HAUSA NOVEL

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

????Na Jeeddah jao????????

1⃣⏯5⃣

Gudu yake kan wani farin doki mai kyaun gaske da ka ganshi kasan a rude yake ,wata mata ce a bayanshi ta ‘kank’ame shi sai zare ido take yi yayinda shi kuma sai ‘kara gudu yake ,da an hau tudu ko tsauni sai matar ta sa ‘kara ta rike ciki da hannu daya, da ‘kyar ya samu wani kogon dutse ya shige ga dukkan alamu Matar na’kuda take yi domin dauke take da juna , ‘karar dawakai da yaji sun tukaro inda kogon yake yasa ya toshe wa Matar baki da hannun shi ganin tana kuka duk jikinta yana b’ari ,mutanen suka gama dube -duben da zasuyi sai wani daga ciki yace “sun yi nisa sosai!! Mu koma kawai ,a lab’en da suke babu wanda ya motsa har mutanen suka tafi sannan ya cire hannun shi daga bakin Matar da tuni na’kuda ya zo mata gadan-gadan, Allah cikin ikonsa ya jiyo ‘karan ruwa daga d’ayan ‘bangaren kogon ya mayafin ta ya nufi hanyar da gudu ,kafin ya dawo ma har ta haifu Yar cikin Jini Kwance a ‘kasa itama uwar haka ,ruwan da ke jikin tsumman ya d’an matsa a fuskar ta ta dan farfado ,shi da kanshi ya gyara yarinyar ya mik’a mata. Murmushi take yi tana hamdala amma hawaye ne zafafa ke bin kuncin ta ,ta sumbaci yarinyar sannan ta rufe idonta hannunta ta sa ta damk’e hannun mutumin wanda da ka ganshi kaga sadauki, tana salati rai yai halinsa.

 

????wani ‘kara mutumin ya saka wanda duk kogon sai da ya d’auka, ya kifa kai a cikin matar yana ta rusa kuka mai ban tausayi ,idanuwan shi suka rine kamar garwashi ya mik’e tsaye ya d’aga jinjirar sama cikin murya mai firgitarwa yace” masarautar KALAHARI !!! Sai na mayar muku jin dad’i da walwala !! Na lashi takobi!! da ikon Allah sai  JASEENA ta zamo ciwon ido ga azzalumi JALALUD-DEEN!!!!

???? ????????????????????????????????????????????

Asalin labarin

Masarautar Kalahari babbar masarauta ce wanda ake sakota a matsayi na farko cikin jerin masarautu, mai kuma cike da tarihi, mayak’a da kuma kayan ma’adanai na ‘kasa kamar su lu’ulu’u , gwala-gwalai da sauransu. Sarki Hameed shine ke mulkin Wannan masarauta, mutum ne jarumi ,mai tausayin talakawa gashi da kwarjini. Hameed shine d’a na  biyu kuma na k’arshe gun mahaifin su ,ma’ana yana da wa mai suna JALALUD-DEEN ,wanda ya kasance baya son talakawa kuma shi duk abunda zai yi in dai don ya musguna ma talaka ne toh ya fi burgeshi, son zuciya gareshi , hakan ne yasa da aka tashi bada sarautar sai dattijawan gari suka zabi a bawa Yerima Hameed kasantuwar d’abiun sun daban ne kwata kwata JALALUD-DEEN bai chanchanta ya mulki Kalahari ba, a fuska JALALUD-DEEN ya nuna babu wani abu amma dai na ciki na ciki !!domin zuciyar sa tafarfasa takeyi kuma a nan ne ya k’udiri niyyar ganin bayan Hameed !!!

Jeeddah jao????

[3/3, 7:07 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔ 2016

???????? Jeeddah ja’o????????

6⃣⏭1⃣0⃣

Bayan an na’da Yerima Hameed a matsayin sarkin Kalahari sai Jalalud-deen ya fuskanci cewa matar sarki Hameed Sarauniya JASEENA tana dauke da juna biyu hakan ya tunzirashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko baccin kirki bayayi tsabar Kishi domin gani yake yi in har Hameed ya samu magaji to tabbas babu makawa ko ‘kamshin sarautar ma zai daina ji…………

