KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yayannaki da kuke ciki daya?,wanne irin hauka ne wannan?”
“Ba ciki daya muke ba,riqonshi inna tayi,kuma almajirin malam ne,dalibinsa ne” sak munira ta tsaya tana kallon iman,tarin mamaki ne fal saman fuskarta,sai iman ta gyara zama ta gaya mata duk yadda akayi.
Fuska munira ta yatsina
“To don yana sonki shine me?,kawai saiki zauna a rabaki da wanda zuciyarki takeso?,wanda zai zama hutun rayuwa a gareki matuqar kika aureshi,karki manta,’yammatan wannan zamanin SHI SUKE BURI” Kai iman ta girgiza tana jin tashin hankali na sake ninkuwa cikin ranta
“Munira…..bakisan halin malam ba,na tabbatar baya magana ta tashi,kuma wallahi wallahi indai ya ameen ya tabbata yana sona malam ya sake fahimtar hakan babu wanda ya isa ya hanashi bashi ni duk duniya” murmushi munira ta saki,sai ta matso kusa da iman din sosai
“Kinga,ayi me baro baro kawai a wuce wajen……ki bude bakinki malama,karki cuci kanki,ki gayawa kowa kina son bassam,kuma shi kike da burin aura,ki gayawa ameen bassam kikeso kanki tsaye,idan kikace zaki tsaya kunya ko kara,to wallahi kina ji kina gani za’ayi babu ke,ni dama na dade ina zargin sonki yake,shi yasa ya tajura rahuwarki ya hanaki sakewa kamar kowacce diya,abu daya ne ya ciremin zargina da kika gayamin cewa yayanki ne…..amma Allah na tuba,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa,ki duba surarki da kyau….banda ma yiwa kai kasada me zaisa yace yana sonki a irin wannan lokacin da arziqi ya qwala muku kira?,me yake dashi da zai riqeki iman?,ina cewa makarantar da zaici gaba ma kokawa suke shi da ita da fafutukar ganin ya sameta,idan kika auri bassam…..bashi kansa ba,hatta da abokansa dana kusa dashi…..danginsa na qauye rankatakaf sun huta,amma shikenan saboda ya dankwafe rayuwarki sai yace wai yana sonki saboda cuta da mugunta,yana da kyau yana da kwarjini na daukar hankali,amma magana ta domin Allah bashi da sinadarin riqe mace kamarki…….da dinki zaici da ke?,koda karatun da bashi da tabbacin samunsa?ke rabu da gaibu fa ki kama dahir,kuma shima matuqar yana sonki ai zaiso ci gabanki ne,bawai ya aureki ku dankwafe waje daya babu ci gaba ba” ire iren maganganun munira kenan data ci gaba dayi,kamar zata ari baki.
Iman tana saurarenta tsaf,ita ba wannan bace damuwarta,babbar damuwarta soyayyar bassam da zuciyarta ta saba da ita,kuma batajin zata iya jurewa rasashi.
"Gashi inji bassam......,jiya ya aiko yaranshi ya kawo min da daddare saboda ya kikkiraki jiyan bai jiki ba,ya damu sosai,shi kansa yaron nasa idan kinga motar da yake hawa ko......hmmmm" tayi zancan sanda take fidda waya sabuwa dal tana miqa mata.
Wannan karon batayi musun karba ba,jiki a sanyaye ta amsa,saboda tana jin wannab shine lokaci mafi dacewa da su kasance tare da juna da bassam din.
Nan da nan labari wayar ya karade cikin qawaye da classmates dinta,tanajin mazan ajin suna fadan kudin wayar,mamaki ya kamata,ta jujjuya wayar a hannunta tana mamaki yadda mutum zai iya narka kudi kamar haka ya siya waya qwaya daya jal.19
Cikin jiki zuciya ruhi da kuma idanu ya tabbatar akwai matsala,irin matsalar da duk sanda zuciyarsa ta gaya masa akwaita yana qoqarin qaryata kansa da tunaninsa,komai da komai din na iman ya canza kuma ace ya janye daga muhalli da bigiren da ya santa ada,duk dacewa ba mazaunin gida bane shi.....amma kuma gaba daya iman din ta yiwa idaniyarsa qaura,ya daina ganinta,walau da safe koda dare,tamkar wasan buya ta tsiro dashi a tsakaninsu a tsanake,yasha ganin wucewarta wuf a duk sanda ta karanci motsinsa a waje ki tahowarsa izuwa wajen.
