KUFAN WUTA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Subhanallah,sannu”
“Yauwa,da sauqi ai,malam ya kamamin ya sauka” ya fada ganin yadda fuskarsa ta nuna damuwa
“Kaine ma man,ka dinga kwanciya wasu kwanaki kana hutawa,kana stressing kanka da yawa wallahi” murmushi kawai ya sakar masa ba tare da yace komai ba,shi a karan kansa a jikinsa yakejin akan struggling bai fara komai ba,namijin duniya dan gwagwarmaya ne,abinda ya saba gayawa sadiqu kenan.
Basu shiga gida ba anan suka yada jam'in sallar magariba su da sauran jama'ar dake salla a wajen duk sanda malam ke kusa,aka idar suka sake zama hira,irin zaman da ba kasafai lokaci ke basu damar yinta ba,saboda baqi da kuma yanayin aikinsu,daga bisani malam din yayi baqo,suka shiga tattaunawa,hirar sauta koma ysaka insa da sadiqu,sunaga qus qus dinsu saboda kada malam yaji,saboda hirar irin tasu ce,yana bashi labarin yarinyar datace tana sonshi,al'ameen din nata sukar abun,saboda shi sam yana qalubalantar mace tace tanason da namiji a irin wannan zamanin,daga qarshe malam ya tura daya daga cikin almajiransa su sanya a fito da abinci,wanda dama da wuya kaga anyi girki a gidan dai dai cikin masu gidan,saboda baqin da malam din kanyi lokaci zuwa lokaci,sadiqu yacewa yaron ya gayawa iman ta hado da nasu.
Cikin gidan babu kowa sai ita,don haka inna ta tsaida yaron malam din,ta taya iman shirya abincin,yaron ha daukar mata wani ita kuma ya dauki wani suka fito dashi.
Tunda ta doso wajen idanuwansa na kanta,cikin lullubin hijab har qasa,duba daya zaka yiwa hijabin kasan tsafta ta wadaceshi,don harda karin guga,idan kuma ta kusanto inda kake zaka iya jin qamshin body mist din da take amfani dasu,'yan 300 ne,saidai suna da sanyin qamshi,tana da maitar son qamshi da turare,don haka tun kafin ma takai haka ta iya zaben turare, training din al'ameen dince,tun daga tsafta zuwa son qamshi,girki ne kawai aikin inna.
Har zuwa sanda ta fara isa gaban malam ta ajjiye musu nasu abincin bayan ta duqa ta gaidashi shi da baqonsa idanunsa na a kanta,girma da 'yammatancinta yana sake cika sosai,ta zama budurwan gaske,saita qaraso gabansu a hankali,daidai sanda baqon malam ya furta wata magana data dauke hankalin al'ameen daga wajen kwata kwata ta maidashi kan hirar su malam din.
"kada dai ace hajarunka ce ta girma haka?" Murmushi malam din yayi
“Itace mana” kai ya gyada
“Ikon Allah,girman dan mutum babu wuya”
“Ka kwana biyu baka ziyarcemu bane shi yasa” malam ya amsa masa gana wanke hannunsa cikin kwanan wanke hannu dake gabansa wanda inna ta hado dashi
“Lallaifa an kwana biyu” sai yadanyi shuru kadan sannan yace da malam
“Ni kuwa malam khalilu,da zaka amince ai da mun qulla wani alkhairi” daga kai malam yayi ya dubeshi sanda yake qoqarin bude kwanonin abincin
“Ina saurarenka malam basiru”
“Me zai hana yaron wajena ilyasu yazo yaga hajaru,bamusan me Allah zaiyi ba,kaga idan Allah ya daidaita tsakaninsu ai mu shikenan,kakarmu ta yanke saqa,tuwona mai na”
Saura kadan maganar tayi tafiyar yaji da numfashin al'ameen,idanunsa suka fara laluben iman dake duqe a gabansu tana ajiye musu nasu abincin sabida bacewa ganinsa da take neman yi,zuciyarsa tayi wani bugawa tare da qara adadin gudunta.
