KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Muje na taka miki” bushira ta fada itama tana janyo hijabinta suka yiwa ummansu sallama suka fito tare.
SANNU SANNU*
Kwanaki ke shudewa sa iman cikin makarantar nasreen,zuwa sannan bata da wata qawa ko aminiya data wuce munira,shaquwa me qarfi ta fara shiga tsakaninsu,duk da banbancin halaye da kuma dabi'u dake a tsakaninsu,gami da sukunin rayuwa.
Cikin sati uku ta fahimci wace munira,'ya mace guda daya tilo da mamanta ta haifa bayan yara maza qannenta guda hudu,tana ji da ita ainun,tana bata kulawa da gata,kusan mafi yawa daga cikin familyn su munira masu arziqi ne masu sukuni,saidai shi mahaifin muniran rufin asirin Allah gareshi,mamarsu muniran ta fishi kudi,hakan ya sanya komai na gidan take tafi dashi yadda takeso idan ma maigidan yayi wanda baiyi mata ba,tana ji da munira sosai,hakan yasa ta daukaki rayuwarta,tanason rayuwa me tsada sosai,hakanan takan kutsa kanta inda Allah bai kaita ba,gidajen 'yan uwan mamanta masu dashi ainun babu inda bata sani ba,wani lokaci idan ta shilla ta debi kayanta ta tafi daya daga cikin gidajen nasu,takan jima bata dawo nasu gidan ba,har ma sai kayi zaton 'yar gidan ce.
Da yake fara ce hakan sai ya sake qawata fuskarta,ya kuma ja hankalin samari a kanta,tana da samari sosai,kuma dukkaninsu 'ya'yan manya ne,wayar hannunta kuwa a lokacin babbar iPhone ce,dukkan abinda take ta'ammali dashi,tun daga sutura zuwa cima masu tsada ne,komai zatayi saita siya me tsada,saboda mamanta ta tsaya mata,batason sam taga muniran tata ta shiga cikin danginta an raina ta,hakan ya sanya take kashe mata kudi tuquru.
Saidai kuma muniran nada kirki daidai gwargwado,hakan shi yake taimakawa wajen boye da yawa daga halayyarta da basu dace ko kamata ba.
Ba komai na halayenta iman ta sani ba,tunda iyakarsu makaranta,da an rabu shikenan,sai kuma washegari,iya abunda ta sani muniran tana da kirki da kuma yawan kyauta,duk da tana zillewa duk wani abu da zaisa muniran ta kashe mata kudinta,kamar tafiyarsu tare,da yawan lokuta zillewa take tayi tafiyarta saboda kada muniran tace zata biya mata kudin motar.
MONDAY MORNING
Cikin clean uniform dinta da suka dauki karin guga kyakkyawar matashiyar hajar Ibrahim Khalil ke takowa tana nufar ajinsu,kafadarta daya saqale da jakarta,daya hannun kuma dan madaidaicin flask din abinci ne a ciki.
Kana duban fuskarta zaka karanci ranta a bace yake,saidai hakan wani kyau ya qara mata na musamman,sandin bacin ran nata makara datayi,aka kuma shanyasu a bakin gate har na wajen awa daya cikin rana,wanda wannan shine irin punishment din makarantar tasu.
Kamar ance ta daga kanta saman varander dinsu,ta daga kyawawan blue eyes dinta,idanunta sauka ga malamin,sir arabi,malamin daya takurata tun zuwanta makarantar,da shegen kallo naci da kuma shishshigin shiga harkarta,shike daukarsu darasin turanci wato English,yammatan makarantar da yawa suna yinsa,saboda motar da yake hawa,kana kallonsa kasan ba talauci ko babu suka sanyashi koyarwar ba,saidai ita sam imani hakan bai dameta ko ya dadata da qasa ba,don sam jininsu ita bai hadu dashi ba,ya fiya jin kansa saboda yaga yana tashen samartaka,yana sanya shaddodi da hawa mota,ita sam a rayuwarta batason mutum me jin kansa ma,izza da fadin rai,shi yasa tako ina ya al'ameen yake burgeta.
Yana da wani irin kwarjini gami da aji,uwa uba miskiline naqin qarawa idan baiso ba,hakan yasa baya daukar raini ko izgili,amma sam baida girman kai ko dagawa.
Ta sauke nata idanun tana jan tsaki qasa qasa,gami da qare hade ranta gab da zata shiga cikin ajin nasu,sabida yadda yawanci lokaci irin wannan sanda tazo a makare mazan ajin ke binta da kallo,abinda ta tsana ita kuma kenan,don haka a dake ta shiga ajin.
