KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Iyayen sun ga rashin yuwan haka da dace wan abin.

Amma angon yace babu damuwa da haka Aisha ta warke aka cigaba da shagali, Joy taso ‘kin yadda amma ganin halin da ‘yar uwan ta take ciki yasa ta amince.

•••••••••••••••••

Rana bata ‘karya, wanna haka yake domin yaune aka shaida d’aurin auren Aisha da Abudurrahaman.

Ayi cikin kwanciyan hankali kuma a yau d’ine daga d’aurin aure suka wuce da amarya.

Sai dai muce Allah basu zaman lafia.

                                  -------------------------------

Zaman Joy a Abuja….

Zama ne cikin jin dad’i da walwala, bata da matsalan komai da kowa.

Sai dai tunanin Auwal da take lokaci zuwa lokaci, maganan tafiya service d’in ta na tashi KD suka tura ta, sai ta nuna bata shi’awan can.

Saboda haka sai Abdurrahaman ya mata cuku cuku aka barta a Abuja, don haka bata da matsalan komai.

Don sosai Aisha da mijin take ‘ko’karin faran ta mata da sata farin ciki.

Kullum cikin tarairayan ta suke, itama tana ‘ko’karin kyauta ta musu, tana bama mijin Aisha girma sosai tamakar wanta ta d’auke shi.

Zaman ta a Abuja ne Aisha tayi mata sha’awan musulunci, nuna mata tayi bata da ra’ayi. Don haka babu wanda ya matsa mata akan hakan.

Joy ta samu kwanciyan hankali don haka ta’kara wani mugun kyau.

Samari ko sai dai bata fita ba, ko kallo basu ishe taba, sabgan gaban ta kawai take, a haka har ta kammala bautan ‘kasan ta cikin kwanciyan hankali.

Don haka sai ta fara zancen aiki babu ‘bata lokaci Abdurrahaman ya nema mata aiki a wani aisibiti babba ta fara tafiya.

Aisha taso itama ya samun mata, amma yace shi bai da shi’awan iyalen sa da aiki kome take so ta fad’a masa zai mata.

Don haka sai ta bu’kaci jari, bai ko jah ba ya bata ta fara kasuwanci.

Watarana Aisha da mijin ta na zaune ranan weekend ne har Joy na gida, Africa TV3 suke kallo su biyu sai ga Joy ta fito, shirin yara ake a lokacin.

Zama tayi cike da shi’awan yaro d’an ‘karami dake karatun al’qur’ani mai girma.

Murmushi kawai take, bata tashi ba har sai da aka cire shirin.

Tun daga wanna ranan shirin nan bai wuce ta. Yawan kallon shirin yasa taji tana matu’kar son musulunci don tana shi’awan itama ta iya karatun al’qur’ani.

Rana tsaka ta samu Aisha har cikin d’akin ta lokacin Abdul bashi ya tafi wurin aiki ita kuma night duty take da.

“Besty har kin tashi?” tace da ita lokacin da take shigowa.

Bata bata ansa ba illah ‘karisowa da tayi ta zauna kusa da ita fuskan ta d’auke da murmushi.

Ri’ko hannun ta tayi tare da cewa” Aisha inason na musulunta” daga haka ta tsuke bakin ta.

Waro ido Aisha tayi tare da cewa cikin tsantsan farin ciki” da gaske my besty?” d’aga mata kai tayi.

Don haka Aisha ta rugume ta cikin tsantsan farin ciki, har da hawayen ta.

Babu ‘bata lokaci Aisha ta kira mijin ta ta sanar masa, babu ‘bata lokaci yace suje wurin limamin anguwan su.

Koda sukaje ba’a wani ‘bata lokaci ba ta’kar’bi musulunci.

Aisha ta za’ban mata Suna Fatima, wani irin natsuwa da kwanciyan hankali taji yana wanzuwa a gare ta.

Ga wani irin farin ciki da takeji.

Fatima wanda suke kira da (Zarah) tana d’aukan abuabuwan addinin musulunci da ake koya mata fiye da tunanin ku.

Babu abinda tafiso a ciki rin Qur’ani, don haka ta mai da hankali sosai tana koya, saboda ‘kwa’kwa da kuma son abun.

Cikin wata hud’u tayi sauka, zo kaga murna da farin ciki wurin ta da uwan uba Aisha, don haka gaga rumin walima aka shirya mata.

Sai dai abinka da boko da kuma ansaba shigan ‘kananun kaya nana sai ma wanda ya ‘karu sai dai na d’an d’aura ‘karamin mayafi.


Fatima mai farin jinine tun tuni balle ta musulunta don haka abin sai ya ‘karu.

Maza da mata kowa nason ta kulasa tayi mu’amala da ita.

