KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

     Haka kawai ya samu kansa cikin rashin nutsuwar da yake da tabbacin ya fada kogin soyayyar iman ne farat daya,ya dinga satar kallonta lokaci bayan lokaci,har sai da iman din ta ankara,ta kuma tsargu,tare da tuhumar kanta na meye xata shiga motar wasu,koda rana zata kasheta?,sai ya basar,ya fara soko musu hira,yana kuma jan iman din din

“Wanne layi zamu shiga?” Ya tambayi iman din kai tsaye,idanunsa na kanta ta cikin mirror

“Ya isa,anan ma zan sauka” ta fada tana sake gyara jakarta

“A’ah,ai da kin barmu mun cikasa ladanmu ko?” Ya fadi yana dan saki murmushi,munira ma ta saki nata tana gyada kai

“Aikuwa dai”

“A’ah na gode,babu nisa,zan qarasa da qafata” bai sake cewa komai ba ya fara qoqarin faka motar,sannan ya saka hannunsa a aljihun gaban motar ya budeshi,ya ciro wrapper din ‘yan dari dari sababbi ya miqa munira

“Bata,tasa kati a waya”
“Ina taga waya,saidai tasha chocolate” munira ta fada cikin sigar zolayar iman tana miqa mata kudin.

   Kememe iman taqi amsar kudin,saima ta soma takawa tayi gaba abinta tana cewa sai gobe

“Ni nasan ba zata karba ba,amma ka barni da ita,zan kai mata gobe” tace da sadam,saiya sauke ajiyar zuciya,cikin kasala ya tada motar

“Ban taba ganin yarinyar data yimun ba irin qawarkin nan ba,ki shigemin gaba don Allah na mallaketa” dariya munira ta saki

“Karka damu,indai zaka saki kudi duk ba zaya gagara ba”

“Mayyar kudi,bansan ina zakikai son kudi ba muni” dariya ta sake

“A’ah ya sadam,kudi fa abun sone,babu meson wahala ko talauci,ko aikin nan da kake yanzu ba kudin kake nema ba?”. Murmushi yayi kawai,don yasan wajen magana badai a kada muniran ba,gaba daya shi yanzu hankalinsa ya tafi ga iman.

     Koda washegari taje mata da kudin makaranta cewa tayi ba zata karba ba wallahi,harda qarin handset daya siya ya dora mata akai,kusan fada sukayi da iman din akan hakan,ita ta dage saita karba,dan uwanta ne,kuma babu dadi maida hannun kyauta baya,yayin da iman din tace sam batasan wannan zance ba,kawai daga haduwa da mutum sai ta karbi abun hannunsa?,tace waye ya bata ma a gida?. Wani kallo muniran tayi mata

   "Au daman duk yammatan da samari ke musu kyauta nunawa suke a gida suce wanene ya basu?,kowacce boyewa take tayi amfani dasu abunta,ki karba kawai,don gaskiya bazan iya maida masa ba,don bansan bayanin da zanyi masa ba"

     "Ki riqe na baki kyauta tunda ba zaki iya mayarwa ba" 
      "Bani ya bawa ba,amma zan ajjiyesu har zuwa randa zaki amsa" ta fada cikin bacin rai tana zuge handbag dinta ta jefasu ciki,zancan bikin qawayensu guda biyu dake matsowa da aka zauna yi shi ya raba gardamar,duk da haka muniran bata sauko ba.

      Koda aka tashi tun daga bakin gate ta lura da motar jiya ce tazo daukan muniran saita zame ta gudu,ta canza hanya ta shiga motar haya tayi gida,washegari ta dinga mita da qorafi iman din tace da ita

“Kada ma ki soma batawa kanki rai,don Allah bazan sake shiga motar wani a gida baa sani ba” tasan da gaske take idan tayi magana,don haka bata sake cewa da ita komai ba,sai kumbure kumbure da take mata alamun tashi fushi,dariya ta saki

“Kyayi ma ki sauko” amsar da iman din ta bata kenan.

      ********.  ******.  ********

    A nutse ya ajjiye almakashinsa saman keken da yake kai,sannan ya miqe ya nufo inda iman ke zaune saman wani stool tana fuskantarsa.

     Ganin ya dosota saita dauke idanunta a hankali,ya saki qaramin murmushi da ya sake qawata fuskarsa,ya zauna saman wani keken dake daura da ita,ya dora qafarsa daya saman wata kujerar roba da babu kowa akai.

