KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Girgiza kai kawai yayi tare da shigo wa ciki.
Wurin break fast ne mami taje neman sa ta tadda bashi shine Dady ke samar mata da akan idon shi ya fita.
Jikin tane yayi sanyi, RAHAMA ma tashi tayi gaba d’aya tabar dining d’in mijin ta yabi bayan ta .
Mamin kanta kasa karyawan tayi, kiran layin sa tayi bai shiga, don haka ta buga uban tagumi hawaye na kwaranya akan fuskan ta.
Dady ya matso kusa da ita tare da bata baki sannan tabar kukan.
Auwal ko daga gida asibiti yayi, koda ya bud’e office d’in sa kwanciya yayi kawai tare da runtse idanun sa.
Wanene Auwal??????
Asalin sa, ko nace tushen sa.
Alhaji Bashir da malam Isma’il ma’kotan junane, kuma aminan juna. Idan ba wanda yasan su tuntuni ba zai tsammanin ‘yan uwan junane, don yadda suke mu’amala ya wuce ka kira su da aminai, domin sun zama ‘yan uwan juna.
Yadda mazajen suke haka ma matan su.
Alhaji Bashir mutumin kirkine, yana da arzi’ki dai-dai gwargwado, arzi’kin sa bai rufe masa ido ba sam, yana matu’kar taimakon talakawa, yana daraja ma’koci, matar sa d’aya itace HAJIYA Umma, macece mai kirki da zumun ta.
Sun d’au tsahon lokaci Allah bai basu haihuwa ba, tun suna damuwa har ya zamana sun fawalawa Allah.
Watarana suna zaune abokan junan nan suna fira, sai Bashir ya dubi Ismail cikin damuwa yake cewa” na rasa wani laifi nayi wa ubangiji na” sai kuma yayi shiru.
Sai Ismail yace” d’an uwa mai yasa kace haka?” numfasawa yayi sa’an nan yace” wallahi rashin haihuwan nan na matu’kar damuna, ka duba tsahon shekaru goma sha da auren mu amma har yanzu shiru bamu ta’ba ko ‘bari ba, ga fitinan dangi”.
Murmushi Ismail yayi tare da cewa” bai kamata kasa damuwa a ranka ba, duk bawa bai wuce jarabawan ubangiji ba, wannan shine jarabawan mu nida kai, saboda haka kar mu gaji, mu cigaba da addu’a Allah na sane damu, Allah ya bamu ikon cin jarawan nan”.
Magagganu mai dad’i Ismail yayi masa, maganan ta shige sa, don yayi aiki da ita.
Bayan wata biyar da maganan su sai gashi Allah ya bawa matan Bashir ciki, zoka ga murna wurin iyalan nan
Bayan wani lokaci ta haifi d’anta mai tsanani kyau aka samasa suna KABIR.
KABIR nada shekaru biyu ta sake samun ciki, wannan karon itama matan Ismail ta samu ciki. Sai dai wannan cikin yazo ma matan Bashir wani iri domin yana bata wuya sosai.
Kullum cikin ciwo, ranar da ta haihu na biyu tace ga garin ku nan.
Wannan karon ma namiji ta haifa, Bashir yayi kukan ba’kin ciki sosai malam Ismail ne yaba shi baki yazo har yasama zuciyar sa salama.
Bayan rasuwan ta da kwana uku yaro ya fara neman abinci, hankalin Bashir ya tashi sosai.
Fara zaga dangi yayi don neman mai shayar masa da yaro ya biya amma daga nasa har na matar sa anrasa.
Don mursisi suka’ki, damuwa yasa duk yabi ya zaganye, ga jariri anrasa mai kar’ba ga kuma yayyayye babu mai kulwa dashi.
Ismail ne ya share masa hawaye ya kar’bi jaririn ya bawa matar Amina ta had’a ta shayar dashi tare da yaron ta Muta’ka don itama bata dad’e da haihuwa ba.
Tsakanin su kwana biyu, yayi farin ciki matu’ka sosai gaya, don haka zumuncin su ya’kara ‘kaimi.
Malam Ismail bai tsaya nan ba har da KABIR ya kar’ba yaba wa matar sa ta cigaba da kulawa da nata da nasu bata ta’ba nuna banbanci ba sam.
Bayan shekaru shida yara su uku maza sun taso kusan kai d’aya cikin gata da soyayyar iyayen su uku.
Alhaji Bashir ya had’a su kaf ya sasu makaranta boko, na addini kuma ko dama malam Ismail na koyar dasu shida matar sa.
Yarane kyawawa, ana haka umma ta sake haihuwa kamar yadda suke kiran ta, macece aka samu zokaga farin ciki wurin iyayen da kuma yayyin yarinyan, ranan suna yarinya taci suna MARYAM.
MARYAM ‘yar gata ‘yar gaban goshin wannan ahali, kowa bai son kukan ta.
Shekaru uku da haihuwa MARYAM aka sake haihuwan ‘ya mace ita kuma Bilkisu .
Yara sun taso cikin gata da soyayya ga tsantsan tarbiya.
