
Sai dai kuma kash! ashe dai ganin kitse ake wa rogo. Masu sha’awar cewa Hauwa Bello Ado Bayero na kwance a cikin daula ba su san cewa kamar a kan ƙaya ta ke zaune ba saboda wani mugun yanayi da ta samu kan ta a ciki a tsawon shekaru aƙalla 15. Yanayi ne wanda ta daɗe ta na ɓoyewa har zuwa yanzu da ta ga uwar bari ta yanke shawarar ta sanar da duniya irin halin ha’ula’in da ita da ‘ya’yan ta su ke ciki domin gudun abin da ka je ya dawo, wato kada sai ita ko mijin ta wani ya ƙaura wata ƙurar ta tashi, a riƙa cewa to me ya sa ba ta faɗa ba tun tuni?
Hajiya Hauwa dai ta kasance cikin wannan ƙangi mai hana barci ne ba domin komai ba sai saboda wai ita ‘yar fim ce a da, sannan kuma ba ta da kowa a dangin ta wanda ya isa ya ƙwatar mata ‘yancin ta. Shin me ya faru?
Tsohuwar jarumar ta tattauna da mujallar Fim (da izinin mijin ta) a ranar Laraba, 11 ga Mayu, 2022 saboda a kai mata agajin gaggawa ita da yaran ta. Ga yadda zantawar su da wakilin mu na Kano, MUKHTAR YAKUBU, ta kasance:
Ga Bidiyon hirar da akayi da ita ku saurara.
[ad_2]