KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tare da barin gidan, bata son hawa motar ne saboda wani saurayin ta mai nacin tsiya ya sayo mata.

Motar babu ‘karya ta had’u.

Husna ke driving d’in sai faman santin motar take.

Wani tamfareren gida suka shiga, parking Husna tayi Tare da kallon Zarah tace” Zarahty ya kikaga gidan surukan nawa?” don taga tun daga get d’in gidan take kallo har suka shigo gidan.

Yatsina fuska tayi tare da cewa” gidan yayi”.

“Muje to” tace tare da ‘ko’karin fita daga cikin motan.

Rufe motar Suka yi tare da shiga ciki, sallama sukayi a bakin ‘kofan babban falon gidan, shiru babu ansa.

Don haka suka shiga daga ciki, part d’in mami suka nufa, a nan suka tadda mamin. sallama sukayi ta ansa fuskan ta d’auke da fara’a.

Shiga sukayi har gaban ta suka gaida ta, ta ansa idon ta nakan Zarah da tunda ta gan ta taji wani irin fad’uwan gaba.

Idon ta nakan Zarah tace ” Husna ‘kawar kice wannan?”

“Eh mami” tana murmushi tare da kallon Zarah taga kanta a ‘kasa kamar wata muna fuka.

Mami tace” sannu ko” take ce da Zarah.

Ansawa tayi sai mamin tace” tashi ku zauna a cushion mana, nasha gaya miki Husna kibar irin haka bakiji”.

Tashi sukayi Husna na murmushi tace” Allah huci zuciyar mamin mu baza mu’kara ba”.

“Allah sa, ya momyn naki?”

“Tana nan lafia qlau, tace a gai daki”.

” Masha Allah, bari a kawo muku abinci” .

“Mami mun ‘koshi” mamin tace tana hararan ta” dama nace baki ‘koshi bane? kullum dama ke a ‘koshe kike zuwa gidan iyayen naki”.

“To yau sai kinci” tace tana ‘ko’karin mi’kewa. Cikin murya mai dad’in amo da sauraro cike da natsuwa Zarah tace” mun ‘koshi mami, don abinci muka gamaci muka fito”.

Gaban mami ne ya sake fad’i dajin wannan muryan, tsayawa tayi cak tare da waigo wa tana kallon gefen da Zarahn take.

Had’a ido sukayi still fad’uwan gaba ne, murmushin ya’ke mami ta sakin mata tare gyara zama.

“Husna amma ‘kawar nan naki ba ‘yar nan bace ko?”

Murmushi Husna tayi tare da cewa” ‘yar nasarawa ce, amma tana zaune a ne a garin nan”.

“Oh sannu” tace da Zarah.

Ansawa tayi dai-dai nan RAHAMA ta shigo Auwal a bayan ta da sallama d’auke a bakin su.

Amma na RAHAMA ne ya fito, na Auwal kuwa sai idan ka kalli bakin sane zaka gane yayi sallama.

‘Karisowa inda su mamin ke zaune tayi, shiko dodon mutane tsayawa yayi daga bakin ‘kofar shigowa yana mai cewa” mami mun dawo zan tafi office sai na dawo” daga haka ya juya.

RAHAMA ko zama tayi tare da cewa” wassh mami nagaji walla…………” bata samu zarafin ‘karisawa ba sakamakon fuskan Zarah da tagani.

Idon ta da ‘kwallan da ya taru cikin sakonni tace” mami kina ganin abinda nake ganin kuwa?”

Mami tasan me take magana akai amma tayi mata shiru.

Taso wa tayi tazo ta dur’kusa kusa da mami tare da kamo hannun ta tana mata nuni da Zarah tace” mami anty ce fah nake ganin, sai dai kuma jikin ta ya nuna na yara ne, dama idan ka mutu ka dawo yaro kake koma wa?”

Shirun mami yasa tace lokacin hawaye ya fara zuba” mami anty ce ko?… Itace ta dawo gare muko? dama ina mafarkin ta mami bata mutum ba, kullum haka take gaya min a mafarki, tana cemin zata dawo. Zata dawo ta rayu da Auwal d’in ta “.

” Mami taso, taso” tace tana janta, fizge hannun ta tayi tare da cewa cikin tsawa” RAHAMA ba ita bace, kina haukane? a ina kika ta’ba ganin mutum ya mutu ya dawo? Kuma ma idan itace sai tazama yarinya? kin manta tana da d’an da ya isa aure da yayi da wuri idan Allah ya albarkaci auren da yaran sa biyar ko hud’u”.