????cikin Sarauniya Jaseena yana wata tara ,haihuwa ko yau ko gobe ,tana zaune cikin dakinta mai cike da kayan ado da k’yal-k’yali sarki Hameed ya shigo ,mutum ne mai tsayin gaske ga haske kyakkyawa ne wanda ba sai na tsaya misalta shi ba haka ma Jaseena kasantuwar a kasar masar ya auro ta , zama yayi kusa da ita yana zolayan ta suna ta hira ,basu ankara ba sukaji ‘kara a waje ,a tare suka mik’e cikin firgici Jaseena ta rike Hameed ta ‘boye ta bayan shi jiki na rawa yayin da shi kuma ya zare takobin shi ????ya rik’e yana dube-dube don yaga ko waye zai shigo Kwatsam sukaji an banke k’ofa kamar daga sama mutanen suka yo kansu nan suka kaure da fad’a ,gashi mutanen fuskar su a rufe da kyar ya iya fisge mayafin d’aya daga cikin su ,abun da ya gani ya matuk’ar girgiza shi !!! Amintaccen shi na fada ne Zakar da wasu wanda ya tabbata fadawan shi ne ,da yaga sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi kaway ya figo Jaseena suka fita yayinda mutanen suka bi bayansu ganin Jaseena ta gaza yasa ya kwantar ta bayan wani k’aton tukunya yace yana zuwa ,cikin sand’a yake tafiya har ya isa gurin da dawakai suke ,fito kawai yayi wani kyakkyawan ingarma ya nufoshi fari ne fes ,ya shafa kan Dokin sannan ya haura shima ya nufi inda ya bar Jaseena,ya sameta yanda ya barta cikin ciwon na’kuda ,take ya umarci dokin da ya kwanta ,hakan yayi ma Jaseena daidai yanda zata samu sauk’in daidaitawa a saman dokin ,kafin su ankara sukaji harbi kibiyar ta chaki Jaseena ta gefen ciki ganin sun kusa far musu yasa ya fita a d’ari da dokin suma suka hau dawakai suka bi bayan su har suka samu suka shiga Wannan kogon dutsen……..

????????????????????     JASEENA.        ????????????????????

Hameed ya d’auki gawar Jaseena ya fito bakin kogon ya tsaya , kasantuwar bai taho da komai ba daga shi sai takobin shi haka ya dinga tono da Wannan takobi har rana ta fito yayi gumi ba na wasa ba hannuwan sa duk sun salube sun ya’yyanke har saida ya gama tono ya sallace ce sannan ya binne ya d’au takobin ya koma cikin kogon ya zauna ya k’urawa jaririyar ido ,tsananin tausayin ta ya kama shi kasantuwar ta zo duniya ne lokacin da uwarta take gangaren barin duniya ,gashi shi bashi da abincin da zai ciyar da ita gata kuma abar tausayi kasancewar ta bak’uwa a duniya ,ya d’aga hannayen sa biyu yace ” ya Allah ga baiwar ka ta zo duniya lokacin da zalunci ya mamaye al’umma Kowa burinshi yaga shine a gaba ,Allah na rok’eka ka raya ta kan tafarki madaidaiciya kuma ka bata ikon kare hak’k’kin duk wani wanda aka zalunta a gaban idon ta ,ya Allah ka kareta da ikon kariyar ka!!!

????    Kukan Jaseena(sunan mahaifiyar ta ya maida mata) ne ya katse shi  ya je da sauri ya dauketa ya rasa ta inda zai fara domin kuka take na fitar hankali ,kamar ance d’aga kanka sama kawai ya hango wani haske ya hasko cikin kogon kuma ba daga asalin k’ofar da ya shiga ba ne, ya mik’e ya nufi gurin dokin shi ma ya bishi kasantuwar kogon makeken gaske ne …..,

Abunda idon shi ya gane mishi yasa ya zaro idanuwa ya d’aga hannu yana godiya ga Allah .,……..,????

Jeeddah jao????

[3/3, 11:10 AM] Jeeddah ja’o????: ⚔????JASEENA????⚔

????????Jeddah ja’o 1⃣1⃣⏭1⃣5⃣ Wata sabuwar duniya ce domin kogon nan zagaye yake da wani dutse wanda tsakiyar Wannan dutse ya kai girman rabin masarautar Kalahari gashi kuma jeji ne sosai mai yawan duhuwa ,kayan itatuwa kuwa babu kalar da babu ga ruwa yana gudana daga saman dutse tsuntsaye sai shawagi suke a gurin ,???????? , ‘kara da yaji ta wani 6angaren ya tabbatar masa akwai namun daji ciki kuma masu cike da had’ari????

????ya ja dokin sa har inda ruwan yake hannun shi d’aya kuma rik’e da Jaseena. Ruwa ne mai kyaun gaske ,yanda yake gudana ma abin kallo ne a nan ya dauraye jikin Jaseena dokin shi ma ya sha..nan ne fa Hameed ya fara sabuwar rayuwa daga shi sai dokin shi Zabil da kuma Jaseena wanda mahaifin ta ya maida ruwan kwakwa abincin ta, shi kuma yakan kama kifi ya busar don ya samu abin ci ,ko kuma y’ay’an itatuwa..haka suka yi ta rayuwa a jejin………..????

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button