KWAI CIKIN KAYA 5

Adadin shekaru na hawan farko suka cika ga duk waɗanda suke kan mulki, mai makon Alhaji Abdul-aziz ya koma sai jama’a suka nuna shugabancin ƙasar gaba ɗaya suke bukatar ya karɓa. Wannan lamari yaso gigitashi sosai. A fili ya nuna sam bazata yuwuba, amma ina jama’a sun tsaya kai da fata suna masa magiya da kai kukansu wajen ALLAH.
To duk abinda ALLAH ya hukunta sai ya kasance koda bawan da abin ya shafa bayaso, kana nakane ALLAH yana nashi, nashiko shine gaskiya.
ALLAH ya ƙaddara sai ya zama shugaban ƙasa, sai ga shi kuwa ya zama, dama wanda yake kai ya gamane gaba ɗaya.
Zuwa yanzu Jawaad ya girma, dan shekarunsa bakwai a duniya, yaro mai wayo da ƙyawawan ɗabi’u, kamar yanda ƴaƴan talakawa ke makarantar gwamnati sai ga Jawaad ma a ciki, dan mahaifinsa yace ita shima yayi, a ma ƙauye, to ɗansa ma can zaiyi babu tantama. Aiko hakance ta kasance, dan sai ga ɗan shugaban ƙasa a makarantar gwamnati, abin ya burge jama’a, tare da jan hankali ga sauran masu mulkin suma duk sukaita maida ƴaƴansu can.
A gefe kuwa Alhaji Abdul nata sake cusama Jawaad son aikin ɗan sanda, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi yayi tasiri a ran yaron, dan babu sunan da yake ƙauna a ransa kamar JAY-P! da Abbansa ke kiransa dashi, ma’ana (Jawaad Abdul-aziz Yuseef police).
Ko kayan wasan Jawaad duk zaka samu suna kamanceceniya ne da kayan jami’an tsaro, abin ya riga ya shiga yaron jini da ɓargo.
Shekarar Alhaji Abdul-aziz ɗaya akan mulki ALLAH ya jarabcesa da ciwon da har ya kwanta, ashe hawan jinine bawan ALLAH, kwanansa uku kacal da wannan ciwo zuciyarsa ta buga yabar duniya????.
Tashin hankali kenan wanda ba’a saka maka rana, wannan lamari harma bansan a yanda zan musaltashi masu karatu su fahimta ba, dan kuwa ƙasarce baki ɗaya ta harmutse tare da komai na cikinta, mutuwar Shugaban ƙasa Abdull-aziz ba batun iyalinsa kawai akeba, maganar al’umma kawai akeyi, waɗanda sukeji basu taɓa gamo da rashi mai taɓa zukata da aiyuka irin wannan ba.
Tunda wannan rasuwa ta gudana bilkisu ta rasa hankalinta, sam an kasa gane kanta, hauka take tuburan wanda ya kai ga har an rufeta a ɗaki ma.
Mama maryam tsohuwa mai tawakkali da hakuri, baka ganin hawaye saman fuskarta sai dai na zuci kawai.
Ƴan uwansa kam su kansu ka kalla abin tausayine, lamarin yay masifar ruɗasu, dan Abdul mai biyayyane a garesu tare da ƙyautata musu, suka tuna irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa da bajintar da yay musu a rayuwa sai suji hankalinsu ya kuma ƙololuwa a tashi, sunyi kuka harsun godema UBANGIJI.
ALLAH sarki Jawaad, duk da bai kai hankalin da za’ace ya fahimci komaiba ya ɗanyi kukansa ganin kowama yanayi, musamman ma halin da mahaifiyarsa take ciki na hauka, sai dai zuwa wani lokaci kuma sai ya saki ransa, yakan dai zo ya tambayi mama maryam ina Abbansa? Yaushe ne zai dawo?.
Sam bata ɓoye masa, takan ce masa Abbansa ya tafi inda ba’a dawowa.
Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin kuma yay zugum yana tunani kafin kuma ya saki ransa ya koma wasa cikin yara sa’oin sa.
A haka aka share wasu watanni, riƙon Jawaad ya dawo hannunsu mama maryam, bilkisu kuma ana cigaba da nema mata magani, dan bata ma ƙasar an kaita asibiti.
Haka rayuwar ta cigaba da shurawa, an maido Bilkisu gida, kamar taji sauƙi sai kuma abu ya dawo sabo, lokacin har Jawaad ya fara wayo, yana shekara ta goma sha huɗu, ajin secondary js2, ranar wata juma’a sai aka wayi gari Bilkisu ta bar gida, nema iya nema anshasa amma babu ita babu dalilinta, lamarin ya girgiza mama maryam har itama ya zama sanadi a gareta.
ALLAH yayma mama Maryam rasuwa sakamakon ɓatan bilkisun itama, wannan karon kam Jawaad yaji zafi sosai na rasuwar kakarsa da ɓatan mamansa, yayi kuka har abin ba’a cewa komai.
Ƙanwar bilkisu taso riƙon Jawaad ya dawo hannunta amma dangin mahaifinsa suma suka ƙi, sai Abba Naseer babban yayansu Alhaji Abdull na farko a gaba ɗaya gidan ya amshe shi ya koma hannunsa da zama.
