RAYUWAR HUMAIRA Complete Hausa Novel

Advertisements
Posted on October 23, 2015
[25/09 9:19 PM] Aishat muh’d: [23/09 4:41 PM] aishat muh’d: 1RAYUWAR HUMAIRAT
Yarinya yar kimanin shekara 15 aduniya nagani tana kuka sosai ta chusa kanta cikin cinyarta tanata kuka chan sai naga ta dago kanta dafarko dai abunda nafara gani shine yarinyar bakace irin tayan kenya tanada manya manyan ido wanda kwayoyin ido blue ne kaman na mage haka Allah yayita.. ga gashin goshi dasuka kwanta lub lub tanada dogon hanci dai dai ita kaman na besty na humi ..sanan ga lips dinta wani irin lips takeda shi tsakiyan pink sai ta kasa kasan baki abun sai ya karama fuskarta kyau.. sosai kuka take amma bai hana dimple dinta duka biyun sun lotsaba duk sheshekan da tayi…batada tsawon gashi amma gashinta wani irin coily hair takedashi,gashin iya wuyan tane amma baya taba kitsuwa tsabagen sansi ,humairat nada sanyin hali ko kadan batada fada tanada hakuri ga juriya batada hayaniya amma tanada tsoron duka tanada tsoron mutanen da basa murmushi tanada tsoro sosai dazaran taga wani baya murmushi to ta dinga tsoronshi kenan, a school kowa yasanta da tsoron duka..humairat yarinyace dat is soo adorable and sweet tanada yawan murmushi amma batada surutu tanada kyauta batada rowa….tana dagowa ta share hawayen fuskanta naga ta mike tai garden…
Maman shakur
[23/09 4:54 PM] aishat muh’d: 2RAYUWAR HUMAIRAT
Tana zuwa dai dai saitin wani bishiya ta tsugunna ta waiga sai chan ta hango wata yar adda tadauko ta chaka har saida ta haka rami mai tsawo tasa hannu cikin ramin gani nai tafito da wata akwatin karfe ta mike ta koma wajen kujeru ta zauna ahankali ta bude akwatin taciro wani envelope ta maida akwatin ta ajiye a gefe ta dau envelope din tabude tasa hannu ta ciro wata letter taga anrubuta my daughter karki karanta letter dinan sai kin mallaki hankalinki sai kin kai munzulin budurwa sai kinkai akalla 18,ahankali humairat ta share hawayenta tace mumy i have to read dis latter now inason nasan maisa Anty ke zagina??maisa ta tsaneki mumy,tace mumy am sorry but i have to read it now
Maman shakur
[23/09 5:08 PM] aishat muh’d: 3RAYUWAR HUMAIRAT
Tabude latter din tafara karantawa kamar haka..
“Assalamu alaykum my dear baby my luv my happiness my everything kafin nafara fada miki komi inason kisan u are d most important thing in my life humairat ina sonki sosai tun ranan dakika fado duniya…i remember ranan dakika fara kirana mo..m..y i was so happy i remember all u birthdays ur smiles ur hugs humairat i luv u soo so very much ahankali humairat ta share hawayen idonta tace and i luv u more momy tacigaba da karatun..humairat ina addu’a Allah ya rayamin ke Allah ya sanya miki albarka humairat ki kula da kanki ki rike mutuncin ki and always pray 4 me kice Allah kayafema momy…humairat ina rokonki da inkikaji labarin nan karki tsaneni dan Allah karki tsani momy dinki ,humairat nasan i made a lot of mistakes but i regret dem all plz dont hate me my daughter ga asalin labarina……
Maman shakur
[26/09 5:45 PM] Aishat muh’d: [23/09 5:35 PM] aishat muh’d: 4RAYUWAR HUMAIRAT
Alj usama shine sunan mahaifinki yanada yaya mai suna Ahj ustam su biyu iyayensu sukahaifa yanzu iyayensu sun riga sun rasu.su biyu iyayensu suka haifa usman ne babba sai usama mahaifinki suna son junansu alh usma shine ya dage yay karatu yadawo shahararen dan kasuwa while babanki secondary yagama yace shi zai dinga taimakonshi a kasuwanci to abunda yafaru kenan duk kudin dakikaga babanki nadashi wanshi ne usman ke bashi…alh usman ya aure mata mai kirki sunanta aisha har Allah yabata ciki bayan ta haihu tasamu namiji mai suna islam ansha shagalin suna yaron nada 5 years Allah yamata rasuwa…alhj usman yay rashi sosai da kyar ya yarda yakara aure inda ya auri mata mai suna zainab amma Abu ake cemata tunda tazo gidan ta tsani islam ta takura mishi amma alh ya taka mata birki alokacin da islam yakai shekara 15 tsnan datake mishi yakaru dan ta haihu itama ama bayason kultum dinta kaman yanda yakeson islam akwai wata rana yashigo gidan ya shiga kitchen kawai yaganta tana barbada magani a abinci yadawo falo ya zauna tana fitowa ta tafi dakin islam tabashi har zai fara ci alj ya shigo ya dau abinci yasa islam a mota da abincin suka je asibita aka gwada abincin akaga ai poison ne aciki..
Maman shakur
[23/09 5:51 PM] aishat muh’d: 5RAYUWAR HUMAIRAT
Alh usman was shocked yace yanzu Abu kashe islam takeson yi aranan da daddare ya nemana ma islam makaranta a Malaysia ya shirya komi yabiya kudin online…washe gari da safe yaje dakin islam yahada mishi kayanshi acikin akwati islam ne ya matso yace dad menene ina zamu??ahj usman ya kalleshi yace son inason kaika Malaysia kayi karatun ka achan banason zamanka da Abu kaga ban cika zama a gidaba gwara u should go far away ya rungume babban yana kuka yace dad amma banason nai nisa dakai dad ya dago ya share mishi hawaye yace ya isa kadena kuka zan dinga zuwa ina dubaka akai akai yace to dad ya share hawayenshi dan shima yaji dadi bayason zamanshi da Abu bata sonshi ta tsaneshi…aikuwa suka shirya suka tafi dad har makarantan yakaishi….
