LabaraiMatasa

Wassu Matasa Sun Hallaka Matar Dake Boye ‘Yan Bindiga A Kaduna

Rahotannin dake shigo daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu fusatattun matasa sun hallaka wata mata a garinMariri da ke karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna, Hajiya Bilkisu, bayan da aka gano cewa tana boye barayin da ake nema ruwa a jallo a gidanta.

Al’ummar yankin sun samu labarin haka ne bayan da sojojin ‘Operation Safe Haven’ suka cafke ‘yan bindigar a gidan Bilikisu, kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar.

Aruwan ya bayyana sunayen ‘yan fashin da Bilikisu ke ba mafaka kamar haka:

Musa Adamu, Abdullahi Usman, Suleiman Hasidu, Usman Jibril,Saidu Isah, Hassan Abdulhamid, Idris Sani.

Kwamishinan ya bayyana cewa an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri game da motsinsu. Hakazalika, kwamishinan ya bayyana jin dadin gwamnatin Kaduna na kame ‘yan ta’addan, tare da umartar su da ci gaba da yin cikakken bincike.

A bangare guda, ya gargadi mazauna da su daina dokar a hannu, su kasance masu hada kai da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button