KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Na gode yaya”

“Amma garin yaya kikayi dare haka?” Dan raurau tayi da fuskarta

“Allah yaya munira na raka wajen event din cousin dinta,kuma ta yiwa inna bayani”

“Ki kiyaye please,kinga ke Queen ce,bai kamata sarauniya guda a dinga ganinta a araha a waje ba har dare” murmushi ya sake subuce mata,ta gyada kai tana murza yatsun hannunta,daidai sannan sadiqu ya fito daga bandaki

“Zubamin nima ina zuwa,abu me sanyi yau nake sha’awar sha” ya fadi yana nufar qofa

“Inna tana kiranka ma”
“Tom” ya qarashe amsa matan yana ficewa.

      Yana cin abincin yana satar kallonta,sake kyau da zama cikakkiyar budurwa take,hatta da fuskarta ta nuna hakan balle gangar jikinta,kamar ma so take ta haura shekarunta,tana dagowa suka hada ido,sa ya mata nuni da wata leda

“Ga mayafinki can” cikin murna ta tashi ta dauko tana dubawa

“An gode yaya,Allah ya qada budi,amma yaya kala biyu ne fa”

“Wannan zai hau kowanne kaya cikin ankon,kiyi amfani dashi,daga baya saina sama miki dayan” kai ta gyada kawai,amma bataso hakan ba,saboda anyi duka qawayensu kala daya zasu saka.

     Tana maidashi cikin ledar sadiqu ya shigo da lemukan a hannunsa,ya miqa mata wasu

“Ki dauki daya ki kaiwa inna sauran” ta karba tayi godiya sannan ta fice.

      A wajen inna abincinta ta karba tace zataci a daki,hankalinta da tunaninta duka ya koma kan wayarta,koda ta shiga dakin,kunna wayar shine abu na farko data fara yi,tana gama kunnuwa saqonni suka fara rigen rigen shigowa a jere kusan guda biyar,saita koma ta zauna,murmushi na subuce mata tana qoqarin budawa ta karanta.

[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 15
YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:

THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME

DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN???????? 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU

KHUMRAHS
KULACCAMS
TURARUKAN WUTA
NA TSUGUNNO
NA KAYA
NA GIDAH
NA GASHI

NA WANKA
NA WANKI
NA MOPPING

AIR FRESHENER
CURTAIN AND CHAIRS SPRAY
WARDROBE BALLS
SCENTED PEBBLES

ARABIAN OIL PERFUMES
HAIR SPRAY AND CREAM
DILKE AND HALWA SET

KABBASA
BURNERS
KASKO
TONGS
COAL IGNITERS

SKIN CARE PRODUCTs
OUR TURARE SAMPLE SETS
BRIDAL SET (SAITIN AMARE)
KUJERAR TSUGUNNO

SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA

MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE

SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED

instagram:yerwaincense_and_more*

WhatsApp: 08095215215


    Dukkan saqonnin nasa suna tafe da kalaman dake nuna rudun da ya shiga kan katsewar wayar da kuma jinta a kashe da yayi bayan ya sake kira,magiya yake mata kan ta taimakeshi ta buda wayar tata,ta daure tayi kiransa,murmushi ta kuma saki,yanzu kashe wayarta kawai ya sanyashi a damuwa?,wanne irin so ne wannan?,har ta dannan kiransa ta fasa ta katse,ta ajjiye wayar ta jawo abincinta tahau ci,saidai tana ci gefe guda kuma zuciya da qwaqwalwarta suna dawo mata da abubuwan da suka faru wunin yau,tun daga haduwarsu kawo yanzu,duk kyanta da yake fadi gani take ya fita,saita miqe ta isa gaban mudubi tana qarewa fuskarta kallo,kalamansa a kanta na dawowa kanta turyan turya,sai ta kuma sakin murmushi,ta juya ta dauki kwanon abincinta da kayan ciye ciyen bikin da muniran ta hadota dashi don ta kaiwa inna ko zata iya cin wani abun a ciki.

Washegari****. Da saqonsa tayi karin kumallo,wasu irin shiryayyun kalamai dake dauke da dandasa dandasan kalaman zallar soyayya,dolenta murmushi ya subuce mata bayan ta kammala karantawa,yakansa ta shiga mamakin wai ita din me muhimmanci ce har haka?,itama ashe watace data cancanci samun qauna maqura?,tana wannan tunanin saiga kiransa,ta sake yin sauri wajen saka wayar a silent.