A haka ne tayi wata ‘kawa a ma’kotan su mai suna Husna, Husna yarinyan nacin masifa. Kad’aci ke damun ta, da yake basu dad’e da tare wa ba. Kuma su biyu ne kawai ‘ya’yan gidan daga ita sai wanta, da wannan dalilin yasa take shige-shigen ma’kota. Shine Allah ya had’a ta da Fatima taji ta Shiva ranata, sai ta maida gidan su faty ma kamar nasu tai ta shige mata. tun Fatima na ‘kalleta har sai da yazo suka fara ‘kawance domin sam bata da zuciya.

Tana zuwa gidan su Zarah sosai, amma ita dai-dai da rana d’aya bata ta’ba shiga gidan nasu ba.

••••••••••••••••••••••

“Don Allah ki rakani yau mana” cewa Husna suna zaune kan gadon Zarah bayan sun gama cin abinci.

“Kiyi ha’kuri gaskiya babu inda zani” cewar Zarah.

“Haba Zarah kullum nazo miki da bu’katata sai ki ‘kimin, bansan mai yasa kike min haka ba. Wallahi ba kyau wula’kanci, har yanzu kin’ki sakin jikin ki dani. Wallahi Faty ina matu’kar ‘kaunar ki har cikin raina, keko kin’ki sani a zuciyar ki ko kad’an”.

“Meyasa? wallahi hakan bai dace ba”.

” Allah baki ha’kuri tunda baki sona baki aminta dani ba nayi nan nagaji haka, kullum ni kenan nan nai ta bibbiyan ki kamar wata sarki to nagaji ba dole ‘kawance” tace cikin fushi tare da mi’kewa idon ta cike da hawaye don tana matu’kar ‘kaunar Zarah.

Amma ga dukan alamu ita bata son mu’amalan su.

Kamo hannun ta tayi tare da cewa” idan ba zamu dad’eba muje don inason naje wurin aiki 2pm dai-dai”.

Dawo wa tayi tare da rungume ta tana maijin farin ciki.

“Ki muje idan ba haka ba na fasa”.

” A’a muje hajiya ta mai ajin tsiya sai har dani za’a rin’kama wa?, gidan su hayati zani Maman sa ke nemana kinsan biki ya taso sauran sati uku, zani na kur’bi tsumi, kai matan nan Allah ya samata son d’an nan kamar shikenan mata”.

“Bata gajiya sam wurin gyrani yanzu haka sati mai zuwa zamu India a min gyara na musamman, wanna kuma yayar sace ta d’au nauyi”.

Ta’ba baki nayi tare da cewa” muje ni kada ‘batan lokaci na’ki zuwa kimin kuka”.

“Don idan na biye miki takan mutumin da bai San kinayi ba zamu iya kaiwa dare”.

” Wallahi ni har mamaki kike bani ace wai macce kamar ke ki mutum ma mutumn da Sam bai ra’ayin ki, wallahi ko shine autan maza sai haka” ta ‘karisa tare da sakin tsaki.

“‘Karin kayan takaicin bai zuwa sai dai ke kije gidan su ku zanta, anya wannan auren za’a sami kwanciyan hankali kuwa?”

Murmushi mai ciwo Husna tayi tare da cewa” baza ki gane ba yarinya gayen ya had’u, yadda kika san ba mutum ba saboda kyau, ni tunda uwata ta haifeni ban ta’ba ganin kyakkyawan mutum irin saba”.

“Oh really?”

“Allah kuwa idan kika gansa zaki ce na gaya miki, don gayen ‘karshe ne”.

Ta’ba baki tayi tare da girgiza kai ina mama kin ta, sai tace” muje fah kada na ‘bata lokaci kije ki fasa rakani”.

Fito wa daga cikin d’akin Joy sukayi suka mufi na Aisha kwance take tana duba wani littafin.

Sallaman su yasa ta kauda fuska daga littafin tare da zuba musu ido tana mai ansa musu sallaman.

Tashi tayi daga kwancen tana mai cewa” sai ina kuma ‘yan mata?”

Husna tace” anty Aisha zata rakani wuse ne gidan ‘kawar momy”.

“Hummmm kice dai gidan siri kan mu” murmushi kawai tayi tare da cewa” sai mun dawo”.

“Besty baki sallameni ba” cewar Aisha ganin Husna ta jata zasu bar d’akin.

Murmushin ta mai burgewa ta jefe ta dashi tare da cewa” sai mun dawo to” daga haka suka bar d’akin, ita kuma ta bisu da addu’a dawo wa lafia.

A compound d’in gidan suka tsaya Zarah tace” jeki d’ako motar ki ina jiran ki a nan”.

Shagwa’be fuskan ta tayi tare da cewa” don Allah my Zarah yau mu fita a sabon motar can ta’ki”.

Hararan ta tayi tare da cewa” na’ki” marairai ce mata tayi, ba don taso ba haka tasa aka fito mata da motar suka Shiga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button