Labarai

Ko Buhari Ya Sauka A Mulki Matsalar Tsaron Najeriya Ba Za Ta Kare Ba ~ Fadar Shugaban Kasa Ga Dattawan Arewa 

DAGA Comr Abba Sani Pantami

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kiran da dattawan Arewa suka yi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta a Arewa.

Kungiyar dattawan Arewa ta yi wannan kiran ne da yammacin ranar Talata 12 ga watan Afrilu, kamar yadda rahotanni suka kawo, Daily Trust ta ruwaito.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya ce murabus din shugaban kasar ba zai taba zama mafita ga matsalolin tsaron kasar nan ba.

Kakakin shugaban kasar, ya ce nan ba da jimawa ba za a fara gudanar da sauye-sauye a harkokin tsaron cikin gida.

Ya kuma bayyana cewa tuni hukumomin tsaro suka kara kaimi wajen magance yawaitar ayyukan ta’addanci a baya-bayan nan, musamman a jihohin Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta daidai da umarnin shugaban kasa.

A cewarsa, rundunar tsaron ta sake daidaituwa tare da sake tsara ayyukan da ake gudanarwa a yankunan da abin ya shafa domin samun sakamako mai kyau.

Fadar shugaban kasar ta zargi “masu zagon kasa” da nufin bata gwamnati da nuna ba za ta iya magance abubuwan da ke faruwa a kasar ba, kamar yadda Daily Post ta tattaro.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button