KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

+234 818 401 7452

Tasted and trusted????????????????https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

FREE PAGE 02

ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha’awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki

CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA

GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER

+234 818 401 7452

Tasted and trusted????????????????


Basu shigo gidan ba su duka sai bayan sallar isha’i,saboda suna tsayawa daukan karatu wajen malam cikin almajiransa,hannunsa riqe da baqar leda wadda taketa maiqo dauke da awara me zafi da tasha cabbage da yaji mai uban yawa.

    Dai dai lokacin da iman din ke zaune gefan tabarma tare da innarmu wadda ke lazumi bayan ta gama tata sallar,abincinta na gefe bata tabashi ba,innar tana ankare da ita amma bata kulata ba,iman din irin yaran nan ne da ko kadan basa qaunar abinci,wani lokaci har sai innar ta ajjiye madoki kusa da ita sannan zata ci abincin,wannan dalilin yasa bata da kumari ko kadan,kusan duka sa'anninta sun fita girman jiki.

 Tana jin sallamar alamin ta miqe daga shirin kwanciyar da takeyi,ya qaraso gefanta ya zauna yana ajjiye mata ledar awarar,fuskarta a wadace da murmushi ta janyo ledar ta fara budawa tana cewa

“Na gode yaya alamin” shima murmushi kawai yayi ba tare daya amsa ba,suka bita da kallo sanda ta miqe zuwa kitchen,da alama plate din da zata juye awarar take nema.

    Kusan lokaci daya suka dauke idanunsu shi da inna,sai innar ta ajjiyr carbin hannunta gefan daddumarta tana cewa

“Zauna aminu” sabule slippers din qafarsa yayi,ya zauna daga gefa,cikin yanayi na nutsuwa

“Me yasà koda yaushe saidai ka yita biyewa shirmenta?,ta yaya ku da kuke nema ya kasance koda yaushe baka da aiki sai batar mata daa kudi?,yanzu meye laaifin daambu da bazata ci ba,saidai awara?” Murmushi ya saki kawai,sannan a nutse yace

“Inna mu din mune dolen imaan,mu ya kamata ace munyi mata daman,idan bamuyi mata ba waye zaiyi mata,kuma bata roqan kowa a waje saimu da muke yayyenta,kuma ma amfanin neman kenan inna,iman ba wani abu take tambaya ba da ya wuce dan abun marmari” kai kawai innar ta raausayar,dama tasan zaa rina indai lamin ne,wannaan ba shine karo na farko da magana irin wannan ta ratsa tsakaninsu ba,ta rasa wacce irin qauna da kulawa ce wannan da yakewa imaan din,duk da cewa sun kyautata masa matuqa da gaske,kyautatawar da duniya ma ta shaida da hakan,amma kulawar da iman ke samu daga gareshi ta musamman ce.

 Koda ta matsa wajen ganin cewa ta hanashi,ko kuma ya rage tasan bata bakinta ne kawai,lamin din bazai sauya ba,a nata hasashen da ganin kamar ya kamata ya rage din,tunda ko babu komai akwai yayarsa dake aure a qauyensu,wadda wasu nauye nauye nata dana yaranta duka ya daukesu bisa wuyansa,kasancewarsa yaro jan gwarxo,mai himma qoqari da kuma neman na kansa,komai dadi komai wuya,kuma komai rintsi,kwata kwata baisan wata kalma ta lalaci,son jiki ko kuma qyuya da ganda ba,dukkan wani aiki da zai samar masa da kudi na halak yana tallafarsa,ya kuma karbeshi hannu bibbiyu yayi,babu girman kai babu ha'inci ko son jiki.

“Shikenan,Allah yayi muku jagora,yasa albarka a nemanku”

“Ameen inna…ameen” ya fada yana jin dadin addu’arta,uwa ce me yawan addu’a ga ‘ya’yanta,kome qanqatar alkhairi idan sukayi,bakinta baya gajiyawa da yi musu addu’a dare da rana.

