KAUYEN 'YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

KAUYEN ‘YAR KADDE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kayi Kyau” tace a hankali tare da matsa masa a kan hanya.
Ya fara tafiya yaji kamar ana binsa a baya, bai waigo ba sai da yaje ‘kofar asibiti sanan.
Ganin wace ke bayan sa ya had’e rai tare da shigewa.
Cigaba da bin nasa tayi har ‘kofar office d’in sa, bud’e wa yayi tare da shiga, zai rufe ta turo jikin ta.

“Kibar wurin nan”, ” doctor nazo fa domin lafia tane, da gaske banda lafia ka yarda dani” ganin kallon da yake mata yasa tace haka.
Bud’e mata yayi ta shiga, zai duba ta kodon maman ta.
Zama yayi a kujeran sa, ita kuma tana nan tsaye, nuni yayi mata da hannu alaman ta zauna.
Zaman tayi sa’an nan yayi shiru yana jira daga gare ta.

Tasani sarai tagane nufin sa amma ta share sai ma ‘kare masa kallo da take.

Gajiya yayi ya mi’ke domin zuwa duba marasa lafia, itako tana nan zaune ko motsawa batayi ba.
Fita yayi ya barta ba tare da yace da ita komai ba.

Kallon office d’in take lungu da sa’ko, ba wani babba bane tunda na ‘kauye ne, amma da yake na d’an gata ne ba laifi yayi Kyau.

Tashi tayi taje kan ‘karamin bed d’in marasa lafia da yake office d’in ta kwanta tana mai lumshe ido lokacin ne taji ciwon ya taso mata, don haka sai ta fara mur’kususu.
Dai-dai nan Auwal ya bud’e ‘kofar, ganin bata a kujeran da take yasa shi ajiyan zuciya tare da cewa “mayya kawai ta tafi…….” Bai ‘karisa zancen saba yaji nishi .

Waigawa inda yake jiyowa yayi kwance ya ganta a gadon.

Tana mur’kususu, d’auke kansa yayi kamar bai ganta ba, abinda yazoyi yayi ko ya gama don haka sai ya tattara abinda yazo dashi domin koma wa gida.

Aje key d’in office d’in ya aje tare da ninyan fita yana cewa kamar mai ciwon baki “idan kin tashi sai ki rufe musu office d’in su”.
Kuka mai had’e da ehu ta saki tare da cewa ” wayyo doctor zan mutu kataimakeni please, mama tace nazo ka dubani”.
Dawo wa yayi tare da cewa idon sa na kallon gefe “meke damun ki?” “tunjiya da dare nan kemin ciwo, ina kenan?” yace ba tare da yajuyo ya kalle ta ba.
“Nan” tace, shi kuma yace cikin gajiya da ‘kufula “shi wurin baida suna ne?” shiru tayi tana mai cigaba da kukan ta.

Haushi yaji zai fita, itako ta dage iya ‘karfin ta tasaki ehu mai ‘karfi.
Toshe kunnin sa yayi tare da kallon da azafafe ya nufo ta.

Kamar zai bugeta yace “wallahi kika sake min ‘kara a kunni sai naci…..” sai kuma yayi shiru.

“Ina kemiki ciwo? yace yana hararan ta.
Maimakon ta bashi ansa sai ta cigaba da kukan ta.

” Tashi kibarmin office yanzun nan kafin ranki ya ‘baci” yace yana matsowa kusa da ita.

Bai aune ba kawai yaji ta kama masa hannun, da mamaki da ba’kin ciki yake kallon ta.
Bai gama mamaki na yaji hannun sa a lallausan jikin ta.
A han maran ta ta d’aura hannun nasa.

Cikin kuka tace “nan ne kemin ciwo” fisge hannun sa yayi cikin masifa yace yana tofar da yamu.

“Banza ‘kazamiya, amgaya miki kowa ‘kazami ne irin ki? ko ance miki ni Auwal irin karnikan kine ‘kazamai Wanda basu san inda yake musu ciwo ba irin ki”.

“Zan miki gargad’i da babban murya ni Auwal nafi ‘karfin ki, nafi ‘karfin ‘kazan taccen jikin ki, kuma ki fita harka ta, idan ba haka ba ki kuka da kanki”.
” Banza kawai, Auwal ba jaki bane, kisani koda ni mazinaci ne irinki to bancin sauran wasu, kina mace mai aji da kima da daraja amma kinzubar dasu, koba abun abun mamaki bane arna zasuyi fiye da hakan”.

Ya sake tofar da yamu idanun sa ya rufe yayi ta surfa mata ba’ka’ken maganganu.

Koda ya gama bai damu da kukan da take da juye-juyen da take ba.

Yabar office d’in tare da sanar da mai gadin wurin idan ta tafi ya rufe masa office d’in ya’kara gaba.

