HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Inna tace inajin ka , ALLAH yasa inada Abin bakun!

Hassana Najin su tanata karanta (wayansurika llahu nasran Aziza) acikin zuciyar ta Dan cinma nasara a Kan Inna ….

Alhj yace Auren Aishatu (Indo) nazo nemar ma safwan Dan soyayyar ki d ma’aiki ki amince d rokon mu sakamakon wata matsala ko lalurar hakan d ta taso Mana cikin gagawa badan mun Raina kima d darajar indon ba ,duk d nazo Miki d wani zancen da Zaki iya tunani kala2 akai ,rokona dake kiyi tunani maikyau akai …

“Tun da Alhj ya fara mgn y Fadi buk’atar sa ,gaban Inna ne yayi mumunar fad’uwa ,cikin kaduwa d mamaki tacema Alhj ..

Auren Indo Kuma ,ckin kankanin lokaci ?

Alhaji yace eh ,bukatar hakance ta taso d gagawa ,kinsan sun rabu d iyalin sa rabuwa Mara Dadi ga rashin lpy sa yanzu Yana bukatar iyali a kusa dashi ,uwa uba Mai kulamai d yara ,ganin Indo tafi cancanta d sanin duk wani muradan yaran yasa yaga Indo tafi cancanta d tazamo Mata agare shi Dan ita tafi sabawa d gidan d sanin komai n gidan d yaranshi da Kuma shima y zabeta d kansa batare d tirsasawar kowa ba …

Inna t numfasa duk ganin girma d kimar Alhaji t hanata kin Amincewa ,Amma Bata Amince din ba kuma tace sai sun tatauna d indon sanan wani hanzari b gudu ba sunsan Indo b kowa bace ?

Alhj yace Indo kowace tunda tanada ke datijuwar Arziki …

Inna tace hakane nice koman Indo ,Dan Ni CE komai nata tun ranar d mahaifiyar ta” ta haifeta har t koma ga ALLAH ..

Nan lnna taba Alhj lbr Rayuwar su d yadda Indo t taso marainiya ….

Yadda yadda mahaifin ta y bar gari har aka kawo Mata lbr rasuwar shi har ka yau d rashin gata su sai n wurin Allah sai wata Yar Inna d tuni t Jima d Rasuwa sai iyalan ta su Kuma Basu d zumunci ko neman Inna basayi Dan haka Inna ma Bata nemansu ,sai lbr kanin baban Indo d shima yaki kula d Indo tun Bayan barin babanta gari Dan haka Basu d kowa sai su biyu sai gidan d suka malaka ta hanyar Saida gonar ta tasiyi gidan d kudin gonar shine y zama malakain ta suke Rayuwar su sukadai acikin sai abokanen Arziki d suka zame musu tamkar Yan uwa Dan yanzu baban nawara shine y zamar ma Indo kamar uba Dan Suma halin kusan daya d naku suna Jammu a jikin su duk d matsayin mu ba daya ba ,Amman basa baya baya d mu …

Alhj y Kara sauraren lbr Indo duk d Ammy t taba sanar Mai y Kara samu wasu ababen tausayawa a tare dasu yanzu cikin lbr Inna ,y Kara son hada zuriya da su kwarai d Kara tausaya musu matuka …..

Har Alhj ze tafi yace ma Inna sai y ji daga gareta Dan Allah Kar Abun y wuce sati daya Dan tarfado d Rayuwar safwan d tausaya Mai ….

Inna t zazaro Ido tace ,sati daya fa kace Alhaji ?

Alhajin yace eh Dan ALLAH karkice komai ,zabin ALLAH d neman Alkhairi Abin muke bukata zansa Indo sosai akan Rayuwar jikarki zata Sami kulawa d tatali fiye d tunanin Mai tunani insha Allahu..

“Alhaji y gama d’aure Inna d jijiyoyin jikin t d tausasan kalamansa masu sarke zuciya …

Alhaji y ce zasu tafi zuwa jibi zai Zo yaji shawarar da suka yanke ,y umarci hassana d taso su tafi …

Bayan fitar Alhaji ,kafin hassana t ta bishi su tafi sai da ta tsaya t Kara rokon Inna sosai Tana Mata magiya Kan t Amincewa bukatar su …..

Inna dai ta ce Allah y kaimu jibin …

**********
Bayan komawar Alhaji asibiti,y sanar ma d safwan d Ammy duk yadda sukayi d Inna safwan bece komai ba Amman Yana sauraron su ,ganin yaki cewa ufan Ammy d Alhj sukaga kamar hankalin sa be kwanta d bayanan Inna bane ko gani yake kamar baza a bashi Auren Inna ba Dan haka y kasa furta komai ..

Kula d yanayin sa ganin Kar yasa damuwa aranshi ,yasa Ammy d Yaya d Alhj suka dinga kwantar Mai d hankali cikin dabara d dabaru irin na manyar datijai ….

