KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“To amma me yasa yake cemin me idon mage,mummuna?” Ta tambayeshi tana tura baki,saiya sake sakin murmushi,indai yana tare da iman din bata bari fuskarsa da bakinsa su huta

“Ki rabu dashi,kishi yake dake” ta saki qaramar dariya cikin nishadi,tana jin dadin zama da ya lamin fiye da kowa cikin gidansu,duk sanda zai bata amsa,yana bata amsa ne ta yadda zata dace da ra’ayinta da kuma abinda takeson ji,indai yana nan baya bari bacin rai ya zauna saman fuskarta,da irin wadan nan hirarrakin sannu a sannu har suka samu abun hawa,ya kaisu inda daliban shekarar daga makarantun wannan qaramar hukumar zasu zana jarrabawar.

        Sai daya tabbatar da shigewarta exam hall din sannan ya juyo zuwa gida,a qafa ya zabi ya tako zuwa gidan,saboda kudin dake gareshi su isa kawosu gida shi da iman din zuwa la’asar idan an gama jarrabawar.

        Yana gab da isowa qofar gidan nasu ya hangi yarinyar na tahowa,ubaida ‘yar layinsu ce,ya fuskanci duk sanda xasu hadu da yarinyar saita dinga wani sinqe sinqe,idan sukayi clashing kuwa haka zata gaidashi cikin girmamawa,duk da cewa kwata kwata shekarun da ya bata basu wuce biyu ko daya ba,saidai yanayin garin jiki da kuma kwarjinin da yake dashi,zaka zaci cewa wani babban yayanta ne.

       Yanzun ma yana kallonta tayi wuf ta shige soron wani gida ta buya,saidai taci gaba da leqensa har ya wuce ta sannan ta fito.

       Yana da yawan gumi,don haka sanda ya isa dakinsu ya jiqe da zufa,ya samu sadiqu ya fito a wanka daga bandakin da ba’a dade da yi musu ba cikin dakin nasu,wanda suka hada kudi abinsu shi da saddiqun aka musu,saboda girma da sukaga sun fara,lamin ne ya kawo wannan shawarar,kuma ta kwantawa saddiq din,da yake dakin ma sha Allah yana da girma,don ya dauki katifunsu guda biyu bayan leda me kyau dake malale a dakin,da yake ba wanda yake shigar musu kuma wuni suke wajen sana’a ledar lafiya lau take,sai kujera guda daya doguwa da kuma kwabet ta katako mara tsaho amma kuma tana da fadi,anyi mata bangare biyu kowa da sashen kayansa,kusa da kujerar akwai wani dam teburin na katako da talabijin ta zaune,da receiver a kanta,wadda suka jona daga maqota,dama ba wani kallon arziqi suke ba,sunfi kallo sanda ake ball da wani waje,shima kusan sadiq ne me wannan nacin,lamin din yafi ga sauraren news a redio.

       Suna hada ido ya harari sadiq din wanda yake daura tazugen gajeran wandonsa

“Baka kyauta ba wallahi,abinda kake sam bai kamata ba”

“Allah ya sani bazan iya irin rayuwarka ba,yarinya sai shegen fi’ili da shagwabar banza da wofi,kamar wata yayayya,ayita riritata,yarinyar da an kusa bude mata littafin ayyukanta nan da wasu shekaru kadan” sadiq din ya amsa masa yana zura riga a jikinsa,harararsa lamin ya sakeyi

“Idan bamu kula da ita ba da waye ne zamu kula?,ita kadai ce fa a gabanmu?,kuma ma ina wani shagwaban yake?,kaidai matsala ce dakai kawai,kuma idan baka canza ba bazamu taba dai daitawa ba” daga haka yaja towel dinsa dake hannun kujerar ya shige bandaki,yana jiyo sadiq yanata qananun maganganun indai iman bata canza ba shima bazai canza ba.

      Kansa kawai ya kada cikin takaici,dukkaninsu har yau sun kasa karantar iman,kamar shi daya shi da.malam ne suka fuskanceta,ba shakka tana da sakalci da shagwaba wani lokacin da gabunta irin na yaran da ake haifa daga qarshe,to amma fa tana da hankali da wata irin nutsuwa,haka kuma tana da fikira da saurin fahimtar abu,ko yaya ka zauna da ita zaka san cewa uwa ta gari ta taka muhimmiyar rawa wajen nutsuwarta da dabi’unta,yarinta kuwa har yanzu bata wuce lokacin ba,so dole sai an dinga mata uzuri ana nusasheta harta wuce lokacin.