         Sai data katse ya qara kira sannan ta daga

“Beauty…..girmanki ne,amma kuma so kike na haukace na kasa aiwatar da abinda ya kaini abuja?kinsan kuwa samun hadin kanki shine kawai abinda zai bani nutsuwar aiwatar da abinda naje yi din?” Murmushi ta saki a boye

“Ni wacece da hakan zata faru da kai?”

“Kina mamakine ko kina tantama?,lallai da alama har yanzu bakisan irin matsayin da kike dashi a wajena bane,kinsan tunanin kina da wani masoyin da ranki keso kadai daga jiya zuwa yau ya sanyani nayi zuru zuru,zakiyi mamakin yadda na koma,please beauty……kicemin ni kadai ne wanda ya fara yaqin neman soyayyarki,duk nasan mafarkine kawai nakeyi,amma mace kamarki lodi lodin maza nasan ke gware a kanta” yadda yake maganar cikin laushi da sanyi ya bata dariya,har batasan tace dashi

“Kai kadai ne” ba,wani qaramin ihu ya saki,wanda yake nuna zallar farincikin da zuciyarsa ke ciki

“Yes…..kice na sanar da mommy a daidai” idanu ta zaro

“Me?” Ta tambayeshi cikin mamaki da fargaba

“Eh, already labarinki yaje wajen mommy,tun a jiyan ban iya barci ba sai dana gaya mata komai dana sani game da ke,infact ma ita harta matsu taga beautyna,na gaya mata,ta qara haquri har na shawo kanki tukunna”

“Bassam” ta kira sunanshi a karon farko

“Nifa na yiwa yayana alqawarin bazanyi soyayya da kowa ba, already ma yace shine zai zabarmin miji” wani mummunan faduwa gabansa yayi,take ya rikice mata,har abun yayi matuqar bata mamaki,da gaske yake kan duk abinda ya fada,da gaske ne yadda yake kururuwar sonta

“Please give me a chance beauty,ki bani dama….na miki alqawari indai na kasa sace zuciyarki da samun soyayyarki zan amshi sunan looser,zan kuma rabu daki,amma na tabbata yayanki baya nufin abinda ya fada” sai data ce ta bashi damar sannan taji salama da sukuni cikin muryarsa.

     Da hanzari tayi masa sallama tana katse wayar,ganin ya kusa cinye mata lokacin aikinta,ta cusa wayar qasan pillow,sannan ta janyo dankwalinta ta daure sassalkan gashinta ta futo tsakar gida,qirjinta cike fal da bitar kalamai da al'amuran da suke gudana tsakaninta da bassam,tun daga haduwarsu kawo yau.


      Tana tsaye a kitchen tana dama kunu,tayi nisa cikin tunaninta,a hankali ya qaraso bakin qofar kitchen din,idanunsa suka sauka a kanta

“Assalamu alaikum” yayi sallama cikin tattausar muryarsa dake cike da wata irin nutsuwa ta halitta,ta waiwayo a hankali suka hada ido,sai ta saki murmushi tana dan motsawa kadan

“Wa’alaikumussalam,ina kwana ya amin”

“Lafiya qalau queen,ki tashi lpy?”

“Lpy qalau…..”

“Ma sha Allah,na godewa Allah da queen ta tashi lpy” murmushi ta sake,sai taji kalamansa na mata kama dana bassam

“Zan samu ruwan dumi?” Tunda taji haka tasan daga motsa jiki ya dawo,shi yasa suk safiya bata rabo da ruwan dumin saboda shi,matuqar tana kitchen din,tasan yana shigowa zai nema

“Eh yaya” ta fada da sauri,tana juyawa zuwa inda ta ajjiye flask din ruwan zafi,ta fara zuba masa,idanunsa na biye da ita.

     Daidai yadda tasan zai iya sha ta zuba ta miqa masa,hannu biyu yasa ya karba

“Na gode” murmushin da ya sake fidda dimple dinta tayi,tana jin kunya ta masa abu ya gode mata.

