KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

    "Yanzu kai malam al'ameen haka za'ayi dakai?" Cikin fargabar ko wani laifi ya yiwa malam ya daga kai ya dubeshi,malam din ya fahimci abinda ke yawo saman fuskarsa,sai ya saki murmushi

“Kai da zaka zama magidanci nan gaba,haka zaka zauna sai abinda takeso zakayi mata?,shifa namiji kullum so ake ya zama tsayayye,yana da kyau a dinga bawa mata dama kan raayi da zabinsu,amma kuma bafa akan komai ba,qarqashinka zata zauna nan gaba kadan,to dole tun yanzu ka dinga azata akan tsari da tafarkin da kakeso ta kasance akai” cikin hikima malam din ya dinga nusasheshi,daga bisani kuma suka fada hira,wanda wannan ba sabon abu bane dama tsakaninsa da malam din ba,sunawa juna kallo da da mahaifi ne.

    Ya jima yana nazari kan maganganun malam,su suke ganin kamar yana biyar son ran iman dinne,wanda sam shi ba haka bane,duk abinda yakewa iman....tun kafin ya soma jinta da wani matsayi daban a cikin zuciyarsa kawo yau,yana mata ne saboda ta cancanta ta kuma dace yayi mata hakan,sau tari kuma zabu da ra'ayinsu ana samun arashi yana zuwa daya,iman din ta dabance cikin rai da rayuwarsa,duk da yana ganin abubuwa sosai tattare da ita,ita dinma kamar ta canza,amma nan gaba kadan zai qarasa bude mata komai,yana son yabi komai ne bisa tsari na hankali da dacewa,da wannan ya kwanta a ransa.

ZAFAFA BIYAR 2022

BIYAR : DUBU DAYA (1k)
HUDU: 700
UKU: 500
BIYU: 400
DAYA: 300

AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKANFARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE  MU TA

ZAKU BIYA KUDINKU ANAN????????

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biya????????

09032345899

KATIN MTN????????

09166221261

YAN NIJAR ????

+227 95 16 61 77

Ga ‘yan nijer zasu tura katin moov ko Airtel zuwa wannan number


ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

TEAM ZAFAFABIYAR08

LITTAFIN KUDINE,ZAKI IYA TUNTUBAR WADAN NAN NUMBERS DIN DON SIYAN NAKI

09032345899
Ko kuma
09166221261


 Misalin takwas da rabi na safiyar ranar litinin din,zaune take saman doguwae kujerar dake falon principal din nasreen memorial academy,tayi neat cikin shigar uniform din makarantar da shima ya karbeta fiye da makarantar data baro,idanunta sunyi narai narai tana kallon al'amin daya miqe yana sallama da principal din,bayan sun gama komai shi da sadiq sun damqata ga hannun hukumar makarantar,baqunta take ji sosai cikin wannan makarantar,tamkar yau ne rana ta farko data fara zuwa makaranta,al'ameen ya waiwayo a nutse ya sanya hannunsa a aljihun wandon lallausan yadin jikinsa da iya tsahon rigar ya tsaya a gwiwarsa,ya ciro 200 ya miqa mata

“Idan ba zaki iya komawa gida ba ki jirani na dawo,sai na maidake” hannu tasa tana amsa
“Zan iya yaaya” ta amsa mishi a tausashe,principal din yayi murmushi

“Wannan qanwar taka da alama kana ji da ita” ua fada cikin salon barkwanci,sai al’amin ya waiwaya ya dubeshi sannan ya saki murmushi

“Auta ce”
“Oh….i see” ya sake sakin murmushi ya musu sallama yabu bayan sadiq suka fice.

     Tana zaune nan tana rarraba idanu,har principal din ya kira daya daga cikin masu goge goge dake aiki a makarantar,tayi masa kiran Assistant monitor din ss 1,ba jimawa ya dawo yace tana zuwa.

     Ba'a rufa minti biyar ba tayi sallama,cikin nutsatsiyar muryarta,tana sanye da uniform irin na iman din,iman din ta bita da kallo,tana da haske saidai baikai nata ba,tana da madaidaicin kyau,a qiyasce shekarunsu zasuyi daya da ita

“Ga new student nan,ayi mata seat,sannan a shigar da sunanta cikin register”
“Okay sir” ta amsa a ladabce,sannan ta waiwaya zuwa sashenbda iman ke zaune.

     Suna hada idanu ta sake mata murmushi,saita soma takawa zuwa inda take din tana dubanta,har yanzu kuma murmushin bai bar kan fuskarta ba,ta duqa ta dauki hand bag din iman din tana cewa

“Taso muje” saita miqe tana dan jan rigarta tabi bayan yarinyar.