Tafiya yake yana ganin dishi-dishi domin abinda yafaru yana ganin sa a idanuwan sa kamar yanzu ake.

Kuma ya tabbatar da zarginsa ‘yar iskance ita……

Tofah fan’s kunji fan

Kubiyoni domin jin yadda zata kaya, amma hakan bazai samu ba sai naga comments.

Comment & share pls

‘Yar Aliyu ce✍????
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: ????????????????????????????????

‘KAUYEN ‘YAR KADDE

????????????????????????????

Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili

????DA BAZAR MU WRITER’S ASS????

We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all…….. DA BAZAR MU MUKE TUN’KAHO

LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
MASAUKIN SO
SHI NAKE JIRA
BA JINSIN MU BACE
HAMDIYA DA HAMNA

Dedicated to my family

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????1⃣7⃣to1⃣8⃣

“Dole na cire ki a raina, kota halin ‘ka’ka kuwa, zuciya baki min adalci ba, taya zaki sa naso wacce bata dace dani ba? yes bata dace dani ba, bata cancan ceni ba. Ni mai tsaftane ita ‘ka zama, ya Allah fitar da ita a zuciya ta”. yace yana mai rintse ido, lokacin yana kwancen a bed d’in sa, babu abinda yake tunani sai ita, tunani halin da ya baro ta kawai yake.

***Ta d’au tsawon lokaci a wanann yana yin, tana cikin damuwa mai tsananin, abu uku ke damun ta. Na farko ‘kama da Auwal ya kira ta hakan yayi mata zafi sosai, ta gane cewa yana zargin ta da aika ta fasi’kanci, abinda bai sani ba, zina abune da take matu’kar ‘kama, hakan da ya matu’kar tsaya mata a rai.

Na biyu ciwon maran dake damun ta, ba’kin ciki yasa ya rage mata kaso hamsin na ciwon.

Na uku tsananin ‘kaunar sa da bata san tanayi ba sai yau, gashi Auwal yayi mata nisa, kalman sa kawai yasa ta gane tsananin kiyayyar da yake mata.

” Ina son ka, wallahi ina son ka, ina tsananin ‘kaunar ka, ‘kaunar ka shine ajalina zan rayu da son ka duk da nasan baza ka ta’ba sona ba”.

Tace tana mai fashe wa da kuka mai tsanani, a daddafe ta bar office d’in nasa, idan nun ta nata zubar ‘kwallah.

A haka taje gida bata damu da kallon da mutane kema taba sam.

Tana shiga ta tadda uwar ta a tsakar gida, ganin yana yin da ‘yar tata ta shigo yasa ta isa gare ta da sauri ta taro ta.

Tare da tambaya ta abinda ke damun ta, shiru tayi mata tana mai cije le’be.

Tambaya duniya nan uwar ta mata amma ta share ta, ganin haka uwar ta fita harkan ta duk da yanayin da ‘yar tata ke ciki na damun ta.

Kwanciya tayi tana mai tsine ma isah domin shi ya janyo mata tsana da ‘kiyayyar da Auwal yake mata.

••••••••••••••••Yau kimanin kwana hud’u kenan Auwal ya’ki fita ko waje komai a gida yake yin sa, duk yayi wani iri saboda damuwa dake d’awainiya dashi.

Ta kai ta kawo har da Kuka, kwancen yake yana tunani da ya zame masa abinci domin abincin ko damuwa dashi baiyi.

“Na sani ina sonki, so mai tsananin ma kuwa amma sai dai ya kasheni da dai na auri sauran wani, na tsaneki ban sanki daga yau” yace yana maiji zafi a zuciyar sa, domin tuno cewa ita sauran wanine ya hadda sa masa damuwa fiye da nada.

Wanda har tsanan ta wani sashi na zuciyar sa yake.

‘Karar wayar sa ce ta dawo dashi daga halin da yake ciki.

Kallon wayar yayi na wani lokaci kafin ya d’ako, ganin mai kiran sa yasa shi peaking tare da sakin murmushi da ya kwana biyu baiyi ba.

Kafin tai magana ya riga ta da cewa “sweetheart” yana jan numfashi.

Dariya tayi tare da cewa “na’am sweet bros, yakake d’an ‘kanina?” shiru yayi kamar mai tunani.

“My Auwal kanajina kuwa?” shiru ba ansa ta sake cewa “kana lafia kuwa my bros? talk to me please ” tace cikin tashin hankali.

Sanin halin ta yasa shi
‘bata rai tare da cewa “sister ba ‘kalau nake ba sam”.

” Oh my god!!! what happen?, sister my heart” sai kuma yayi shiru.

“Mai ya same ta?, ciwo take sister, kaje a duba ka mana”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button