   Ta zaci fita zaiyi a kitchen din,amma sai taga yaci gaba jingina da qofar,yana kurban ruwan yana binta da kallo,yana monitoring duk wani motsinta,wutar qaunarta tana sake ruruwa cikin ransa,yana jin cewa lokaci kadan ya rage komai yazo qarshe,banda ma delay da ya samu naci gaban karatunsa yadda yaso,da tuni zuwa yanzu komai yayi nisa,saboda ya riga ya tsara ci gaba da karatun iman din a gidansa,hankalinsa sai yafi nutsuwa da hakan

“Akwai wani abune yaya?” Ta tambayeshi cikin jin kunya da kuma nauyinsa,miskilin murmushinsan nan mai cike da nutsuwa da wata izza izza ya sake,ya tashi daga jinginar da yayi ya tako zuwa kitchen din,ya dora mata cup din kusa da ita

“Babu komai…..kawai ina kallom queen dita yadda take qara girma kullum tana zama ‘yar budurwa”

“Kai yaaya” ta fada da sauri tana sunne fuska,shi kuma ya saki ‘yar qaramar dariya mai sauti kadan,ya taka ya fita a kitchen din.

     Wunin ranar gaba daya bassam bai barta ta huta ba,kowanne motsi nashi sai ya gaya mata ga abinda yakeyi,duk wani schedules nasa daga safiya zuwa dare tsaf sai data sani,tamkar tare suke aiwatar da komai.

    Ko wajen kamun surayya haka tayita fama da saqonninsa,yayin da munira ta hanata sakat da zancansa,batasan ya akayi ba sai ji tayi qawayenta sun fara tsokanarta da MRS BASSAM,kowacce a cikinsu cewa take

“Gaskiya ba qaramar sa’a kika taka ba,yaro ne matashin saurayi da jini ke zagayawa a jikinsa,yaro ne da kudi amma hausawa sukance abokin tafiyar manya, friend dina ne a insta,kije kiga yadda ‘yammata ke rushing a kansa,daya daga cikin qawayensu ta fiddo wayarta,ta shiga account dinsa na Instagram ta buda mata hotunansa ta miqa mata.

     Ta jima riqe da wayar a hannunta tana bin duk wani abu nashi daya dora a can,ta yadda da duk abinda suka fada din,daga kan hotunansa dake kan shafin nasa zakasan ba qananun kudi yake riqewa ba,kowannw hoto sutturu na alfarma ne a jikinsa,rabu da matan social media da kyakkyawan namiji,tarin followers ne dashi jingim maza da mata,abun ba'a cewa komai,kowanne hoto nasa ko wata magana da zaiyi,zaka tadda tarin comments da likes rututu a qasanta,ta sake gyara zama tana bin wallafar tasa.


     Ba qarya bane,komai yaji tattare da bassam din,ta sauke ajiyar zuciya tana sakin murmushi sanda wata 'yar ajinsu da ba wani magana suke da ita can can ba ta shigo tana tsokanarta itama da mrs bassam

“Ya hadu guy din,bazan boye miki ba,nayi iya qoqarin na sameshi,to amma nasan ni ba type dinsa bace,shi din sai kyawawa dama irinku,ina tayaki murna gaskiya iman” murmushi kawai iman din ta bita dashi tana sake maida idanunta kan fuskar bassam.

   Kwana biyu sukayi suna casar biki,tana zaune qawayenta nata liqi wa amarya,saboda tasan ita din bata da kudin da zatayi liqin,sai daga bisani ta bude jakarta dauko wayarta don duba lokaci,batason ta sake dare kamar na rannan idanunta suka sauka kan kudin da bassam din ya bata,bata taba komai ba a ciki banda kudin transport datayi musu ita da qawayenta,saita zari masu yawa a ciki,itama ta isa saman stage t fara liqawa ango da amarya,take taji kanta daidai da sauran qawayenta dake wajen,suka dauki ihun sai mrs bassam,abinka da zuciya da kuma aikin dan adamtaka,sai taji kata yana fasuwa a hankali,sannu sannu sai datayi liqi me yawa da ya sanya mc kama sunanta sannan ta sauka ta kona gurin zamanta,cin maganinta ya sanya samari da yawa dakeson kawo mata caffa suka kasa qarasowa inda take.


