NOVELSUncategorized

KWARATA RETURN 7

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



               *KWARATA RETURN…*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_


Rubutawa…
            *JAMILA MUSA…*



       *SAI NA AURI D ‘ K*



???? —— 7



        Ƙasa² nake magana ina cin gurguru cewa. Ƙaryar rashin kunya. Ai sai an bar zomo yake zama guza. Kowa ai ɗan iskan kanshi ne , ni har an nunamin hanyar hukunci , a dai² lokacin daya sake kalloni da dogon kallo , murmushi nayi kaɗan tare da ibar gurgurun kamar zan bashi bayan kuma muna da tazara. Ya² ne ? Zakaci ? Na faɗa ina murmushin nasara. Girgizamin kai yayi alamar a , a , ya bani amsa. Ban sake magana ba na ci a bakina ina cewa saina….. Na nuna da hannun hagguta yankawa alamar zan yanka mishi wuya kenan. Idan bai daina kallona ba kalli can nace ma na ƙara nuna mishi tv…

     Gyara bakinshi yayi ya kalli talabijin. Ni kuma naci gaba da cewa wato da ka kwanta kayi bacci , misalin 12 saura ka tashi. Daga saman gado zaka wuce bayi ka watsa ruwa , zaka fito ɗaure da rigar wanka. Kana fitowa sai ka tsaya jikin madubi , zaka goge jiki da towel , da hannuwa na na nuna yadda ake shafa mai ina shafawa a fuskata , daga fuska naci gaba da nuna duk inda ake shafa mai a jiki. Bayan ka gama saika fara goge fuska , ummm na nuna yadda yake sharce gemu da kuma yadda yake shafa turare dariya nayi sosai tare da komawa da baya na kwanta cikin kujera , bayan ka saka kaya sai ka wani fece abunka. Cikin dariya naci gaba da cewa tou yau Jarumarka ta ɗaure kafafuwan yawo , no cin cingom & no cht na nuna yadda yake riƙe waya da wayata , da hannun dama na sake nuna babu. Ina cewa kaji….??? Na riƙe kunne na dan ya tabbatar min yaji.

     Baiyi magana ba kuma bai kalleni ba yaci gaba da kallon tv kamar yadda na sashi. Banda tuƙuƙi babu abinda zuciyarshi ke mishi , yana ta ƙoƙarin riƙewa da kuma dannewa ya gagara , cikin wata irin murya yace ke kunceni nace miki. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da hannu na nuna karka dameni da baki kuma nace ka fita idona in ba haka ba mizanete kana daga kwancen nan. Kai…………. Nine zaki dakar ? Tou saina kunce kuma saina kashe ki , da sauri na tashi ganin yana fiffizgewa da ƙarfi , saina kashe ki…….. Da gudu na fita a bakin ƙofar fita daga ɗakinshi na zame , shi kuma ihunshi ya ƙara yawa , ninen ma zaki daka ? Yau idan basai na ma kasheki ba tabbas saina kashe kaina…… Da sauri na tashi nayi ɗakina ina kuka ashe har yanzu Dikko bai warke ba. Rufe ƙofa nayi har nayi fitsari saboda tsoro. Har yanzu ina jiyo ihunshi yana faɗin saina kashe ki………..² ƙyarma jikina ya farayi kodai in fita in gudu ? Nine zaki daka ma………. ? To zo ki dakenin , kai………….. Saina kashe ki…………. Kowa da kowa ma saina kashe shi……. Ah² ba lafiya ? Na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. Babu wani ruwana da ciki har babyn shima sai na kashe shi…………….. Kai……… Wai nine ma mace zata zane , a sauƙaƙar murya yace aiko dana zama lusarin namiji. Daga haka ya ɗauke. Tunda ai kunga yana kwance ne , dan dama idan ciwon ya taso mishi kwantar dashi ƙasa akeyi , idan dai aka kaishi ƙasa anci galabarshi. Sai a bashi magani dan idan ya tashi dawowa ya dawo da tunani.

