KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

"Na fuskanci tijara yake ji,don haka bance komai ba na tattaro al'aminu,na wuce dashi chemist saboda yanayin ciwuka da raunin dake jikinsa na tabon bulalai da duka da kuma mari daya dade a qafarsa ya zame masa ciwo. A hanya nake tambayarsa wayeshi da kuma qauyensu,ya shaidamin shi din dan birnin kudu ne,mahaifiyarsa ta jima da rasuwa tun yana qarami,yayarsa da ita ta riqeshi har zuwa sanda ya tasa,mijin yayar yace bazai iya daukar nauyinsa ba saboda shima bashi da komai,yayarsa bata da yadda zata riqeshi saboda shi da itan duka marayu ne,hakan ya sanya mijin yayar ya kawoshi bara,ya damqa shi a hannun malam dan lami,tunda kuma ya tafi bai waiwayoshi ba,duk da cewa bai wani jima a makarantar ba,azaba ba wacce bai gani a waie malamin ba,don kusan karatun ma dana tuntuba ba wani mai yawa bane,azabar da suke sha tafi karatun yawa,wanna dalilin ya sanya na yanke shawarar kawoshi makarantata yayi karatu,zuwa sanda zai warware kuma mu nemi ita 'yar uwar tasa ko mijinta mu gaya masa inda yake a yanzu".
Kai inna ta gyada idanunta na kan lamin,zuciyarta cike da tausayinsa,tunda malam yake kawo almajirai bata taba ganin yaron da taji ya kwanta mata ba kamar lamin din,a dan awannin da yayi dasu wanda bai wuce awa daya da rabi ba,ta fuskanci nutsuwar dake tattare da yaron,komai nashi a hankali yakeyi cikin nutsuwa
“Allah ya rufa asiri,ya gyara mana xukatanmu” shine abinda inna ta fada,suka kuma fara rayuwa da lamin din,wanda cikin kwanaki biyu ya sake da sadiqu,wani irin sabo sukayi sosai dashi,saika zaci sun dade tare.
Tun farko dama aminu din bai soma kwana cikin almajirai ba,cikin dakin saddiqu suke kwana,hakanan hatta da suttura ta saddiqun yake sanyawa,kafin daga bisani malam ya bayar da kudi inna ta samo musu gwanjo masu kyau shida saddiq din,sosai sadiq ke murnar samun dan uwa,lokaci kadan lamin ya shiga jiki da zukatan su inna,saboda yarone haziqi,duk wani aiki da saddiq keyiwa inna da malam alamin din ya daukeshi,sai malam da inna na hanashi suna raba musu kowa ya dauki nasa.
Kusan tare sukayi rainon iman da inna,idan inna tana aiki tofa iman tana hannunsa,yayita tiri tiri da ita kenan,tun tana masa qyuya har ya zamana duk cikin gidan babu wanda take yarda dashi Kamar yadda take yarda da alamin,wani lokaci idan aiki ya kacamema innan idan ya dauki iman sai tayi da gaske ta korashi makaranta sannan zai tafi,sannu a hankali sai sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu,baya son kukanta,baya son abinda zai taba iman din,da a daki iman din gwara a dakeshi,koda malam ya sanyasu makaranta sai ya zamana sai ya fara kai iman sannan shi zai wuce,koda kuwa shi xaya makara,kudin break dinsa kuwa badai yaci a cikinsa ba,komai ya gani shi zai kwasowa iman din ya kawo mata,idan kaga yadda yake matan sai ka rantse da Allah ciki daya suka fito.
Kamanni ne kawai zasu tona asiri,saboda kowa a cikinsu kamanninsa daban,hasken fata ne kawai ya hadasu,tun iman na qarama ta fita daban,tana da kyan fuska qwarai da kuma yalwar suma,wadda ta gajeta daga wajen inna.
'yar lele iman take a wajen alamin tun tana da qananun shekaru,zai iya hana cikinsa ya bata,duk abinda tace tana so to matuqar yana dashi sai ya bata,idan babu kuwa zai nema mata,abinda yasa ya tashi kenan da zuciyar nema,zama da madaukin kanwa inji hausawa sukace shike kawo farin kai,tun saddiqu bashi da ra'ayi har zama da lamin ya sanya ya zama mai neman na kanshi kamar alamin din.
