KannywoodLabaraiMatan Kannywood

Kungiyar matan Kannywood za su maka Nazir Sarkin Waka a gaban kotu kan kalaman da yayi

Labarunhausa ta rawaito cewa a daidai lokacin da wasu jaruman ke kokarin sanyawa lamarin wutar da ta tashi a masana’antar Kannywood ruwa, wasu kuwa kokari suke yi su kara tada wutar ta cinye kowa ma a huta.

A jiya ne dai Mawaki Nazir M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya sake yin wani sabon bidiyo, inda ya roki kowa yayi hakuri, ya kuma bayyana cewa duka maganganun da yayi ba wai yayi bane domin ya bata sana’ar wani ko sunan wani ba, kawai dai gaskiya ce ta fito kuma ya fade ta.

Tsugunne ba ta kare ba a Kannywood

Sai dai kuma alamu na nuni da cewa tsugunne bata kare ba a masana’antar, dominn kuwa kungiyar mata ta masana’antar Kannywood sun fitar da wata sabuwar takarda da suka bukaci Nazir ya janye kalaman sa.

Kungiyar mata ta Kannywood (K-WAN)

Kungiyar ta bayyana cewa matukar Nazir bai janye kalamansa cikin kwanaki uku ba, to tabbas sai dai su hadu a kotu domin a bi musu hakkinsu kan cin zarafin su da yayi.

Abinda takardar ta bukaci Nazir ya yi

Takardar wacce kungiyar ta fitar a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022, ta yi bayani kamar haka:

“Assalamu Alaikum

Kungiyar mata ‘ta Kannywood Women Association Nigeria (K-WAN) karkashin jagorancin kungiyar, ni shugabar kungiya a madadin ‘yan kungiyar.

Duba da abin da ya faru, wanda Naziru M Ahmad ya yi wasu kalamai na cin zarafi ga mata masu sana’ar fim, muna kira gare shi da ya janye kalamansa cikin kwana uku daga yau, in kuwa bai yi haka ba za mu kai shi kotun Musulunci bisa tuhumar ya yi mana kazafi.

Na gode

Hauwa A. Bello

Shugaba

Wannan dai ya biyo bayan dambarwar da ake tafkawa a wannan makon a masana’antar finafinan Hausa, sakamakon furucin Ladin Cima na ƙarancin abin da ake ba ta a fim.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button