     Shagon nasu yanzu babu kowa sai wani dan matashi guda daya daketa faman dinki,da alama masu kayan suna hanya ne,koma bayan sanda ta shigo din da yake cike da matasan,sunata shirin fita wata ball ta abokinsu,shi dinne yace ba zashi ba,don ba wani abokinsa bane na kusa,saboda dama ba mutum ne shi me tara abokai da yawa ba.

     "Banfiyason zuwanki shagon nan ba,kina ganin dai yadda kullum yake cike da mutane" dan turo baki gaba tayi

   "To ya alameen,idan ka dawo gida inna ba zata bari muyi magana bafa.......kuma lokaci yana qurewa,bikin gaba daya saura uku" idanu ya zubawa lips din da take turowar,kamar ya kama ya tsotse haka yakeji,saiya dauke idanun nasa yana tattara kansa waje guda

      "Me yasa baki kirani a waya ba?" Saita fidda idanunta duka a kanshi

“Ka manta ne,inna ta hanani taba wayarta,tace ina qarar mata da kati”

“Haba da Allah haba,ya zaayi ace budurwa kamanki aron wayar inna kike?,ai kinfi qarfin haka,wani idan ya ganki zai zaci babbar iPhone ki manya manyan Huawei kike riqewa” ya fada da salon tsokana.

      Kallon da al'ameen ya jefeshi dashi yasanya shi jan bakinsa yayi shuru,kafataninsu sunsan halinsa baya daukar wargi,hatta da ogansu me shagon wani lokaci kamar shakkar al'ameen din yake saboda kwarjinin da Allah ya zuba masa,uwa uba kuma mutum ne shi mai tsaiwa akan gaskiya,idan kaga ya dage kan abu,to idan akayi zuzzurfan bincike shine me gaskiya

       "Bani mu gani" ya fada yana miqa mata hannu,sai tabi hannun nasa da kallo daya nannade hannun rigarsa zuwa gwiwar hannu saboda yaji dadin kallo,cike yake da gargasa da jijiyoyin da zasu shaidamaka cikin jikinsa a murde yake,kuma qaqqarfan namijin duniya ne.

     Kunya ta kamata sanda ta miqa masa yankin atamfofin guda biyu taga ya janye hannunsa yana jan hannun rigarsa yana rufe hannayen nasa,idanunsa kuma na bisa fuskarta,da alama yaga kallon data bishi dashi kenan.

     Murmushi ya saki sanda taja hijabinta ta kare fukarta,yana qoqari yaga ya gujewa duk wani abu da zai sanya taji wani abu tattare da ita,bayason ya raba mata hankali tun yanzu ko yayi cikakken wasa da hankalinta,saidai lokaci yana nan zuwa da zai mantar da ita kowa cikin duniya saishi kadai.

       Tana miqa masa ta sauka daga kan kujerar don ba zata iya ci gaba da zama ba

“Qawata zata kawo dinki yaaya don Allah,kada kace aiki ya maka yawa”

“Karta damu,indai ta wajenki ta biyo”

“Saika dawo” ta fada tana masa sallama,bai amsa ba illa binta da yayi da kallo,kominta a nutse kuma a tsare Allah yayi mata shi,yana jin sara qiris ya fara tilastata sanya niqab,yana jin ciwo cikin qirjinsa da zuciyarsa duk sansa ta fita koda makaranta ne,yafi jin dadi da samun nutsuwa udan ya dawo gida ya sameta cikin gidan.

     Wani irin shauqinta yakeji yana fusgarsa har ta bacewa idanunsa,ya sauke ajiyar zuciya yana sauka dubansa ga qyallen atamfofin data bashi,ya daga kai a hankali ya dubi matashin daketa aikinsa

“Yahaya……ka dubamin atamfar nan don Allah ka gaya min kudinsu gobe ko jibi”

“An gama” ya fada yana miqewa tare da miqa hannu ya karbesu.

. . ******

   K'arfe hudu da minti ashirin da hudu wayar inna ta kada,iman data kai jug din data hadawa munira lemo kitchen ta dire da sauri ta dawo ta daga tana amsa kiran,munira ta tsammata,kuma ita dince,saita aje wayar tana jan babban hijabinta ta dora saman atamfar dake jikinta,wadda al'ameen ya zauna ya bata lokaci sosai ya tsara mata dinki na gani na fada

“Inna zan leqa waje na shigo da ita”
“Saikin dawo” inna dake zaune tana qoqarin gyara saitin radio dinta ta fada,tana son ta kamo freedom radio don jin shirin mu qyaqyata kafin biyar na yamma tayi. Slippers dinta ta zura ta tako zuwa soron gidansu.

