NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 5

????ƘWAI cikin ƘAYA!!????

           
                  Bilyn Abdull ce????????


                BOOK ONE 
                    Shafi na biyar______________


………..A yanda Abdul-Aziz ke bautama al’umma da hidimarsa, sai ka ɗauka bai ma san ciwon dukiyarsa ba, kokuma a banza ya sameta ba da guminsa ya taraba. Abubuwa yake na bajinta ko tunanin kuɗin zasu iya ƙarewa bayayi, kafin kace kwabo sunansa ya zauna ɗam abakin mutane, ko yaro ƙarami ka ambatama sunan
Alhaji Abdul-aziz tafida da gudu zai amsa maka harma yay maka sharhi gwargwadon fahimtarsa. 
      
        Rayuwa ta ci gaba da shurawa, yayinda wasu da ga cikin jama’a suka fara kafa dandalin kiranye ga Alhaji Abdul-aziz zuwa ga siyasa. Duk da yana jinsu, kuma yana ganinsu, sai ya maida kansa makaho kuma kurma akan batun, dan shi sam siyasa bata cikin tsarin tafiyarsa ko burinsa.
       A na cikin wannan yanayinne ya fara ginin wasu katafaren gidajen gona guda biyu, amma a jihohi mabanbanta. Sai wani katafaren family house da zai haɗa dikkan ahalinsa waje guda, kuma kowa da ɓangarensa babu ruwanka da shiga sabgar gidan ɗan uwanka, Wannan aikinne ya kauda hankalinsa ga nacin jama’a na son ganinsa cikin siyasa.
        Lamarin kuɗi sai mai su, kafin kace wani abu gidajen gona sun kammala, hakama gidansu, matasa da yawa harma da magidanta sun samu aikinyi a ciki, abubuwan alkairi harsun fara fitowa ta gidan, sannan suma sun koma sabon gidansu shi da duk sauran ƴan uwansa da iyalansu, mama maryam ce kawai taƙi tunda dai aure takeyi, sai Alhaji Abdul-aziz ya sayi gida kusa da su suma suka koma.
      
      Duk yanda Alhaji Abdul-aziz ya so zamewa siyasa lamarin ya faskara, dan kuwa sosai ake masa bibiko da naci harta hannun aminan mahaifinsu da mama maryam kanta da mijinta.
       Rana ɗaya suka ware wajen ritsashi, dan gangami akai masa na musamman tare da manyan mutanen da zuciyarsa kejin kunyar bijiremawa. Ba da son ransa ba dole dole ya amsa da addu’ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.
   Kowa ya amsa da murna da farinciki, tare da masa addu’oin na musamman wajen bashi nasarar jagorancin al’umma cikin sauƙi.
       Ƙyawawan halayensa ne yasa shi kasancewa mai kishin jama’ar sa, har suma sukeji a ransu zasu iya sakar masa ragamar rayuwarsu ya mulka, babu ɓata lokaci rana tsaka ya afka siyasa bisa jagorancin abokai da matsawar mutanen gari da suke ganin ya cancanci zama jagoran nasu.
     Koda ya tuntuɓi ƴan uwansa sai suka bashi goyon baya, dan duk ya riga ya gama siye zukatansu, zuwa yanzu ƙauna ta haƙiƙa suke masa da bashi kulawa wajen jansa jikinsu, (kowa yasan ziciya da son mai ƙyautata mata), dama kuma suna cikin waɗanda aka kama ƙafa dasu harya amince da batun.
      Mama maryam ma sai ta bashi goyon baya sosai, tare da binsa da addu’ar alkairi, sai dai sam Bilkisu abin bai kwanta a ranta ba, amma babu yanda ta iya tabi ayarin ƴan binsa da addu’a tunda taga kowa ya bashi goyen baya, bai kamata ita ta zama ƴar ta wareba a cikinsu.

