HEEDAYAH 10

Da asuba bayan an idar da sllh a masallaci da kusan minti sha biyar Shuraim ya mike ganin Abbansa xai fita masallacin don dama shi yake jira, sai
da suka fita masallacin ya isa gun Abban nasa, ya d’an risina yace “Barka da asuba Abba” Abba ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da
tafiya yace “Yauwa….” Shuraim na biye da shi yace “Abba dama ina son baka hakuri ne kan abubuwan dake faruwa….” Abba ya katse sa yace “A’a kaje
dai ka ba babarka hakuri, ita ta fi daukan abun da xafi, sannan kuma dama a bayanta kake as always” Ya girgixa kai yace “A’a Abba, ba wai ina
bayanta bane, just that muna tsoron abinda xai je ya dawo ne a kan lamarin….” Abba yyi murmushi yace “Ehh gaskiya ne Ali, barin ma da ya kasance
cewar duk abinda yaro ya hango ba lallai babba ya hango ba” Shuraim yace “A’a ba haka bne” Abba yace “No haka ne” Shiru Shuraim yyi yana dai biye
da Abban nasa, can yace “Toh Abba tana ina yarinyar ynxu?” Abba ya tsaya ya juya yana kallonsa yace “Do you have any problem with that?” Bai iya
yace komai ba, Abba ya watsa masa wani kallo ya ci gaba da tafiyarsa, Har suka shiga gida babu abinda Shuraim ya sake ce masa. Reaction din Abban
nasa bai hanasa bin sa har cikin parlonsa ba, Abba ya xauna saman kujera ya dau remote xai powering TV, Shuraim ya xauna kasa daga gefensa, a
hankali yace “Kayi hakuri Abba, ni ban ga aibun abinda kayi ba haka ma ban ga aibun abinda Mumy tayi ba, she’s right in many ways” kallonsa kawai
Mahaifin nasa yake, can ya girgixa kai yace “Baxa ka ta6a yin alkibla ba dama, look… Ur mother like it or not dole gidan nan Heedayah xata xauna
har sai naga she’s back to her parent, idan ku ka ga Heedayah bata dawo gidan nan ba to iyayenta ne Allah ya bayyanar, amma I mean it, bbu abinda
xae hana hakan, kuma tare xata dawo gidan nan da matar da xan aura ta kula da ita, ur mother can do whatever she want bbu wanda ya isa canxa
ra’ayina” Shuraim dake kallonsa da wani expression yace “Abba aure?? I’m sorry to say… you want to spoil ur home because of a mere little girl da
baka san ma me ya rabata da iyayenta ba, baka san daga inda ta fito ba, think about it plss Abba, this is wrong” Abba yyi wani murmushi yace “It’s
my home not urs, ko da wasa ai baxa ka gaya ma uwarka irin wannan maganar da kake gaya min ba yanxu, ni kuma ga abokin rainin ka, check out pls my
frnd” Mikewa Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Kayi hakuri” daga haka ya fice daga parlon, lkci daya ya hade rai bayan ya fita ya
nufi dakinsa, who the hell is this forsaken girl that’s trying to cause confusion in their home…. Muryar Mumy yaji tace “Ya aka yi Shuraim?
What’s wrong?” Tsayawa yyi ya juyo bbu walwala yace “Ina kwana Mumy” tace “Lafiya lau, ya naga ranka a bace haka?” Yyi kasa da kai yace “Nothing
mum, xan shirya ne yanxu” daga haka ya juya ya shige dakinsa, sarai tasan daga parlon Abbansa ya fito, ta d’an yi jim kamar me naxari sannan tayi
murmushi ta juya ta nufi dakinta a ranta tace Idan barrister ya san wata bai san wata ba ai…. Karfe sha biyu saura na safiyar ranan barrister ya
isa gidan Yayansa Dr Umar, yana shiga main parlor bangaren Mahaifiyarsu ya nufa, ya bude kofar parlon tare da sallama, a guje kaka ke kokarin boye
bowl din gabanta tana cewa “Naga fitina waye kuma wannan” d’an murmushi yyi ya karasa cikin parlon, tace “Au ashe Amadu ne, wllh na xata yaran nan
ne masu halayyar bera, to idan na ajiye d’an nama na da cin cin sai su bi dare su yashe….” Abba yace “Ina yini Baaba?” Kaka tace “Lfya lau Amadu,