★★★★★★★
Gata sosai Jawaad yake samu a wajen ahalinsa, dan a ganinsu lokacin da zasu nuna jin daɗin ƙyautata musu da mahaifinsa yayi kenan, ɗan gatane ta kowanne fanni, riƙonsa ake tamkar yana gaban iyayensa, ƙilama idan sune bazasu masa wani gatanba irin haka.
Kamar yanda marigayi Alhaji Abdul ya ajiye burinsa akan Jawaad na zama ɗan sanda sai ALLAH ya amince masa yasamu cikar burinsa ta hanyar cusa son aikin ƴan sanda a zuciyar Jawaad, sosai ya ke son aikin ɗan sanda, wannan shine burinsa, mafarkinsa, kuma fatansa. Lokaci ƙanƙani ya samu cikar burinsa kodan tsatson da ya fito, da dattako irin na mahaifinsa da baza’a taɓa mantawa ba.
__________
Shekaru sun shuɗa, komai ya sauya, Jawaad ya zama abinda yay fata, ya girma ya zama babban mutum kamilallen saurayi mai aji da tarin cikar kamala da kwarjini na haƙiƙa, komansa na nagartattun mutane ababen koyi da dubi, gaba ɗaya halayen mahaifinsa sun dawo jikinsa, sam bashi da damuwa sai ta aikinsa tare da ƙyautatama jama’a.
Mutum ne da bai damu da abinda bai shafesa ba ko ba’a sakashiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi, idan har bakai ne ka sakashi a lamuranka ba bazai taɓa shiga ba, bashi da son hayaniya, bai da girman kai, bai da wulaƙanci, sanan sam ba miskili bane ba. Abu ɗayane yake yawo a jinin Jawaad da ke saka jama’a dangantashi da waɗancan ɗabi’un na sama, shine rashin sabo, sam baisan sabo ba, kana takashi zai shata maka dogon layi, tsautsayi ko rawar kai ya saka ka ƙetara to lallai kun ƙulla kenan, kuma ka ɗaura kanka a danja mai haɗarin gaske. Babu ruwansa da kai wanene? Ko kuma ina ka fito? Miye matsayinka a garesa duk ba’abin kallonsa bane.
Jarumi ne ta fannin aiki da rayuwa, sannan gagararrene a duniyar tsagerun mutane, idan ya ɓalle sam bai san bari ba, duk abinda ya saka a gabansa sai ya cimma manufarsa yake yankan filin hutu.
Waɗannan ɗabi’un nasane suka jawo masa abokan tsama ta fannoni daban-daban, a cikin hukumarsu da wajenta, harma da tsagerun gari.
★★★★
Shahuda ɗiya ce ga yayar marigayi Alhaji Abdull, wato Hajiya Humaira, tuni suna ƙasar Holland ita da mijinta, yaransu biyar suma, mata uku maza biyu, asalin sunan Shahuda Sabeerah, dan sunan mahaifiyar Abbansu aka saka mata, amma sai suke mata alkunya da suna Shahuda, ita ce ƴa ta huɗu a gidansu, ƴan gatane na haƙiƙa, waɗanda suka tashi da ɗabi’un turawa a cikin jininsu, sam basu san bari ba, dan bama a faɗa musu.
Hajiya Humaira tana son Jawaad, shiyyasa lokuta da dama take matsa masa zuwa ƙasar Holland wajensu ya ɗan huta. To annan fa Shahuda ta ga Jawaad ta mutu a kansa, tun yana basarwa dai har shima ya zurma, dan Shahuda ƙyaƙyƙyawace ta haƙiƙa, saboda mahaifinsu bafilatanine ɗan asali mai asalin madarar ƙyawu, duk cikin yaran kuma Shahuda tafi biyosa, ga jin daɗi da suke ciki, saboda inda suka taso, wannan ya haɗu ya maida Shahudah son kowa ƙin wanda ya rasa.
Jawaad yana son Shahudah, sai dai halayenta na bashi tsoro, dan kuwa dai irin yarannane da babu kwaɓa babu harara, idonsu ya buɗe da ƙazamar wayewa mai wahalar canja ra’ayi cikin sauƙi. Dan haka sai bai wani cika sake mata fuska ba, dama can yaran Family ɗin shakkarsa suke, dan bayan gaisuwa baya basu wata fuskar shiga huruminsa, sai dai fa yana ƙyautata musu akan bukatunsu, idan abu suke buƙata kafin su tambayi sauran yayyensu sun nema da ga wajensa, kuma inhar yana da halin yimusu yakan musu gwargwado.
Aikin da ya kai mahaifin su Shahudah ƙasar Holland ya ƙare, dan haka ya tattarosu suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, tunda suka dawo Shahuda ta dawo nan Tafida Family house ɗin su Jawaad ta tare duk dan shi. Ba zamuce baya kulata ba, sake mata ne kawai bayayi, wannan kuma badan hulaƙanci yake mata haka ba, rashin sakin jiki da jama’a halinsa ne kowa ya san haka, ita kanta sanin hakanne ya sata bata damun kanta da lamarin nasa, burinta kawai ta mallakesa matsayin miji, dan badan Jawaad ba bazata taɓa dawowa zaman ƙasarba sam, duk abinda ya shafi afirika ɓata mata rai yakeyi, a haukarta bayan aurenta da Jawaad saita ja ra’ayinsa sunbar yankin afirika gaba ɗayanta sun koma turai da zama. (????????Babbar magana shahudah).