Alh usman bai cema Abu komiba koda ta tambayeshi ina shida islam sukaje??yace mata yakaishi makaranta ne a Malaysia bayan kaman wata daya yace mata zai kara aure tai bala’i amma ko kallo bata isheshiba haka ya kara aure mata mai kirki tanada suna khadija tare da ita ahj usman yake zuwa duba islam tanason islam sosai shima islam yana sonta sosai dan duk inzata zata kai mishi danbun nama chin chin da dai sauran su wanan kenan….
Maman shakur
[26/09 4:36 PM] aishat muh’d: 6RAYUWAR HUMAIRAT
Ni kadai iyayena suka haifa suna sona sosai har iyayena suka rasu sanadiyar hadarin mota nakoma wajen kakata muna zaune a kano…tunda nataso kawa daya nakedashi a duniyarnan itane kausar (anty )munason junanmu har mukai girma ahaka…tana yawan ban labari tai saurayi usama amma Allah yasa ni ban taba haduwa da usaman ba saboda a buk nake karatu ba cika zama gidaba…wata rana ina zaune da kaka sai ga kausar tazo tacemin nafito waje takawomin usama mu gaisa nako shirya mukaje zauren tare my daughter ranan itace ranan dabazan taba mantawa a rayuwataba ranan da shaidan ya kane kane a zuciyata yaci galaba akaina..ina fita na daura idona kan usama sai da numfashina yakusa daukewa ji nayi ban taba ganin namiji danake so irinshiba ga kudi ga mota ga uwa uba kyau da fara’a..saida kausar ta tabani sanan na iya bude baki nagaidashi ya amsamin da fara’an shi,, kasa jure ganin soyayyan dasukeyi da kausar nayi nace musu zan shiga ciki yadauko kudi mai yawa yaban da kyar na amsa…tunda nakoma ciki zuciyata tadinga tunanin usama gashi naga yanason kausar sosai toni yanzu ya zanyi da sonshi??harsaida nai zazzabin kwana biyu daga baya na tattara nakoma hostel…wata kawata mai suna maryam a school ta lura na chanza ta matsa min saida nafada mata matsalana son saurayin kawata nake…dayake maryam irin yan duniyan nanne nan da nan ta daurani a hanya mafi muni tace muje wurin wani malam yamin aiki ..alokacin bana tunanin komi sai dai naga na mallaki usama soyayyarshi ta rufemin ido dan bana tunanin gobe bana tunanin anjima balle gaba aiko na shirya mukaje wani kauye mai suna bichi..
Maman shakur
[28/09 6:55 AM] Aishat muh’d: [26/09 4:49 PM] aishat muh’d: 7RAYUWAR HUMAIRAT
muna zuwa muka shigacikin bukkan bokan yay ihu wayihuhu saini boka dan tamasisi dan shege jikan shegiya kakakata ce abun kwari, ubana shine fir’auna babban abokina shine dujal…sai ni boka dan tamasisi mai raba miji da mata, mai raba uwa da da,mai raba jini da jini mai raba yada kanwa,mai raba masoya ya dago da mummunar fuskarshi yace kufadi matsalar ku maryam tace boka dan Alla..h kafin ta ida maganar yadaka mata tsawa dan gusun ubanki ba ahadani da Allah zagi nakeso ki zageni,niko duk na tsorata maryam tace shege dan shegiya ubanka boka babanka boka jikokin ka bokaye sai kai dandan dujal yay murmushi yace ya isa haka nasan matsalarku kawarki nason usama shikuma usama kawarta yakeso kausar ranan nai mamaki ya akayi yasani mukace hakane boka yace zan muku aiki yadena son kausar yasoki harkuyi aure amma miliyan gomane kin yarda na kwalalo ido na kalli maryam ,maryam tace boka yanzu batada miliyan goma amma dazaran anyi auren mai kudine sai takawoma boka yace shikenan nan da nan yabasu wata hoda yacemin nashafa a fuska amma nai makesure nahadu da usama ranan nai murna mukai godiya muka karba nagode ma maryam sosai nadawo gida nafara tunanin ya za’ayi na hadu da usama alokacin natuna kausar tafada min kullum yana zuwa da daddare…
Maman shakur
[26/09 5:02 PM] aishat muh’d: 8RAYUWAR HUMAIRAT
A ranan da daddare naci gayu nashafa hodan naje gidansu kausar aiko nasamesu ita da usama suna fira tunda na shiga naga usama ya kafeni da ido nikuma inata kwarkwasa har nakai wurin su nagaidasu kausar tace kawalli yadai na ganki da nyt nace mata missing naki nayi usama dai sai kallona yake nace mata amma yanzu naganki bari najuya tunda bako kikedashi namike natafi kausar ta kalli usama da har na kule kallona yake tace luv ya kake ne ya kalleta ya balla mata harara karki kara cemin luv i hate u ya mike yaja mota sai gidanmu itakuma kausar ta tsaya tunanin metai mishi hardai tahakura gobe ta kirashi hala wani abu ne yabata mai rai,….yana zuwa gidanmu dama na tsaya ina jiranshu dan nasan zai biyoni yazo harda kuka wai dan Allah yana sona zai auran yadawo kaman yaro dan nagama mallake zuciyarshi nadagoshi nace nayarda gobe yaturo…
Nasamu yatafi ina komawa nafadima kaka cewa aure zanyi gobe za’a turo tace wane nai dariya nace usama nan kaka tafaramin fada ita bata yardaba dan yaudara mijin kawata kaza kaza abunku da rainon kaka nace mata wlh bazai yuwa inhar ni jinin kice dole kimin abunda nakeso na dinga mata rashin kunya tace Allah shiryani dan nafi karfinta yaturo duniyace zan gani nace mata eh din … Aiko washe gari yatiro alh usman aka sa rana sati daya ko fadinma kausar banyiba..itako kausar duk hankalinta yatashi usama yadena daukan wayanta gashi yaki zuwa kuma bata ganina balle tafadamin matsalanta
Sati daya nacika aka daura aurena da babbanki muka tare gidan gonansu dake cikin bicci mai kyau dukda kauyene amma badai kyauba munata chan amarci bana tunanin gobe har Allah yaban cikin ki baban ki yay murna ba kadanba..duk tsawon lokacin nan kausar bata saniba wata rana naji ana bugamin kofa da safe ina budewa naga kausar ta shakemin wuya tana wlh saina kasheki nizaki yaudara nizaki kwacema saurayi ki aura kwata kwata nakasa kwace kaina dan kausar akwai karfi muna cikin haka usama yafito da gudu yakwacrn ya nakadama kausar duka nadunga mata gwalo yay mata koran kare nace bana sonki dolene….