   Duk sanda tayi masa addu'ar sai yaji dadi qwarai da gaske qasan ransa,ya rasa mahaifiyarsa tun hankali bai fara riskarsa ba,sai gashi Allah ya musanya masa da wata makwafinta a sanda baiyi zato ko tsammani ba,a lokacin da ya dauke haso ya kuma debe tsammani daga samun dukkan wani tattali kulawa ko kuma jin dadi,cikin tausayi da kuma jin qai na ubangiji ya hadashi da wasu kwafin na iyayensa.

    Daga inda take zaune take binsu da kallo,sanda ya karbi awarar da kansa ya juye cikin farantin robar da iman din ta dauko,sannan ya zauna yana gutsutsura mata da daya da daya yana miqa mata tana ci suna hira,kallo daya xakayi musu ka tabbatar da cewa lallai akwai shaquwa me girma a tsakaninsu.

   Lumshe idanunta inna tayi,bahaushe yayi gaskiya da yake cewa

“Da da da dukiya babu wanda yasan me morarsu sai Allah” ta Sauke idanunta tana tuna ranar farko da suka fara sanin lamin,ya kuma shigo rayuwarsu ya zama daya daga cikin iyalan gidan.

   Malam ibrahim khalili shine cikakken sunansa,haifaffen garin maiduguri,cikakken babarbare wanda ya fito daga gida na ilimi da karatu,asalin gidansu malam khalili gida ne na malamai,da suka gaji karatu tun daga kakanninsu,malam khalili yana daya daga cikin yara uku da suka gaji mahaifinsu,duk kuwa da cewa su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa Allah yayi mata rasuwa.

   Khalili ya tashi da son karatu da kuma nema tuquru,wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sanya yabar maiduguri,ya shiga duniya neman karatun qur'ani dama na addini haiqan,daga gari zuwa gari,har ma wasu qasashen da muke maqwabtaka dasu.

  Sosai karatu ya daukewa khalili hankali,bai samu yin aure da wuri ba,har zuwa sanda ubangiji ya nufeshi da zuwa qasar niger.

  A canne ya hadu da fatima buzuwa,tana zuwa daukan karatu makarantar wani abokinsa,yarinya ce a sannan me qwazo da kuma hazaqa,don lokacin ma ta kusa kammala haddar qur'ani,tana izifi na hamsin da biyar,tun daga baqara take rubutawa a allo ta haddace sannan ta wanke a sake yi mata qari,ta samu tarbiyya me kyau da kuma kulawa,duk da cewa mahaifinta ya rasu,amma mahaifiyarta batayi sakaci da tarbiyyarta ba,saboda ita daya Allah ya basu.

    Lokaci daya soyayya da shaquwa ta shiga tsakaninsu,suka fahimci juna da kyau,manya suka shiga maganar aka tsaida maganar aure,ba dadewa suka angwance,ya kuma daukota ya taho da ita garin kano,inda anan ya bude tsangayarsa shima,yana karbar almajirai daga kowanne gari ko qasa.

     Almajirancin makarantar malam khalili ba kamar sauran almjirci bane da muke gani ayanzu,wada aka watsar da duk wani mutunci da kuma kimarta a yanzu,yara suke wahala da sunan neman ilimin alqur'ani me girma,wanda sam hakan bashi da tushe bare asali sam cikin addininmu.

   Dukka yaron da zai karba sai ya kasance makusancinsa ne ya kawoshi,zaa rubuta adreshinka da lambar wayar wanda ya kawoka,sunan gari dana qauyenka da kuma inda za'a iya samunka,sanna bai yarda a kawo masa yaro babu haka ziqau ba babu abinda zaici,abun kwanciya da kuma kayan baqatun yau da kullum,saboda shi din bai yarda da fita bara a makarantarsa ba,karatu aka kawo yaran shi sukeyi,yakan baka zabi idan ka soma hankali,kana da sha'awar karatun boko?,idan kana dashi zai shaidawa iyayenka ya sanyaka a makaranta,idan baka buqata kuma zaka kama sana'a ne,don bai yarda da zama babu sana'ar yi ba,saidai kowacce sana'a kake kana yinta ne bisa sanya idanunsa da kulawarsa,da kuma tabbatar da cewa sana'ar da kakeyi din bata sabawa addini da kuma al'ada ba.

