Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Ad

_____

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
When ever u open this Document pls Pray for me 🙏🙏🙏

💖💖💖💖
💖💖💖
💖💖
💖 ABBAN SOJOJI 💖
💖💖
💖💖💖
💖💖💖💖

The father Of Soldiers

Story
&
Written
by
Hafsat Bature
~(Boss Lady)~

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Special thanks to Fadeela Lamido & Sadeeq Abubakar. Wannan littafin sadaukarwa ne a gare ku, jinjina ta musamman.

Proud Of My First Novel💋

Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina in kuma mutun yayi shi da Ubangiji 😇

Sa’an kada ki karanta Littafin nan in har yakasance lokacin Sallah ne !!! ko kuma lokacin da iyayenki suka saki aiki ko mijinki, in har kikayi hakan wlh ke zata shafa 👌

Page 1-2

Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, “Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani.”

“Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d’an iska!”

Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.
Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.

Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, “Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?”

Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, “Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon ‘yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi.”

Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, “Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?”

Girgiza kai ta yi, “A’a babu kowa, ba mu da kowa, ni da ‘yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!” Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.

Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, “Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!”

Riko hannunta ya yi tare da cewa, “Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji.”

Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d’an wani lokaci kafin ya ce, “Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu’a ‘yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su.”

Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman ‘yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.
Lekensa ta dinga yi tana kallon ‘yar butar karfen da yake dafa shayin da ita, ta burge ta musamman abin da ke cikinta. Kofin ya dauko ya tsiyaya mata a ciki, mika mata ya yi. Hannu biyu ta sa ta karba don rabon ta da ta ci wani abu a cikin ta tun jiya. Sannan shi ma ya zuba wa kansa a d’ayan kofin yana kurba yana ba ta labarin gizo da koki.

Sam ba ta gane me yake cewa, d’an ruwan bunun da ya ba ta ya dauke mata hankali saboda dadinsa musamman daya sanya sugar a ciki, a hankali take kurbarsa, kusan so uku tana shanyewa yana kara mata, a karshe ya ce “Aradun Allah shegen ci ne da kai ga shi harka shanye mini ruwan bununa, idan hajiya ta samo maka aiki ka fara yi sai ka biya kudin shayina.”

Murmushi ta saki tana sauraron shi tana mamakin yadda yake suffanta ta da namiji, ga shi shi dai ba makaho ba sarai ya gan ta da kayan mata a jikinta,
har marece ya yi hajiya ba ta dawo ba, da lokacin sallar Azahar ya yi da kansa ya bude musu kofar dake a jikin gate din suka shiga. Ruwa ya debo musu a buta, suka yi alwala tare sannan ya shimfida musu tabarma, shi ya ja su sallar yana gaba tana daga bayansa.
Bayan sun gama , suka ci gaba da zama a saman sallayar yana jan cazbi a hannunsa ita kuma ta shiga tunanin duniya, a haka har La’asar ta yi suka sake kabbara sallar, tun kafin su sallame yake jin karar motar hajiya alamar ta iso.

Dadi har cikin ranta yau dai Allah ya yi za ta gana da hajiyar nan, yana sallame sallar da sauri ya tashi ya bude mata kofa, ta shigo da dankareriyar motarta, wucewa ta yi da motar zuwa wajen ajiya. Zuge kofar ya yi sannan ya bi motar hajiyar a baya yana mata kirari kamar yadda ya saba.

Farinciki ya sa ta kasa rufe bakinta sai faman murmushi take yi, ba ta tashi daga samman sallayar ba, zama ta yi tana jiran maigadin ya yi wa hajiyar maganarta. Bude mata motar ya yi ta fito, ma sha Allah irin matan nan ne masu jiki ‘yar dumurmur da ita, ta ji hutu fara ce tas amma da alama tana karawa da man bleaching, jikinta na sanye da tsadadden leshi shudi wanda aka yiwa ado da stones, ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta kashe daurin kallabinta, hannunta na sanye da diamond rings, haka sarkar wuyanta ta diamond ce, kwalliya ce sama-sama a fuskarta tana da dara-daran idanu ga hanci dogo, tubarkalla, sai jan-baki da ta shafa ja ne.

Cikin girmamawa ya ce, “Barka da isowa hajjaju makkatu!”

Ya mutsa fuska ta yi da alamun gajiya a tare da ita ta ce, “Yawwa Aku sarkin dumi akwai wanda ya zo ba na nan?” Ta yi maganar ne a yayin da take bude kofar motar ta baya, saboda ba ita kadai ta zo ba akwai ‘yammatan da ta zo da su daga kyauye.

Maigadin ya amsa mata da cewa “E mutane sun zo sosai amma duk ban rike shunansu ba na dai ce musu ba ki nan kin yi tafiya, sai dai akwai yaro d’aya da ya zo neman ki kullum shai ya zo yau dai na ce mashi ya jira ki dawo.”

D’aga idonta ta yi tana hangen ‘yar yarinyar da ke sanye da hijab saman sallaya, mayar da idonta ta yi kan ‘yammatan da ke zaune cikin motar, ganin ta bude musu motar amma sun ki fitowa, tsaki ta ja tare da cewa, “Kwana za ku yi ne a cikin motar?”

Washe baki su ka yi wata mai surutu a cikinsu ta ce, “Hajiya wallahi dadi motar nan ga wani sanyi da ke ratsa zuciyata kamar kada na fito.”

Girgiza kai hajiyar ta yi tare da sakin guntun murmushi ta ce, “Ai irin wannan sanyin da kuke sha na A.C ne kuma in mun shiga ciki ma akwai A.C ko ina.”

Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button