    ********Washegari**********
 Wunin sakina,ranar ne kuma za'a kaita,saidai dukkaninsu basuje ba sai yammaci,dukka qawayen suka hadu,cikin daya daga cikin lafayoyinta da bata taba sanyawa ba ta shirya kanta,duk tafisu tsada shi yasa ta zabi ta sanyata,milk color ce me haske,sai adon gold a jiki,takalmin qafarta me tsini ne kuma mai tsinin dunduniya,ta ciki wani lace ta sanya mara nauyi,wanda ya amin yayi mata dinkin straight skeet da riga me dogon hanu,ta tara gashinta tayi masa nadin alkaki ta qasan daurinta samfurin ture kaga tsiya.

      Fadin kyan da tayi a lokacin bata bakine,saika rantse da Allah daga gidan wasu hamshaqan ta fito,saboda kulawa da take samu gami da sutura me kyau,kowa kaffa kaffa da dama dama da ita yake cikin qawayenta,abinda ta lura dashi ya fara faruwa tun sanda munira ta shaida musu bassam shine masoyinta

“Komai yaji,wanka iya wanka,amma wallahi kika fito da wayar hannunki sai naji kamar zan nutse” munira ta fada dai dai yadda iman dince kadai zata iya ji.

       Sauke wayar tayi tana duban munira,wanda dama ta dauko wayarne saboda jin qarar shigowar saqo,wanda kuma take da yaqinin ba daga kowa yake ba illa bassam

“Kinyi kyau iya kyau baby…….,yanzu na shigo gida daga tafiya,amman bazan iya daurewa ba…..sai nazo naga wannan kwalliyar beautyna” wannan shine saqon da taci karo dashi,wanda mamaki ya kamata kan ta ina ya hangi adonta.

   Maimakon ta bawa munira amsar maganarta saita buge da tambayarta

“Ya akayi bassam yaga kwalliyata?” Idanu munira ta wara

“Wallahi ban sani ba,shida baya nan yana abuja?”

“Ya dawo gida yanzu,kuma yana zancan zuwa ya ganni ba tare daya nemi address ba,bari naga gudun ruwansa,ta ina zai lalubo ni?” Ta fada tana gyara zamanta gami da gyara rufin lafayarta.

      Murmushi munira ta saki

“Har yanzu bakisan waye bassam ba,mai kudin da idan yaso zai iya sanin duk wani motsi naki,amma bari mu gani,da rabon muje gidan amarya a lafiyayyar mota” munira ta fada cikin murna,batabi ta murnar munira ba,don tasan babu lallai yazo din,tunda baisan ina suke ba,saita dan goce kadan ta jingina da kujerar dake daura da ita.

     A hankali zuciyarta da qwaqwalwarta suka shiga tunani,suka shiga hasko mata fuskokinsa data gani cikin hotunansa na ista cikin mabanbantan yanayi da shiga kala daban daban,tarin tulin 'yammata daketa commenting akai,da kuma qoqarin jan hankalinsa zuwa private chat,a hankali taji shauqin son ganin fuskar tasa na saukar mata,saita lumshe idanunta tana bitar lausasan kalamansa da suka zame mata abokai cikin kwanakin nan,dasu take kwana dasu take tashi,ta kuma hadasu da fuskarsa iya shiga da tsari na jikinsa,take taji komai yayi mata dari bisa dari,sai ta lumshe idanu tana sauraren hirarrakinsu,tare da kasa kunne taji xai kirata ko zai turo saqo ya nema address?.*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*

16

   Taji mamaki sosai sanda yake shaida mata yana qofar gidan,ta dubi munira duban tuhuma,ta daga hannayenta sama alamun ba ruwana.

     A matuqar darare fa shiga motar sanda ya bude mata da kansa ya mata izinin shigar,shima saboda idanuwan yammata dake qofar gidan ana shirye shiryen daukar amarya da sukayi musu caa kamar zasu cinyesu.

     Nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana shafar qirjinsa

“Thank God,sai yau dana ganki sannan naji kamar an ciremin qaya, beauty,i really missed you” kunya ce tadan saukar mata,taja lafayanta ta sake boye fuskarta ta murmushi

“I liked it baby,inason kunyar nan taki,amma dai ya kamata adan fara rageta,a nunamin soyayya ko?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button