   Wannan dalilin ya sanya makarantarsa ta kasance mai tsari,mutane da dama sukeso kawo yaransu karatu nan wajensa,saidai duk shekara akwai adadin da yake dauka,idan suka cika kuma baya sake dauka sai wata shekarar.

   Zamansa da fatima wani irin zama ne me matuqar dadi da kuma ban sha'awa,khalili wani irin mutum ne managarci,mai halaye da kuma dabi'u masu kyau,tsayyen akan harkar gidansa da kuma sauke nauyin iyalinsa,idan kaga fatima zakayi tsammanin tana auren wani me halin ne,saidai ko daya,tsabar kula da take samu ne da kuma tsaiwar mijinta wajen sauke nauyinta,babu abinda ta nema ta rasa,tana matuqar jin dadin xama dashi,kamar yadda shima yake yaba mata,yake kuma matuqar jin dadin xama daa ita,saaboda ita din macace ta gari,mai tarin biyayyawa mijinta,wadda tasan dai dai ta kuma san akasin hakan,bai taba cewa tayi ta musa ba,kamar yadda bai taba cewa ta bari taqi ji ba,Shi yasa shima yake qaunarta,da kuma qoqarin ganin ya hidimta mata iyakar iyawarsa,bata nema komai ta rasa ba cikin gidanta,cikin wannan yanayin,shekara biyu da aurensa Allah ya albarkaceta da samun haihuwar santalelen da namiji,aka sanya masa abubakar saddiq.

  Daga kan saddiq tayita haife haife suna mutuwa wato WABI,makusanta da wasu cikin dangi sukayita so malam khalili ya qara aure,amma yace sam baiga dalili ba,yanajin dadin zama da matarsa,bai nema komai ya rasa ba,idanma ta hahuwa ce,kana iya haifar yaro guda daya amma ya zame maka me albarka fiye da masu tarin yaran,indai yana da rabo a haihuwa zata qara,ita kanta a sannan ta bashi dama amma yace bazaiyi ba,Cikin ikon Allah kuma sai Allah ya basu haihuwar hajar iman,haihuwar da duka fidda rai da ita,zuwan iman a daidai wannan lokacin ya janyo mata soyayya mai tarin yawa,saboda tazo a sanda basu zata ba,ta kuma zo a dai dai lokacin da suke marmari da buqatar qaramin yaron cikin gidan.

   Shekarar iman daya a  duniya da watanni biyar lamin ya shigo rayuwar cikin gidan a lokacin.

   Yadda jama'a keta yabawa malam khalili kan yadda makaranta da kuma dalibansa suke a tsare ya sanya malaman wasu tsangayun dake unguwarsu da kuma wasu unguwannin suka shiga adawa da kuma takun saqa dashi,suke kuma matuqar jin haushinsa,ganin cewa ya fita daban da sauran malaman tsangayu,babu bautarwa ko azabatarwa ga dalibansa,kamar yadda bai yadda ya zama cima zaune me matacciyar zuciya ba,sai abinda iyayen yara suka dauko suka bashi,aah,shima kamar kowa,duk sanda ya tashi dalibansa shima yana tafiya neman kudinsa,ya dawo kuma lokacin da aka kusa sake zama ci gaba da karatu,komai nasu na tafiya a tsare ne,kana ganin dalibansa da yadda yake tafi da komai dole ya baka sha'awa.

   Daren wata jumma'a ne,tana zaune tsakar gidanta daya kasance sai ita daya,sai hajar dake kwance a gefe saman wani abun shinfidarta me hade da katifa maras tudu,duk kuwa da cewa akwai motsin almajirai da hayaniyarsu daga qofar gida amma cikin gidan ba kowa,saboda babu wanda ke shigarwa malam gidansa gaba gadi don suna almajiransa,idan kaga yaro cikin gidan,to qaramine wanda shekarunsa basu wuce wanda shari'a ta wanzar da hani na shigarsa gidajen matan aure ba,tana da mai mata aike da maiyi mata wanki ana biyansa duk a cikinsu,bai yarda suyi mata aiki ba tare daya biyasu ba,saboda yace su din mutane ne suma kamar kowa.

