KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Imani….ki dauka ki aje wajenki,idan zan fita jibi ki tunamin”
“To yaya” ta amsa masa sanda yake fita.

     "Wow....wow,wannan shine ya al'ameen?,badan wani abu ba da na saka kai wallahi" harara iman ta balla mata

“Ba zaki yaudararmin yayana ba,saboda nasan baida kudin da zaki tsaidashi takara” dariya ta saki,tabbas abinda ke cikin zuciyarta kenan,saidai ba zata iya fitowa kai tsaye ta gayawa iman din ba,tako ina al’ameen yakai namiji,abu daya ya rageshi rashin ‘ya’yan banki masu yawan gaske da zasu maisheshi wani,amma banda haka tabbas gawurtacce kuma isashen namiji ne.

      "Yanzu haka maganar ci gaba da karatunsa ce ta futar dashi" iman tadan bata labari

“Allah sarki yayanmu,Allah ya bada sa’a”
“Ameen” iman ta amsa mata,daga haka suka fada wata hirar.

. *Tana daga zaune gefan katifar dake shimfide dakin iman,bayan ta karbi dinkunanta da sukayi kyau sosai wanda al’ameen din yayi mata,wayarta na hannunta tana ta danne danne,da yake gwana ce qwarai ita din wajen danna waya,shi yasa babu inda ke mata wahalar shiga loko da saqo na kowacce irin waya

“Kiyi sauri don Allah muje kada mu samu layi” munira tace da iman wadda ke shiryawa zasu wuce gidan qunshi,saboda gobe zaa fara bikin qawartasu

“Na gama ai,hijabi kawai xan saka” ta fada tana ware gogaggen hijabinta me kyau

“Kiwa Allah ki aje hijabin nan,wallahi wajen ‘yan gayu ne sai kisa a dinga mana kallon tara saura kwata,ko kamar nawa mayafinne ki saka,tunda kinga dai babba ne,kuma bashi da shara shara” inan din ta buda baki zatayi magana munira ta dakatar da ita

“Nasan yanzu zaki kawo karatun ya Alameen,goben ma kenan haka zakiyi?” Murmushi kawai iman tayi,don kamar ta shiga zuciyartata,maganar al’ameen din ya hanata saka mayafai zatayi mata,saita aje hijabin,ta bude ma’ajiyar kayanta,ta ciro daga cikin sabbin lafayar da yagana ta bata,wata ‘yar uwar mahaifinta har guda biyar masu azabar kyau da tsada.

     "Kai kai kai,ke kinga kyan datayi miki kuwa,ma sha Alla,da ana musayar kyau Allah da tuni na karba naki na hadaki da nawa" munira ta fada cikin nuna santi da yabawa da kyan iman din tayi,wanda zahirin gaskiya gaskiya ta fada,wani kyau lafayan tayi mata,idan ka kalleta kamar ba zaka dauke ido ba,ita kanta dai data juya ta sake kallon kanta a madubi ta gasgata hakan.


     Tana tsaka da sanya halfshoe dinta da ya alameen ya siya mata 6k wanda ya dace da lafayar jikinta wayarta da ya alameen din ya bata tecno ta dauki tsuwwa,munira ta kalli sashen da wayar take,ta tuntsire da dariya tana cewa

“Ana kiranki a rakani kashinki?’ sai data manna mata harara sannan ta isa inda wayar take
“A haka nakeson kayata”

“Amma dai wallahi ba girmanki bane,dressing dinki sam bai kamaci wannan wayar ba” ta saba da jin wannan lafuzzan daga bakin muniran,don haka tayi banza da ita ta isa inda wayar take ta daga abunta.

     Sai data gama wayar ta dubi muniran

“Su hamra ne,already wai suna wajen,har an fara yiwa wasu,mu kadane bama nan”

“Nasan zaa rina dama,munyi delay da yawa” munira ta fada tana daukar ledar kayanta.