Kusan duk kudin daya samu wajen nemansa fiye da rabinsa siyawa iman wannan ne siya mata wancan,tun bata isa ado ba yake mata siyayyar kayan kwalliya da qyale qyale,tun malam da inna na fada,har suka fahimci a jininsa yake kulawa da iman,bazai iya dainawa ba,dole suka haqura suka sanya masa idanu,saidai innan tayi masa fada da kuma dabarar ya dinga aje wani abu saboda yayarsa,wadda a yanzu shekaru ke sake jaa nauyi na dada hawa kanta,tana kuma da buqatar taimako ko yaya ne.
Alamin shine kewa iman komai,itama duk abinda take da buqata alamin din take durafafa kanta tsaye,bata ko kallon sadiqu dan uwanta,saboda yana da zafi shi din,hakanan yanzu yanzu ba wani abu bane yakai mata bugu idan tayi ba dai dai ba,sabanin alamin.....wanda bashi da daukan zafi a kanta,hasalima yana tare duk wani abu da yasan xai bata ranta ko ya cutar da ita,idan tayi ba dai dai ba cikin ruwan sanyi zai nusasheta ya kuma gyara mata,tana kuma daukan maganarsa fiye data kowa cikin gidan.
Dinki dashi lamin yafi qwarewa,ya iya dinkin mata kamar masifa,har zuwa yanzu da yake kan shekara ta kusan goma sha shida,wannan yasa iman dake da shekaru goma sha daya cikin rayuwarta tun a sannan ta zama abun kallo,indai tayi kwalliya kowa sai ya yaba,tana da kyau sannan kuma alamin din yana fitar da ita da dinkuna sai kace wata qatuwar budurwa,don idan kaga dinkunan da take sanyawa saika tambaya waye yayi mata,sau tari idan yayi dinkuna ya samu kudi sosai,yakan je kasuwa ba tare daya gayawa kowa ba,ya samo mata atamfa falle bibbiyu masu sauqin kudi ya mata skert da riguna tsala tsala,saboda bata iya daura zani ba har yanzu,abinda yake hadata da inna kenan,kullum fama take amma har yanzu iman din bata iya ba,koda yaushe saidai ayi mata riga da skert ko kuma doguwar riga.
Idan kaga iman din saika dauka diyar wani ce,saboda bata rasa komai ba,kullum tsaf zaka ganta cikin suturu masu kyau.
Amin Abubakar haifaffen garin birnin kudu ne dake jahar jigawa,bafulatani ne uwa da uba,abinda yasa ya gaji kyau kenan shima tun quruciyarsa,tun shekarunsa basu fara nuna ba,yaro ne da tun a halittarsa Alla ya masa baiwa masu tarin yawa,yana da nutsuwa qwarai da gaske wadda ta hade masa da miskilanci,miskilancin da tun zamanin quruciya ya sanya ba kasafai zaka ganshi cikin wasanni irin na yara ba,yafi ganewa yana zaune daga gefe yana kallonsu,idan abu ya burgeshi ya saki murmushi kawai.
Kafin rasuwar mahaifiyarsa ya samu tarbiyya qwarai daga wajenta,wannan tasa ya zama wani na daban,idan yana wasu abubuwan saika dauka wani babba ne me shekaru.
Yadda malam da kuma inna suka riqeshi abune da bazai manta dashi kafatanin rayuwarsa ba,sun masa wani gini sun kuma zame masa garkuwa kuma ginshiqi cikin rayuwarsu,ya fahimci daga inna sadiq da kuma malam dukkaninsu suna qaunar iman,suna dannewa ne saboda yanayi irin na tarbiyya,shi kuma baiga abinda zaiyi ya faranta musu ba fiye da kula da abinda sukeso,hakan yasa ya sanyawa kansa bawa iman din dukkan kulawa,sannu sannu kuma sabo da shaquwa suka shiga tsakaninsu.