Ajjiye murfin hannunsa malam yayi yana duban baqon nasa
“Zanfi kowa jin dadi matuqar hakan zata kasance,inama ina da wata diyar bayan hajaru da na baku,kuyimin aikin gafara,tuntuni na bayar da hajar,lokaci kawai muke jira a zartar da komai nan kusa in sha Allahu”.
Nannauyar ajiyar zuciya alameen din ya saki,yana share gumin dake goshinsa tare da duban tsakiyar blue din qwayar idanun iman din dake haske cikin dan hasken dake kewaye da wajen,kamar tasan ita yake kallo saita daga kai suka hada idanu,ta sakar masa da murmushi tana sadda kanta qasa cike da jin nauyi da kunyar abinda ya faru dazun,abinda ke alamta masa cewa bataji maganar dasu malam ke tattaunawa ba,nauyin numfashin ajiyar zuciyar da ya saukar ne ya sanyata daga kai suka hada ido da ita.
Kusan baici wani abincin kirki ba ya tattara ya koma cikin gidan,dakinsu ya fara shiga saidai ya kasa zama,yanason yin magana da iman din,ba kasafai ya fiya son kebewa da ita ba saboda kare haqqin sharia sa kuma gujewa shaidan,amma dole ya zaqulo dalilin da zai sanya su zauna suyi magana da ita,don haka ya dauki sabuwar wayarsa daya siyo a dazun ya juya da niyyar fitowa,dai dai sanda sadiq ya shigo ya wuce cikin gidan ya barshi a dakin yana amsa waya.
Dakin malam da ya gani a bude ya tabbata malam din ya shigo cikin gida,kuma idan ya shigo din inna na tare dashi,hakan ya sake bashi qwarin gwiwar isa ga rumfar inna.
Cikin saa ya sameta zaune tsakiyar litattafanta,ta bajesu tanata qoqarin gwada assignment din da aka basu a yau din,wanda zasuyi zanen zuciya ne tare da fitar da kowanne chamber na cikinta.
A hankali ta daga kanta tana amsa sallamar tashi,sai kuma ta maida kan nata ta duqar tsakanin qafafunta tana juya abun zanen dake hannunta,ya sake sakin murmushi,ya qarasa a hankali kan kujerar dake daura da ita ya zauna saman hannun kujerar,cikin lallausar muryarsa daya ragewa kaifin sauti yace
“Hajar ‘yammata” ji tayi tamkar zata lume a wajen,sautin muryarsa a yau din ya zama na da an cikin kunnuwanta,uwa nauyinsa da takeji ya ninku cikin ranta daga sanda yaga abinda taje wankewa dazun
“Ina fatan kin kwashe wankinki,saboda banason kowa yazo ya gani” saita saki abun rubutun ta juyar da kanta ta sanyashi saman kujerar tana boye dariyarta cikin jin nauyi,ta tabbata zaiyita tsokanarta ne idan batace wani abu ba,don haka cikin siririyar muryarta tace
“Don Allah ya alameen….don Allah” yasan me takeson fada,saiya saki qaramin murmushi me dan sauti kadan,ya zamo ya zauna sosai saman kujerar yana cewa
“To shikenan….duk da dai an boyen…..shikenan dai,ungo wannan,sakamin a charge” a hankali ta juyo tana avoiding hada idanu dashi,tasa hannu biyu ta karba wayar da yake miqo matan
“Laaaa yaya,taka ce?” Kai ya gyada mata tana juya wayar a hannunta
“Tawa ce” saita narke kadan,duk da bata bari sun hada ido ba
“Don Allah yaya yaushe zaka siyamin nima,kaga fa na shiga senior” ya santa qwarai da son waya,saidai a yanzu bashi a ra’ayin ta riqe qaya torching kwata kwata saboda wasu dalilai
“Wannan bata ishemu ba?,abuna ai naki ne”
“Yaaya,idan ka fita fa da abarka zaka dinga fita”
“Zan dinga bar miki ita duk weekend kina danawa,shikenan?” Cikin murna tace
“Yauwa yaya,na gode”
“And….idan naga yanayin performance naki a wannan term din,zan siya miki qaramar keypad indai inna da malam sun bari” sosai ta nuna murnarta,ta tashi ta fara qoqarin saka masa a chargyn
“Idan kin gama kizo zamuyi wata magana” ya fada yana saukowa tare da buda takaddan data fara zanen yana kallon zanen nata.