      Saida suka biya wajen inna,munira ta yiwa innan sallama da kuma godiya,ita kuma iman ta karbi kudin qunshin sannan suka fito suka wuce.

       AMARYAR KB BEAUTY PARLOR,katafaren wajen gyaran amare da uwayen gidaje,yammata harma da zawara,waje ne na alfarma wanda ya kasance iya kudinka iya shagalinka,wajene daya amsa sunansa,duk sanda kaje haka zakaga manyan hajiyoyi suna karakaina,suna dukkan wani nau'in gyaran jiki da kuma kayan magunguna na gyaran jiki da aka warewa waje na musamman a ciki.

       Amarya sakina itama iyayenta da danshinsu,hakanan wanda zata aura din shima ba baya bane,tun asali gidansu basu damu da karatun boko ba,kasuwanci sukafi bawa qarfi,don haka sanda miji ya fito mata ya kuma tabbatar musu zai siya mata dukkan wani certificate,basu wani jinkirta ba aka cireta daga karatun aka fara shirin auren nata.

     Tun daga shigarsu wajen iman tasan waje ne na matan da suka isa,dukkaninsu qawaye ne,saidai bata wani saba can dasu kamar yadda suka shaqu da munira ba,don haka bayan 'yan caftarsu ta qawaye da murnar shigowarsu,sai ta samu waje saman kujerun da aka tanada a wajen tayi zamanta,tana sauraren hirarrakin dake tashi a wajen,da kuma shige da ficen 'yan gayu mazansu da matansu.


       Hira suke irin ta matasan yammatan dakeji da tashen quruciya,dukkansu babu wadda ba daga babban gida ta fito ba,kusan ita daya ce ma kawai zaa ce  iyayenta ba wasu masu kudi bane,saidai ita din ma shigarta fes take,kai bakace hakan ba.

    Abu daya ne idan ka lura dashi zaka gane banbamcinsu,manya manyan wayoyin dake hannun kowaccensu,da kuma irin kudaden dake jakarsu,kowacce ta fito da tata tana harkar gabanta.

       Mutum uku cikinsu saida samarinsu sukazo har qofar wajen suka basu kudin lallaen da gyaran gashi,kowanne cikin babbar mota,hakan kudin da suka basu sababbin ne a rafarsu.

       Kafin zuwan nasu suka saka gasa,duk wadda kudin da aka bata yafi na sauran yawa ita zaa fara yiwa,daga qarshe fahima ita ta cinye,dole ita aka saka za'a bari a fara yiwa.

      Ita dai nata idanu,sai wata matashiya dake kusa da ita wadda batafi sa'arsu ba da aka sawa lalle,tun dazu ake kiranta babu me daga mata,don haka iman din ta matsa kusa da ita

“Bari na daga miki”
“Yauwa na gode” ta fada a yagance tana murmushin jin dadin hakan da iman din tayi mata,ta riqe wayar da kafadarta ta fara amsa kiran,murya can qasa,wanda da alamu saurayinta ne ya kira,don sunyi doguwar waya sosai,har aka gama yiwa amarya sakina qunshinta da qawarta da sukazo tare,ango yazo daukarta,dukka suka tashi mata takiya,munira na cewa sai sunje sun gaisa.

     Ko alamar motsawa iman batayi ba,amma munira ta finciki hannunta,dole ta bisu.

     Yana jingine jikin fara qal din motarsu,wadda da alama sabuwa ce,su biyune shida wani matashin saurayin kamarsa,cikin fara'a da barkwanci irin na angwaye da qawayen amarya,tana tsaye daga gefe tana kallonsu,don ita komai ma sabo ne a wajenta,saboda wannan shine karonta na farko na bikin qawa a waje,ko cikin dangi ma ba kasafai take zuwa ba saboda nisa da suka dan mata,daga na uwa har na uban,sai dai daiku dake nan garin da suke.


