kwance har da darinyan ta.
Ji take kamar ta zura da gudu tashiga gidan sa, amma ina a wanan lokaci ne miskilancin ta ya tashi, tsaye kawai tayi tana kallon gidan.
Tana tsaye Auwal ya dawo, tun daga nesa ya hango ta, tafiya yake kawai amma idanun sa ita yake kallo.
Murmushi ya saki lokacin da ya ‘kariso, idon sune ya sar’ke ana juna.
Kallon junansu suke na tsahon wani lokaci, Joy ne ta fara jenye nata tare da juyawa gida.
Dariya ya fashe dashi kuma tajisa sarai tai shige wanta, “‘yar rainin wayo kawai, sai da tagama kalle kyakkyawan mami tsaf kamar ta lashe, kuma hakan take marmari nagano tsaf, wai ita miskila ta wani juya fuw tayi gida”.
” Dawo ki cigaba da kallon abinki ” yace yana murmushi tare da shige wa nasa gidan yana girgiza kai “hmm, yarinya kenan wai ita aji, bari ya tsinke muga sai inga ta tsiya”.
Yace dai-dai da iso warsa farfadan gidan, zama yayi a fararen kujerun sa dake gefe a tsare a gidan.
Yamitsa fuska yayi tare da cewa ” ta rame wallahi, ta rame sosai Allah sa dai ba ciwon cikin bane, ko…….” sai yayi shiru yana nazari.
Murmushi yayi tare da cewa “kai so ba’ine, so masifa ne, yunwa fa nakeji amma sakamakon ganin masoyiya ya tafi. Hmmm”
•••••••••••
Dariya nima nayi lokacin da na dawo cikin d’aki, don sai lokacin tazo “jishi kamar aljani saboda kyau, Allah yayi wa Auwal kyau tamakar shi yayi kansa”.
” Allah sa ya dawo ne yace yana sona, wuw da nayi farin ciki mai tsanani “.
Kwanciya ta nayi tare da lumshe idanuwa na…..
Share pls
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
Dedicated to my lvly fan’s
Musamman
MY besty (maman Muhammad)
Bilqess
Maman Aliu
Fauxy
Fulani Gal
Maman Inteesar
Jidda h garba
Da dai sauran su ina tsanani ‘kaunar Ku fan’s , much luv sisters iya wuya ana tare????????????????
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
????2⃣7⃣to2⃣8⃣
6:10pm na sake rangad’a wankana na zauna na tsantsara ‘kwalliya na, nayi masifar kyau, kamar a sace a gudu, ina zaune a far fada, ina duba notebook d’ina. Sai ga mama ta shigo tunda na d’aga kai na naga ita ce na mai da kai na a littafi na, na cigaba da nazari.
Ban sake d’ago wa ba sai da naji tace “shigo mana doctor”, sa’an nan na d’ago gaba na na fad’i na jin ankira rayuwa ta.
Shigo wa yayi muka had’a ido dashi, hannu sa ri’ke da kaya, idon sa na kai na yace ” a ina za’a aje?” mama tace “bani nan yaron kirki na aje”.
Murmushi yayi mai ‘kaya tarwa tare da cewa ” nu namin kawai na aje” yace yana mai kauda fuskan shi daga kallon na.