Tana gama sanya chargyn waigowar da zatayi taga ita yake kallo bayan hannunsa na riqe da zanenta,wani weakness ya saukar mata,duk kuzarinta na daxu ya gudu,batasan wane irin power da magnet ne a idanun yayan nata ba,wanda a baya da babu su sai a yanzu
“Zauna a nan” ya mata nuni da wajen da yake buqatar ta zauna din,inda zai zamana suna fuskantar juna ne,ta zauna ta lanqwashe qafafunta
“Wa kikeso a zuciyarki?” Ya jefa mata tambayar kai tsaye,abinda ya sanyata daga kai ba tare da tako shirya ba ta dubeshi saboda jin saukar ba zata da tambayar tashi tayi mata,idanunsa cikin nata ya jinjina kai
“Yes…..zuwa yanzu kin girma queen,ke din ba yarinya qarama bace kamar yadda kike kallon kanki,zuciyarki zata iya fadawa soyayya at any time…….wa kikejin kina so” sosai ya jefata cikin nazari,kafatanin rayuwarta batasan kowa ba bata saba da kowa ba sama dashi,bata taba kallon kowa ba taji wani abu na daban a kanshi ba sai shi,inda tasan soyayya ko alamominta,ba shakka zata iya cewa wala’alla shi takeso,amma yanzun batasan shaquwa ko ganin girma bane,duk bata sani ba.
Maganarsa me nauyi ce,don haka ta girgiza masa kai kawai
“Uhunnn….. talk to me mana,ki gaya min” sake girgiza kai tayi da qarfi,murmushi me qarfi na son qwace mata,wanda ya cakuda da kunya
“Don Allah yaya,babu kowa fa” kamar yace
“Harda ni?” Sai kuma ya danne wannan a ransa,ya saki nannauyar ajiyar zuciya,ya sake cooling muryarsa sosai
“Bani aron hankalinki iman” sau daya ta daga kai ta kalleshi ta mayar qasa tana sake gada nutsuwarta kamar yadda ya buqata
“Inaso ki bani dama guda daya tak a rayuwarki iman,ina da wani tanadi na musamman cikin rayuwarki”
“To yaya” ta fada a sanyaye.[04/06, 4:54 pm] +234 903 165 5683: 10
Wannan littafin na kudi ne,game buqata zaki iya tuntubar wadan nan numbers din
09032345899
Ko kuma
09166221261
"Imannnn" ya danja sunan nata,ta amsa da na'am,har yanzu idanunta suna qasa
“Bana so ki kula kowa,banason kiyi soyayya da kowa….. infact ma,na miki zabin mijin aure wanda zai dace dake in sha Allah…..kin yarda?” Kai fa gyada tana sake saukar da kan nata qasa
“Kinyimin alqawari?” Saita sake jinjina masa kan,ya sauke numfashi mai nauyi daga qirjinsa yana furta
“Alhamdulillah”.
Shuru yadan ratsa dakin,yana ci gaba da kallon zanen nata,saidai zuciyarsa ta rarrabu kashi kashi wajen tunani iri daban daban
“Zanen nan yayi kyau,ina tunanin yadda kika iya zanen zuciya har haka…..soyayyarki zata kasance me kyau haka” da sauri ta daga kanta suka hada idanu,wadanne irin manya manya kalmomi ya al’ameen ke mata amfani dasu ne haka,gashi ya ritsata da idanu yana kallonta,sai ita ta janye nata idanun tana sake qunshe fuskarta waje daya,ya saki murmushin nasarar da yake hangowa,yana iya hasashen yadda yake samun ci gaba da kuma galabar narkar mata da zuciya kowacce rana idan ta bullo kafin ta fadi.