Wani lokaci har mantawa yakeyi,yakan kallo iman din a matsayin 'yar uwarsa ta jini,har sai idan wani abun ya gitta da zai sanya ya tuna cewa ba jininsa bace.
shimfida kenan……muje zuwa
ina matan dake fama da qaranci ko daukewar sha’awa saboda gajiya qarancin sinadarai ko kuma gajiya a jikinsu?,kina fama da maigida wajen rashin samun gamsuwa fannin auratayya?,dukka matsalarku ta yanke da HILTI UNISEX CHOCOLATE,maza garza kizo ki nema taki
CHOCOLATE CE da zaki shata kamar sauran chocolate,saidai kuma aiki a jiki,ba ruwanki da neman tarkacen magunguna mata marasa inganci,AKWAI TA UWAR GIDA AKWAI TA MAIGIDA
GAME BUQATA KO KUMA SON QARIN BAYANI,SAIYA TUNTUBI WANNAN NUMBER
+234 818 401 7452
Tasted and trusted???????????????????????? KUFAN WUTA????????
NA
HUGUMA
Free page 04
MASOYA ‘YAN QASAR NIJER,ZAKU TURA KATIN WAYA(AIRTEL/MOOV) TA WANNAN NUMBER
+22795166177
Zaune take saman kujera ‘yar tsugunno,sanye da uniform na makarantar primary din da take zuwa,tana ta qoqarin daura takalmin sandal a qafarta,komai nata tsaf kuma fes,karin guga ya kama uniform din jikinta sosai,shaidar cewa suna samun kulawa yadda ya kamata,hatta da takalmin sandal din qafarta qyalli yake,kamar yadda farar safarta take qal kamar baa sakata.
Wannan kusan duka aiki da horon lamin ne,idan baiyi mata da kansa ba,to ya riga ya koyar da ita,iman din akwai tsafta kamar yadda lamin din yake,bare ma kafin ta yiwa kanta wani abu sau daya yayi sau goma,wankinta da nashi duka suna wuyansa,kama daga uniform dinsu zuwa kayansu na zaman gida.
Lamin din na tsugunne gefan kitchen yana shirya mata abinci a wani dan qaramin kwando me kyau,wanda shi da ita sukaje ta zaba ya siya mata,tana ta masa surutu yana biye mata,wanda duka akan jarrabawar common interence da zata zana ne a yau,inna na daga cikin kitchen din tana zubawa shi yana shiryawa har ya gama,dai dai sanda ta gama sanya safa da kuma warin takalmi daya,dayanne ya gagara,don haka lamin din ya qarasa wajen ya tsugunna ya kama takalmin yana daura mata,sannan ta miqe tana diban takardunta sabon pencil biro har ma da cleaner dasu sharpener da lamin din ya siya mata.
Suka miqe suna yiwa inna sallama,saboda lamin din ne zai kanta har can inda zasu zana jarabawar da kansa,daidai lokacin malam ya shigo
“A’ah,har kin gama shiryawa kenan,to ai Allah yasa motar bata tashi ta barki ba” malam ya fada yana danna wayarsa Tecno keypad dake hannunsa saboda yaga lokaci
“Dama ba tare zamu tafi ba,ya lamin ne zai kaini” iman ta fada tana duban malam
“A’ah,wanne irin sakarci ne wannan,ya ga motar makaranta zaki ce saidai laminu ya kaiki?,ki wuce ki shiga cikin ‘yan uwanki dalibai ku tafi”
“Ai malam kada ma ka bata bakinka,babu yadda bayi dasu ba,tun jiya nake sababi,amma dole ne naja bakina na tsuke,saboda shine yake goya mata baya,wai kada ta shiga cikinsu uniform dinta ya cukurkude……sai kace tafi kowa” jin inna ta sako baki ya sanya iman ta fara narai narai da ido kamar me shirin sanya kuka tana duban lamin din,so take ya sanya baki,kada su malam su hanashi ya rakata.
Zahiri ita tsoro takeji,saboda yadda taji wadanda suka gama primary wancan shekarar suke fadan wahalar jarabawar,duk da yadda lamin din ke qarfafa mata gwiwa tare da nuna mata cewa ba wani abu,suma sunyi fa,iya karatu tasan ta yishi,don a rana suna kwashe awanni masu yawa lamin din yana mata lesson,tana da matuqar qoqari da fahimta,saboda haka duk karatun da yake mata tana daukeshi,wannan dalilin ne yasa lamin din yaci burin tayi karatu mai zurfi,duk sa’ilin da suka zauna suna hira kuwa rabin maganarsa kenan,wannan abu yayi tasiri itama cikin ranta,bata da burin daya wuce ta ganta ta gama qaramar makaranta ta shiga jami’a,ta zama likita lawyer ko ‘yar jarida,cikin ukun nan takeso ta zama daya.
