NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 6

Bilyn Abdull ce????????

Shafi na shida.


……….A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗinkace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce, kowacce ka
zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta, saɓanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurɓatacciya.
       A yau dai ga ni a matsayin marainiya, wadda babu ɗumin duka mahaifa guda biyu, sannan babu bangon jingina daga tsatson zuminci ko guda ɗaya. Rayuwata ta cigaba da tafiya a hannun mutanen kirki ahalin fiddausi, sun zamemin uwa da uba bayan ƙasa ta rufe idanun nawa, yanzu sune ci na sune shana da dukkan buƙatun rayuwa da aljihunsu sai iya ɗauka.
     Zuciyata na kewar iyayena, amma jarumtata na ɓoye hakan a koda yaushe, haƙuri kuma ya zamemin sandar jagora yayin tafiya ba tare da na lalubi hanya ba saboda makantar zuci.
    Tabbas rayuwar gidanmu ta canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da iyayena na raye akanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna ƙyamata ko hantara ta ma kai tsaye, idanun maman firdausi ne kawai kan hana wasu cin zarafina koda da harara ne, amma da zaran babu ita a tsakar gidan to kare ma ya fini daraja.
        Matsala ta farko dana fara cin karo da ita a gidan mai ƙona zuciya da barin tabon da ba’a mantawa shine zuwan mai gidan Alhaji lado naira, koda iyayena suka rasu bana tunanin Alhaji lado yazo gidan gaisuwa sam, amma rana tsaka sai gashi danƙyas-danƙyas yazo koramin bayanin na kwashe kayana daga ɗakinmu zai zuba ƴan haya.
          Cikin ƙarfin hali da dogaro da kuɗin hayarmu na shekarar basuyi ko rabi ba na shiga kora masa bayani akan ai da sauran lokacin tashinmu.
      Alhaji Lado ya bankamin harara tare da watsamin yatsun hannunsa biyar cif alamar zagi (daƙuwa) “Kinci uwarki, kujimin lalatacciyar yarinya, yo ko yau kuka biya tunda wanda yay biyan ya tafi barzahu ai kuɗinku sunyi isfaya (expire) kuma, to dan shelen uwarki ma????, gidan tsohonki ko nawa da har zaki zauna jamin sharaɗi. Maza tashi kiyo waje da komai tafe nake da mai fenti, ki zauna wannan bacar har kuɗin su kare, dan itama zaki fara biyan kuɗin hayane tunda yanzu ƙofar ɗakin wasune”.
     Kasare nai ina kallonsa tamkar wata wawuya ko sokuwa, wasu da ga jama’ar gidan ko dariya suketa tuntsurawa, ƙalilanne basu ji daɗin lamarin ba, amma babu wanda yace ma Alhaji lado baiyi dai-dai ba, dan sunajin tsoron ya shuka musu shika-shikan rashin arziƙinsa suma, kaɗanma da ga aikinsa yace kaima ka tashi ka bashi ɗakinsa. Baka da yanda zakai dashi kuma dolenka ka tashi, inba hakaba ya saka yaransa subi tsakkiyar rana ko duhun dare su naɗa maka na jaki????????‍♀️…….
      Tsawar da ya dakamin ce ta sakani zabura na miƙe tsaye, ya nunamin ƙofar ɗakinmu yana haɗe fuska tamkar kashin ƙato na farar safiya.
    Jikina na ɓari na nufin ɗakin, dan fuskar Alhaji lado tafi baƙin kashin shanu barazana idan ya murkite ta, ina shiga itama firdausi na shigowa, itace ta taimaka min wajen haɗe kayan muka ƙuƙƙulle ina sharar ƙwalla, sauƙina ɗaya ma kayan bawani uban yawane da suba, marasa amfanin ciki kuma sunfi masu amfanin yawa.
      Bayan mun gama haɗesu ta taimaka min muka fiddosu zuwa cikin bacar da muke kwana, wadda kayan suka mamaye kusan rabinta, dan dama bawani girman azo agani bane da ita.
     Alhaji Lado bai kuma bi takaina ba sai ma yaransa da suka shiga suka fara fente ɗakin da fenti mai ƙyau da ya bama kowa mamaki, dan duk ɗakunan gidan da farar ƙasa aka shafesu  maimakon fenti

            Da daddare munacin abinci a ɗakin su Firdausi innarsu ke bani haƙurin abinda ya faru da rana, dan ɗazun bata da sukunin nuna tausayina suma ta shafesu, shiyyasa sukai gum da ga ita har baba.
     Murmushi nai mai ciwo ina faɗin, “Babu komai inna, ALLAHN da ya bashi muma bai manta da muba ai”.
    “Hakane Bilkisu” inna ta faɗa tana murmushi, ta dafa kafaɗa ta tana ƙara nuna min muhimmancin haƙuri da amfaninsa.
    Naji daɗin bayaninta, dan naƙara samun ƙwarin gwiwar ɗaura ɗammarar zama 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button