    Tare suka jera cikin yanayin baqunta,saita waiwayo ta sake sakar mata murmushi

“Sunana munira hasan……nice assistant monitor na ss 1,monitor dinmu namiji ne…..kefa,meye sunanki?”

“Hajar ibrahim khalil”
“Yadda kike da kyau haka sunanki yake da dadi” munira ta fada tana sakin murmushi gami da kallon iman.

    Martanin murmushin iman din ta maida mata tana cewa

“Na gode” sukaci gaba da takawa,maganar muniran na maimituwa a ranta,sai ta sanya hannu ta shafi fuskarta a fakaice,an jima ana fadin ita me kyau ce,saidai ita bata taba ganin kyan ba a karan kanta,hakanan bata taba baiwa maganar wani muhimmanci ba.

      Kai tsaye munira ta kutsa kai cikin ajin,wanda ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga allon da malamin dake tsaye yaketa cikashi da rubutu daliban suna kwafa suna mayarwa zuwa ga litattafansu. Sallamarsu sai taja hankalin kowanne dalibi dama matashin malamin dake tsaye gaban allo,ta qarasa daura da malami tana cewa

“Sir,sabuwar daliba ce inji principal,yace a saka sunanta cikin register” kai ya gyada gami da cewa

“Okay”idanuwansa nakan fuskar iman,wadda ta fara jin wani iri,saboda yadda idanuwa sukayi mata caa na dalibai maza da mata,musamman ita da banda primary data yi da maza lokacin bata da wayo, junior dinta ajinau mata ne zalla,kasancewarta government school

“What is your name?” Malamin ya jefa mata tambayar da harshen nasara,cikin sassanyar muryarta data sake janyo mata idanuwa ta amsa masa,sai ya jawo register din kusa dashi ya rubuta sunan,sannan ya bawa munira umarnin tayi mata wajen zama.

     Kai tsaye seat dinta ta matsa mata,saboda tsarin zaman duk seat daya mutum biyu yake dauka,da su biyu ne akai ita da qawarta,to bayan an shiga sabon term sai aka canzawa qawartata makaranta,hakan ya sanya take zaune ita daya,saboda ba da kowa ita din take jurar zaman ba.


   Ranar farko a makaranta ga duk sabon dalibi rana ce dake cike da baqunta da rashin sabo,kusan hakan taso faruwa ga iman,saidai kuma kirkin munira ya hana hakan faruwa,saboda janta data dinga yi da hira,koda aka fita break tare sukayi break din,aka dawo suka zauna a seat dinsu,tana ta bata labaruka da suka danganci makarantar da yadda take,har zuwa lokacin da aka kada bell an tashi kenan,iman din ta saba jakarta tana nufi qofa bayan ta yiwa munira sallama.

     A qafa ta fara takawa sabida tadan qara gaba inda babu cunkoson dalibai sosai,tana tsaka da tafiya taji muryar munira na kiranta,saita dakata ta kuma waiwayo suka hada ido,kowa ya sakarwa dan uwansa murmushi,ta dakaci muniran har ta qaraso inda take,suka jera sukaci gaba da tafiya tare,kafin daga bisani muniran tace

“Ya na ganki kina takawa a qafa?” Waiwayawa iman tayi tadan dubeta cike da mamakin tambayar tata,to ame takeson ganinta?,kamar taji tambayar da ta yiwa kanta sai ta dora
“Ko mai daukarki ne bazai samu zuwa ba?,ranar farko a makaranta kuwa ai bai kamata ya barki kiyi tracking ba”. Sai yanzu ta fahimci zancanta,saita murmusa

“Dama can motar haya nake hawa,saidai wataran idan hanya ta biyo da yaa al’ameen ta qofar makarantarmu ya jirayeni mu koma gida tare” kai munira tadan jinjina,tana cike da mamaki,saboda kallon farko data yiwa iman,ta mata duba ne na yaran da suka fito gidan hutu,sam kyan qira da dirin da Allah ya bata tayi zubin gidan yaku bayi ba,ta tsammaci zata ga wata shimfidediyar mota tazo daukarta ne,saita aje tunanin nata tana tambayar iman din unguwar da take.

    Sanda ta gaya mata idanu ta fiddo

“Ai bamu da nisa da juna,abun hawa daya zamu hau,tunda nima yau shuru ba’azo daukata ba” ta fada tana saka hannu tana tsayar musu da adaidaita sahu,suka masa bayani suka shige,iman din na qoqarin neman ragi kan kudin da ya gaya musun,amma sai taga muniran bata damu da price din da ya fada ba,don haka itama sai tayi shuru kawai.

