NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR ALHAYAT 81-90

 Umma na lura da khadijah dake jujjuya abincin gabanta, ko bata gaya mata ba taga alamar tana da damuwa sosai, Umma tace “Khadijah” da sauri ta dago ganin 

yanda Umma ke dubanta ta debi shinkafar gabanta ta kai baki, tana son tambayar Umma ko magana tayi mata amma tayi shiru tana cin abincin, Umma tace “Tell me 

ur problem, what are you thinking of?” Khadijah ta wara manyan idanuwanta tace “Ba komai Umma am just tired ne” Umma tace “Toh ki gama cin abincin sai kiyi 

isha ki kwanta” A hankali khadijah tace “Toh” da kyar ta dinga tura abincin don gaba daya bata da appetite, why is she finding it hard to erase jawahir’s 

hurtful words from her mind, mikewa tayi daga karshe ta wuce kitchen da plate din shinkafar, tana wankewa a sink Sudais ya fado mata, tasan baxai ji dadi ba 

ta taho bata gaya masa ba, tayi deciding ta tura masa test kawai ta gaya masa, tana dawowa parlor ta dau wayarta ta xauna gefen Umma ta shiga rubuta masa 

text din cewar ta dawo yanxu, ta   kuma basa hakuri da bata gaya masa ba while coming back, Unfortunately Wayar na bedroom din Sudais, shi kuma ya shiga 

bathroom, dai dai shigowar jiddah dakin text din ya shigo, Atm dinsa dama tayi niyyar shigowa ta dauka without his consent, ganin wayarsa dake gaban mirror 

yyi haske ta nufi wayar da sauri, dauka tayi ganin message ta sa finger ta jawo yanda xata iya karanta content din, she was very cautious kar tayi erasing 

message din daga gaban screen din wayar, sake baki tayi tana kallon text din, ta nanata Ummu Shureim a xuciyarta ya fi a kirga, tayi wani murmushi, wato 

Amira ya mayar Ummu Shureim don kar ta gane, da sauri ta ajiye wayar jin alamar xai fito ta kashe wutan ta shiga dube dube a drawern mirror with a very 

serious face, sudais ya fito daure da towel yana kallonta, he was very surprise seeing her… da yake tun da ya kawo mata kayan fadar kishiya ta daina 

kulasa a gidan, ta kallesa fuska daure tace “Why are you staring at me that way?” Bai damu da abinda tace ba yace “Me kike nema?” A takaice tace “Razor 

blade, naga wani shekaranjiya a nan ina gyara, I want to sharpen my daughter’s pencil tayi assignment” tabe baki yayi yace “Duk Miscellaneous school 

materials dinta babu sharpener sai kin shigo nan neman razor?” wani kallo tayi masa tace “Ae dai you are not blind kana ganin komai ta kai makaranta xubarwa 

take ta dawo min haka kamar wata wawiya, or am I to become a razor to sharpen her pencil???” Bata sake saurarensa ba ta fice daga dakin, ya girgixa kai ya 

nufi gaban mirror, wayarsa ya kunna, ganin text din khadijah gaban wayar ya xaro ido sosai, can ya kalli kofa da sauri, shi dai bai ga alamar da ya nuna ta 

taba wayar ba, beside da ta dauka ai bude message din xata yi kuma baxai gansa gaban wayar ba, hakan yasa ya tabbatar bata dau wayar ba, Jiddah na komawa 

daki ta xauna gefen gado tana tunane tunane, to ita yanxu shawarar wa xata nema, anya jiran da tace xata yi har sai an daure auren bai yi nisa ba, kai 

gaskiya yayi nisa sosai, kawarta Amina ta shiga kira tana dauka tace “Amina don Allah gobe ki taho da sassafe, Ina cikin babban matsala” Aminar tace “Toh in 

sha Allah xan taho kuwa” Ajiye wayar tayi ta mike tana xaga dakinta, kai ina ma Allah xai bata sa’a taga Amiran nan ta fara nakada mata duka kafin ta bude 

mata sirrinta da ta sani, fita tayi dakin ta nufi dakinsa ta bude a hankali don taga mai yake, babu kowa dakin kuma ya dauke wayarsa, ta sauka downstairs da 

gudu, ganin an kunna wutan kitchen ta gane yana can, waya taji yana yi a kitchen din, ta labe jikin bango dai dai nan taji yana cewa “Alryt dear, my regards 

to him, gobe da safe xan taho…” Da sauri jiddah ta tafi stairs jin xai fito, yana fitowa ta maxa ta juyo kamar tahowanta kenan, Bai kalleta ba kamar yanda 

bata kallesa ba ya isa kan kujera ya xauna rike da cup din tea. Khadijah na kwance da Umma misalin sha daya na dare Umma tace “Ya Khaleel da matarsa?” 