    A hankali hayaniyar tasu ta fara raguwa,da alama an gama rabon abincin dare ne,wanda ake auna cikin abincin kowa a hada,manya a cikinsu su dafa a rabawa kowa,a wani gida da suke zaune wanda yake daura da gidan malam din,gida ne da wani bawan Allah ya bayar kyauta su dinga kwana,hankalinta bai wajen sosai,yana can ga tunanin abinda ya tsaida malam da din bai dawo yadda ya saba ba,shi da saddiqu da yayi masa rakiya.


  "Taho a hankali....riqeshi sadiqu" ta jiyo maganar malam din tun daga soro,abinda yasa ta ajjiye allon da take rubuta fasayakfika humullah ta maida hankalinta ga qofar shigowa gidan.

  Malam dinne da sadiqu da wani dan farin yaro da bata sanshi ba,ta miqe tana masa sannu da xuwa,ya amsa hankalinsa yana kan yaron

“Maza dora ruwan zafi innar saddiqu” malam din ya fada yana tsugunnawa a gaban yaron,yana yage ragowar rigar jikinsa,da hanzarinta ta koma madafa,ta hada ragowar itacen data gama girki ta kunna ta dora masa ruwan,sannan ta dawo tsakar gidan,inda malam ke tsugunne gaban yaron yana masa sannu,sadiq na tsaye a saman kanshi yana kallonsu.

  Kujera 'yar tsuguno ta jawo ta zauna,idanunta akan yaron da yake cikin hali na galabaita ta yiwa malam sannu da zuwa

“Yauwa binta” ya amsa da alamun rashi na a bace ne

“Ki duba maganin zafi don Allah idan akwai,idan ruwan yayi zafi ki juye sadiqu ya tayashi gasa jikinsa,bari naje na dawo” daga haka malam din ya miqe ya fita.

   Duk yadda malam din yace tayi haka tayin,ya gasa jikinsa da kyau,sauran ta sakashi ya shiga bayi yayi wanka dashi,cikin kayan sadiqun ta zabo wasu ta bashi ya sanya,don xasuyi kai daya dashi,yana gamawa ta zuba masa abinci,ta koma ta dauki iman data tashi ta fara rigima ta fara bata nono,daga inda take din tana kallon yadda sadiqu ya sanyashi a gaba yana kallo,tun dazun shima zuciyarsa a karye take fuskarshi ta nuna hakan.

  Malam ne yayi sallama,ya qarasa gaban yaron yana duban yaron daya ambata da lamin,ya bashi paracetamol din daya shigo dashi da kuma ruwan tea me zafi a leda,yace idan ya gama yasha yasha maganin,sai saddiqu ya kaishi daki ya kwanta.
https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

Da ɗumi-ɗuminsa????????????????????????????????

Please
Follow me
Share
Comments akan abinda ya shige maka duhu.

ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA????????????????????

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

TEAM ZAFAFABIYAR????????????????


KUFAN WUTA????????????????????????

     _AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar????????????????????????_

YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –

Enter your name: (Cikakken sunanki)

Enter your mail: (Email ɗinki)

Enter an username (Sunanki)

Enter your password: ( misali 12341234)

Confirm password: (misali 12341234)

Sai a taɓa Sign Up shikenan an buɗe account a ArewaBooks????????????.

Continue with Google – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

Register – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

AREWABOOKS LINK kai tsaye

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com

Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine.

MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER

+234 903 177 4742

Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan????????????????????????.

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????03

https://arewabooks.com/book?id=628235bbb77ff582983d6c6b

????????????????????????????????????????????????????????

ZAFAFA BIYARRRRR

INGANCIN LABARAI

FASAHA NUTSUWA DA IYA SARRAFA ALQALAMI

TSARI DA TSANTSAGWARON HIKIMA

SOYAYYA MAI RATSA ZUKATA DA NARKAR DA ZUCIYA

JIGON LABARAI DA YASHA BAMBAM DA NA SAURA MAI SANYA ZUCIYA MAMAKI DA TUNANI

YIN LINQAYA CIKIN DUNIYAR LABARI KAJI KAMAR DAKAI AKEYI DA GASKE NE

DUKA SAI CIKIN GAMAYYAR LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR

ADADE ANAYI SAI GASKIYA

HIKIMA KASHIN KWANCE

ABOKAN HIRA NE GA WANDA KE CIKIN KADAICI!

