Kona Kur’ani A Kasar Sweden Yaki Ne Da Duk Musulmin Duniya –Iran


A cewarshi matakin ba komi bane illa hauka da rashin wayewa da nuna kiyayya ga al’ummar Musulmi sama da Bilyan 2 a duniya.
Saeed ya ce, wannan cin zarafin da wasu suke yi da gangan musamman a watan Ramadana mai alfarma, nuni ne ga irin kiyayya da take hakkin Musulmi, da neman tsokana, wanda kuma yin hakan daidai yake da take hakkin Dan Adam.
“Ya kamata gwamnatin kasar Sweden ta gane sa yawonta ake cin zarafin Musulmi da yawansu ya zarta Bilyan Biyu a duniya, in kuwa ba da yawunta ake yin hakan ba, ya kamata ta hukunta masu yin wannan danyen aikin.” Inji Saeed
Ya kara da cewa; Ya wajaba ga al’ummar Musulmi su tashi tsaye don hada kansu wajen dakile irin wannan cin zarafin da makiya suke yi, musamman ganin cewa Kur’ani littafi ne da dukkan wani Musulmin duniyar nan yake ganinshi a matsayin littafi mai tsarki.
Rasmus Paludan shine mutumin da ya jagoranci aika-aikar kona Kur’anin, inda ya samu rakiyar jami’an ‘yan sandan kasar, duk kuwa da gungun masu zanga-zanga sun nuna rashin goyon bayansu ga matakin, amma hukumomin kasar Sweden din basu hana mutumin aikata hakan ba.
[ad_2]