Khadijah tace “Suna can lafiya” Umma tace “Ya sani xaki taho?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh ya sani, Umma Aliyu ne yyi accompany din mu” Umma ta daga kai 

tana kallonta kafin tace “Yana kasar ne?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh can yake xama” Umma bata ce komai ba ta koma ta kwanta, khadijah ta dinga nuna ma 

Umma kayayyakin da Sudais ya sa mata a lefe ta waya, don komai ya siya sai ya tura mata ko tana so, Umma tace “Maa Sha Allah, Allah sanya Alkhairi” khadijah 

tace “Ameen” a hankali tace “But Umma how will I cope with studies and marriage, ko ki ce masa kawai ya bar ni a can kasar in gama kawai idan anyi auren” 

Umma tace “Kwana nawa ne hutun naku?” Khadijah tace “Ba yawa fa, wata daya ne da few weeks” Umma tace “Bikin kuma nan da sati nawa yace maki?” A hankali 

tace “Biyu” Umma tace “Kema kin san baxai hana ki karatu ba, Kar ma ki ce masa komai, but surely xai bari ki gama” khadijah tace “Toh Umma” Umma tace “Allah 

ya kai mu lokacin lafiya” a hankali khadijah tace “Ameen, Amma Umma sai gabana yayi ta faduwa” Umma tace “Sai ki yawaita addu’a, babu abinda mutum ya isa ya 

maki wanda Allah bai maki ba” Washegari da safe tun da Jiddah ta tashi take tunanin yanda xa ayi ta san inda Sudais xai je ganin har ya gama shiryawa cikin 

suit yana xaune dining yana shan shayi ta sa hijab ta fita kamar xata xubda shara, ko amsa gaisuwar mai gadi bata yi ba sanin duk bakinsu daya da sudais 

komai ya faru gidan sai Sudais ya tambayesa, kamar kawayenta nawa suka xo a rana kuma duk da jan kunne da take masa sai ya fada masa, duk ta fita gidan to 

sai Sudais ya sani, har bakin titi ta taka suka gaisa da mai filling din gas dake bakin titi da d’an shagon container sa, yace “Maman Amira kaddai ki ce har 

gas ya kare in je in dauka, naga ko sati biyu ba ayi ba na cika” Tace “A Haba kamar muna shan gas a gidan, ba shi ya kawo ni ba malam rabilu, wani taimako 

nake so ka min don Allah, Kuma wlh ni me biyan ka ko nawa ne, amma kuma sirri ne tsakanina da kai” tana magana ne tana kallon cikin layi ko xata hango motar 

Sudais, Rabilu yace “Tohhh… Sirri kuma maman Amira” tace “Kaga ba wani abu bane, yanxun nan Abban Amira xai fito a motarsa, to don Allah so nake ka tada 

Machine dinka ka bi bayansa ka gano min inda xa shi, wllh ko nawa ka bukata xan biya ka Rabilu, kar ka ji komai ba wani sanin ka yayi ba” Dariya sosai 

mutumin yayi yace “Kai yanxu shi Barristern xan bi a machine maman Amira?” Ta hade rai tace “Kai dai biyan ka xan yi babu ruwan ka, Kuma ku din ne sai da 

haka, ban yarda da takun sa bane kwanan nan, yanxu dai don Allah ka rufe container din nan ka hau kan babur din ka ka jira sa anytime soon xai fito na sani, 

xuwa anjima xan dawo in ji yaya, da kudin ka kuma xan taho in sha Allah” daga haka ta koma cikin layin, ta kusa gida sai ga motar sudais kuwa, Dauke kayi 

tayi, ya tsayar da motar yana kallonta yace  “Jiddah?” Ta juya fuska daure tana kallonsa, yace “Da ixinin wa kika fita, Kuma ina kika je?” Tana nuna masa 

gidan dake kusa da nasu tace “Matar gidan can ta kira ni yaronta ya kone da mai, Toh sai kar in je? Ko baka ga a gigice na fita ba?” Rufe glass dinsa yayi 

ya ja motarsa ya wuce, ta tabe baki ta shige cikin gida, office Sudais ya nufa direct don client na jiran sa. Khadijah dake kitchen tana duba miyar kubewar 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button