            Shekarar da Abdul’aziz ya shiga siyasa a shekarar Bilkisu ta sake samun ciki a bazata, ai farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu bashi da kwatankwaci sam. 
      Bilkisu tanata rainon cikinta hankali kwance, ga kulawa tana samu ga kowa, watanta tara cif da wasu kwanaki ta haife ɗanta namiji sargaɗeɗe, inda ranar suna yaci sunansa Jawaad.
            Jawaad ya tashi cikin kulawar dangi da mahaifa, gashi yaro abin san kowa a zuciya, dan danan ya fara wayo, gashi da jikin girma masha ALLAH, shekararsa ɗaya da rabi Bilkisu ta yayesa, dan yana tafiyarsa ko ina, ga haƙora reras a baki, sai dai kumafa baya magana, dan har Jawaad ya kai shekara biyu da wasu watanni baya magana, bayama yunkurin yinta, hakan yasa kowa yake ɗauka ko bebe ne, dan sun tabbatar yanaji da kunnensa, tunda idan akai masa magana yana fahimta, bakinsa ne dai baya furtawa. Tunma Bilkisu na damuwa harta daina ta maida komai hannun ALLAH, dan koda Alhaji Abdul-aziz yace zai kaisa asibiti itace ta hana, acewarta a jira aga zuwa wani lokaci dai.
     Domin farin cikinta ne kawai ya so barin zancen sai dai kuma da ga baya saiya kasa hakan, dan abin na damunsa, ga dai Jawaad da wayau harma na tsiya, amma yaro bai da maraba da dutse a fannin faɗin albarkacin baki. Kuma zama yay ya lallaɓa bilkisu akan kai Jawaad ɗin asibiti, da kyar ta yarda dai aka kaishi, sai gashi kuwa an gano yana da matsala ne a ƙasan harshensa da maƙoshinsa, nan akai masa aiki yay tsawon sati uku yana jiyya kafin ya warke su dawo gida. Ba’aja wani dogon lokaci ba Jawaad ya fara magana, zo kuga murna ga wannan ahali, kowa na sake miƙa godiyarsa ga ubangijin al’arshi buwayi gagara misali.
         Babu daɗewa da samun lafiyar Jawaad, a cikin matan Alhaji Yusif ɗaya ta rasu, Wannan rasuwa ya mugun girgiza wannan ahali sosai, musamman ƴaƴanta.
         Bayan wucewar komai na rasuwar jama’a suka takura ma Alhaji Abdull akan ya fito takarar shugabancin jihar, sam ki yayi, danshifa dama bai shiga siyasa dan yazama shugaba ba, ya shigane kawai dan ya zama jagora da zai tsaya kan masu mulkin su tallafi talakawa kawai, amma badan yay mulkiba.
     Nanma dai caa aka sake masa, babu yanda ya iya sai ya amince kawai yabi ayarin ƴan takara. 
     Abin zai baku mamaki idan nace muku komai yimasa akeyi, duk da talakawa sunsan yanada kuɗin da zai iyama kansa komai haka suka tattalafa da kansu sukai komai, acewarsu ai sune sukace yayi, dan haka sune zasuyi masa komai. 
      Wannan lamari ya sake girgiza duniyarsa, dan yarasa miyasa jama’a suke masa irin wannan makahon soyayyar?

 Ni ko nace Alhaji Abdul ai masu iya magana kance (Nagari na kowa, mugu sai maishi).

       Bayan kammala duk wani hatsaniya da ruguntsumi na kamfen akai zaɓe, tunma ba’ai nisa ba kowa ya fahimci Alhaji Abdul-aziza Yuseef ya bige abokin takararsa,  tunkan sakamako ya fito mutane har sun fara shagulgula, ana faɗa gari ya sake harmutsewa.
     Shi Alhaji Abdul-aziz ma ana faɗan yaci kuka ya kamayi, dan haka kawai yaji zuciyarsa ta karye ya shiga share ƙwalla. 
      Lokacin Jawaad na jikinsa yana wasansa, sai ya tsirama mahaifin nasa ido yana kallo duk da baisan mike faruwa ba, murmushi Alhaji Abdull yayi ganin kallon kurilla da Jawaad ke masa, ya ja kumatunsa kaɗan yana faɗin “Haba ɗan sanda kallon fa na minene? Yau nauyi ya haye Abbanka mai girman gaske, kai min addu’a ALLAH ya bani ikon saukewa”.
       Duk da Jawaad baisan ma’anar maganarba sai ya ƙyalkyale da dariya shima yana jan kumatun abbansa kamar yanda yay masa.
     Murmushi Bilkisu da ke gefensu tayi kawai, dan batasan dalilin da yasa mijinta keson kiran ɗan nasu ɗaya tilo police ba, tun baima kai hakaba yake kiransa da suna JAY -P!, tunma bata fahimci ma’anar sunanba har dai ta tambayesa ya gaya mata.
    Ko a lokacin batai masa jayayya ba sai fatan alkairi yazama ra’ayin Jawaad ɗin kenan idan ya girma shima.
    Tun a lokacin ya fara amsa wayoyin taya murna har ma kansa ya nema fara ciwo.

         Bayan abubuwan da suka biyo baya dai a ƙarshe aka rantsar dasu, Alhaji Abdul ya koma gidan gwamnati shi da iyalansa, sai dai su mama maryam basu bisuba, sunce zasu rayu anan gidan da ya saya musu.
      Harkar mulki ta fara gudana, inda Alhaji Abdul yazoma duniyar ƴan siyasa da sabon salo mai ban mamaki, gaba ɗayan albashinsa ya sakashi a taskar gwamnati, an ware aiki na musamman za’ayi ma talakawa aiki da kuɗin, sannan ya dage tsayin daka wajen gyara jiharsa ta kowanne fanni, dandanan sunansa yay amsa kuwwa a ƙasar, komansa ya zama abin koyi da alfahari ga al’ummar da yake jagoranta, ya zama zakaran gwajin dafi sannan tauraro mai haskawa da zamaninsa.
     Gashi sam bashi da girman kai, kowa nasane, babu ruwansa da wani banbancin jam’iyya ko yare, tsakaninsa da ALLAH yake aikinsa cikin ƙwarewa da jagorancin UBANGIJI.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button