"keda mutumin naki ne?,na hangeshi tsaye upstair" munira ta fada tana danne dariyarta sanda iman ke zama kusa da ita,tana duba littafin subject din da akeyi
“Shine mana,me shegen kallon tsiya,banason mutum me kallo”
“Tsaurin idanu dai,kwata kwata baki dace irinsa bama,shi bai gani ba kedin kalar matar manya ce” waiwayowa iman tayi sanda take dora littafin saman table dinta
“Kamar yaya?” Murmushi munira tayi tana ci gaba da copying note dinta
“Kamar har yanzu bakisan baiwar kyan da Allah yayi miki ba,ai kyan kyau irin naki ki morewa babban gida,inda zaa jiqaki da kudi da mota,fita qasashen waje babu kama hannun yaro,shine kika mori kyanki,amma ba kowanne irin kalar namijine zaizo ya tsaya gabanki da sunan yana sonki ba” tsaki iman taja,saboda ta dauki maganar munira a matsayin shirme,ta bude littafinta ta fara kwafar note din da sauri da sauri don ta fuskanci ya kusa dawowa ya goge wanda ya fara.
“Am telling you fa,kina ganin kamar wasa ce maganata?,to Allah koni da ban kama rabin qafarki a kyau ba,zakiga kalar mijin da zan zaba”
“Don Allah ki shiru ki barni da bacin ran da yake damuna” dariya muniran ta saki tana ci gaba da rubutun,har zuwa sanda malamin ya kammala yayi musu explanation ya sallamesu.
"Me ya hanaki zuwa makaranta Friday ne?" Iman ta tambayi munira tana maida littafinta jaka,sai data juya manya idanunta,da alama amsar da zata bayar amsa ce da take mata dadi cikin ranta sosai sannan tace
“Kinsan biki muke na wata cousin dita,so ran Friday muka tafi garinmu acan zaa daura aure,kuma ina cikin wanda aka siyawa ticket zasubi flight,kinga ko bazan bari nayi missing ko damata ta wuceni ba,nayita neman number dinki na gaya maka,sai dana fara checking wayana naga ashe bamu taba exchanging numbers ba……ki bani number dinki saboda irin hakan,kinga nama canza sabuwar waya,ranar aka bani gift dinta” munira ta fada tana saka hannunta a aljuhun rigarta.
Kallo daya zaka yiwa wayar kasan cewa bata qananun kudade bace,hakanan sabuwa ce fil sai sheqin sabunta take,munira tabi wayar da kallo sannan ta amsa mata
“Nikam ai bani da waya,ta ya al’ameen nake ara duk weekends nayi game ko browsing” kallon mamaki qarara munira ta jefi iman dashi,harda dan ja baya
“Kina ss 01 amma ace baki da phone iman, jokes apart please,wasa kikemin ko number dince ba zaki bani ba?”
“Tunda baki yarda ba ai babu amfani na dage saina gamsar dake,duk yadda kika dauka hakane”
“Am sorry my friend,Allah na dauka wasa kikemin….amma kuma,ba sani ba wallahi,da dana canza na baki dayar,sai qanina na bawa wanda yake bin me bina” idanu iman ta fidda
“Ni shegiya kaza,ya al’ameen bazai bari ba,amma ina saka ran muna gama wannan term din zai siya min keypad sabuwa in sha Allah,yayi alqawarin idan nayi abun kai zai siyamin” dariya sosai munira ta saki tana kallon iman
“See you don Allah,wani irin keypad?,to ko ‘yan aikin gidanmu banjin akwai me keypad,don Allah karma ki fada wani yaji,sai ajinki ya zuba,mazancan da kike jawa aji saisu rainaki,su dauka qaramar yarinya ce ke”.
Rai sosai iman ta bata tana dubanta
“To sai me?,ni ina farinciki da duk abinda nake dashi,kuma iya abinda yake ganin ya dace dani kenan,kuma ina farinciki da hakan”
“Wait mana iman” munira tayi saurin dakatar da ita ganin kamar taji haushi
“Nifa ba abinda nake nufi kenan ba,ki fahimceni…..ina nufin yanzu budurwa kamarki,ai ya kamata a sakar miki mara a siya miki waya me kyau saboda gudun raini daga wajen tsararrakinki…..na tabbatar yana da kudin da zai iya siya miki babbar waya,ko yaya ne kaima kayi dan abun xamanin nan da kowa yakeyi” duban munira kawai take,tabbas ya al’ameen idan tace tana so zai siya matan,amma a hakan ma babu lallai su malam su yarda ba,sai tayi shuru bata sake cewa komai ba,saboda isowar wata ‘yar ajinsu da tata wayar,tazo munira ta tuttura mata pics da wasu videos,da kadan kadan sai ga masu wayar suna zuwa,sunata sending ma junansu abunda kowa keson sawa a wayarsa.
Tana daga gefe tana kallonsu,kowacce wayar hannunta babbace,wata daga gidansu wata kuma saurayine ya siya mata,ba shakka tana bala'in son waya da maitarta,amma ba zata takura ya al'ameen din ya siya mata sama da wadda yace zai siya matan ba.
[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 11________________
Huuuuuum! Idan kaji hanci a sama yayin gittawar mata ƴan ƙwalisa ko shiga gidajensu kasan maganar ta ƙamshi ce
Ina magana ne aka kayan ƙamshi ƴan gaske ba saka iska ta hure maka ba
Ina mata ƴan ƙwalisa ma’abota so da ƙaunar ingantattun haɗin turaruka ƴan gaske? To kuzo maza ga dama a tafin hanunku cikin sauƙi da sauƙaƙawa.
