NOVELSUncategorized

KWAI CIKIN KAYA 5

           ★★★★★★★★

    Hankalin Hajiya Humairah ya tashi ganin tunda suka dawo ƙasar Jawaad yaƙi yay maganar aurensa da Shahudah kusan shekara uku, hasalima yafi maida hankalinsa ga aikinsa fiye da komai, ga Shahudah kullum cikin damunsu take akan batun Jawaad.
      Shiryawa hajiya humaira tayi ta nufi Tafida family house domin tattaunawa da ƴan uwanta akan batun auren, dama gashi lokacin meeting ɗinsu na family ya kusa. Koda takai kukanta akan zancen sai kowa ya bada goyon baya, aka kuma tuntuɓi Jawaad akan maganar.
        Haushi abun ya bama Jawaad matuƙa, dan sam bai shirin wannan auren nan kusa ba, so yay sai ya maida Shahudah cikin hankalinta da aƙidar yankinta da addininta, amma sam an wani zo an masa titsiye. Cikin ƙuluwar haushi akan zancen yace suyi duk yanda ya dace kawai.
          Wasunsu sun fahimci bai soba, amma sai suka watsar da fushin nasa aka hau shirin biki na ƴaƴan gata, dan dama babban burinsu suga yayi aure kamar sauran yaran gidan kodan su gujema zaginsu da jama’a keyi akan sunƙi sakashi yay aure.
           Sam ƙin bama bikin muhimmanci Jawaad yayi, hasalima hankalinsa na kan aikinsa, komai sai iyayensa keyi, sai da Shahudah ta sakashi gaba da kuka sannan ne yaɗan maido hankalinsa shima ba duka ba.
     Haka dai dangi sukaita lallaɓata akan ta manta da lamarinsa tunda kowa yasan halinsa ayi auren kawai, idan ta shiga zai bata kulawa insha ALLAH.
      Son da take masane ya sata yarda da shawarwarinsu akai biki lafiya aka tashi, sai dai a hidimar bikinma ta mugun shaƙar baƙin ciki, dan ƙin zuwa yay taro ko guda ɗaya har dinner ɗin da suka shirya bayan ɗaurin aure ta garari ta nunawa a gidajen tv saboda tsabar haɗuwarta, sam baijeba, a ranarma tsabar iskancin Jawaad a wajen aiki ya kwana, a washe gari kuma yaƙi yarda ya hadu da kowa a gidan saboda tsiyar da ya tsula musu.
        Shahuda kuma tace bazata tareba sai yazo ya bata haƙuri.
     Nanma sharewa yay kamar baisan sunayiba, sai da Hajiya Ummah ƙanwar mama bilkisu mahaifiyarsa ta kirasa tai masa faɗa sannan yaje, mai makon ya bata haƙurin sai ma ya sake gaggasa mata magana, ya kuma ce inma bata tareba baida matsala da hakan.
       Da yake su kaɗaine a ɗakin sai Shahudah ta ci kukanta ta share hawaye da burin sai ta rama amma a gidansa, ga sauran ƴan uwa kuwa sai ta nuna musu ai ya lallasheta ne itako tanata masa shagwaɓa (????????).
       Kowa ya yarda da batubta, dan an tabbatar Jawaad nason Shahudah, halinsa na nuna ko in kula da abu ne yake sakashi ɓoyewa, amma yanda ma yake ɗan kulata fiye da sauran yaran gidan zai tabbatar maka da yana sonta.
       Daga ƙarshe dai sai amarya ta tare a nan gidan sashin Alhaji Abdull mahaifin Jawaad, dama tun bayan tashinsu babu wanda ya shiga sashen, yanzu kam sai Jawaad yay masa gyara mai burgewa aka saka masa amaryarsa anan. 
      A farkon amarci abin nasu ɗoɗa-ɗoɗa, amma son jiki da shegen ɗaukar dala babu gammo na ɗabi’un Shahudah ne ya zamarma auren nasu matsalolin da baibayi da sukai ma zaman nasu ƙullin goro. Tunda gashi har Jawaad na complain a kan auren watanni bakwai kacal????????‍♀……….✍????


Mun dawo labari☺


https://www.youtube.com/channel/UCWiytn-_Bo_l8P5pZrYub8A/


ALLAH ka gafarta na iyayenmu????????????

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button