ya aikin” yace “Alhmdllh, ke daya ce gidan kenan” Da sauri tace “To da fa?? Ai Kullum a haka suke bari na, kar fa kayi xaton basu gidan, duk suna
nan wllh, dama wannan yaro Aliyu ne me shigo min, shi ma kuma na koresa gaskiya, don raini ya shiga tsakanin mu” Abba yace “Daga gun aiki nake nace
bari in xo mu gaisa” Kaka tace “To ae ka kyauta, Allah yyi maka albarka, Wai ya maganar da kayi ranan na cewa xaka kara aure ne naji shiru” yace
“Ehh dama xan gaya maki maganan na nan in sha Allah…” Kaka na washe baki tace “Toh Alhmdllh, yar ina ce?” Yace “Nan kaduna” kaka tace “Abu me
sauki, to ni dai Allah ya sa ta kirki ce, don Maryam ta gasa mana Aya a hannu gaskiya, to ta amince xata rike yar makauniyar??” Abba yace “Ehh ba
matsala” kaka tace “Atoh ita da ke tsoron Allah kenan, Maryam ae shaidaniya ce sanye da kaya irin na mutane” Abba ya mike yace “Bari in je kaka sai
na shigo ko gobe” Kaka tace “Toh, ni dai haka nn nake sae bin yara nake ina rokon hamsin, dari, suna xagina suna ba ni” Abba ya juya yana kallonta
da sauri, ta tsuke fuska tace “A’a kai ba ubana bne da xaka min kallon tuhuma Amadu, idan gantalalliyar dubu ashirin din ka ce ta shekaranjiya to
ta kare tun jiya wllh” Bai ce komai ba ya nufi kofa ya bude yace “Sae anjima” Daga haka ya fita. Hajiya Rahinah ce xaune tare da Barrister kan
kujerun dake karkashin inuwar bishiyar tsakar gidanta, barrister ya ajiye wayar hannunsa yace “Sae kuma kika yi shiru” Sae a sannan ta kallesa tace
“Ehh shirun naga xai fi, barrister in dae har sbda wannan yarinyar kke son aurena, ina nufin indan sbda in riketa ne to kar ka damu ni me iya rike
little girl din ne har bayyanar iyayenta idan Allah ya yrda, ina hada ka da Allah ka rabani da xancen auren ka, bbu aure a tsarin rayuwata
ynxu….” Shiru yyi yana kallonta, sannan ya d’an yi murmushi yace “Sae dai fa kiyi hakuri Rahinah, you can’t stop me from marrying you, Heedayah
kuma gidana nake son ta xauna ba wani waje daban ba” Mami ta tabe baki sae dai bata ce komai ba, Budewar gate ya sa duk suka juya, Junaid ne ya
shigo compound din hannunsa rike da Makullin mota, har ya isa inda suke ya fara gaida Abba sannan ya gaida Maminsa, Abba yace “Kana aiki ne
Junaid?” Yace “Ehh ina aiki tare da Uncle dina a hospital dinsa” Abba yace “To that’s good ya fi ka xauna, Allah ya taimaka” Yace “Ameen” daga haka
ya wuce ciki, Abba ya kalli Mami yace “Ya kusa gama masters din nasa ne?” Mami tace “Ehh months suka rage masa idan Allah ya yrda” Abba yace “Allah
ya taimaka” Junaid na shiga parlor ya ga Heedayah ce kadai parlon kwance saman kujera tana bacci, ya dauke idonsa ya wuce sama xuwa bedroom dinsa.
Sae kusan la’asar Abba ya bar gidan har sannan kuma bai yi convincing Hajiya Rahinah ba dake kan bakanta na cewa bbu aure a gabanta. Yau dai har
sha daya saura na dare Hajiya Maryam na xaune parlor tana jiran ganin lkcn da barrister dake compound yana ta waya xai shigo, yau kwana biyu kenan
da ta lura da hakan duk da kasancewar ta mai bacci da wuri yau kam coffee me kauri ta sha tayi xamanta a parlor tana jiran ganin ikon Allah, lkci
lkci take tashi ta leka waje ta dawo, lekawar da tayi na karshe ne taga ya gama wayar xai shigo ciki, da sauri ta shige kitchen ta kulle don ma kar
ya san idonta biyu, sae da taji ya wuce part dinsa sannan ta fito ta dinga xaga parlor tana jiran ya kwanta sanin bashi da wuyar bacci, a haka
Shuraim ya sakko downstairs ya sameta, ganinta da mamaki yace “Mum baki kwanta ba” Tace “Ehh yanxu dai xan je in kwanta na gama kallon wani film
ne” Bai ce komai ba ta wuce sama shi kuma ya shiga kitchen, sae da taji Shuraim ya shiga dakinsa ta fito ta nufi part din mai gidan nata, a hankali