NOVELSSHU'UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

SHU’UMIN NAMIJI COMPLETE HAUSA NOVEL

     *SHU'UMIN NAMIJI !!!*

(Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne, wanda na ƙirƙira, bakuma naso ajuya min shi tako wani siga….)

WRITTEN BY
phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER KHABEER

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition
 *WATTPAD*

@fatymasardauna

Вisмiιιαhirra hamanirrahiм

Chapter 1

Wani irin gudu black colour car ƙirar RANGE ROVER ke falfalawa akan babban titin dake cikin garin ABUJA

Gaban wani irin makeken gate motar ta tsaya, minti kaɗan kuma ta soma wani irin ƙara kamar zata cire kunnen maisaurare, cikin mintuna ƙalilan maigadi da jikinsa ke rawa ya wangale makeken gate ɗin, da gudun bala’i ya cinna hancin motar tasa ciki, daga yanayin yanda yayi parking kaɗai ya’isa nusar dakai cewa wanda ke cikin motar, cike yake da iskanci haɗi da zallan taɓara… Duk yanda naƙosa wanda ke cikin motar yabayyana nasamu damar ɗauko muku hoton fuska da surarsa amma abun yaci tura, domin dai shegen ƙin fitowa yayi bare nasamu ganinsa…….

15 minutes ya kwashe cas batare daya sanyo kansa waje ba, a hankali yasako ƙafarsa waje wacce ke ɗauke da tsadadden black canvas mai ɗauke da fararen igiyoyi a samanta, a hankali yagama fito da duka jikinsa daga cikin motar, Masha Allah !! shine abun dana furta lokacin dana gama sauke idanuna akan shi, kyakkyawa ne ajin farko, haɗaɗɗen matashi maiji da kyau haɗi da zallan kuɗi uwa uba hutu, fari ne tas banda sajensa dakuma tulin gashin kansa babu abun dayake baƙi ajikinsa,, saurayi ne mai cikar zati da kuma haiba, yana da cikar sura dakuma ƙaƙƙarfan jiki, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa mutum ne ma’abocin yin gym, kyakkyawar fuskarsa tana ɗauke da yalwatattun idanu masu ɗauke da brown eye balls acikin su, sannan kuma yana da dogon hanci gwanin burgewa, bakinsa kuwa ɗan ƙarami ne, mai ɗauke da ƴan saffa saffan laɓɓa light pink colour, gashin girarsa dana idanunsa a yalwace suke tamkar dai wanda yayi ƙari, wani irin haɗaɗɗen sajene yayi mawa fuskarsa ƙawanya, wanda kuma haddashi yaƙara wa fuskar tasa kyau, jikinsa kuwa gaba ɗaya a murɗe yake, sanye yake da White t-shirt fara ƙal ƙal da’ita, yayinda wandon jikinsa yakasance black pencil jeans wanda ya kamasa sosai, sai ƙafarsa dake sanye da black canvas, kunnensa kuwa saƙale yake da earpiece, da’alam dai ƙiɗan sa yake sha,, yayi matuƙar kyau sosai, fuskarsa tana ɗauke da wani asirtaccen murmushi mai ƙayatarwa da burgeqewa,, hanunsa riƙe da car key ɗinsa yadoshi wani haɗaɗɗen gini, dake cikin harabar babban gidan nasu, da’alama dai nanne babban falon gidan…..

Wata haɗaɗɗiyar Farar Mata wacce bazata wuce 47 years ba ke zaune akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon, tasha ado cikin wani irin danƙareren lace mai kyau da tsadar gaske, a zahiri idan kaganta zakai zaton batawuce 35 years ba, bakomai yasanya hakan ba fa ce tsananin hutu dakuma tsantsar jindaɗi da yabayyana ajikinta wanda hakan ya ɓoye asalin shekarunta,, iya gwala gwalan dake sanye a wuyanta haɗi da kunnenta, kaɗai ya’isa ya tabbatar maka dacewa itaɗin baƙaramar mai tarin dukiya bace…. Da wani irin fito yashigo cikin falon yanayi yana kaɗa makullin motarsa dake saƙale cikin yatsarsa manuniya,,

“Hello Mom “
saurayin yafaɗa cikin unigue voice ɗinsa…

Murmushi wacce aka ƙira da suna Mom tayi haɗe da cewa ” Your Well Come My Son”

Bai amsa mata ba saima zama yayi akan kujeran dake kusa da’ita yana mai yunƙurin cire takalman dake ƙafansa……

*((Wannan salon na dabanne My Fans kubiyoni domin jin wanene *SHU’UMIN NAMIJI !!* wayeshi ? menene halinsa ? wace gwagwarmaya za’a tafka ? Saikun biyoni zakusan komai, takunce dai Mrs Sardauna, kada kumanta wannan labarin yasha banban da sauran…. ))

(I’m sorry my fans Insha Allah zakujini da cigaban MENENE MATSAYINA ? a bubuwane suka shamin kaina shiasa kukajini shiru….)

10/October/2019

MRS SARDAUNA
????????????????????????????????????????

     *SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*

phatymasardauna
????Mrs Sardauna????

Dedicated To My Lovely Brother Khabeer

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
    *WATTPAD*

@fatymasardauna

Editing is not allowed ????

Chapter 2

“Inakaje ne wai ΖAID tunsafe rabon dana saka acikin idanuna ?” Mom tatambayeshi,

ɗan taɓe bakinsa yayi haɗe da cewa “aiki ne yaimin yawa a office, Labisat takawomin abinci.. ” yanakaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon…. Murmushi kawai Mom tayi domin tafahimci cewa Shu’umanci’n Zaid ɗinne yatashi….