     Kowa cikinsu ta fara gabatar masa da kanta da kuma sunanta,har aka gama,munira ta waiwayo

“Matso mana iman” abinda yaja hankalin angon da abokin nasa kenan”

      Idanu abokin ya zuba mata sosai,ya furta

“Subhanallah” har zuwa sanda ta iso idanunsa yana kanta

“Itama cikin qawayenku take?” Saurayin me suna hashim ya tambaya bayan ta gama gaidasu

“Eh….iman,ba kasafai ta fiya son shiga jama’a ba ai”

“That’s good” ya fada yana gyada kai,still ita yake kallo,abinda yasa ta takura kenan,taja da baya tana fadin

“Bari naje kafin ku gama,kada azo kanmu babu kowa”

“Wait iman….ki tsaya ki karba kudin liqi mana” kafada ta daga

“A’ah,na gode sosai wallahi” daga hakata qara sauri tayi ciki tana mita cikin ranta,gaba daya batasan me yasa mazan yanzu suke da shegen kallo ba.

      Basu jima sosai ba suka dawo,sauran su uku kenan da suka rage ba'a yiwa ba

“Haba iman…..haba da Allah,me yasa kike abu kamar baki waye bane,ke dan samarin nan ma na yayi da akeyi ki kasa yi,guy iya haduwa amma ki yarfashi ki taho,ke kinga yadda ya rude da zancanki bayan kin taho,Allah annabi a hadaki dashi?,at last dai dole muka bashi number dinki” idanunta ta zaro

“Me yasa zaku bashi don Allah,me yasa zakuyimin haka?” Ta fada adan rude,dukkaninsu suka sanya dariya

“Seriously da gaske nake,yanzu me zance da ya al’ameen idan yaga wani ya kirani?”

“Waima…..wai.ya al’ameen,to meye a ciki?,shi kansa yasan kin isa a kirakin,waima idan bai bari an kirakin ba,jiqaki zaiyi yasha?,a yadda Allah ya halicceki iman saidai idan ba zaki dinga fita ba a gida zaki boye kanki” munira ta qarashe bayanan suka kuma goyi bayanta

“Gaskiya kam,koni da za’a bani dama yaya na zan yiwa kamu” budurwar da ta taimaka mata dazu ta sanya baki a hirarsu,kowa ya sanya dariya.

    Ko a jikin munira ta qara gaba ta cire dan kwalinta don a fara yi mata gyaran gashi,yayin da iman ta dinga binta da harara tana gasa mata ita.


    Daidai sanda aka gama musu wayar muniran ta dauki tsuwwa,ta daga da hanzari 

“Ina zuwa…..Allah bazanyi missing ba,gani nan zuwa” shine abinda muniran ta fada tana maida wayarta jaka

“Don Allah don annabi qawalli ki rakani kamun nan,ban zaci abun haka aka shiryashi ba sai yanzu da batula ta kirani,ba zamu jima ba in sha Allah zamu taho,kinga hanya daya zamuyi,gida zan koma zan debo kayana,sai gobe zan wuce gaba daya” da farko uzuri ta bata kan yamma tayi sosai,kafin suje ma magariba tayi,kuma malam yana fada idan tayi dare a waje,haka ya al’ameen,da qyar munira tasha kanta,tace zata rakata har gida ta yiwa inna bayani,zannan ta aminta,nan cikin kayan data amso dinki ta zabi daya daga ciki ta sauya,ta kuma biya aka mata lite makeup,tayi tayi iman ta dauki wani a ciki itama ta sauya tace aa,kayan jikinta sun isheta.

     Tun daga shigansu wajen iman ta tabbatar lallai bikine na manya,wadanda sukaci suka tada kai,wani mahaukacin gida ne mai dauki da tafkekiyar haraba,wanda ama qawata ta da decorations irin na biki,duk yawan jama'ar dake wajen ta daukesu tsaf,harda ragowar sararin da motocin gidan ke fake abinsu basusan anayi bama.

     Tunda suka shiga din iman ta samu seat ta zauna,daga inda take din tana iya hango yadda komai ke wakana,amarya tayi kyau iya kyau tare da angonta,sai gudanar da komai ake cikin fariya boko da kuma nuna wadata.