     Gab da zata fita shi kuma yana qoqarin shigowa,saura kadan suyi gware,taja da baya tana yarfe hannu tare da yamutsa fuska,abinda ya taimaka qwarai wajen fitowar dimple dinta duk sanda ta motsa fuskarta,yayin da shi kuma yaja da baya yana qare mata kallo.

     Yana iya hangen yadda tayi wani kyau duk da cikin hijabi take,yana jin shi daya ne a duniya yake iya ganin kyanta koda cikin lullubi take,kuma a kanta kadai yake da wannan baiwar

“Ina zakije?”
“Qawata din nan da zata kawo maka dinki zan shigo da ita”

“Koma ciki” saiya koma da baya ya qwalawa daya daga cikin almajiran gidan kira,yace ya duba layin,idan yaga wata baquwa tana neman gidan nan ya shigo da ita,ya dawo ya zarce dakinsu sannan tuni iman ta kona ciki,duk da taso ya barta taje da kanta ta shigo da ita,saidai ba zata iya yi masa musu ba.

     Ba jimawa saiga sallamar munira,iman ta fito da sauri,suka rungume juna cikin murna,kamar wadanda suka jima basuga junansu ba,kai tsaye suka fada dakin inna.

     Cikin girmamawa ta gaida inna,innan ta amsa mata,sannan ta miqe ta fice zuwa dakin malam da tun daxu dama takeson shiga ta gyara masa kayan sawarsa ta barsu su biyu cikin rumfarta.

          "Hajar ibrahim khalil" munira ta fadawa iman wadda keta qoqarin zuba mata lemo da abinci bayan ta qarewa falon nasu kallo

“Munira sulaiman”
“Yaudai gani a gidanku,naga randa zakizo nima namu gidan” hararta tayi cikin wasa

“Aiba zuwana kikayi ba,kawo dinki ne ya kawoki ko?”

“Eh duk da haka,inda hakanne ma ai da shagon zan tambaya nakai musu direct,da qyar mafa yaron da kika aika ya ganoni” ta fada tana daukan lemon takai bakinta

“Nazo fita mukaci karo da ya al’ameen,shi yace na koma ya tura sa’idu” ajjiye lemon tayi

“Yaudai zanga ya alameen da zancansa ya cika mana kunnuwa aka hanamu sakat,ya al’ameen din nan me shegen tsauri da takura,hala ku biyu inna ta haifa kawai” kai ta girgiza mata tana murmushi

“Mu uku ne,kawai yaya sadiq”

“Amma ban taba ji daga bakinki ba” zamanta fa gyara saman kujera

“Barshi wannan,bamu cika shiri dashi ba” dan dariya muniran tayi suka ci gaba da casa hirarsu,har ta soma bata labarin bikin wata cousin dinta da zasu fara,wanda tsiran kwana ukune dana qawarsu amina,wadda ta kawo dinkin ankonta yanzun.

      Yadda taketa bawa iman labarin bikin da yadda aka tsara komai ya tabbatar mata tana matuqar ji da bikin,har ta zolayeta da haka

“Keee,ba dole ba,kinsan manyan mutanen da zasu halacci bikin?,inda naji dadi ana ya gobe dinner din amina zaayi kamu,ran dinner din amina ranar event din gidansu ango za’ayi ba namu bane,so babu lallai naje,washegari ne zaa tashi bikin gadan gadan”

“Wai ita aminan dinner zatayi?”

“Eh mana,wannan atamfar ai ita zaa saka ranar” tabe baki iman tayi,saboda ita duk wata harkar dinner ba zuwa take ba,bata damu da ita ba,koda ta damu dinma tasan ba dabi’ar gidan bace,babu me barinta

“To inajin babu ni a zuwan”
“Saboda me?,ya al’ameen zai hanaki ko?” Dariya ta kubcewa iman

“Au,sharri zaki masa?har kinyi tafsiri ma?” Itama tana dariyar ta amsa mata

“Eh to ai nasan qarshen zancan kenan,nidai badon yayanki bane Allah cewa zanyi da wata a qasa,wannan tsanani da boyo haka?,barima dai ya shigo inga ya yake ya alamin din” maganarta saita dan shigi iman,duk da haka tana dariya ta miqe

“Yama fa shigo gidan amma kin jishi shuru,bari na duba koya gama na masa magana” ta fada tana ficewa,ta manta bata dauki hijab din nata ba.