Maman shakur
[26/09 5:18 PM] aishat muh’d: 9RAYUWAR HUMAIRAT
Kausar tai ciwon son usama dan har labari yazomin saida tai karamin hauka…nikoko ajikina inata shan soyayya abina nahada kai da matar alh usman ta farko Abu muka dinga cusgunama khadija matarshi tabiyu dayake dukanmu a gidan gonar muke amma bata taba kulamuba…
Ranan dana haifeki anyi murna muka baki suna Aishat HUMAIRAT kowa nasonki da kausar taji labari sai da tai ciwo kullum tunani take yanda zata rama abunda namata gashi takasa auren kowa sai zaman gida…
Haka muka cigaba da rainonki har kikakai 11 lokacin kin iya magana in baki mantaba akwai randa kika dawo daga islamiyya nace me aka koya muku kikace momy mallam yace muji tsoron Allah haramun ne bin boka mutun na shiga wuta kuma mudinga yin abu mai kyau bansan mesaba maganarki ta shigen aranan nai nadamar abunda nayi washe gari bayan kin tafi school na shirya naja motana naje naba kausar hakuri nace mata zanje wurin boka yakarya asirin tayafemin abunku da so ta dinga murna tace to nace mata nan da sati daya zaki auri usaman ki da zaran asiri ya karye har mota ta rakoni na wuce gidan boka amma ina zuwa nasamu labari boka ya dade da mutuwa nai bakin ciki yanzu wazai karya asirin? mezan cema kausar?na koma gida istigi fari kawai nake ina sallolin dare yanzu yazanyi da kausar nadau waya nakirata nafada mata boka ya mutu ta dinga zagina munafuka karya kike wlh sainaga bayanki ta katse wayan..
Bayan sati daya naga kausar a gidana da fara’an ta na tarbeta ta zauna mukai fira sosai ko maganar bata min ba nace bari nakawo mana drinks nakawo kofi biyu daya nawa daya nata na ajiye tacemin plz kawomin abinci yunwa nakeji ina shiga kitchen kausar ta ciro wani magani tasa a nawa drink din tadau nata tahau sha…..nakawo mata abinci ta karba tafaraci nadau drink dina nasha batare da wani tuniba ina gama sha nakai guiwowina kasa nariko hanun kausar kiyafemin natuba nai nadamar abunda namiki nai miki alkawari duk yanda zanyi sai nasa alhaji yasakeki wani tari naji yazomin nahau tari ba kakkautawa…
Maman shakur
[26/09 5:30 PM] aishat muh’d: 10RAYUWAR HUMAIRAT
Kausar ta tunkudani ta mike tsaye tai shewa tace kina wasa dani wlh bazan taba yafe mikiba kinga yaudarata dinan dakikayi i promise all ur generations will pay 4 it…..kausar tacemin nasa miki slow poison a drink dakika gama sha kwana daya zakiyi kafin ki mutu kinga babu wanda zai taba zargina….ta kara kallona tace kinyi kuskuren yaudarata da haintata amma hausawa sunce ramuwar gayya tafi ta gayya zafi inaso nai miki abunda zai fi miki ciwo abunda koda kina kabari duk randa nataba abun sai kinji a jikinki wanan abun kuwa shine HUMAIRAT yarki nasan duk duniya kinfin sonta, nace mata kausar duk abunda namiki karki hukunta HUMAIRAT dan batasan komi kanshiba d child is innocent ina rokonki karkima yata komi dan darajan Allah, tai wani dariyan keta tace wlh duk abunda kikamin akan humairat zan rama zan maye gurbinki dazaran kinmutu zan auri usamana wlh wlh wlh saina wulakanta RAYUWAR HUMAIRAT zansa ta tazama abun kyama a idon mutane abun tausayi abun gudu bazan kashe taba wanan nai miki alkawari dan banason tamutu amma RAYUWAN dazatayi zata gwammace gwara tamutu ina kuka inaba kausar hakuri karta miki komi amma tacemin abunda kikayi shizaki girba takama hanya tabar gidan…
Maman shakur
[26/09 5:43 PM] aishat muh’d: 11RAYUWAR HUMAIRAT
Duk kina makaranta akai wanan draman ranan nai kuka humairat nai kuka nai nadama.. abunda kausar tafada gaskiya duk abunda ka shuka shizaka girba..amma kome bai kamata tataba ki ba cos u are not responsible hasalima lokacin ko duniya baki zoba amma kinsan me humairat such is life haka rayuwa take saisa burina kizama uwa tagari ga yayan dazaki haifa babu wanda yasan gobe…mutum yay wulakanshi yacima wasu mutumci yay zalinshi amma akarshe kiga wayanda ka zaluntan insuka tashi ramawa sai surama ta hanyar illata abunda kafi so aduniya bazasu taba tunanin kaine kai musu laifiba akanka yakamata su rama saidai su sami abunda kafiso su rama zalunshin akansu…humairat ranan nai kuka..chan sai namike na dauko takarda narubu ta miki wanan wasikar nasa akwati dan na yarda kausar tasamin poison saboda tarin danake tayi mai wani irin wari…humairat wanan shine labari na plz kiyafemin wahalar dana janyo miki ina miki addu’a Allah ya kulanmin dake ya rayamin ke nasan kuasar bazata iya cutar dakeba duk abunda kikaga yafaru dake ki dauka mukaddari ne daha Allah ubangijinmu..kaka ta tarasu dasai nace ki gudu wajenta hakuri zakiyi nasan babanki nasonki zaiyi iya kokarin shi wajen kula dake humairat kimin addu’a Allah ya jikana duk randa kika karanta wanan wasikar Allah kuma ya yafemin dahaka nake cemiki bissalam
I luv u daughter….