Shi ya zauna ya tayata aikin gaba daya kasancewar science yayi shima,banda rashin zamowarsa dan wani shi din mutum ne me matuqar qwaqwalwa daya kamata ace ma zuwa yanzu yayi nisa a karatun likita da yake jarabar so,suna aikin yana dan janta da hira don ta saki jikinta,tadan sake amma ba kamar yadda suka saba ba,bai bar cikin gida ba saida inna ta fito daga wajen malam,sannan ya wuce dakinsu ya barta da tarin tunani cikin kwanyarta.
WASHEGARI
Bayan tasowarta daga makaranta wanda shima tare da munira suka taho,ta kuma sake biya mata kudin mota,bayan tayi wanka ta sauya kaya taci abincinta inna ta bata dakan garin kunu wanda akewa malam,tace takai bayan layinsu ta tsaya a daka ta taho dashi
“Don Allah inna zan leqa gidansu bushira” bushiran ba boyayya bace a wajensu,nutsatsuyar yarinyace da suke taba qawance da iman,wanda tun quruciya itace kadai ta dauke halayyar iman din,duka sauran irinsu rahama abokan fadanta ne,banda yanzu da girma da hankali yazo ake gaisuwar mutunci a wuce wajen.
Tana kaiwa mai dakan kudin ta zarce gidansu bushira,wanda gidajen dake tsakaninsu da gidan dakan bai wuce gida shida ba,tayi sa'a fa sameta a gida,dama kuma ba inda take zuwan,islamiyya ce,kuma makarantarsu daya,anyi musu hutun sauka sai wani satin xasu koma
“Wata sabon gani” bushira dake cire lallen data yiwa yatsu hannunta ta fada tana tabe baki bayan sun shiga dakinta da suke kwana da qannenta,murmushi ima tayi suka shiga tsokanar juna da hirar duniya,kafin daga bisani iman din fa budewa bushira abinda ke tafe da ita.
Shuru iman din tayi na kusan minti goma tana juya bayanan da bushira tayi mata,baya ta gama bata labarin komai,ta dauke hannunta daga kumatunta
“Amma bushira,ta yaya yaya al’ameen zai soni,bayan yayana ne?”
“Yayanki,ciki daya kuka fito?,ko yaya sadiqu ne?” Kai ta girgiza alamun a’ah
“To kuwa kinga ya halatta kuso juna ku kuna qaunaci juna,dama kuma abinda yafi dacewa kenan,don kusan dama ke din rainonsa ce……kuma ko ke qarya kike kice baki sonshi munafuka” bushira ta qarashe maganar tana ɗakawa iman duka a cinya gami da sakin dariya wadda ta sanya uman din dole ta tayata
“Ya al’ameen ya gama haduwa iman,idan ma bakiso wata ce zata daukeshi,yana cin list na sahun farko na kyawawan unguwan nan wanda babu na biyunsu,duk yadda zan gaya miki yadda ‘yammatan unguwar nan ke sonshi da fatan ya sosu ba zaki gane ba,abu daya ya rage miki….ki jira sanda zaice kawai yana sonki ki karbi tayinsa hannu bibbiyu…..idan ma yayi nauyin baki ke ki furta kawai a wuce wajen” duka iman ta kaiwa bushira a gadon bayanta
“An gaya miki bani da ajine,duk yadda muka taso tare dashi bazan bari ajina ya zuba ba”
“Gaskiya ne tawan,kema a unguwar yayinki ake,kawai shakkar malam dasu ya al’ameen din ya hana a fara tareki ko sallama dake,amma ni kaina masu kamun qafa dani a kanki suna da yawa,harda masu motoci wallahi” miqewa iman tayi tana daure gashinta mai santsi da ya ware wanda dama babu wuya ya warware din,ta maida hijabinta saman kanta tana fadin
“Su riqe motocinsu…..kinga na manta shaf da aiken daya fito dani ma”