Iman din dake tiri tiri da dukkan wani abu da ya shafeshi a yanxu ba ita bace,iman din dako yaushe take shiga kokwanto da wasi wasi duk sanda wasu awanni suka shude bataji motsinsa ko gilmawarsa ba,dukka a yanzu sun kau,kwanaki biyar din da suka biyo bayan maganarsu bai sake sanyata a idanunsa ba,koda muryarta zai iya cewa baifi sau uku ya jiyota ba tsayin kwanakin.
Wata iriyar rayuwa yake a kwanakin wadda shi kansa baxaice ga inda ta dosa ba,saboda rashin gane ainihin abinda iman ke nufi,ina tasa gaba?,meye alqiblarta?, Duka bai sani ba,tarin damuwar dake danqare cikin zuciyarsa ta bayyana cikin ayyukansa na yau da kullum,ada idan gana dinka riga goma a wuni daya,a yanzu biyu yake iyayi,sauran duka tunani ya cinyeshi.
wannan kenan
K'arfe takwas na dare bayan kammala sallar isha'i ya shigo gidan,wanda direct daga masallaci gidan ya nufo,tunda dama can shi ba ma'abocin zaman majalissa bane,koda ya zauna din baya wuce minti goma zuwa ashirin zai sallama dasu ya wuto gida yaci gaba da sabgoginsa.
Sanda yake sanyo kai cikin gidan tare da sallama a bakisa yaga kamar wani abu ya gifta wuf zuwa daki,inna ta daga idanunta tabi iman da kallo wadda ita dince tayi hakan,cikin mamaki tana amsa sallamar amin din,ta fuskanci wasu sauye sauye sosai game da alaqar ameen din da iman,yau dinne kuma idanunta suka ganeta real,zuciyarta tadan tsinke kadan,tana fatan kada ubangiji ya sanya wata matsala ce ta afku tsakaninsu komai qanqantarta,don basa fatan hakan,saboda ko a jiya sun jima ita da malam suna tattauna batu akan aminu da iman din
"Barka da dare inna" amin ya fada cikin murmushin sannan me sanyi da akullum yake fuskantar innar dashi,fuskantar da da zai yiwa mahaifiyarsa cikin girmama a tarin ladabi.
Cikin nata salon kulawar da kuma nuna qauna ta sakar masa fara'a
"Yauwa aminullahi,sannu da qoqari,an samu shigowa?" Ta qarashe maganar tana tura masa kujerar tsuguno,sai ya zame ya zauna kan shimfidar abun sallar da iman ta tashi yanzu akai,ya zauna sosai akai ya tanqwashe qafafunsa yana gaidata kamar wanda ba tare suke gida daya ba.
Cikin kulawa ta amsa masa,sai 'yar hira ta shigo kan wajen aikin nasu,aduk sanda wata matsala ko ci gaba suka sameshi kam aikinsa,da ita yake shawara,da ita yake tattaunawa,su kashe su binne,inna takanji matsalarsa dari yayarsa dake jigawa bataji guda daya ba.
Duk wannan hirar fiye da rabin hankalin inna yana kan dakin iman,tana zuba idanu tare sa saka ran ganin fitowar iman,tana fara'a gamida nuna kulawa dayi masa sannu da zuwa,ta kuma debo abincinsa ta gabatar masa kamar yadda suka saba,sabanin haka shuru kakeji.
Hankalin inna ya dan daga kan,ranta kuma sosu,ta kasa jurewa sai data daga murya cikin sauti mai qarfi ta qwalawa iman din kira.
Kai tsaye kuwa kiran ya isa kunnuwan iman,wadda ke kwance rub da ciki kan katifarta,ta nutsa cikin duniyar chart da bassam,wanda har bata iya jin hirar dake gudana tsakanin inna da bassam dake zaune daga qofar dakinta.
Da hanzari ta danna wayar qasan pillow,tunda dama babu wanda yasan da zaman wayar,koda yaushe kuma a silent take,ta tashi da wani irin reaction na rashin gaskiya ta fito waje tana gyara daurin dankwalinta.
Tamkar batasan ya shigo gidan ba,tamkar ba dalilin shigowarsa yasa tabar tsakar gidan ba ta gaidashi,duba daya yayi mata yasan lallai mawuyacine abinda zuciyarsa keta gujewa ba shine ya afku ba,iman din dake marmarinsa a yau ita ke gaidashi babu wani doki babu komai,fara'a da ya santa da ita babu kaso casa'in cikin dari.