Maman shakur
[28/09 8:30 AM] Aishat muh’d: [28/09 7:21 AM] aishat muh’d: 12RAYUWAR HUMAIRAT
Humairat ta kulle latter ta share hawayen dake idonta tace mumy bazan taba tsanan kiba kullum innai sallah zan miki addu’a Allah ya jikanki…tace bayan rasuwanki dad yadinga dauremin fuska yana yawan hantarata saida Abba (baban su islam ) yakirashi gefe lokacin ban gane mai suke fadaba amma naji Abba yana ce mishi kome yafaru ba laifin yarka bace kama godema Allah daya azurtaka da yarinya tagari mai natsuwa kaman humairat banason nakara ganin ka musguna mata kaduba maraicinta dad yace to yaya naji bazan karaba ,saikuma Abba yace tunda kace zaka auri kausar din bazan hanaka ba zaka iya zuwa ka aureta amma ka kula da humairat karka bari wani abu yasameta yace to…tundaga ranan dad yadena mun komi yana kula dani sosai yana sona sosai yanemamin admission a QUEENS SCIENCE ACADEMY boarding school ne…jiya muka sami hutun ss1 zamu shiga ss2 shine na tarar dad yayi sabon aure (kausar) bataimin komiba sai dazu tana ganin dad yafita ta nakada min dukan tsiya tace wai ina takama da ubana wlh saita rabani da kowa a duniyan nan Abu da anty amarya duk sun bata hakuri takiji daga baya ta kyaleni tadau gyale tabar gidan anty amarya itane keta lallashina itako Abu cewa tayi abunda muguwar uwarki ta shuka shi zaki girba tai tsaki taja yaranta suka koma daki….
Mumy namiki alkawari zan jure komi zan hakura da duk abunda za’amin Allah ya jikanki mahaifiyata yasa kin huta….
Maman shakur
[28/09 7:33 AM] aishat muh’d: 13RAYUWAR HUMAIRAT
Jitayi an tabata tai maza ta dago dakai taga Anty amarya ce tai mata murmushi, ahankali anty amarya tace humairat har yanzu kukan kike ta share mata hawaye tace ya isa karki damu Allah na tare dake namiki alkawari zan kula dake kaman yata, Humairat tace anty bakijin haushina kan abunda mamana ta miki??anty amarya ta kalleta tace ni munyi zaman mutun ci da maman ki,humairat tace Anty nariga nasan komi tanuna mata letter ta karba ta karanta tajuyo ta kalli humairat tace inason kisani kowa na kuskure yanemi gafara Allah ya yafemishi wlh nadade da yafema mamanki kuma ni yanzu zan maye gurbinta bazan bari kausar ta cutar dakeba sai inda karfina yakare humairat ta rungumeta tace nagode mamana tadinga shafa mata baya daga baya ta dagota tace jekiyi mata wankin data saki karta kara dukanki tace too harta mike Anty amarya tace ranan iti yau islam zai dawo daga Malaysia tai murmushi tace nidai haryau ban taba ganinshiba duk in yazo hutu ina makaranta anty amarya tace ai yanzu yadawo kenan dan yariga yagama karatunshi..alhaji ma yace dukanmu zamu koma cikin kano humairat tai tsalle tace nidama banason kauyen nan mamana ,anty amarya tace to ki kwantar da hankalinki mun kusa barin kauyen tai dariya tawuce ciki…..
