KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

       Yana jin sadiqun yana mitar yanzu kallon qwallon ma sudanje gidan kallo suyi cikin mutane amma abu ya gagara,kowa yana can ma su suna cikin gida kamar mayu.

        Shi sam irin wadan na shirmen na tashen girma Allah ya tsameshi,baya bashi sha’awa ko kadan,yadda yake gudanar da rayuwarsa yafi masa dadi,shi mamaki ma yake idan yaga sa’anninsu suna soyayya,tome zasuce a wadannan shekarun nasu?,dariya suke masa idan ya fadi hakan,sau tari sukance

“Dama mune muke da kyau irin naka?,kai don bakasan yadda ‘yar mata matan nan ke sonka ba,miskilancinka kawai yasa suke shakkar yi maka magana”.

        Hannu lamin ya sanya kan locker din tasa bayan ya gama wannan tunanin,ya ciro wani man fito da saje da qasumba da sadiq din ya siyo tun rannan,wurgi lamin yayi dashi saman kujera

“Shi yasa dama ka siyo wannan saboda kayi sauri ka hada gemu kai dole gaka babba ko?” Yadda lamin yayi maganar cikin jin haushi ya sanya sadiq qyalqyalewa da dariya dole

“To wai kai din da kaketa haka waliyyi ne kai?,girman nan fa yana tahowa na gaya maka gaskiya,don ko a yanzu haka habarka ta fara gemu,toni kuma saina zauna a haka a rainani?,ko kai rannan ina ganinka kanata matse matse?,waye yayi wankan asuba shekaran jiya?” Ya qarasa fada qasa qasa saboda kar a jiyosu.

        Kafin sadiq ya ankara lamin ya kwada masa wani comb da yake taje sumarshi,a baki yaso ya sameshi Allah ya taqaita masa ya goce ya samu kafadarsa,sai yayi qofa yana sheqa dariya

“Kaga kenan gwara ni,kiran girman kawai nake,kai kuwa ya fara samunka,idan ka gama shiryawa ina jiranka a wajen inna” saboda wajen sana’arsu zasu wuce,don suna hutu ne saboda sun kammala rubuta jarabawar qualifying,suna jiran wucewarsu S S3,bugu da qari ma kuma weekend ne.

        Yana shiryawa maganar sadiq na dawo masa,a ranar ya faki idanun sadiq yayi wankansa ne baisan yana ganinsa ba,bayason sadiq din ya sani,saboda yana kunyar abinda zaice masa,duk da cewa daga shi har sadiq din ba jahilai bane,tun kafin zuwan wannan lokacin malam ya musu bayanin xuwan nasa,saidai shi abun naso yazo masa da wani yanayi na daban,yana jin cewa halittarsa ta dabance,don kusan bai taba ganin ko ji daga sadiq din ya shiga yanayi irin nasa ba.

       A nutse ya shirya,kamar ko yaushe tsaf dashi,cikin wani yadi mai sanda sanda me sauqin kudi,yayi kyau,dai dai da matashi mai qananun shekaru.

        A tsakar gida ya samu inna da sadiq din,ya miqe suna yiwa inna sallama,ta rakasu da kyakkyawar addu’a da kuma fatan alkhairi,ta bisu da kallo tana jin alfahari da ‘ya’yan nata,wanda tsakanin sadiq din da lamin bata banbace wanda tafiso a cikinsu,tun bayan shigowar lamin din rayuwar gidan.

      Tun qarfe uku ya katse dukkan ayyukansa bayan ya dauki uzuri waje ogansu ya koma daukar iman din.

       Baifi jiran minti talatin yayi ba daliban daga makarantu daban daban suka fara fitowa,yana tsaye harde da hannayensa ya hangota,ya zuba mata idanu yana murmushi ganin yadda take waige waige,ya tabbatar da cewa shi take nema,yadan sake sakayewa kadan don ya gani ko zata iya ganoshi,saidai batayi wani nisan zango ba golden eyes dinta ya hango mata shi,saita taho da dan gudunta ma gauraye da quruciya tana dariya,tana zuwa ta daneshi.

        A hankali yasa hannunsa yana zareta daga jikinsa,ita kuma tana sake maqaleshi tare da fadin

“Ya lamin mun gama….”
“Imaannn” ya ambaci sunanta yana dan dagewa kadan

“Sakeni mana” turus tayi bayan ta sakeshi tana kallonsa,baki a tabe alamun shagwaba

“Yaya me nayi maka?”ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jin dadinta saiya duqa a gabanta yana duban golden eyes dinta

“Iman…..daga yau kin girma fa,kin zama babba,ko baki gani bane?,kin zana jarabawar fita daga primary,zaki tafi secondary,duk wanda yaje secondry kuwa ya girma…..wadda ta girma kuma ba’ason tana taba maza kinji?” Saita tura baki gaba

“Ni bana kula kowa Allah ya lamin,ko mazan ajimu ma Allah,kaine kawai,kuma kai ba yaya na bane?” Kansa ya gyada yana sake fidda murmushi

“Yayanki ne,amma ko nidinma daga yau na hana kinji?saboda kin zama big girl” Kanta ta gyada,saidai da alama har cikin ranta bata gamsu ba,yana ankare da ita yadda tayi kicin kicin da rai,duk yadda yake janta da hira kan yadda taji jarabawar taqi sake masa ta bashi labari,bai gaji ba yaci gaba da janta da hirar har suka iso bakin titi don su tari abun hawa.