    Suna tafe muniran na jan iman da hira,a dan zamansu na awanni iman din ta fuskanci muniran kamar daga gidan masu dashi ta fito,koma ba haka ba to tabbas gidan data fito sunfi nasu wadata,tadan saki jiki kadan da ita tana biyewa hirar tata,har aka kawo inda muniran zata sauka,wanda daga nan zuwa gidansu iman baifi naira 20 ba kudin mota.

      Kudin da ya buqata munira ta ciro ta biya musu,iman zata doje tayi gaba abinta bata tsaya ma sauraren qorafinta ba,mai adaidaita yaja sukayi gaba,cikin ranta kafin su qarasa gida tana ta yaba kirkin muniran da karamcinta,azamansu na wasu taqaitattun awanni.


    A dan gajiye ta shiga gida,saboda akwai qaerin lokacin tashi kadan a wannan makarantar kan makarantar data baro.


 Da sallama ta kutsa tsakar gidan nasu qarfe biyu da rabi da minti biyar,inna dake duqe tana baza masarar data wanke don ta samu tasha iska akai niqa ta dago tana amsa sallamartata,idanunta akanta,ta sabule jakar bayanta ta zauna saman kujera 'yar tsuguno tana dan goge zufar goshinta tare da yiwa inna sannu da gida

“Yauwa,an taso kenan?” Ta fada tana juyawa zuwa ga aikinta

“Wlh inna,duk na gaji,makarantar tafi waccan nisa”

“Ah to,aishi sa kai yafi bauta ciwo” tasan mita sarai inna zata dorar,don haka ta saki dariya kawai ta miqe tana daga jakarta

“Amma inna karatun da ake mana a waccar makarantar baiko kama qafar rabin na wannan makarantar ba”

“To Alla ya taimaka” ta amsa mata.

    Kamar zatayi gaba sai kuma ta dakata

“Inna ya al’ameen bai dawo ba?”

“Tunda ya fita dai bai shigo ba” saita daga hannunta duban fuskar siririn agogon silver dake hannunta tana duba lokaci,wanda yau ta fara sakashi,kuma al’ameen dinne ya siya mata saboda makarantar

“Amma dai inna ba tuwo zakiyi ba”

“Zanyi ko zakiyi?” Kai ta gyada cikin salo na zaquwa da son jin amsar innar

“To zanyi inna”

“Bashi bane maqiyar tuwo…..dambu nakeso wai nayi” sai fuskar iman din ta dan saki,don ita gaba ce tsakaninta da tuwo,tunda taji batun dambu kuwa,tasan saboda malam da al’ameen za’ayishi,don haka tayi damarar zagewa tayishi yayi kyau yayi dadi ko don al’ameen din,tana matuqar jin dadin yadda yake yaba mata idan tayi girki,da yadda yake nuna jin dadinsa,koma bayan sadiq dake kusheta,wani lokaci har sai malam ya shiga sannan zai qyaleta,duk da shima yana yine kawai saboda tsokana,bawai don bata iya din ba,don ta fannin girki inna ta yarda da ita dari.bisa dari,tun tana da shekara takwas innar ta fara shiga madafa da ita,tana da shekara sha biyu kuwa ta sakar mata girkin,saidai ta dinga tayata ko duba mata,zuwa yanzu kuwa da ake magana fa gama zama cikakkiyar qwararriya.

    Ruwa kawai ta watsa tadan tsakuri abincinta kamar yadda ta saba ta fito ta kama aikin,yau dama babu islamiyya,anyi bikin yaye wasu dalibai da suka sauke alqur'ani,don haka aka basu hutu,wanda ida an koma su iman dinne 'yan babban aji,duk da ita dama already tana biyo bayan duk inda aka biya matan da hadda wajen malam,wani lokaci kuma idan abubuwa sunwa malam din yawa al'ameen ya karba mata.

      Cikin karsashi da kuzari take aikinta,tana yi tana yiwa inna surutun makarantar,wanda ada al'ameen din ta tarawa labaran,saidai tasan ba lallai ta sake ta bashi labarin sosai ba,sabida kaifi da nauyi da idanuwansa a yanzu suke mata,ta rasa dawa kuma zata tattauna wannan,qawarta daya a unguwarsu,to itama takan jima basu hadu ba saboda yanayi na karatu da kuma tsarin tsaron fita a gidan kowannensu,saidai tanata timing da sanya lokacin da zata fita taje susha hira da ita.