Maman shakur
[28/09 7:54 AM] aishat muh’d: 14RAYUWAR HUMAIRAT
kausar ce zaune gaban boka wanda kawarta ce takaita gidan..boka yace nasan matsalar ki humairat ce, so kike mukasheta??ko mu turata duniya??ko mu wulakanta rayuwar ta?? Kausar tai murmushi nasara tace boka banason ai mata kodaya daga cikinsu,idan humairat tabi duniya ai ban ci ribaba dan banga tasha wahala a idonaba,, idan kuma tamutu ai shine worse dan ban gana mata azabar danakeso ba,, idan kuma ka wulakantata shima banyi nasarar daukan fansar abunda uwarta tamin ba…tace boka inason humairat ta dandani azabar been alone kowa ya kyamaceta kowa ya zamto bayason zuwa kusa da ita..boka ya kalleta yace kinaso asa mata cutan kuturta ne??tace a’a idan tanada cutan kuturta mutane zasu taimaketa abata sadaka kuma ni tsoro bazai bari nazauna da ita gudun kar yarona suje su tabata sudau ciwon ,boka yace kinaso tana kashin kwance??tace a’a saboda zata damemu da wari a gida ga kuda,yace to kinaso tana fitsarin kwance??tai shiru sai chan tace eh…tace boka ta dinga fitsarin kwance sanan inaso kasa ubanta ya tsaneta sama da komi a duniyar nan dan naga yana sonta sama da yaron dana haifa mishi kabir..boka yay wata dariyar mugunta ya dauko wasu bebin roba guda biyu ya juwa bayansu yahadasu yace kinga yanda bebin nan suka juyama junansu baya haka usama zai juyama yarshi humairat baya zai tsaneta zai wulakantata sanan zansa ki mallakeshi yanda kome kikace yayi zaiyi kaman yankar wuka amma da sharadi tace inajinka boka yace akwai turaren dazan baki kullum cikin dare karfe 2 zaki fito kiyishi a tsakar gidanku tare da kiran sunan humairat sau 3 tace ba matsala zanyi yace duk randa bakiyiba asirin zai dinga karyewa kadan kadan kuma inkikayi kwana uku baki yiba zata dena fitsarin kwance yakawo maganin yabata ta ajiye mishi dubbanin kudi suka tafi tana mai murnan samum nasara…
Maman shakur
[28/09 8:30 AM] aishat muh’d: 15RAYUWAR HUMAIRAT
Tana komawa gida ta tarar humairat tagama duka aikin tai wanke wanke tai gyaran daki tai girki tadafa shinkafa jellof dama tadawo da yunwarta ta debi shinkafar tana kai cokali daya baki taji wani tsami tsami ga uban gishiri kuma bataji alamu magi da attarugu ba ta kwalla humairat kira a zuciye, da gudu humairat tafito daga daki kausar tace dama boarding school din dakikaje babu abunda suke koya muku?yarinya shekara 15 amma baki iya girkiba wlh yau zakici ubanki kuwa Humairat tafara kuka sosai dan ita kausar tsoro take bata tace yakuri anty wlh ni nai iyakan kokarina a girki. aikuwa abincin da kausar din tadiba mai zafi ta kwara mata ajiki humairat tai ihu tarike wuyanta da yay ja dan anan ta watsa mata kausar ta dauko duka kular abinci tace gashi cinyeshi inba hakaba yau saina kusa kasheki tai mata wani wawan dundu a baya wanda saida cikinta ya murda tawuce kitchen kafin nagama girki ki tabbatar kin cinye tawuce abunta, humairat na kuka ta gyra zama tafara cin abincin tana hadiyewa da kyar aiko kabir yaron kausar dan shekara 4 yazo yazauna yasa hannu yanaci abunku da yaro ba ruwanshi da rashin dadin abincin humairat tayi tayi yabarci yakiji, dama yaron nadaci kaman jaki nan da nan yakusa yin rabin kular suna cikin ci dad ya shigo daidai lokacin kausar tafito daga kitchen har cikin zuciyan humairat taji dadin zuwan baban nata dan saboda zai ceceta yana shigowa ya ganta yawani daura fuska ita kuma kausar tace dan ubanki shine kikasa yarona nacin abincin?tafara rantse rantse wlh nahanashi yaki ji, dad yadakama kabir tsawa tashi kabar abincin nan yazo gaban humairat ya kuma kanta da bango wanda saida taga jiri wayace kisa dana yaci abincin nan??tama kasa magana saboda azaba itako kausar murna kaman ya kasheta saboda hakonta ya cimma ruwa
Maman shakur
[28/09 6:44 PM] Aishat muh’d: [28/09 5:40 PM] aishat muh’d: 16RAYUWAR HUMAIRAT
Tana kuka tasamu ta chusa abincin a cikinta alokacin dad da kausar sun riga sun shiga cikin daki…tana gama ci tashiga bayin dakinta ta dinga kwara Amai tana kuka sosai tana gamawa ta wanke bakinta tai alwala tafito tai sallan mangariba tafito falo taga dad kausar da kabir nacin abinci, duk kanshi ya cika mata hanci kausar tace mayya da katon idonta kaman na uwarta, dad ya daure fuska bar falon nan duk in ina gida karki yarda na daura idona akanki inba hakaba sai na kusa kasheki ,ahankali tamike hawaye na tsayaya daga idonta tazauna a dakinta tana kuka yanzu me tayima dad??kausar ne taji tana kwalla mata kira da gudu tafita jikinta na rawa kausar ta rankwashi kanta tace shegiya kwashi kayan nan kikai kitchen ki wanke, ta kwashe tai kitchen dasu ta wanke ta koma dakinta bayan tai sallan isha tai karatun Al Qur’an sanan taduba littafan bokonta bayan tagama ta kwanta tai baccinta…
Karfe biyu dare kausar tafito kaman mayya ko tsoro babu tahada turaren tako kira sunan humairat sau uku..ita kuma lokacin humairat tana bacci tana mafarki gata abayi tana fitsari….