     A firgice na juya inda na yada wayata tana ƙara , ummm na faɗa tare da goge zufar dake bin fuskata. Rairafawa nayi inda take na ɗauka , Ashiru ne yake kirani , ɗauka nayi cikin kuka nace Dikko ne baida lafiya , ke kina ina ne ? Na kulle a ɗakina. Waye ya ɗaureshi ne ? Cikin kuka nace ai kaine ka siyo igiyar , Ashiru yace ba wanda ya siyo igiyar ba wanda ya ɗaure shi nake magana , nice na ɗaureshi , meya haɗaku ? Shiru nayi banda abin cewa , Ashiru yace kizo ɗakinshi. Cikin kuka nace ni gaskiya bazan zo ba , ranki ya daɗe kizo mu duk muna ɗakin , tou na faɗa tare da ajiye waya. Toilet na shiga na wanke jikina sannan na fito na gyara inda na ɓata da fitsari , kaya na canza bayan na gama na kira Ashiru yana nan ? Ya tabbatar min suna nan , hijabina na saka na buɗe ɗaki na nufi ɗakin Dikko.

      Gaba ɗaya su Ashiru suna wurin , Dikko yana kwance a ƙasa ya dafe kanshi da hannun damarshi cikin yanayin jigata , ya fiffizge igiyar , wurin saukowa daga saman gadon ƙafarshi ta riƙe shi yasa ya faɗi kenan ? Kallona Ashiru yayi cikin ɓacin rai yace amma me kika faɗamin maganar siyo miki igiya ? Shiru nayi ina ta karkasa ido kamar an kama ɓarawon “ya “ya ina kallon Dikko sai kuma in kalli Ashiru. Gaskiya baki kyautawa abinda kikeyi. Mai gida dai kike ma haka ? Ya faɗa yana jinjina kanshi , kausasa murya yayi da fushin zuciya yace tabbas ke yarinya ce. Amma komin yarintarki ya kamata ki riƙayin abu da lissafi , tunani da kuma hasko abinda kaje ya dawo. Wannan ɗin dai da kika raina shine bangon rayuwarki idan har kika ɓata mishi ko wulaƙantashi kanki , idan kuma ya mutu tabbas ke zaki shiga3nki. Shawara da neman mafita ya rage naki. Ya ƙarasa maganar yana gyara mishi kwanciyarshi.

    Durƙusawa yayi gaban Dikko yana kuka kamar ranshi zai fita , bayan wani lokaci yayi magana cikin hayaniya cewa ke bake kaɗai ba. Bango ne kuma jegone ga duk wani da kika ganshi yana tsaye a wurin nan yayi maganar yana nunasu hada kanshi , ƙasa² yayi da murya cewa duk yawancinmu nan da kika ganmu kusan mu goma sha wani abu rabin mu duk mu marayu ne , rabi daga cikinmu duk basu da uwa uba ko ahali , haka akaje aka kwaso mu aka kawo mu domin kula dashi , an ɗaukomu ne kamar karnukan shi muyi haushi yayin da wani yake tunkaroshi , babu wanda yasan darajarmu ko tausayin mu rayuwar da zamu shiga. Mu rayu ko mu mutu ba damuwar su bane ba shiɗin dai ake so mu ba rayuwarshi kariya , muyi haushi wan² yayin da wani yake zuwa dan taɓashi , mu kula dashi bayan ƙarshen wata biyu abamu naira dubu hamsin.