       Ganin ta kammala hada komai,dambun ya hau wuta,kuma tsakar gidansu babu kowa,saita debo 'yan qananun brassier dinta da ta fara amfani dasu a boye ta zuba a botiki ta zauna daga bakin famfo,wanda yake daura da qofar shigowa ta fara wankesu.

    Ta jima tana ajiyarsu,tun wani lokaci da sukaje nijer,anty raheena 'yar uwar inna ta bata tace ta ajjiye zasuyi mata amfani,bata aminta da hakan ba sai sanda amfaninsu ya taso mata,ta rasa wanda zata gayawa tana buqatarsu.

       Babu irin wannan hirar tsakaninta da innarta tun farko,ya alameen din nata kuma koda wasa ba zata iya tunkararsa ta gaya masa tana so ba,sai ta tuna da ajiyarta, doon haka ta debo abunta ta fara amfani dasu hankalinta kwance,amma tanata boye boye,don sai irin haka gidan babu kowa take wankesu ta shanyasu a bayan qofar dakinta,ko idan ta shiga wanka.


    Tana wankesu tana dan rera karatun qur'ani da tausashiyar muryarta mai cike da sanyi nutsuwa da kuma tashen 'yammatantaka.

     Daidai lokacin da al'ameen wanda kansa ke ciwo ya shigo cikin gidan,tun daga soro yayi sallama kamar yadda ya saba,saidai muryarsa bata da wani qarfi me yawa saboda gajiya da kuma ciwon kai,wanda ya tabbatar stress ne na dinki.

    Sam bataji shigowarsa ba,kamar yadda shima ya ganta bagatatan a farkon qofa,don sam bai kawo samuwar wani mutum zaune a wajen ba.

       Saman fuskarta ya fara sauke ganinsa,ta langabe kanta gefe guda,qaramin bakinta me dauke sa jajayen labba yana motsawa a hankali,sautin karatunta yana fita da kadan da kadan,gefan da kanta ya karkatan jelar manyan kitso guda hudu dake kanta sun kwanto ta nan har saman qirjinta.

       Tayi masa kyau ainun,fuskarta da maqerin budurci ke aikinsa a kanta tayi wani fresh tare da annuri na daban,saiya lumshe idanunsa qirjinsa yana bugawa,wani abu mai sanyi da qarfi da girma ya tsaga qirjinsa ya sauka saman zuciyarsa,ya tabbatar wani feeling ne me cike da soyayya da kuma qauna ya saukar masa,sai ya bude idanun nasa yana saukesu zuwa ga abinda take wankewar.

    Idanu ya qurawa brasssier din nata yana mamakin yaushe ta fara amfani dasu,qaramin murmushi ya qwacewa fuskarsa,ya sani tunda can tana da yawan zama da hijabi cikin gidan,to amma kwanaki yaji yadda inna ke qorafin bata cirewa ko cikin daki tasha iska,wala'alla yana da nasaba da hakan?.

     A firgice ta dago sanda taji sallamar mutum saman kanta,a zabure ta miqe saboda ba zatan ganinsa,har tana fatali da ruwan wankin da abebaden dake ciki tayi dakinta da gudu,sai ya bita da kallo,dariya ta qwace masa,ya duqa a hankali ya kwashe mata abubuwanta da hannu daya ya maida ga botikin,sannan ya tako zuwa cikin gidan yana aake jaddada sallamarsa,inna dake can uwar daki ya fito zuwa rumfarta tana amsa sallamar,saiya taka a hankali zuwa rumfar innar yana cire takalman qafarsa,rabin hankalinsa na ga dakin iman din data turo qofar ya murmusa ya shiga rumfar innar.

HILTI UNISEX CHOCOLATE STILL AVAILABLE, GRAB YOURS NOW,DAB TAKE DA QAREWA????????????????????????????????