Wani duka taji ajikinta yasa ta kwalla wani ihu ta mike a tsorace wazata gani kausar tace anty ina kwana tace dan ubanki dama fitsarin kwance kike fitsari ga shegen zarni alokacin ne humairat ta kalli jikinta taga ajike abun yabata mamaki ita tasan ko kadan bata fitsarin kwance rabonta da fitsarin kwance tun kafin mamanta ta rasu ,tace anty wlh nibana fitsarin kwance hala kabir ne yazuba min ruwa aiko kusar ta dauketa dawani wawan mari dana zakima shairi tare dake yake kwana?tace yakuri bazan karaba kausar tadinga jibgarta humairat na ihu..chan dad yaji hayaniya yafito yarigama ya shirya office zashi yana fitowa daga daki yaji hayaniya yayi dakin humairat wani zarnin fitsari ne ya ziyarci hancin shi ya taushe hanci yacema kausar maiya faru tana huci tace fitsarin kwance tamin a gida katuwar yarinya haka 15 da ta isa aure ne ke amalala belt din dake jikinshi yaciro humairat tafara ihu tana kiran ceto yadinga dirkarta kausar cewa take kara mata kara shegiya mai kama da uwarta
Maman shakur
[28/09 5:57 PM] aishat muh’d: 17RAYUWAR HUMAIRAT
Sai da yay mata lilis yaga ko motsi bata iyayi da kyau sanan ya maida belt dinshi yafita abunshi,dakin yayanshi alh usman ya shiga yagaida shi yace yaya gani,usman yay murmushi dama yau zanyi tafiyan zuwa England saboda wanan business meeting din yanzu kaine zakayi handling komi gobe zaku koma cikin kano saboda islam yakusa dawowa kuma banason ya sauka a kauye..usama yay murmushi yace to yaya hakan za’ayi muje nakaika airport din tare suka fito har airport yakaishi sukai sallama harzai shiga jirgi sai kuma yajuyo yace usama,yace naam yaya, yace ka kula da humairat da kyau kaga kausar bawani sonta takeba kuma marainiyace kanajinako yace naji yaya….har cikin ranshi yanajin son yarshi amma dazaran yaga fuskanta saiyaji yanajin haushinta sosai baisan mesaba…
Humairat da jan jiki ta iya shiga bayi Allah yasa akwai water heater da ruwan zafi tai wanka tana wash wash ta wanke kayan fitsarin tadauko mope tai mopping dakin sanan tazo dauko kaya tasa taga babu kayanta saidai wani kala dayan atamfa kacal da bra daya da pant daya amma duk sauran kayanta babu haka tasa kayan batada karfi ko kadan ahankali take tafiya tafito falo taga kausar,har kasa ta tsugunna anty ina kwana ciki ciki ta amsa lpy tsoro yama hanata tayi tambayar kayan nata, kausar ne ta kalleta tace kayanki ko??na kwashe nabama almajirai ke yanzu kala biyu ne kayanki danke baiwa ce daga yanzu ,tace nasan kinajin yunwa ga abincin da kabir yarage chan jekici saboda kisamu karfin aiki….ta mike ahankali taje tadau abincin duk yay jagwalgwalon yara a ciki ga ruwa ya zuba a gefen abincin rufe ido tayi ta cusa abincin dan yunwa takeji tana gamawa taje tai wanke wanke ta gyara gidan duk da kyar jikinta zafi rau..tana gamawa kausar takawo mata zanunnuwan gado irin manyan nan masu kauri kusan kala 5 tace taje ta wanke kafin ta tashi daga barci ta tabbatar tagama,takarba jikinta na rawa, tafara wankin tana tabbatar da tai bacci dagudu tayi side din anty amarya
Maman shakur
[28/09 6:11 PM] aishat muh’d: 18RAYUWAR HUMAIRAT
Ta shiga dakin da sallamanta anty amarya ta amsa lokacin tana koyama yaranta karatun Al qur’an yan biyu takedashi hassan da hasanat shekaransu 10,anty amarya na ganin yanayin humairat ta taso ta tareta aiko kaman jira take fadawa tayi jikin anty amarya luuuu,anty amarya ta rude humairat maiya sameki??tama kasa magana tsabagen wani ciwon kai datakeji ta nunama anty amarya kanta anty amarya tace yana miki ciwo??ta daga kanta alamun eh da sauri takoma daki ta dauko mata paracetamol suko yan biyu harsun fara kuka dan sunason humairat sosai ita kadai ke sonsu yaran Abu dukansu suke..anty amarya ce tace ya isa kuwuce dakinku zataji sauki suka shige dakinsu, ta dauko maganin tabata da kyar tasha anty amarya ta kunna Ac tare da kama mata kan tai mata addu’a ahankali ciwon kan ya sauka anty amarya tace sannu kinji humairat maiya sameki jikinki rudu rudu??nan da nan humairat tafara kuka sosai tana wlh wlh wlh mamana ki yarda dani dan Allah kema karki daken wlh bana fitsarin kwance amma anty tace wai ni nayi ,anty amarya ta share mata hawaye ta lura yarinyar a tsorace take, tace humairat ya isa nasan baki fitsarin kwance amma yanzu cool ur mind fadamin yanda komi yafaru…tace mamana nidai nasan nai mafarki ina fitsari abayi daganan kawai naji duka ina bude ido naga gari yawaye nan kuma tafara kuka tace mamana kinga dad ya tsaneni yanzu bansan mena mishi ba yanata dukana,,,kuma innai kudina nazama likita mamana ke kadai zan ginama gida da Abba bazan ma dad komiba tunda baya sona….