        Dalibai ne birjik da masu daukarsu,daga gefansa wata ‘yar matashiya ce riqe da hannun wata daliba,da alama qanwarta ce,tunda ya shiga wajen dauko iman ya lura da yadda taketa satar kalloshi,dauke kai yayi yanzun ma kamar dazu,ya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya fito da baqin glass dinsa da yakan sanya lokaci lokaci.

      Sanyawar da yayi saita sake haska kyanshi cikin farar fatarsa,ya miqa hannu yana tsayar musu da adaidaita sahu,gaba kadan dasu ta tsaya,ya taka ya tsaya yana masa bayani inda zai kaisu.

       Yana shirin shiga yarinyar ta qaraso tana fadin inda zata itama

“Shiga muje” mai adaidaitan ya fada mata jin hanya daya ce,abinda yasa fasa sanya qafafunsa,ya kuma dauke kwandon iman da ya zura a motar yaja baya yana cewa

“Kuje kawai” binsa ta danyi da kallo

“Dukkanmu qannenmu muka dauko,kowa gida kuma yakeson zuwa,kuma tunda yace muje ai hanya dayace ko?” Ta fada tana dan fara’a,kai ya gyada

“Ga wasu ‘yan uwanki can daga gaba,idan hanya daya zaku shikena sai ya cike dasu” yanayin fuskarta ya nuna bataso ba,amma haka ta saka qanwartata itama ta shiga.

       “Yaya sun tafi fa,dama shiga kawai mukayi” sosai ya kalleta sannan ya amsa mata

“Babu kyau hada maza da mata guri daya,nima bazanji dadi ba idan kika shiga keda wani” tadai jishi ne,amma bata fahimta abinda yake nufi ba.

      Basu dade ba suka sake samun wani abun hawan,a hanya ya siya mata tarkacen alawoyi,abinda ya sanyata sakewa kenan,ta dinga bashi labarin jarrabawar,da kuma yadda ta amsa kowacce tambaya,don kusan duk abinda ya karanta mata shi taga ya fito.

1~ KUFAN WUTA????
Safiyya Huguma

1~ BAQAR INUWA????
Billyn Abdul

1~ RAYUWAR MACE????
Hafsat Rano

1~ MASARAUTA????
Miss Xoxo

1~ NOOR ALBI❤‍????
Mamuhgee

Guda 1????300
Guda 2????400
Guda 3????500
Guda 4????700
Guda 5????1k

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

TEAM ZAFAFABIYAR???????? KUFAN WUTA????????????

NA

HUGUMA
ZAFAFA BIYAR????????????????????

LAST FREE PAGE

GA WADDA KE BUQATAN BIYAN KUDINTA,ZATA IYA TUNTUBARMU TA WANNAN NUMBERS DIN

09032345899
KO
09166221261

  Tun bayan zana jarabawarta ya soma mata tanadin tafiya zuwa makarantar gaba ba tare da kowa ya sani ba,ya siya duk abubuwan da yasan zata iya buqata da kadan da kadan,zuwa lokacin ya fara canza yanayin kusancinsu,sabida girma daya fara zuwan mata,a sannan ta shiga shekara ta goma sha uku,duk wasu abubuwa daya kamata ace ta sani yana koyar da ita cikin dabara da kuma hirarsu,abubuwan da ya kamata diya ta sani a shekarun fara girmanta,bugu da qari innarta itama ba baya bace,sau da dama idan ya gaya mata wani abun takan ce inna ta gaya mata,saidai bata fiya daukarsa serious ba kamar idan shine ya gaya matan,tafi maida hankali idan shine ya fada mata da kansa.

  Cikin sa'a jarabawarsun ta fito,taci wata government school da basu da nisa da ita,ba bata lokaci malam ya fara mata shiryen shiryen komai,saidai ya tadda amin yaci rabin aikin,shuru malam yayi cikin mamaki tare da qara qaunar amin din har cikin jininsa,irin kulawa da iman ke samu a wajensa ko dan uwanta da suke ciki daya sadiq bata sameta ba.