0818401745209

Game buqatar biyan kudin zafafa biyar,zai iya tuntubarmu ta wannan number

09032345899
Ko kuma
09166221261


  "Tunda ta shigo ta fara tambaya da cigiyarka,nasan kuma labarine kawai cike taf da bakinta zata baka na makaranta" inna ta fada mishi bayan sun gaisa,tana ninke abun sallar data bari a wajen ta gashi ta shiga ciki,murmushi ya sake yana dan shafo kansa,yana funa dramer dinsu ta yanzu yanzu

“Aiki take tayi ai inna,na dauka yau zata huta sabida gajiyar sabuwar makaranta” dan satar dubansa kadan inna tayu,duk sanda ya nuna wata kulawa kan iman din hakan namata dadi qwarai,kuma dama shi ba baqon abu bane a wajensa,tana da tabbaci da yaqinun diyarta qwaya daya tilo ta dace da mijin aure,namijin da yasan abinda yake,mai yawan tausaya mata da qaunar farincikinta

“Diya macace al’aminu,gwara taci gaba da sabawa akan hakan,na gana nauyun iyalinta ne zai hau kanta,mace bata da wani hutu da ya wuce tayi abinda ya dace a matsayinta na mace,to daga baya saita huta din” dan nauyin innar yaji ya kamashi,saiya gyada kai sannan ya miqe yana yiwa inna sallama.

      Koda ya fito tsakar gidan babu ita har yanzu,hakanan babu motsinta,ya gifta inda ta tashin idanunsa nakan botikin wankinta,ya sake sakin murmushi ya wuce soro,ya saka key ya bude dakinsu ya shiga.

     Saman kujera ya zube yana furzar da iskar daya zuqota tun daga hunhunsa,hannunsa yana saman kansa yana shafa sumarsa daga gaba zuwa baya a hankali,yanajin yadda kansa ke sarawa,gefe guda kuma yana qarewa dakin nasu kallo,yasan hargitse kadan yana buqatar gyara,kwana biyu bashi da isashen lokaci da zai zauna ya gyara din,dinki yake na jama'a tuquru saboda gabatowar azumi,yanason ya samu isashen kudi a hannunsa da zai yiwa gidan siyayyar kayan azumi,ya yiwa iman kayan sallah sannan yaje ya gano yayarsa itama da nata kayan azumin dana sallah,inna tasha hanashi saboda sadiqu da malam duka suna tasu siyayyar,amma sam yaqi yarda,inda daga qarshe yace baya jin dadin hakan a ransa,sai yaga kamar innar ta warshi ne shi,wannan furucin yasa ta qyaleshi,bata sake magana ba.

     Ruwa ya fara diba ya shiga wanka ko zaiji dadin jikinsa,bayan ya fito ya murzawa qofar dakin nasu key,duk da yasan babu me shigo musu kai tsaye,ya sanya boxer da singlet ya koma ya kwanta saman doguwar kujerarsu yayi rub da ciki.

      Idanunsa ya runtse gam,tunanin iman na dawo masa,surorinta na bayyana cikin idanunsa,wani yanayi na mamayar ilahirin jikinsa,tsigar jikinsa na tashi,sai ya sake gyara kwanciyar tasa yayi rub da cikin da gaske,ya sake rufe idanunsa a hankali yana ci gaba da dulmiya cikin tunaninta,murmushi na qwace masa saman fuskarsa lokaci bayan lokaci,sai daga bisani yaso dakatar da kansa saboda ganin yadda tunanin ke neman qara ta'azzara ciwon kan nasa,don haka ya haqura da kwanciyar,ya miqe ya balli paracetamol biyu cikin magungunansa yasha,ya sanya jallabiya ya jawo qofar dakin nasu ya fito zuwa qofar gida.

      Yaci sa'a malam yana nan,an gama karatun yamma yana shirin sallamar yara,ya cire takalmansa yayi tattaki cikin girmamawa zuwa gaban malam din,yayin da shima malam ya bishi da kallo wanda ke nuna tsantsar kulawa.

    Gefansa ya zauna,bai kuma yi magana ba har ya gama sallamarsu

“Al’ameenu…..lafiya kake kuwa?” Malam ya jefa masa tambaya,sai ya daga kansa cikin murmushi ya dubi malam,yana yabawa da jinjina qoqarin bayin Allahn,yadda suke iya hakaito damuwar daje tattare dashi,ta ciwo ce ko akasin hakan

“Kaina ne yake dan min ciwo”
“Subhanallahi…..matso nan” malam din ya fada,saiya matsa gabansa kadan,ya sanya hannu saman kansa ya kama masa shi da addu’o’i,ya matsa bayan ya gama yana masa godiya,wanda babu jimawa yaji ya fara sauka,daga bisani ma suka shiga tattaunawa,har zuwa sansa sadiqu ya dawo dava wajen aikinsa shima ya zauna nan wajensu yana cewa

“Na biya ta wajen aikinku mu taho tare,saina taras waika taho”

“Kaina ne ya fara ciwo,saina yanke na dawo gida na huta” cikin yanayin nuna alhini da damuwa yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18Next page

Leave a Reply

Back to top button