Maman shakur
[28/09 7:09 PM] Aishat muh’d: [28/09 6:25 PM] aishat muh’d: 19RAYUWAR HUMAIRAT
Anty amarya tai murmushi ta lura har yanzu akwai yarinta akan humairat, tace humairat baban kine karkice haka ki dinga addu’a kullum Allah yasa yadawo yana sonki,tace mamana bazan kara zama a wurin suba wlh zasu kasheni nidai wurin ki zan dawo ,anty amarya tace bazai yuba karki sani a masifar kausar, ki huta yanzu anjima saiki tafi nan humairat tafara kuka da kyar anty amarya ta lallabata tai shiru takawo mata abinci taci takoshi har yamma tana wurin tana hutawa taji dadin jikinta sosai dan anty amarya tasa ta cire kaya ta gasa mata inda dad yadaketa…
Kausar tunda ta tashi daga bacci take neman humairat bata ganiba gashi bata gama wankin da tabata ba har karfe shida lokacin dad yadawo tafada mishi ranshi yabaci yanzu guduwa tayi,,sunyi carko carko a tsakar gida aiko saiga babello yarinyar Abu tazo wucewa tagaidasu harta wuce kausar tace babello kinga humairat tace laa naganta dazu ta shiga dakin anty amarya (kai su babello iyayen gulma
lol )azuciye dad da kausar sukai side dinta…
Ita kuma lokacin anty amarya nafama da humairat ta tafi sai kuka take wai kasheta zasuyi
Bugun kofa dasukaji anayine yasa tamike tabude kofa dad tagani fuska daure da kausar dad yace ina yata??Humairat naji muryan dad talabe bayan kujera anty amarya tace alh dama inason magana dakai kan humairat yawani daka mata tsawa dakata….
Maman shakur
[28/09 6:44 PM] aishat muh’d: 20RAYUWAR HUMAIRAT
Malama dakata bani yata ko yarkice? wlh duk randa nakara ganinta a dakinki saina bata miki rai munafuka kin mallake yayana kin zaci nima kin mallakenine maganar yabatama Anty amarya rai juyawa tayi takoma dakin ta riko hanun humairat tafito da ita ahankali tace kullum asace zan dinga zuwa ina dubaki humairat kuka take sosai tana ihu ta mikama alhj ita tace gashinan ku kasheta inkunga dama duniya zata tambayeku,dad yaja hanun humairat sukabar wajen…duk abunan Abu na tsakar gida tana kallo shewa tayi tare da tafa hannu maganin masu shisshigi ahayye duniyar ga da abun kallo kike ,tai tsaki taja yaranta dasuketa dariya suka shiga daki anty amarya itama takoma daki tana addu’a Allah yayema humairat halin datake ciki….humairat kuka take tana dad dan girman Allah karka dake duk iya kokarinta ta kwace kanta daga hanun dad takasa yafara kokarin cire belt tana ganin haka tasume warwas harzai fara dukanta kausar tace kyaleta saita farfado tajashi daki sukabar humairat anan falo kan sanyi tiles…….
Humairat ta tashi da asuba taga tayi fitsarin kwance kuka tahau yi oo Allah wanan wani irin matsalane Allah kayayemin ta dinga addu’a kar kausar tashigo tai maza maza ta gyra dakin tai wanka ta wanke kayan jikinta Allah yasota kayan jiya sun bushe su tamaida sanan tai salla tafito falo…kausar na sane tai fitsarin amma batai mata komiba yau dan tanada plan din wani abu…humairat ita tai aiki parking kayan dasuke bukata na komawa cikin kano karfe 10 komi ya kammala sai kanon dabo kuma yaune islam zai dawo amma karfe 4 jirginsu zai sauka….yaudai humairat murna take ba’a daketaba saidai tasha aiki kaman jaka ta gaji tai lilis ita tai gyara ta share dakin nasu dana kausar…karfe 3:30 anty amarya ta shirya tatafi dauko islam …..
Banda lpy kumin addu’a plz
Maman shakur
[29/09 9:22 AM] Aishat muh’d: [29/09 8:27 AM] aishat muh’d: 21RAYUWAR HUMAIRAT
Saurayine kakkyawa matashi masu garin dan shekara 30 a duniya yake saukowa daga jirgi mai zanen common flag amma blue da baki,fari ne ma’aboci tsayi da fadin kirji yanada ido amma basuda girma kaman na yan china..yanada saje mai tsawo wanda ya zagaye fuskarshi gashin kanshi mai kyau sai kyalli yake yaji gyara,yanada tsawon hanci sanan akwai shi da cikan gira inka ganshi zaka zaci alh usman ne sai dai jikin yarinta kaman shi sak da baban shi..islam yarone mai hankali da natsuwa akwai shi da tausayi ga taimakon talakawa matsalanshi daya shine zuciya tamishi yawa yanada saurin fushi in ranshi yabashi baya iya magana da kyau sai kaga yafara i’i’na saboda tsabagen bacin rai kowa yasanshi da halin saisa dad ke gudun bacin ran islam saboda bai iya fushiba.. ahankali yake saukowa daga matakalar benen jirgin shima yana sanye cikin kayan sojojin amma na Air force dan islam sojan jirgin sama ne…idan yaki yataso su sojoji ne masu dealing da yakin sama jirgi su ake kira da Air force…yana karasowa sai murmushi yakema anty amarya ya duka yace anty na ina wuni nasameku lpy?tai murmushi tace islam manya kenan sannu kasha hanya muje gida kaci abinci yay murmushi anty zata fara tuki yace haba anty kina tare da ni kiyi tuki kawo key din ni zan tukamu tai murmushi tafito tabashi yajasu har sukakai gida….da sallamanshi yashiga gidan su kultum babello fiddausi da meena sai oyoyo suke mishi duk ya rungume su danshi mutumne da dukda tsanar da uwarsu tai mai baisa ya tsani kannenshiba yana kula dasu yana sonsu kuma duk inyazo gida yana kawo musu tsaraba humairat kawai basu taba haduwaba dan duk inyazo tana makranta rabonshi da ita tun lokacin da mamanta ta rasu yazo gaisuwa….yace oya muje nagaida mum dinku suka shiga dakin har kasa ya tsugunna yagaidata ta amsa da kyar yaran basajin dadi yanda maman su ta tsani yaya islam haka yamike yace musu kuje ku gyaramin daki sukace to suka tafi shikuma yay side din anty amarya dan yaci abinci….