ABOKAN TAFIYA GA WANDA KE CIKIN NISHADI

WARWARAR MATSALA GAME NEMAN MAFITA

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

TEAM ZAFAFABIYAR


Ajjiye iman inna tayi sannan ta nufi daki,ta dauko babbar tabarmar malam din da yakan zauna a kai ta shimfida masa,sannan ta gabatar masa da abinci da ruwan wanke hannu,ta zauna nesa kadan dashi tana ci gaba da shayar da iman wadda ke rigima saboda bata qoshi ba,ta sakeyi masa sannu da xuwa

“Yauwa sannu binta,ya hidima ya gida”

“Alhmdlhi” ta fada tana dan murmushi,duk data saba da irin wannan kulawar tashi,amma duk sanda ya tambaya din hakan yana mata dadi,saboda tasan cewa mata da yawa ne suke neman hakan basu samu ba

“Wannan yaron da kike gani sunansa lamin,na tsinceshi ne a can unguwar da naje nida saddiqu dubiyar abokina,abinda ya bani mamaki yaro qarami yashe gaban famfon tuqa tuqa,jikinsa duka tabo na duka,yasha ruwa yanata amansa,wadda ina tsammanin babu komai ne a cikinsa,yayimin kama da almajiri don haka na matsa kusa dashi,sai daya dan rage aman na tambayeshi sunansa da kuma inda yake,yamin bayani,ashe almajirin makarantar malam dan lami ne,sai na tuna kwanaki uku da suka wuce tabbas naji ana neman wasu cikin daliban,na tambayeshi me yakeyi to a nan,kansa tsaye ya shaida min guduwa yayi,na masa fada na kuma nemi dalilin da yasa yabar makarantarsu,shi baya jin tsoron wani abun kada ya sameshi,a yadda na fahimta tsoron malamin da makarantar yafi tsoro akan duk abinda zai sameshi,abun takaicin kudi malamin yake sanya musu duk ran laraba,kowa sai ya kawo wadan nan kudaden,idan kuma ba haka ba,zai ma yaro duka mai tsananin da zai gwammace koma ta yayane ya samo ya kawo masa,to shi kusan duk sati sai an dakeshi,saboda baya iya kawo komai,don yace bazai iya yadda sauran sukeyi ba,don cikinsu harda masu sata don kawai su kawo,lamarin ya dagamin hankali,na daukeshi na maidashi gaban malamin,duk da inajin tausayinsa,amma babu gatan da xanyi masa da ya wuce hakan,saidai abun mamaki abun takaici kuma abun haushi,sanda naje ga malamin,tunda ya tambayi waye ni ya fara yimin wani kallo,nasa ma’anar kallon,tunda sarai nasan waye malam dan lami,yana daga cikin masu adawa da tsarina,amma ni hakan bai dameni ba,burina da fatana shine kowa ya gyara,tun kafin nakai ga cewa komai ya soma dakawa lamin tsawa,tare da jifansa da miyagun sunaye da kuma kalamai,ya kuma fara hanqoran neman manya cikin dalibansa su dauke lamin su saka masa shi a mari,abinda bai jima da fita daga ciki ba,a nan na nuna masa nima ainihin xafina,na hana kowa yaxo wajen ya taba yaron,a nan malam dan lami ya tada husumar cewa dalibinsa ne,kuma babu wanda ya isa ya hanashi yi masa duk hukuncin da yaga dama,tunda a hannunsa aka danqashi,indai kuwa bazai hukunta laminu ba,saidai yabar masa makarantarsa,ya koreshi,ya kori yaron ba tare daya tsaya yaji meye zance ba,bai tsaya yaji me yaron shima zaice ba,bai kuma sanar da magabatansa ba bare susan ina yaronsu ya koma”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button