  Bashi da abinda zaice masa banda godiya,godiyar da take saka amin din jin nauyi da kunya,saboda shikam har yanzu a nasa ganin bai sakawa su malam din da komai ba,don har kwanan gobe arziqinsu yakeci,sun sanyashi cikin iyalinsu,yana kwana ya tashi muhalli daya dasu,kuma har kwanan gobe malam din bai daina ciyar dashi da dauke masa wasu buqatu irin na uba da dansa ba.

   Duk da haka malam din ya kwakkwafeshi kan ya dinga adani da tanadi,ya daina qarar da duka nemansa akan iman din kadai,ya shaida masa yana taru,bai nutsu ba sai daya samu tabbacin hakan daga bakin sadiqu.

  Bangaren inna ma saidai addu'a da fatan Allah ya jiqan mahaifansa,amin din hannun kyauta gareshi,abun duniya bai rufe masa idanu ba sam,kulli yaumin baya taba shigowa hannunsa rabbana cikin gidan,wannan dabi'a tasa har sadiqu ya koyeta,hakan kuma bai sanya ya manta da yayarsa dake garinsu ba wadda tasha dawainiya dashi ba,duk sanda zaije ganinta yakan riqe wani abu me kauri yakai mata.

   Cikin nasara iman ta fara zuwa makarantar,yarinya ce mai hazaqa da kaifin basira,gefe daya kuma ga alamin,ya soke hirar dare saidai karatu,idan sun gama karatun ayi hirar kafin inna ta korata ta kwanta,cikin qanqanin lokaci tayi suna cikin makarantar.

    Sannu a hankali rayuwa keci gaba da tafiya musu cikin nasara,iman ta gama js 1 ta tafi js 2,har ta tafi zuwa js 3,a sannan tuni yammatanci ya fara zuwar mata,duk wani baiwa da surar kyau na 'ya mace ya fara bayyana a jikinta,wani irin sassanyan kyau wanda hatta da inna ya sanya take sake saka hankalinta da kulawarta akan diyartata,don ko ita duk da tashen kyau da tayi zamanin quruciya bata kai iman din ba,inda Allah ya taimaketa iman din nada wani irin nutsuwa da kuma kamun kai,bata da hargagi ko hayaniya,ko rawar kan yaran da suke tashen girma.

   Ta bangaren alamin ma ya sanya kulawarsa sosai akan iman din,bama shi ba harda sadiqun da suke ganin kamar bai damu da al'amuranta a baya ba,saboda lokacine na sabbabin qawaye,kuma lokacine da qananun samari da suma suke tashen girma suke iya shiga rayuwar yarinya,su sauya ta tare da koya mata dabi'u kala daban daban.

  A sannan Allah ya fara sanyawa nemansa albarka,don cikin shagon nasu da suke dinki a yanzu haka shima ya mallaki keke nasa ma qashin kansa,idan bashi da makaranta zama yake ya wuni yana dinkinsa,idan kuma yana da lectures sai ya bada haya wani ya hau,da kudin dinkinsa yake sponsoring karatunsa da komai na rayuwarsa,ya taimaki yayarsa da a yanxu babu abinda zatace dashi sai hamdala,hakanan daga inna har malam gajiyar alamin din sukeci sai godiya.

    Yana da tsari da kuma bin komai a sannu,bai dauki rayuwarsa da zafi ba,bai kuma dauki kansa a wani ba,komai nashi moderate yake yinsa tsaka tsaki,babu qarya a ciki,baya kallon wai collage yake,dole sai yayi abinda wane da wane sukeyi,idan ka ganshi baka isa ka aibatashi ba ko kai waye,yana da tsafta da sutura ta zamani bakin gwargwado,saidai duk abinda yasan zai zame masa wahala baya kawoshi cikin rayuwarsa,hatta da wayar hannunsa mai matsakaicin kudi ce,bai damu da sai ya riqe babba ba,tunda wannan din zatayi masa komai da babbar zatayi masa,yakanyi tunanin gwara ya sanya kudin cikin sana'ar dinkinsa,don a yanzu wani keken yakeso ya sake siya banda wanda yake dashi.

    Dukkan wani rufin asiri da kuma kyautatuwar rayuwa ya sameshi,iya shi da sadiqu a qananun shekarunsu sun tsayawa gidan,sun saukewa malam abubuwa da yawa su sukeyi,don hatta da harkar karatunsu,kama daga kudin registration da sauransu su sukewa kansu da kansu.

**Kamar yadda al’adar gidan ranar kowacce juma’a tuwon shinkafa akeyi miyar taushe,wannan juma’ar ma hakan take,gefin magariba IMAN ta gama komai,ta kuma killace gidan kamar yadda ta koya daga mahaifiyarta,saboda a yanzun da shekarunta suke goma sha biyar,dukkan wani aiki da ada yake wuyan innar yanzu ya dawo wuyanta,ta horu da wannan tun tana da shekara goma a duniya,don haka sam komai baya bata wuya a yanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button