       Sanda ya fito lallausar sumarsa mai santsi da zaka zaci relaxer yake sanya mata tanata digar ruwa,zuwa sannan har sadiqu ya shiga cikin gida ya karbo musu abun karyawa,kunu ne me zafi sai qamshin lemon tsami yake,sai kuma fanke da qosai wanda ya tabbatar qosan nashi ne,saboda shi fanken bai dameshi ba,qosai ne koda ya huce zai cishi a haka yana jin dadinsa,koshi ko alala,sau tari sadiq na tsokanarsa da cewa

“Wai lallai saika nuna kai cikakken bafullaci ne,qauna ce shadidiya tsakaninku dama da qosai” wani lokaci yayi dariya ya barshi,wani lokaci kuma ya rama.

       “Yauwa,daga kan plocker dinka akwai saqo gashinan an bani,ka duba” sadiq ya fada yana qoqarin kai cup din kunun bakinsa,ajjiye towel din da yake goge kansa dashi yayi ya qarasa gaban locker din,wadda take dauke da tarkacen kayan shafa na maza,kai kace wani zabgegen saurayi ne,tarin turaruka ne kala daban daban,kama daga roll-on, sure,body spray,body mist masu sanyi,da turaruka na kaya  shaving cream,da body cream masu sauqin kudi,man wanki baki da mayukan gashi na maza,sai kuma man saka takalmi yin qyalli.

         Hannu yakai ya dauki farar takardar da aka nannadeta four corners,ya ware a hankali,sannan ya zuba mata sleepy eyes dinsa da suke a lumshe,yana bin yadda aka zane takardar da zanen furanni da kuma tsuntsaye,sannan ya sauka ga saqonnin soyayyar dake rubuce a tsakiyar wani lafcecen heart (zaku iya tunawa da wasiqar soyayya da ake rubutawa zamanin quruciya?,ya kai zunzurutun zinaren mazirarin zuciyata?????).

        Maida wasiqar yayi sama a qasa yana lalubo sunan marubuciyar,sunan ubaida ya bayyana,saiya linke takardar,sannan ya waiwaya ya dubi sadiqu

“Yaushe ka mayar dani dan iska ka fara karbo wadan nan abubuwa kana kawomin?,bari to na ajjiye na kaiwa malam,kada wataran ya kamaka ya zaci bakinmu daya,ko kuma ni nake aikenka” da hanzari sadiq ya tashi yana danne dariyarsa yasha gaban lamin dake zura jallabiyarsa ta barci

“Kaga…..ni kada ka yimin sharri,ni ina ruwana?,ina zaune ta aiko qanwarta ta kawomin,kaga kenan bani na janyota ba ko bare kace” tsayawa yayi yana duban sadiq din,ya sanshi qwarai da rawar kai,saboda yawancin lokuta idan yaga ana tashi daga aiki lamin din ya biyo masa ya sakashi a gaba sunyo gida,suna isowa anyi magariba sunyi masallaci,saga can sun zauna karatu da malam,ana tashi hira cikin abokansu lamin din baya bari su zarce awa daya zai takura sadiq din kan su shiga gida,ko su zauna a dakinsu suyi wata hirar,ko suyi karatu,ko su kalli ball idan nepa sun agajesu da wuta,ko kuma su zauna tare da inna kafin malam ya shigo,yakan yi qorafin

“Waikai…..sai kace wasu mata da Allah,kai ko dan ‘yammatan nan da akeyi na layi bamu da,kana gani su buhari fa,yarinyar nan ta bayan layinmu har dan wasiqa suke aikawa junansu” kallonsa kawai lamin yakanyi

“Shekararmu nawa ne?”
“Sha bakwai mana,ni harda watanni ma”

“Tabdijan,a shekara sha bakwan har mukai wannan matakin?,meka ajjiye?,me kake dashi?,wanne mataki ka taka a karatu?”

“Mtseeww,ka gane mana,bafa wai aure zamuyi bafa,kawai irin dai soyayyar nan da kowa ke tabawa ce,ai abun kunya ne a yadda mukafi dukka samarin unguwar nan kyau amma ace mune bamu da budurwa”

“Nidai a wajena ba abun kunya bane,amma tunda kai a wajenka haka yake,kaje Allah ya bada sa’a” daga haka ya maida hankalinsa ga qaramar tvn dake gabansa,wanda suke hasko wasan da ake bugawa ta gasar nahiyar turai,tsakanin Manchester da Barcelona.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button