KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tashi nayi na shiga toilet tare da sakin ma kaina ruwa, hakan yasa naji d’an sanyi kad’an.

Don haka sai na fito bayan na cire kayan jiki na tare da d’aura towel a jiki na.

Goge jikin nayi ba tare dana shafa komai ba na bud’e wardrop na d’au dogon riga mara nauyi nasa .

Kwanciyan nayi tare da cigaba da tunani na.

A haka barci ya d’auke ni, ranan na manta da zancen wani office.

Don duk ringing d’in da waya ta take tayi banji ba Sam.

Bani na tashi ba sai bayan la’asar, kuma ma Aisha ce ta shigo ta tasheni.

Mi’ka nayi da sallati, sa’annan nayi addu’an tashi daga barci tare da kallon Aisha itama ni take kallo.

Murmushi tayi min tare da cewa” yaushe kuka dawo?” ya mutsa fuska nayi tare da cewa” d’azu”.

“Shine koki fad’an kin dawo? ina can inta faman tunanin har yanzu baku dawo ba. Tunanin zuwa d’akin nan nayi shine na shigo na cima kina barci, gashi la’asar ta wuce bakiyi salla ba. Sai ki hanzar ta”.

Sauke ‘kafafuna nayi a ‘kasa ba tare da nace da ita komai ba.

Toilet na nufa, wanka nayi tare da d’aura alwallah na fito.

Tana nan zaune inda na barta a bakin gado, wuce wa nayi na d’akko wani dogon riga ba’ki na zirah tare da saka hijabi.

Shimfid’a dadduma nayi tare da fara sallah, cikin natsuwa take komai nata.

A haka ta gaba tar da sallan azahar da la’asar, duk Aisha na kallon ta har ta idah tayi addu’a.

Bayan ta gama sai ta jingina kanta a jikin gado tare da rintse ido, hawaye taji yana son zubo mata matsewa tayi batai ba.

Sakkowa daga gado Aisha tayi tare da zama kusa da Zarah dafa ta tayi tare da cewa” besty meke damun ki?”

Shiru tayi bata bata ansa ba, “besty ina magana kinmin shiru”.

“Mai ya faru?” bud’e runannun idanun ta tayi. Kallon Aisha tayi tare da cewa” babu komai”.

Ganin yadda idanuwan nata suka rine ya’kara tayar ma Aisha da hankali, don haka.

Cikin lallashi Aisha tace” yanzu bazaki sanar min da damuwan kiba ko? haba my Zarah, don Allah gaya min, ni kad’ai kike da duk fad’in garin nan, idan baki gayan ba waza ki fad’a mawa? idan kuma so kike nai kuka kuma shikenan “.

Ta’karisa tana majin damuwa a zuciyar ta.

” Aisha kin ta’ba ganin baba na? kin sanshi? ko kin ta’ba jin labarin sa? wai ma anya ina da uba?” tace hawaye na zubowa daga cikin idanun ta.

Sakin baki Aisha tayi da mamaki tana kallon ta har ta idah zancen ta.

Tace” wani shegen yace baki da uba? eyeh!” .

“Waye? nace waye?” Aisha tace cikin masifah.

Kamo hannun ta nayi tare da cewa” ba kowa, babu wanda yace bani da uba. Nine nace ma kaina, domin ban ta’ba ganin uban nawa ba, ban kuma san asalina ba shiyyasa nace haka”.

“‘Karya kike akwai dalilin da yasa kika ce haka ban yadda da abinda kikace ba, idan kince haka mai yasa tuntuni baki ta’ba zancen nan ba sai yau da rana tsaka?”

“Husna ce tamiki gorin uba ko kuma wani matsiyaci ne?”

Murmushi nayi tare da cewa” nace miki babu kowa, wallahi babu wanda ya tambayeni ubana”.

Ganin ta’ki yadda da zancen tane yasa ta kwashe abinda ya faru a gidan su surukan Aisha ta fad’a mata, ta’kara da cewa” Allah jikina na bani inada ala’ka dasu”.

Shiru Aisha tayi don bata san mai zatace ba.

Don gaskiya bata san mahaifina ba, don ‘kawayen ta na ‘kauye sunsha ai bantani a gaban ta bata ko kulasu sunsha cewa ta rabu dani donni shegiyace bani da uba.

Don iyayen su sunce da ciki uwan na tazo garin ita da wata ‘kawanta kuma bata wani jima ba ta haifeni, ana tunanin tayi cikin shegene iyayen ta suka koro ta.

To me zata ce?

Ganin Aisha tayi shiru yasa tace” gobe zan tafi keffi insha Allah, don inason nayi magana da mama ina son sani ni wacece? meye asalina? tun kafin lokaci ya kuremin”.

