Labarai

Kotu ta raba auren da ya Shekara 8 saboda rashin biyan haƙƙin Miji

Kotu ta raba auren da ya Shekara 8 saboda rashin biyan haƙƙin Miji

Wata kotun Jos ta tsakiya da ke zamanta a Kasuwan Nama 1 a ranar Alhamis, ta raba auren shekara 8 da aka yi tsakanin wata Samira Makama da mijinta, Muhammed Musa, bisa rashin iya ciyar da iyalinsa.

Kwamitin alkalan da suka hada da Malam Sadiq Adam da Mr Hyacinth Dolnanan a wajen amincewa da bukatar da Makama ya gabatar, sun ce duk kokarin sasanta bangarorin ya ci tura.

Alkalan sun umarci mai kara da wanda ake kara da su bi hanyar Sasanci amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

Kotun, ta umurci wanda ake kara da cewa ya rika kula da ‘ya’yansa duk wata tare da biyan kudin makarantarsu, inji rahoton NAN.

Tun da farko dai matar ta roki kotu da ta raba auren nasu, inda ta ce mijin nata da ta yi aure shekaru 8 da suka gabata ya kasa kula da ita da ‘ya’yansu biyu.

Ta shaida wa kotun cewa tun farko mijin nata ya sake ta har sau biyu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan kuma ya yanke zumunci da ita.

Ta ce ta je kotu ne domin neman a raba aurenta da Mijin nata.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button