      Cikin ɗaga murya yace amma shi bai mai damu karnuka ba……….. Shine ya jawo mu jikinshi ya ɗauke mu kamar “yan uwanshi , ya soke wata banzar dubu hamsin da Mai gidansu yake bamu {{ wato Dady }} bayan ya nuna mana kowa yaje yayi rayuwarshi , haka mukai ta kuka ya rufa mana asiri ya barmu mu zauna dashi koda an daina biyanmu albashin zamu zauna dashi saboda dubu hamsin ɗin dashi bai ɗauketa kuɗi ba , ganin yadda muka shiga tashin hankali yasa shi da kanshi yace zai riƙa biyanmu , shin kinsan farashin da yake biyan ko wane ɗaya a cikinmu ? Me mukeyi masa ne ? Bamayi masa wanka bama dafa mishi abinci bama masa wanki bama shara komai bamuyi mishi , zaiyi fita goma bai fita damu ba. Muci musha kowa dake wurin nan mazaunin shi yana a cikin gidan da yake rayuwa. Duk inda yake muna da gidanmu muma a can ƙarshen gida , palo bedroom toilet yadda yake da A C a ɗakinshi muma namu dashi. Yaga munyi kuka shi yasa yake san ya rayu damu domin muma muyi farin ciki kamar shi. Masu kuɗi nawa sukeyin haka ? Wanda sun ɗauki duk wani ɗan aikinsu kamar wani jakinsu. Shi yasa suka kira talaka da suna bawa………. Cikin kuka yace wai talaka shine bawa , wai bawa ? Kuma alere dangin jaki wai ya mutu gobe a sake sabo. Tou shi bai banbanta ba saboda soyayya , abincin da mukeci shi kanshi abun duba ne , idan ciwo ya kama ɗayanmu shine magani kuma ba’a cikin wanda zai bamu ba , albashin kowa a cikinmu da yake biyanmu idan kikaji sai kanki ya kwance , kafin albashi kuma ya bamu׳ , ya ƙara mana² , kullum cikin bamu yake , da marainiyar murya yace wai dandai muyi farin ciki , shi bai ɗauki duniyar a bakin komai ba dan ba itace gabanshi ba , tsaye yake ba dare ba rana , ya hana idonshi bacci zuciyarshi da kwalwarshi sunƙi samun natsuwa , bawai dan ya rasa yake nema ba. Ba kuma dan zai rasa yake tarawa ba , akwai su… Kullum zuwa suke da yawa….. An tarasu tun ba’asan amfanin kuɗi ba , tashi yayi ya ganshi cikin arziƙi tunda ya buɗe idonshi duniya kuɗi ya fara gani ba labarinsu yaji ba. Tunda Mai gidanmu ya girma suma kuɗin san ganinshi sukeyi , da kansu suke zuwa domin suma kansu sun san shine zai yaɗasu domin suje inda ba’a da labarinsu. Yana nema ne domin al ‘umma kuma nemanshi yanayin shi ne domin ya gina rayuwar duk wanda yake da rabo a ciki. Akan Mai gida gaba ɗayanmu zamu iya sadaukar da rayuwarmu dan nema masa farin ciki. Ya ƙarasa maganar yana dukan ƙirjinshi bisa gaskiyar shi. Mu bazamu yadda ba , haka kuma bazamu lamunta ba , idan ke baki san darajarshi ba mu mun sani , idan bashi da amfani a wurinki mu yana dashi a wurinmu , idan kin gaji mu bamu gaji ba. Ya ƙarasa maganar suna maida Dikko saman gado. Duk ma wani mai cewa Mai gidanmu bashida mutunci ko ɗan duniya ne ko ya raina mutane koma dai miye mu yana da kyakkyawan hali a wurinmu. Mune muka sanshi muka zauna dashi muka kuma san ɗabi’unshi dan haka mune zamu faɗi ko waye shi…… Yayi maganar yana kaima bango naushi da hannunshi. {{ yadda yayi maganar hasashe na ya bani da Inna yake… }}

           Duƙawa yayi tare da dafa gefen allon gaban Dikko yana ci gaba da cewa. Me kike so ? Idan soyayyar ce an baki , kuɗi ne damuwarki ? Suma an baki. Sultana me kike nema ne wai …..? Ko har yanzu kuɗirin fansa bai goge ba ? Rungume Dikko yayi ya ƙara yawan kukanshi yana cewa bawan Allah da wannan dalilin ya ƙwammaci ƙare rayuwarshi ba aure. Yana sanki amma yarinta da rashin tunani ya hana ki fahimta. Iya ruwa iya fidda kai……… Ko wae’…iya allonshi ya wanke. Gaki ga Mai gida tunani da samun mafita yana wurinki , dabara da sanin sirrin rami ya rage ga mai shiga rijiya. Daga haka bai sake magana ba ya riƙe hannun Dikko cikin soyayya yana mishi kallo mai nuni da tausayi , janshi aka suka bar ɗakin Ashiru yana ci gaba da kuka.