Numfashi Aisha ta sauke tare da cewa” Allah kaimu, idan Hubby ya dawo sai na mai magana idan yaso sai mu tafi tare”.

Gyad’a mata kai tayi ba tare da tace komai ba.

Zama sukayi shiru-shiru babu mai magana a cikin su, kowa tunani ne fal a zuciyar sa.


Husna bayan tabar gidan su Zarah gidan su ta shiga, zuwa tayi har d’akin momyn ta ta same ta.

Momyn nace da ita” har kun dawo?” ita kuma nace da momyn” momy dama ba Hajiya MARYAM bane ta haifi Auwal? “

Da mamaki uwan ke kallon ta, sai tayi murmushi tare da cewa” ba ita bace ko momy?”

“Injiwa ya fad’a miki haka dan ubanki?”

“Su da kansu”.

” Da kansu kamar ya?” tace fuskan ta cike da mamaki.

Nan Husna ta kwashe abinda ya faru tasanar mata.

“Eh hakane ba itace ta haifesa ba”.

” To momy waye mahaifiyar sa?”

“‘Kanwan MARYAM d’in Balki itace ta haifesa, yayin da ‘kanin mijin MARYAM d’in yanka sance shine uban Auwal d’in”.

” To ina suke momy?”

“Bakiji mai RAHAMA take cewa ba? koke da’ki’kiya ce? to ta rasu tun Auwal na jariri”.

” To mahaifin nasa fah?”

“Ke ubanki tashi ni duk kin isheni da tambaya, maza bar nan wurin”.

Cikin sanyin jiki ta tashi tabar wurin.

‘Dakin ta dake kusa dana momyn ta ta bud’e ta shiga, zubewa tayi a kan cushion tare da buga uban ta fumi.

Tace” meye al’kansu da Zarah? tabbas akwai dangan taka na jini a tsakanin su, domin ban ta’ba lura ba sai yau akwai kama a tsakanin Zarah da Auwal kama ma na’kin ‘karawa. Sai dai tafi Auwal hasken fata, shi kuma ya fita kyau”.

“Tabbas akwai cakwakiya”………….


Bayan natsuwa ya zoma RAHAMA ne sai tace da mami cikin sanyin murya” mami anya kamace kawai tsakanin anty da yarinyan nan babu wani abu ba bayan shi?”

“RAHAMA kibar maganan, domin bamu da wani al’ka da yarinyan nan, domin daga jihar nasarawa ta fito kuma bamu da kowa namu dake can. Ikon Allah ne kawai” daga haka tayi shiru.

RAHAMA dai bata wani gamsu ba tace” anya kuwa mami? a dai bincika, don wannan kaman ya wuce misali”.

Shiru mami tayi ba tace komai ba.

Ganin haka yasa itama RAHAMA tayi shiru.


Abdul bai dawo ba sai wurin ‘karfe shida da rabi, don sai da yayi sallan magariba sa’annan ya shigo cikin gidan.

Zaune ya taddasu jigum jigum, da mamaki yabisu da kallo dukan su, da alamu ma basuji sallaman saba.

Ta’ba kafad’an Aisha yayi firgigif ta dawo duniyar mu, kallon sa tayi tare da mi’kewa had’e da murmushin ya’ke tace” hubby sannu da zuwa”.

Bai ansa mata ba sai ma cigaba da kallon ta da yake famanyi.

Shagwa’be fuska tayi tare da cewa” hubby ina magana kamin banza”.

Kamo hannun ta yayi suka nufi cikin d’aki, har lokacin Zarah bata dawo ba ita, ta tafi can duniyar tunani.

Koda suka shiga d’aki zaunar da ita yayi akan sofa shi kuma ya du’ka a gaban ta tare da kallon cikin idan uwan ta yace” maike damun matana da har zan shigo bata san na shigo ba?”

Hawaye ne ya zubo mata, zaro ido yayi tare da tara hannun sa hawaye na d’iga a ciki.

Yace” My Esha lafia kike min asaran hawayen ki?”

Kwantowa tayi kansa tare da cewa” don Allah hubby kada ka matsamin na san sani abinda ke damuna, domin sirrin besty nane. and gobe tace zata keffi don Allah kamin izini muje tare”.

Numfashi ya sauke tare da cewa” shikenan amma don Allah abar kukan nan, a rage damuwa don za’a shiga ha’kina gaskiya “.

” sannan magana tafiya Ku bari sai jibi Saturday sai na kaiku”.

Cikin murna takai masa sumbata a goshi daga nan ta taimaka masa yayi wanka suka fito cin abinci.

Kwana biyu nan Zarah tayi sane cikin za’kuwa da damuwa kai har da fargaba ma.

Ranan da zasu tafi ta riga kowa shiryawa.

Bayan sun kintsa suka d’auko hanya………………..

COMMENTS
&
SHARE
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button