    A hankali ta daga kanta ta kalli yadda sama ta fara duhu,alamu suna nuna anyi kira sallar magariba zuwa yanzu,duk da bata iya jiyo kiran ba saboda tashin kidan daya karade wajen. Kome take kuma ko a ina take bata wasa da salla,haka aka tarbiyyantar da ita,don haka ta laluba wayarta ta fara kiran munira babu qaqqautawa,wanda sai a kira na biyar ta samu ta daga,tace mata gatanan zuwa,ba jimawa kuwa sai gata,da alamu biki yayi biki

“Nifa zan wucw gida gaskiya,gashi har anyi sallah mu bamuyi ba”
“Don Allah ki bani minti goma kacal,ummi ce zata bani saqo na tafi dashi” mahafiyace,ba zata iyace mata karsu jira ba,saita rausaya kai

“Idan na koma gida malam ya koroni kyasan inda zakiyi dani,kaini wani wajen nayi sallah” dariya ta saki

“Ba korokin da zaiyi,ya kori auta ai babu wannan maganar,muje na rakaki” tare suka jera da ita,saidai duk inda suka gifta sai an kalli iman din,yawanci kallo ne na baqunta da kuma tsarin surar da Allah yayi mata,wadda ta fita daban data sauran mata.

      Ganin yadda hanyar shiga gidan ke cike da mutane sai iman din ta dakata da bin munira

“Gaskiya ki samarmin wani gurin inda zan kebe ni kadai nayi sallata,cikin gidan nan da alama a cike yake,kuma ni babu wanda na sani” tayi qoqarin nuna mata babu komai ta shiga amma tace a’ah,don haka ta jata can bayan gidan,inda garden din gidan yake,wanda ke wadace da grass carpet,da kuma famfunan da ake bawa lambun ruwa

“Yauwa,yanzu naji daidai” iman din ta fada tana ware idanunta cikin wajen saboa yadda ya birgeta,wata iska ta daban wajen yake fitarwa,bugu da qari shuru yake kamar ba cikin gidan dake cike da hayaniyar biki yake ba

“Ki kirani idan kin gama saimi wuce,ni hutun sallah nake”

“Baki da matsala,amma dana gama zazu zamuyi gida”
“In sha Allahu” ta fada tana juyawa da sauri zuwa ciki,iman ta bita da kallo,cikin ranta tana mamakin yadda muniran ke bala’in son alaqa da masu kudi,take kuma qaunar bikinsu,saita dage kafada,qila don ta taso taga haka danginsu yake.

       A hankali take takawa zuwa wajen wani famfo daketa zuba shi kadai yana aika ruwa zuwa sasannin shuke shuken dake fadin lambun,ta tsaya a gabansa cikin nutsuwa,ta waiga ta tabbatar babu kowa,sai ta fara ware lafayar dake jikinta don kada ta jiqe,ta ajjiyeta gefe,ta daura alwalar,sannan ta dauketa ta yafata a matsayin mayafi kawai ta tada sallarta,sai data idar sannan ta miqe,ta zameta daga kanta ta fara daura abarta a jikinta.

      Sau uku tana nadata tana jin batayi mata dai dai a jikinta ba,karo na hudu taja tsaki ta fara warewa da xummar sake daurawa

“Kawo na tayaki tunda kin kasa” sautin muryar daya daki dodon kunnenta kenan wanda ya razanata,ta kuma rude gaba daya,ta damqe lafayar tata da hannayenta gaba daya,a kuma matuqar tsorace sannan a razane ta waiwaya don ganin waye?,daga ina kuma ya shigo ko ya fito?.

ZAFAFA BIYAR

BIYAR : DUBU DAYA (1k)
HUDU: 700
UKU: 500
BIYU: 400
DAYA: 300

AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA:

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

YAN NIJAR ????

+227 95 16 61 77

Ga ‘yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number


ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button