Da wani mugun bin qwaqwafi inna ke karantarsu gaba dayansu,saita danne tace da iman
“Wanne irin sakarcine wannan,ki wuce ki dauko masa abincinsa,kin kama kin wani qule daki?,haka kawai kin koyi nunqufurcin banza da wofi na zaman daka?,inacewa baki jima da fitowa ba?,me kika koma yi a ciki ko wutar nepa babu?” Gabanta ya fadi saboda tasan halin inna sarai,tana matuqar qoqari wajen kiyayewa duk wani abu da zaisa inna ta zargi akwai wata a qasa amma a banza,mutum ce ita me mugun kula da kuma tsantseni
“Inna kayana na fito dasu na manta zan gyara na barsu a waje” ta fada cikin marairaicewa
“Saiki wuce ki debo masa abincin” ta sake maimaitawa tana miqe qafafunta da sukeso su fara mata ciwo,dama kwana biyun daurewa kawai takeyi
"Zan fara watsa ruwa,kamar nan da minti ashirin sai a kawomin"
"To shikenan....,idan zaki hada masa ga kwadon xogale can ragowar na malam da yayi buda baki dashi saiki hada masa dashi" da to ta amsa tana nufar kitchen,saidai ranta a bace yake sosai,kawai saboda amin din innan ta sakata a gaba take mata fada,yadda innar ke nuna masa kula da tattalinsa koda yaushe ko ya sadiqu bata yi masa haka,abincinma sai an wani hada masa kulli yaumin kamar wani magidanci,rana dai daine zai shiga kitchen ya dauko da kansa yaci.
Tunda take dashi bata taba ganin aibun hakan ba sai yau,sai yau da zuciyarta ta karkata zuwa wani hanya daban ba wadda a baya take kai ba.
Kwata kwata bata qaunar su kebe da amin din baki daya,wannan shine babban dalilin da haduwarsu cikin gidan ma ta haramatata,saboda batason ya sake dauko.mata magana makamanciyar wadda yayi mata a rannan,shurunsa da rashin nemanta da baiyi ba shima a kwanakin ya sauqaqa mata dukkan wani tsoro da kuma zulumi nata,koda bata buda baki tayi magana ba tana kyautata zaton ya zuwa yanzu ya gane inda ta dosa.
Tana hada abincin tana mita qasan ranta,fuskarta a hade,hakanan bakinta yana ta motsawa,tasan yayi hakkanne kawai don ya samu damar magana da ita,kuma batajin zata sake bashi wannan damar.
Data gama hadawar saita koma daki dauko hijabinta,hasken wayarta dake alamta shigowat saqinnin bassam ya zaunar da ita,ta saki murmushi sanda ta fara bin saqonnin nasa,saita manta da aikin da zatayi ta shiga maida masa amsa.
Ya jima tsaye gaban mudubi gana sharce kansa yana kuma duban fuskarsa,kwanyarsa na masa bitar tarin maganganun dake cunkushe daga zuciyarsa zuwa bakinsa,mamakin yadda komai yake qoqarin sauyawa cikin qanqanin lokaci yakeyi.
Cikin jallabiyya ya shirya bayan ya feshe jikinsa da turarensa kamar yadda ya saba,hatta da boxer na ciki bai tsira ba,sai ya koma saman kujerar dakin ya zauna yana duba lokaci,tayi delay sosai,amma sai ya bata uzuri,kamar hadda hali da dabi'ansa yake,mutum ne shi mai yawan bada uzuri,zaiyi wuya karon farko ya kamaka da laifi,sai ya dora hannunsa saman sumarsa da har yanzu danshin ruwan dake jikinta bai bushe ba,yana shafata a hankali daga gaba zuwa baya,yana jin yadda damuwa ke sandar jiki da zuciyarsa.
Wayarsa ya maida gefe ya ajjiye yana furzar sa zazzafar iska daga bakinsa sanda yayi kiran layinta yaji busy,wani abu ya tsaya masa a maqoshi ya kuma tokare masa maqogaro,a hankali yaci gaba da shafar sumarsa yana lallashin kansa da kansa,sai ya lumshe idanunsa yana sake fitar da iska mai tsaho wai ko zata rage masa nauyin da yakeji cikin qirjinsa.
Kiran wayarsa da akayi shi ya dauke masa hankali,ya kuma zuqe yawan mintunan data dauka bata kawo masa abincin ba.