      Kamar wata jaka haka nabi bayansu da kallo har suka gama fita daga cikin ɗakin. Goge hawayen daya taru a fuskata nayi. Na maida kallona inda Dikko yake kwance yana bacci. Tou ya haka ? Meya faru Dikko ya sake warwarewa ? Ko wayau yayi min daya bani labari cewa ya warke ? Ko yayi tunanin ni bazan iya ci gaba da zama dashi ba idan bai warke ba ? Labarin daya bani G R A a ɗakinshi ya tunomin da yacemin…..

     _Naso naga Al ‘ Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba. Shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda suka binne tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lunfashi na ya dawo , tunda nake ban taɓajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin numfashi kiji wani masifa ? Hmmm Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba._

       Dogon nazari nayi , na hasko duk maganganunshi na baya. Tabbas a maganar Dikko akwai lauje cikin naɗi. Wato ni zaima ƙarya ? Dani da ku masu karatu idan baku manta ba , ni yacemin wai yaje yayi jinya har na tsawon shekarun da nayi ina zaune a gidan Inna , ku kuma tuno. Tou ya akayi ya saki Jiddah bayan shi baisan inda kanshi yake ba tun daga ranar da ni nabar gidanshi naje gidan Inna ? Ya akayi takebinshi har Abuja ? Me yasa yayi min ƙarya cewa dawowarshi kenan yazo ya tafi dani a ranar daya aiko Abbakar ya kawomin waya ? Bayan tafiyar Abbakar kuma Ummar yazo da Umar ya tafi kuma shi Dikkon yazo da kanshi ! To me gaskiya ? Ni miye matsayi na a wurin shi ? Meya ɗaukeni ne ? Me yake nufi dani ? Tabbas duk yadda akayi maganar Inna itace gaskiya Dikko baya so na……… Mai gemun yaudara na faɗa cikin hayaniya ina cewa yau saina bar maka gidanka kaje ka samu daƙiƙiyar da zata zauna dakai , ka raina mutane ni nafi ƙarfin kai ka rainani…… Wai ni zaka faɗawa ka ɗaure kanka da wayar wuta ni zaka ba labarin “yan sfires {{ Express }}….? Fuuuu na fice daga ɗakin na koma ɗakina. Wayata kawai na ɗauka da makullin mota na fice…..

       Da gudu na fito waje ina kuka har wurin mota ta , ina shiga mota Ashiru ya iso wurin yace ina zakije ne ? Cikin ɓacin rai na nunashi da makulli cewa zanje gidan Babana. Ai kasan nima Babana da Mamana suka haifeni ko ? Yadda iyayen Dikko sukeji dashi kuma suke ƙaunarshi nima Babana haka yake so na , yadda yakeji shima ɗa ne a gidansu nima ɗiyace na nuna kaina , yadda aka haifeshi nima haifata akayi ba ta sama na faɗo ba , har yanzu hannu na yana kan ƙirjina ina nuna kaina. Goge hawaye nayi da hannun haggu na ina ci gaba da cewa duka׳ kullum Dikko saiya dakeni doke²n shine soyayyar da kake iƙirarin yana nunamin wacce har kake min gori akan ta ? An baki soyayya da kuɗi. Cikin marainiyar murya nace shin baka tambayeni me nake nema ba ? Saki nake buƙata daga wurin Mai gidanku. Bana san ɗaya ko biyu a rubutoshi duka a aiko dashi a gidanmu na ƙarasa maganar ina karta makullin motar a jikin sitiyari , zana makullin nayi a goshina ina ci gaba da cewa Sultana bata ɗaukar fansa kuma ba ƙudirin wata fansa zamana da Dikko , kafin insan Dikko inayin rayuwa dan mun rabu yanzu kuma bazai sa in mutu ba , nayi maganar nima ina dukan sitiyari cikin ɓacin rai. Nuna Ashiru nayi da makulli sannan na cije leɓina na ƙasa na tashi mota ina kallonshi….. Riƙe murfin motar yayi yana cewa idan dai kinga kin fita a gidan nan sai idan bana numfashi…..