“Malam kasan wannan shine karonta na farko da zata fita wani waje tayi jarrabawa irin wannan,rakatan kuma zai qara mata qwarin gwiwa,tunda makarantar basu hana ba malam ka bari na kaita” da qyar lamin yasha kansa ya barsu suka fice.
A soron gidan ya dakata yana cewa
“Bari na tada sadiq ya rakani,tafiya bibbiyu tafi dadi”
“Yaaya,Allah bazaije ba koka tasheshi” iman ta fada tana jan tunga,sai ya waiwayo ya kalleta,taso bashi dariya yadda ta tsuke dan qaramin bakinta ta marairaice,ya fuskanci so ne batayi yaje din,don tabbas idan suka tafin tare bazai barta ta sake ba,duk kuskuren da tayi saiya taso mata da fada hantara ko kyara.
“Ina zuwa dai” ya fada yana saka kansa cikin dakinsu.
Saidai duk yadda yaso tada sadiq din ya rakashi ya qiya,sai ya cusa kansa ma qasan filo yana cewa a dawo lafiya,Allah ya bada sa’a,dole ya fito daga dakin ya barshi.
Dadi iman din taji,ta dinga boye dariyarta har sai data fito ta dara,harara lamin din ya watsa mata da lumsassun idanunsa
“Ni kikewa dariya saboda ya yarfani ko?” Sake qyalqyale masa tayi da dariyan
“To ai yaa lamin kai kam baka iya harara ba,hararaka irin ta masu jin bacci ce” fara’ar fuskarta kadan ta ragu
“Ya lamin,ni dakai me yasa dukanmu bamu da lafiyar ido?” Ta tambayeshi sanda suka kusa ficewa daga layin nasu tana dubansa,da alamun damuwa cikin muryarta.
Murmushi ya sake wansa iyakarsa saman lebansa,duk da qarancin shekarunsa amma yanayinsa kamar wani babban matashi,akwai wani iri kwarjini na daban dake fita saman fuskarsa.
Duk da cewa a shekara ta sha bakwai yake amma hankalinsa tabbas yafi na iman din nesa ba kusa ba,kasantuwarsa namiji ita kuma diya mace
Cikin harshen da yake ganin zata iya fahimta ya fara mata magana
“Lafiya lau idanunmu suke ni dake,ba kina gani sosai ba?,ko akwai wani abu da bakya iya gani” saifa girgixa kai alamun a’ah
“To kin gani ba…..nima ina gani sosai,har daga nan ina iya ganin wanda ke tsaye gaban rumfar malam dalha” ya fada yana nuna wajen da yatsa,abinda ya sanyata tada kai ta kalli wajen,kawai tazarar nisa a tsakaninsu,don haka abun ya bata mamaki,har ta fidda idanu,sannan ta waigo gareshi
“Yaaya” kai ya jinjina mata,bata sake kokwanto ko tantama ba,saboda tasan halin lamin din tunda ta fara wayo,qarya itace abu na qarshe da baya kusantarta a rayuwarsa kaf,koda ya gaya mata waye a tsayen,da suka isko wajen saita ga shi dinne kuwa,abinda ya sanyata sakin dariya
“Na yarda Allah yaya,lafiyarmu qalau” murmushi ya kuma saki a maimakon dariya
“Na gaya miki dama,yanayin halitta ce,kowa da yadda Allah ya halicceshi,kamar yadda yayi wani dogo,wani gajere,wani fari wani baqi,wani me kyau wani akasin haka”
“Wani me suma me kyau irin taka,wani kuma tashi irin ta yaya sadiqu ko?” Wannan karon dariya ta bashi,har haqoransa suka bayyana
“Zaki bayani duk randa kika fada a gabansa,shima sumarsa me kyau ce sosai iman….,amma taki tafi tasa kyau sosai” murna ta cikata,tadanyi tsalle kadan
“Don Allah yaya ba na fishi kyau ba?”
“Neeeesa ba kusa ba” ya fada yana duban fuskar dake cike da quruciya,murmushi na fita daga kan tata fuskar