LITTAFIN NAN NA KUDI NE,KI TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN DON BIYAN KUDIN NAKI

09032345899
KO KUMA
09166221261
[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 12

YERWA INCENSE AND MORE: MASARAUTAR KAMSHI:

THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME

DO YOU WANT THAT MAIDUGURI AND SUDANIAN SCENTS THAT LASTS LONGER AND LINGERS? YERWA INCENSE AND MORE GOT YOU AND YOUR BELOVED ONES COVERED WITH LUXURIOUS SCENTS. KAMSHIN YAN YERWA DA SUDAN???????? 20% OFF ORDERS. MUN CIRE KASO 20 NA KUDIN KAYAYYAKIN MU

KHUMRAHS
KULACCAMS
TURARUKAN WUTA
NA TSUGUNNO
NA KAYA
NA GIDAH
NA GASHI

NA WANKA
NA WANKI
NA MOPPING

AIR FRESHENER
CURTAIN AND CHAIRS SPRAY
WARDROBE BALLS
SCENTED PEBBLES

ARABIAN OIL PERFUMES
HAIR SPRAY AND CREAM
DILKE AND HALWA SET

KABBASA
BURNERS
KASKO
TONGS
COAL IGNITERS

SKIN CARE PRODUCTs
OUR TURARE SAMPLE SETS
BRIDAL SET (SAITIN AMARE)
KUJERAR TSUGUNNO

SABULAI NA GYARAN JIKI DA SAURAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAMSHI . KOMAI DA KOMAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA

MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KO’iINA A FADIN NIJERIYA DA KETARE

SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH, 100% TESTED AND TRUSTED

instagram:yerwaincense_and_more*

WhatsApp: 08095215215


  Tun daga bakin qofar dakin nasu qamshin turarensa ke karakaina,ya cika soron gaba daya,taja numfashi sosai ta sheqi qamshin,tana matuqar son qamshin turarensa,har yau kuma bata taba jin kowa da irinsa ba,babu abinda yake kashewa kudi sosai wajen siyansa irin turare.

        Knocking tayi yace a shigo,ta tura qofar a hankali,idanunta suka sauka a kanshi,yana tsaye gaban mudubi yana ajjiye kwalbar turaren da ya gama fesawar yana qoqarin dora hula saman kanshi,yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,dinkin zamani daya fidda samartaka sa zallar kyan da Allah ya bashi.

     Ta cikin madubin ya kafeta da idanu,abunda bataso,sai ta kauda da kanta tana cewa

“Yaaya,ta iso tun dazu tana jiranka”

“Ganinan fitowa,wani waje zani na tsaya ne na shirya gaba daya kar na saba alqawari” ya fada yana daura agogon hannunsa,saita gaza tafiya yaci gaba da satar kallonsa har ya fuskanci haka,ta basar da sauri,sabida wani iri takeji da ganin kwalliyar da yayi din

“Yaa ina zaka da yammar nan” sai daya gama daura agogonsa tsaf sannan ya amsa

“Akwai wani da muka hadu da yace nakai takarduna,wala’alla idan da rabo zan samu scholarship,tunda suna da hanya”
“Allah yasa a dace” tayi masa addu’ar da har cikin ranta haka yake
“Ameen qanwata,na gode” tadanyi murmushi sannan ta miqe ta nufi hanyar waje.

    Cikin tattausar muryarsa yayi sallama cikin falon,munira ta daga kanta daga danna wayarta da takeyi tana amsa sallamar

“Wow”bakinta ya motsa ta furta kalmar qasan zuciyarta,ta gyara zamanta sanda suke magana da iman

“Karbomin fura wajen inna” ta amsa da to sannan ta miqe ta fita zuwa wajen innar,dakin ya danyo shuru,saiya qarasa kujerar dake daga bakin qofa ya zauna a hannun kujerar.

     Cikin fara'a gami da mutuntawa munira ta gaidashi,ya amsa kadaran kadaham,sanda iman din ta dawo da furar a cup ta miqa masa itama ta koma ta zauna.

       Sai daya fara kurbar furar a hankali cike da nutsuwa sannan yace

“Muga kayan” saita dauka ledar ta aje masa a gabansa ta fidda kayan tana masa bayani,baice komai ba harta gama yana shan furarshi,sai data kammala dai dai sanda ya gama sha ya miqe da cup din a hannunsa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button