Wani irin haɗaɗɗen gini naga Zaid yanufa, wanda yake can gefe da makeken lambun gidan, key yasanya haɗi da buɗe wata ƙofa, wani irin haɗaɗɗen falo mai masifar kyau Zaid yashiga wanda nake tunanin nanne mallakinsa, Masha Allah, falo ne daya amsa sunan sa falo, cike yake da abubuwan more rayuwa, kujerune irin leather sit ɗinnan farare ƙal ƙal zube a tsakiyar falon, yanda kujerun suke da haske kaikace ba’ataɓa hawansu ba,, tsakiyarsu kuwa wani haɗaɗɗen brown chanies carpet ne shumfuɗe mai taushin gaske, wasu irin ƙawatattun curtains brouwn colour ne suka taimaka wajen sake bayyana kyawun falon, duk da cewa bawani tarkacen kayan ƙyale ƙyale bane a falon, amma hakan bai hana falon yin kyauba, kallo ɗaya zakamawa cikin falon katabbatar cewa mamallakin wannan katafaren falo, baƙaramin ɗan gayu bane,, tundaga falo Zaid yasoma cire rigarsa yawurga kan kujera, yana tafiya yana cire wandon jikinsa ahaka ya isa cikin haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, saida yacire duk wani kayan jikinsa, kafun ya shige cikin bathroom ɗinsa, koda na leƙa cikin bathroom ɗinnasa saida nayi tsananin mamaki, wai ace banɗaki aka kashemawa kuɗi haka tamkar wani fadan shugaban ƙasa ? hmmm ALLAH yakyauta….

Fitowa yayi ɗaure da towel a ƙugunsa, yayinda jikinsa ke jiƙe da ruwa, gaban makeken dressing mirror ɗinsa dake cike da mayukan shafa haɗi da turaruka kala kala yanufa, saida yatsane ruwan jikinsa, kafun yasoma murza tsadadden lotion ɗinsa akan haɗaɗɗiyar fatan jikinsa,, komai dai cikin tsanaki yakeyi harya kammala,, riga da wando yakuma sawa, saidai wannan karon Blue colour garesu, sun kuwa matuƙar amsar jikinsa,, Wayarsa ƙirar iphone 11 pro max ne tasoma ruri alamar shigowar ƙira,, harta katse Zaid bai ɗauka ba, wani ƙiranne kuma yasake shigowa,, ɗan ƙaramin tsuka yaja haɗi da nufar inda wayar take,, Zee shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi haɗi da kara wayar akan kunnensa batare da yace komaiba, “Hello Baby !! zee tafaɗa cikin wata irin shaiɗaniyar muryarta, ɗan ƙaramin murmushi yayi haɗe dacewa “Ya’akayi ne Zee ?” jin abun dayace yasanya Zee sake gyara zama haɗe da ƙara kashe murya tace ” Ina guest house ɗinka pls Baby kazo… ” Okay ” yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar yacusa cikin aljihun wandonsa,, knocking ƙofar ɗakinnasa akashiga yi, cikin muryan faɗa faɗa yace “Uban waye ke bugamin ƙofa kamar yasamu falon Ubansa ?” Labisat dake tsaye riƙe da tire ɗin abinci ahanunta, taturo baki gaba haɗe da cewa “Bro nice fa, abincinka nakawo ma ka” tsaki yakuma ja haɗe da cewa “Oya maidashi fita zanyi, innadawo nazo naci ” sumi sumi haka Labisat tajuya da abincin…..

Wata haɗaɗɗiyar Blue car yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan…..

Kaitsaye G.R.A yanufa inda acan guest house ɗinshi yake, yana zuwa maigadi ya wangale masa gate yacusa motar tasa ciki……

Jin tsayuwar motar shi yasanya Zee tashi da sauri tanufi hanyar fita daga falon, da sassarfa taje tafaɗa jikinsa haɗe da goga masa breast ɗinta, cikin kirsa tace ” sannu da zuwa babyna,, wannan munafukin murmushin nasa yayi mata haɗe da cewa “Ƴan Mata yakike ?” “lafiya ƙalau ” tabashi amsa daidai lokacin dasuka ƙaraso cikin katafaren falon,, janyeta yayi daga jikinsa haɗe da zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon ” Kawomin ruwa ” yafaɗa daidai lokacin daya cire rigar jikinsa,, cike da kwarkwasa Zee tamiƙe haɗe da ɗauko masa goran ruwan faro acikin friedge,, karɓa yayi yakafa bakin gorar abakinsa, tas yashanye ruwan haɗi da cilli da goran ruwan hanu yamiƙa ma Zee akan tataho gareshi, aikuwa dama jira take dan haka taɓalle duka aninayen gaban rigarta, take manya manyan breast ɗinta suka bayyana,, kansa yanutsa acikin breast ɗinta, bayan yayi mata masauƙi akan cinyarsa, cikin salo yacire mata gaba ɗaya rigar dake jikinta, hatta breziya bai barmata ba, bakinsa yaɗaura akan nipples ɗinta, yashiga yi musu wani irin kalan tsotso yayinda hanunsa, ke kan bayanta yana shafawa ahankali, tuni Zee taƙara rikitasa da salonta, ɗaukarta yayi caɗak suka nufi bedroom, kwantar da ita yayi flat akan gado, bayan yacire komai najikinta, yanda yake wasa da’ita kaɗai yasanya Zee ficewa acikin hayyacinta, domin Zaid ƙwararrene awajen iya sarrafa mace,, cikin mintuna ƙalilan Zaid da Zee suka faɗa duniyar ashsha duniyar Mazinata, (Ya Allah kakaremu daga aikata Zina Ameen)…….

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button