Bayan wasu shekaru Bashir ya kwanta ciwo, hakalin Ismail da yara yayi mugun tashi.
Haka ya kaisa asibiti, haka aka d’au tsahon lokaci ana jinya maimakon sau’ki kullum abin ‘karuwa yake.
Kawai sai shima yace ga garin ku nan, Ismail yayi kuka, yayi ba’kin cikin rashin d’an uwan sa.
Kafin ya rasu ya basa amanan yaran sa, kuma ya kar’ba.
Haka Ismail ya cigaba da kulawa da yaran nan bisa gaskiya da amana, kuma komai da zai musu da dukiyan sa yake, bai ta’ba ta’ba nasu ba.
Sai dai yana jujjuya musu, a haka yara har suka girma bayan gama karatun samarin nan uku sai suka fara aiki.
Baba Ismail na cigaba da kulawa musu da dukiyan su, yayi yayi suyi suwanci fir suka’ki waisu basu shi’awa.
Lokacin ne kuma KABIR ya fara soyayya da MARYAM, shima ‘kanin ba’a barsa a baya ba ya fara shima yace yana son Bilki.
Mukutar dai bai sami budurwa ba shi.
Baban nasu yaso abin baiso ba saboda surutun mutane.
Amma yara sun kafe, ba don yaso ba aka saka ranan auren su.
Gidan ‘kerarre suka tamfatsa a Abuja wuse. Da yake nan dukan su suka sami aiki.
Bayan biki suka tare da matan su.
Shi kuma Mukutar a Abia yake aiki.
MARYAM ta haihu auren su da shekaru biyu, bayan nan ta ‘kara haihuwa kuma duka maza.
Rashin haihuwan Bilki na matu’kar damun zukatan su, haka yayi bala’in ta’ba zuciyar miji da matan nan saboda Allah ya jarabesu da masifan son ‘ya’ya.
Duk da yaran yayin su babu shamaki a tsaknin su amma suna masifan son na kansu.
Shekaru goma baya MARYAM ta sake haihu wannan Karo mace ta haifa.
Hakan sai da zuciyar Balki ya buga, haka sukai fama da ita suna ta jinyan kusan shekaru biyu.
Koda MARYAM ta gano damuwa ‘yar uwan ta sai tabata ‘kautan ‘yar RAHAMA.
Bilki tayi farin ciki sosai, a lokacin ne aka canzawa mijin ta wurin aiki zuwa Kaduna.
Haka suka d’unguma suka tafi da ‘yar su.
RAHAMA ta taso cikin tsanani soyayya da gata, ba’a son damuwa ta haka ma fishin ta.
Bilki na matu’kar ‘kaunar RAHAMA kamar ranta.
Allah bai basu haihuwa ba sai da RAHAMA takai shekara goma shara biyar.
Zoka ga farin ciki wurin su, RAHAMA ma ba’a barta a baya ba murna take sosai za’a mata ‘kani.
Komai taci ta rage ko ta samo sai tace” momy gashi kibawa ‘kanina”.
RAHAMA har tafi su son cikin nan.
Bayan wata tara Bilki ta haihu, ta haifi santalelen d’anta Auwal.
Tunda ta haifi Auwal ta kama ciwo, Auwal bai shekara ba ta rasu.
Batun zaiyana muku irin ba’kin cikin da wad’an ahali subakyi ‘bata bakine.
Mutum ya ta’ba zuka tansu sosai, bayan wata biyar aka ‘kara musu jarabawa da mutuwan mijin Balki AL’kasim.
Sunyi shekaru da yawa kafin ciwon nan ya warke a zukatan su.
Amma na RAHAMA shine ‘kila ajalin ta, don itama kawai za’ace akaima wa mutuwa.
Wannan dalilin ne Auwal ya zamo d’anga tan kowa.
Musamman mutane biyun nan RAHAMA, mami.
Saboda soyayyar da RAHAMA kema Auwal yasa da takai minzalin aure ta’kiyi saboda bata son a rabata da Auwal.
Sai da ‘kar tayi sai da Wanda zata aura ya yadda da zaman gidan su tukuna.
Wannan shine ta’kaitaccen tarihin su.
Comments & share pls????????
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????
‘KAUYEN ‘YAR KADDE
????????????????????????????????
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????
we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all………DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO
Wallahi kuna matu’kar bani haushi, mutum baiji wahalan muku typing ba. Amma ku kuna jin ‘kashin kuma mutum comments. Sai mutum bai ba a isheshi da tambaya, to billahillazi nagaji, idan baku so babu dole kusanar dani sai na aje kawai ba nai ta ti’kin banza ba????. Inga gyara daga wanna idan ba haka ba na aje, kuma wanna ma badon ku nayi ba, saboda masu mun comments nayi, idan baku gyara ba ina iya bari kuma ko kin tambaya idan kikaji shiru bazan ko kalle kiba bare kisa ran ansa???? kuyi ha’kuri idan maganana ya ‘bata muku rai gaskiya ta na fad’a????????????????????????????????