Ana siyarda Turarukan Wuta na yan Maiduguri Set na amare. Ana bada sari kuma.
Sannan akwai kayan gyaran jiki. Akwai zumar qiba result cikin 1 week. Turaren daki, jiki, kaya, tsuguno, humra, colacca, turaren wanka, mopping scents, air freshener.
Address Kano, Mariri Maiduguri Road. WhatsApp number 07068145252.
Sai kunzo????????
Tare suka jero da muniran bayan an tashi kamar yadda suka saba,suna tafe suna dan hira munira na tsokanarta
“Nikam kullum aka tashi daga makaranta dalibai basa gajiya da kallonki iman?” Tsaki taja,itama abun yana damunta,don har ta yanke shawarar fara sanya niqabi
“Sai suyita ai,kamar kai dayane mutum,su ba bil’adama bane ‘yan uwanka”
“Kin fita daban seriously,shi yasa kike shan kallo” munira ta fadi sanda take nufan wata mota ash jaye da hannun iman,dakatawa iman din tayi tana qoqarin kuma zame hanunta daga na munira
“Ina kuma zaki kaini ga hanyar titi?” Waiwayowa tayi tana dubanta,fuskarta dauke da murnushin nan
“Oops,sorry,na manta in gaya miki,me daukana ya dawo da daukata,dama shike maidani gida indai naje gidan uncle jibril,yawanci ina bin motar haya ne idan ina gidanmu” kai iman ta jinjina tana saita hanyarta zuwa titi
“To sai gobe,Allah yabamu alkhairi” da sauri tasha gabanta
“Ban gane ba,bayan ta hanyar unguwarku xamu wuce,ki shigo don Allah,yana da kirki,zai ajjiyeki unguwarku,cousin dina ne sadam,lokacin tashinmu lokacin ne shi kuma yake komawa gida cin abinci,shi yasa yaje biyowa ta nan ya daukeni mu wuce tare” kai iman ta jinjina
“A’ah fa,zanbi adaidaita kamar yadda na saba” dambu taliya ta kada iman amma taqi,har sau da na cikin motar ya fara mata horn,dole ta haqura tace da ita
“Shikenan,bani number wayar to”
“Idan kin kira amma kice ni kike nema,don ya al’amin ko inna cikinsu wani zai daga,saboda numbers dinsu ne” dariya munira ta saki
“Allah ya sawwaqe,yanzu inda saurayi kikayi haka zaki gaya masa kenan?”
“Ke kika sani,ni bani da wani saurayi ma” da wani mamakin take duban iman din,saidai ta share ta soma karanto mata digit’s din tana lodawa a wayar tare sa serving,sukayi sallama tana jajata mata Allah yasa ta samu mota da wuri,saboda sadam ya gaya mata ana wuyar abun hawa yau din,sakamakon taadar da man fetur yayi,da yawa wasu masu ababen hawan sun haqura sun ajjiye abun hawan nasu a gida.
Ta samu tulin dalibai kuwa masu jiran abun hawa,haka nan tabi sahunsu itama,tana fatan su samu da wuri kodon ranar da ake dasawa.
Kusan duk motar da zatazo ta wuce a cike take,wata kuma kafin ta qarasa inda ta tsaya wasu sun shige sun cikata,tana nan a tsaye tsayin wasu mintuna ta hangi kamar gilmawar motarsu munira,sai kuma taga ta tsaya taja da baya ta dawo dab da ita
“Why not ki qyaleta….ba’a dole wajen taimako fa” sadam daya dan hada rai ya fadawa munira
“Qawatace,banason ganinta tana sha ranar nan,kayi haquri minti daya”
“Ok” ya amsa qasa qasa yana jona wayarsa a chargy,munira ta bude murfin motar ta fito ta nufi inda iman take.
Da farko musu taso ta sake mata,sai da taga muniran taji haushi,sannan kuma me motar ya fara buga musu horn sannan ta bita,sanyin ac ya ratsata sanda jikinta ya shige motar,ta maida murfin ta rufe sanda munira ke mita
“Haka kawai ki tsayar da kanki a wannan ranar babu gaira babu dalili,bayan ga abun hawa,ai tsaiwa a ranar nan sai dole”
“Ina yini” tayi qoqarin gaida matuqin motar ba tare data amsa mitar da munira ke mata ba
“Laf….lafiya qalau…. ‘yammata” harshensa yadan sarqe,bayan idanunsa sun sauka a fuskar iman dake ciro jakar bayanta zuwa saman cinyarta ta glass din gaban motar,gabansa yadan fadi,ya zuba mata idanu na wasu sakanni ba tare daya iya dauke idonsa daga kanta ba,tunda yake bai taba ganin halittar mace da komai yaji…..ta kuma tafi da imaninsa irin wannan ba,wani irin kyau mai cika idanun me kallo,abinda yasa yadan daburce har ya qara mata da kalmar ‘yammata kenan ba tare da ya sani ba,kalmar kuma data dan ja hankalin munira tabi sadam din da kallo,don tasan ba dabi’arsa bace hakan.