Safwan jijiga musu Kai kawai yayi alamun gamsuwa d bayanan su …..

“Koda Indo suka dawo d aunty Mai d’inki daga kasuwa sakamakon gajiyar d suka kwaso ,Mai d’inkin tace taje gida t huta zuwa gobe sa fara Aiki …

Koda Indo t shigo Tana kalon inna t gano alamun damuwa atare da ita …

Bayan Inna t Bata Abinci taci tayi sallah …

Indo t tmby Inna lpy dai ?

Inna tace lpy Lau ,itadai Indo tasan akwai wata akasa kawai dai tabar zancen ne ..

Aiko Abu nata damun Inna ta rasa yadda zata farama Indo mgn d yadda zata d’auki abun …

Suna shirin kwanciya inna ta Kira Indo t janyota jikinta ,ta Fara Mata bayanin rashin lpy safwan Indo t zabura ,alamun mamaki d tausayawa ….

Inna ta sake dawo da ita jikin ta ,taci gaba d Mata magana daki daki cikin hikima ,har t Mata bayanin rabuwar safwan d NAWAL gami da rashin Arzikin da ta zazagama dangin safwan din kamar yadda hassana ta Gaya Mata d Alhaji ,daga baya ta rufe Mata k’ofa da rokon Alhaji akan Auren ta da safwan cikin gagawa d suka bukata …

Aiko Indo t zabura ta Fara zaro ido cikin kaduwa Tana tmby Inna Alhajin ne yazo d wanan lbr?

Aure ni da safwan? Mijin NAWAL fa baban su Noor ,Inna sunyi tunani akan matanar kuwa?

Cikin rikicewa tace lnna me kikace musu?

Inna tayi ajiyar zuciya tace na amince musu n karbi kokon barar su don taga yadda lndo zatayi …

Indo tace shikenan lnna kinsiyar Dani kin gama bayar Dani Babu wani Mai karboni a fad’in duniyar Nan ,Tana kuka Tana maimaita kalaman ta ….

Inna tace ki saurareni lndo …

Indo tace ,haba lnna kyauta t kikayi fa kamar kaza ko gyada yanzu d wane Ido Yan unguwa zasu kalemu ?

Na tabata safwan ba Sona yakeyi ba mezeyi Dani ,Sam bandace d Auren shi ba wacece Ni acikin mutane ,na tabata in *KUSKURE* Ya kaini gidan shi toko momyn su Noor seta Miki asarata Dan har gida zatazo ta ilata Ni ,lnna kinsan komai fa akanta kinsan yadda takemin d doramin lefin shiga tsakanin ta d mijin ta d ta doramin ji take Ina wuta ta jefani saboda kyama d tsana g kiyaya Mai zafi yanzu tsakani na d ita d na rasa gane wana kashe Mata ,yanzu Kuma mijinta y aureni tace n Aure Mata miji d Asiri ,wlh aa Inna !

Kai wanan ma wakane Mara dadin saurare , bazata taba yadda dhaka ba ko giyar wake Tasha kuwa lnaa Sam !

Inna dai takara Jan Indo jikinta ganin kuka Indo take d gaske Bata d alamun sasautawa .

Inna tace nifa ban amsa musu b nace sujira tukunna …

Indo t dago d Kai d gagawa ,tace yauwa lnna ta nasan bazaki iya siyar Dani ba bare kyauta ta Dan ALLAH karki Amince matuk’ar ba so kike ki rasa Ni ba nayi imani d momyn su Noor zata iya aikata komai akaina sanan bansan wane zama zanyi a gidan dadyn su Noor ba !

Sede idan zaman boyi boyi zanmai kamar da danayi zama dasu ,to yanzuma shi zankuma Mai hade d takunkumin aure ,lnmai girki ,na kulamai d yaranshi n kula d duk wani bako d zai Zo gidan Kinga shikenan bani d ‘yanci n tabata maragata gaba da baya ganin kima sai y gagareni lnna mukadai muka rage fa muke nishadantar da junan mu Inna kiyi tunani ance abinda babba y hango yaro baya hangowa lnna ki hango Mana Al’amarin Nan d kyau Dan Allah……

Kuka Mai tsanani yaci karfin Indo..

Inna ma Saida tayi kukan n tausayin Indo d son Tama Indo Abin d takeso akan wanan Al’amarin d y taso ….

Ranar sun kwana tunani d rarashin juna d bama juna shawara ,d Nemo mafita lndo dai tace bazata auri safwan ba Dan batasan sunan Auren d zasuyi ba ……

************
Safwan ganin Babu tartibiyar magana akan lndo gashi jikin shi yayi kyau har Ana cewa gobema za’a salame shi Amman next week zezo a sake Mai gwaji aga matakin d yake Kai ,…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button