Maman shakur
[29/09 8:44 AM] aishat muh’d: 22RAYUWAR HUMAIRAT
ya shiga da sallama twins suka zo dagudu suka rungumeshi sai murna suke,sukace yaya islam kaga tunda kadawo kacema dad da anty sudena dukan humairat, hasanat ta fashe da kuka tace yaya kullum kullum saisu daketa taita kuka mama tabata magani kuma yaya humairat ne kadai bata dukanmu a gidanan tana bamu chocolate amma su yaya kultum basu bamu komi saisuyi ta dukanmu yace to ya isa daina kuka my little baby, anty amarya ne tafito tace zaku dameshi da surutun kuko oya get inside jekuyi home work dinku suka tashi suka tafi…Islam yace anty mesa ake dukan humairat??anty amarya ta kalleshi tace islam is a long story yanzu kaci abinci kaje kai wanka sai kazo mu tattauna kan matter din ,,abincin ma kadan yaci dan maganar na damunshi arayuwanshi ya tsani wani abu yataba mai yan kaninshi barinma humairat dan duk kanenshi yafi jinta a ranshi dan gani yake they have something in common rashin uwa, kodan kausar taga uwarta tamutu shine zata dinga dukanta harda dad ma but y??amma ai dad yana sonta maisa zai dinga dukanta ko laifi tayi why??anty amarya ne tace haba islam nace kaci abinci zamuyi maganar ko yace to anty yadan ci kadan yatashi yayi side dinshi..saida yay wanka yasa simple kaya riga da wando sai kamshi yake yatafi side din kausar dan gaidata…yana shiga da sallamanshi humairat ce ta amsa yaga tana kneeldown kallo daya yamata yaganeta dukda takara girma amma kaman ninta bai sauya ba..ita kuma humairat bata ganeshi ba tace anty na daki yace jeki kirata ta mike tai knocking kausar a zuciye tabude kofan shegiya mayya mai kama da uwarta manene kuma ba kneel down nasakiba jikinta yafara rawa tace dama dama ta daka mata tsawa dama me??bako ne yazo ta hankadata akasa saida tai kara takarasa falon taga dan dan alh usman ne…
Maman shakur
[29/09 9:09 AM] aishat muh’d: 23RAYUWAR HUMAIRAT
Da murmushi takarasa shiko duk ranshi yabaci amma yay kokarin dannewa yagaidata tace aa su islam ne har an dawo? yace eh nadawo anty,tace ya makaranta?yace lpy lau ta kwallama humairat kira Amalala da sauri tazo tana share hawayen tace gani anty tace jeki kawoma islam drinks sai alokacin ta kalleshi dama wanan ne yaya islam hakanefa ga kamanshi da Abba nan duk kunya yakamata ahankali tace yaya ina wuni ya balla mata harara yanzu kika ganni kausar ta cafe au dama wanan shegiyar bata gaidaka bako??ta kai mata rankwashi humairat tahau kuka,abun yay ma islam ciwo yace anty haba yarinyace kuma mace kidena dukanta haka karta samu matsala a brain dinta,kausar ta kalleshi shekeke kan wanan kakemin ihu aka lallai islam ka girma kodan kaga kazama soja kasan me uwarta tamin ne??ya mike yace koma meta miki nadai fada miki karki kara dukanmin kanwa yawuce yafita sai huci yake yawuce dakin anty….
Itako kausar tasowa tayi zata dakin humairat dagudu humairat ta shiga dakinta tasa sakata tana makyarkyata…tana mamakin islam kuma….
Islam nakaiwa dakin anty taga yanda yake huci tace mai ya faru yace a…aa…a nn …anty kaaa …uu …sarr kau..sar diinchan anty amarya tana ganin yafara i’ina tasan ranshi yabaci takawo ruwaan sanyi tabashi calm down islam Abban ka yahanaka wanan bacin ran karage plz kaga harka fara i’ina dinko da kyar tasamu ya sauko..ya kalleta yace anty fadamin maiyake faruwa ,mikewa tayi ta dauko mishi akwatin da letter ke ciki dama humairat tabama anty ta ajiye mata…yakaranta yajuyo ya kalli anty yace yanzu dama kausar itane ta kashe maman humairat??anty ta gyada kai shine kuma takeson hakala humairat nan anty tabashi labarin komi har fitsarin kwance da humairat keyi…yay shiru yace anty yanzu dai munsan cewa kausar ce takashe maman humairat amma wanan letter ba lallai bane yazama evidence ba…dole munemi concrete evidence dazamu sa akulleta behind bars,anty tace all in due time islam, amma yanzu wanda yakamata mutai maka itane humairat musan yanda zamuyi mu karbo humairat daga hanunsu kaga yanzu sai yanda kausar tai da dad….islam yace anty Abba ne kadai zai iya tsawatar musu dole mujira harsai yadawo meanwhile zan tsaya tsayin daka bazan kara bari su cutar da humairat ba saida kome dad zaimin yamin…zan dawo uwa kuma uba ga humairat zan cetota bazan taba bari wani abu yasametaba jini nace kuma marainiyace kaman ni hawaye ne yasauko daga idonshi yay maza ya share anty tace zamu kyato humairat daga shairin kausar islam karka damu Allah taimakemu….
Maman shakur