“Idan kina mafarki ne ki farka don ba ita bace” mami ta ‘karisa idon ta na zubar da hawaye .

Tun da suka fara zancen su tsoro ya shigi Zarah, don haka mi’kewa tayi ba tare da ta kalli inda Husna take ba zata fita.

RAHAMA tace” mami kalli zata gudu anty don Allah ki dawo kada ki barmu muna tsananin bu’katar ki.. Munyi kewan ki sosai. Ga habibin ki zaiyi aure kinga ga matar da zai aura nan, Husna jeki, jeki ga mahaifiyar mijin ki can”.

Kan Husna ya ‘kulle shiru tayi tana binsu da kallon musamman ma RAHAMA da take tunanin ta haukace.

Mami ne ta tsinke RAHAMA da wani uban mari mai zafi tace” ki farka RAHAMA ba ita bace, wannan da kika gani tare da Husna suka zo. ‘Kawar tace”.

Marin ya shige ta sosai, natsuwa tayi tana sauraron mami da ta cigaba da cewa” kama ne RAHAMA, ba’a mutuwa a dawo”.

Matso wa tayi kusa da mamin tare da rungume ta, ta fashe da matsanancin kuka.

Rarrashin ta mami ta kamayi ta dad’e tana rarrashi kafin ta fara a jiyan zuciya.

Mi’kewa Husna tayi tabi Zarah da tai gaba, koda ta fito bata kuma ga motar ta a ajiye.

Shiga motor tayi ta fad’a tare da barin gidan…….

Inason idan nayi kuskure fan’s d’ina su gaya mini, nayi kuskure a page d’in baya, wata tamin magana ta PC kuma naji dad’in hakan sosai, don har ga Allah na sani kuskure ne aka samu.
Kuskure kuwa shine da nace bayan kakan Auwal namiji da matar sa ta mutu kakan sa na wurin uwan ya kar’bi jaririn da matar abokin sa ta haifa ya bama matar sa ta had’a ta shayar dash tare da jaririn ta da suka haihu tare, to kunga idan ta shayar dashi babu aure a tsakanin ‘ya’yan su don addini ya haram ta hakan, sorry to sai ba haka naso rubutawa ba akasi aka samu. Madara ta basa ba nono ba.

Don gara, kuskure ko shawara????????08105039568 ‘kofa a bud’e take ngd, and mata kawai.

COMMENTS
&
SHARE
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

we are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all………DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????4⃣1⃣➡4⃣2⃣

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Tafiya nake ba tare da sanin inda nake jefa ‘kafata ba. jefa ‘kafa kawai nake. Har na kusa barin layin sai ga Husna, parking tayi tare da fitowa daga cikin motan, bata ce dani komai ba illah jan hannun na da tayi. Bata saken hannun ba har sai da ta danganani da motar, zaunar dani tayi tare da rufe sead d’in ta zagayo mazau nin ta ta shiga tare dawa mota key muka bar wurin.

Tafiya muke babu maice da kowa komai, don kowa na fama da tulun tunanin a cikin ransa.

Har muka zo gida tai parking, sake jana tayi ta fito dani tare da shigewa dani cikin gida, niko binta kawai nake kamar ra’kumi da akala.

Babu kowa a falon, don haka d’aki na tayi dani, zaunar dani tayi a gefen gado tare da barin d’akin ba tare da tace dani komai ba.

Niko ina nan zaune inda ta barni har na tsahon wani lokaci, tunanin nake shin ma wai meye asalina?, waye ubana?, ina dangin mamana da na babana suke?

Anya ma ‘yar halasace ni?

Tun da nake tunanin hakan bai ta’ba zomin ba sai yau, kuma mama bata ta’ba bani labarin wani nawa ba. Don haka yau ina da bu’katan son sanin meye asalina?

Farko ma dai waye ubana?, ban ta’ba tambaya ba tunda nake, don na taso na ganni tare da uwata ce kawai.

Ban ta’ba ganin wani yazo wajen ta da sunan d’an uwan ta kona babana ba.

Kai anya kuwa? da dai sake, da kawai alaman tambaya.

Dagani sai ita kawai, babu dangi ko guda d’aya.

Akwai sanda aka ta’ba min gorin asali amma ko kad’an banji wani abu akan haka ba.

Don da naji wani abu dana tunkari mama da maganan tun a lokacin, da yake lokacin bansan ciwon kaina ba.

Na d’au lokaci mai tsayi ina ta faman tunanin da zancen zucci, wanda har kaina ya fara min ciwo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button