“To ba damuwa,bari zan kira idan na duba” amsar da ya bayar kenan sanda yaji motsinta,da kuma sallamarta a bakin qofa cikin zazzaqar muryarta,ya bata izinin shigowa yana qoqarin sanya wayarsa a silent,wanda kafin ya gama ya daga kansa harta ajjiye abincin ta juya
“Iman” ya qwala mata kira,ta waiwayo tana jin ba dadi a zuciyarta kan tsaidatan da yayi
“Zo ki zauna……magana zamuyi”
“Yanzu zan dawo” ta amsa masa a taqaice,saiya gyada kai lumsassun idanunsa suna zube saman fuskarta,yana ganin sauyi muraran daga iman dinsa zuwa wata iman din ta daban,ta juya da hanzarinta ta fice,cikin ranta tana jin saidai suyi maganar da wata amma ba ita iman din ba.
Amma kuma tana saka qafarta a tsakar gida inna dake fitowa daga daki ambaci sunanta
“Wai wanne irin baqin hali kika koyo imani?,wannan zobon da kika ajjiye ya gama hada sanyinsa babu mesha ba zaki kai masa ba,bawan Allah azumi yakai fa?” Kamar zata dora hannu aka ta zunduma ihu haka ta dauki jug din zobon ta nufi soron dashi,bata taba jin inama tana da qanne ba irin yau,da babu shakka saidai fa ta tura daya daga cikinsu ta samu ta dawo,domin har a jikinta tana jin bassam nacan yana jiranta,haka fa tura qofar dakin ranta a bace sallamarta a ciki,daidai sannan nepa suka kawo wuta,hasken farin qwan lantarkin dake dakin ya mamaye ko ina,ya kuma taimakawa ameen qwarai wajen ganin yanayin fuskar iman din.
Can nesa ta samu ta zauna bayan ta dire masa jug din,kanta a qasa kamar wata surukarta tace gani.
Baiko motsa ba sabda tayi maganar,sai kafeta da yayi da lumsassun idanunsa na wasu daqiqu,sannan ya miqe cikin nutsuwar nan tasa,ya taka a hankali ya rage tazarar dake tsakaninsu,a hankali ya zame saman carfet ya zauna saitinta,ta yadda zasu iya ganin juna yadda ya dace.
Dakakkiyar muryarsan nan me cike da amo na mazantaka ta fara fita,yau din cikin wani irin yanayi na sany da laushi,duk da cewa dama can ita iman din wannan amon ta saba ji daga gareshi,bai fiya kausasa mata a magana ba
“Iman…..a duniya idan akwai wanda zai fadi halayyata bayan inna da yayata to kece ta ukunsu,banajin ko sadiqu ya sanni yadda kika sanni” sai ya sanyi shuru yana sauke numfashi gami daci gaba da kallonta sannan ya dora
“Kwanaki biyar da suka shude,munyi magana dake…..na bayyana miki komai,saidai kuma har yau na kasa karantar me wannan iman din take nufi?,ina ta fuskanta?,ina ta sa gaba?iman baki sona ne?,ko ya amin din naki bai miki ba?,idan banyi miki ba iman ki fito ki gaya min,saboda ni ba baqonki bane……”ga fada maganar cike da qwarim gwiwar samun akasin abinda zuciyarsa ke raya masa,saida amsar da iman din ta bashi tayi matuqa girgizashi,ta motsa masa zuciyarsa fiye da yadda ya zata ko kuma ya tsammata……amsar da bai taba kawowa koda cikin mafarkansa zai jita daga bakin iman din ba,bai taba zaton zata iya furtata ba
"kayi haquri ya amin........bassam nakeso" ta amsa masa,tamkar dama jira take a bata wannan damar.
Dukkan wata jijiya dake kai saqo jini da kuma iska a jikinsa zuwa muhallansu sai da ta tafi hutu na sakanni,kafin ya samu nasarar zuqo numfashinsa,bayan ya tabbatar numfashin ya koma saman qirjinsa yadda ya dace,sai ya fara kokwanton duniyar zahiri ce ko ta mafarki,saboda haka yayi qarfin halin motsawa kadan
“Iman…..sake maimatawa naji”. Yayi maganar sautin muryarsa na fidda wani amo wanda zai alamtawa mai sauraron da kunnensa da kuma qirjinsa ya cika da hikima cewa lallai akwai wani abu mai tsananin nauyi da yake shirin danne zuciyar da wannan sautin ya fito daga gangar jikinta……