     Ko kayi rayuwa ko ka mutu bai shafeni ba , nasan dai ni na gama magana kuma tunda na yanke hunkunci magana ya ƙare. Ba tare daya kalleni ba yace can baya na taɓa faɗa miki kiyi haƙuri idan baki manta ba , yauma shine nake daɗa baki Hajiya , bayanshi banda abinda zan iya baki a duniyar nan , tunda kike a duniya kin taɓajin wanda yace rashin haƙuri ya sa yacimma nasara ne ? Saidai kiji ance haƙurinta yasa ta cimma nasara , ba wanda zaiyi haƙuri yaji nadamar yinshi saidai nadama takan zo yayin daka gagara haƙuri. 

   Ban faɗa miki maganganun nan ba dan kiyi zuciya ba , raina ne yaimin babu daɗi. Baki gaji fushi da gudu daga gidan aure ba dan wani ƙalilin abu. Tarbiyya kika gada , Babanki idan yana nan bazai so yaga kinyi yaji ko kina cewa a sakeki ko faɗa da miji. Kuma da yana raye ko kin tafi zai dawo dake bayan yayi miki faɗa da ƙara nuna miki matsayi da kuma martabar miji , dika² ma miye abun fushi ? Ya tambayeni yana murmushin ƙarfin hali , yaci gaba da cewa ai anyi wanda yafi wannan kuma anyi haƙuri sai ɗan wannan Hajiya…..? Wanda bai dakeki ba bai zageki ba ? Ki ƙara haƙuri tunda an hau tudu ai gangarewar baya wahala , kalli ya nunomin hoton Papi a wayarshi , ji yanayin farin ciki kin ajiye ɗan digu²n Papi ina zakije ki barshi ne ? So kike yayi kukan rashin uwa bayan kina raye ? Rayuwar aure da kika ganta gaba ɗayanta haƙuri ne a cikinta , idan akayi haƙuri sai a samu mafita , kiyi haƙuri sai Allah ya baki ladar haƙurin , kibi mijin ki zauna lafiya kiyi masa biyayya saiki samu albarkar rayuwa. Ki nemi gafararsa sai ubangiji ya gafarta miki , fito ki koma dan Allah ki kwantar da hankalin mijinki kema sai naki hankalin ya kwanta. Ya ƙarasa maganar da yanayin tausayi….. Yana ci gaba da cewa ba’asan maci tuwo ba sai miya ya ƙare , masha ruwa magirbi karki biye fushin zuciya kiyi abinda zai jawo miki damuwa. Da yaji da tambayar sakin aure sai “yan gidan da basu da tarbiya , ke ko kina da tarbiya da ɗa’a kiyi haƙuri ki koma idan har kika tafi zaki naƙasa matsayinki da kuma mutuncinki. Kiba Mai gida haƙuri zai haƙura kuma bazaiyi fushi ba danshi mutum ne mai mantawa da damuwa , a inda akayi mishi yayi faɗa ya gama da wurin. Yana da zuciya amma yana da ba abun duniya baya….. Fita ki nuna masa ke ɗin “yar Babanki ce….. Ki basa haƙuri domin ya ƙara tabbatarwa keɗin mai tarbiyace , ki nemi gafararshi sai yayi alfahari da iyayenki domin sune suka koya miki tarbiyar bawa miji haƙuri.

      Ko ba komai naji daɗi daya kira iyayena da masu tarbiya duk dai nasan za’ace niɗin eyar ɗan caca ne , ci gaba yayi da magiya yana bani haƙuri , kashe motar nayi tare da zare makullin na wuce banyi magana ba , ɗakina na koma na zauna gefen gado. Yayin da wani sashe na zuciyata yake cemin inyi haƙuri kamar yadda Ashiru yace , kuma in bawa Dikko haƙuri , ba ruwana da wani ciwonshi idan yayi aljannunshi idan ya gaji zai sauka , ya warke ko bai warke ba , ba damuwarki bane ba Sultana , abinda ya hanashi zuwa ya dawo dake tuni shima bai dameki ba , lokacin da ya saki Jiddah da binshi da takeyi dashi da ita da kowa ma can su ta matsemawa , kiyi tunani ki rufawa kanki asiri ki dawo daga rakiyar shaiɗan tun kafin duniya tai gwanjonki.

     Tunda ta gama waya da Sultana take ta ɓaɓɓarka zagi , wayar Mai gilashi ta kira amma kafirawan company suka ce mata a kashe yake. Dan haka ta bugi mota tayi gidanta , ba yabo ba fallasa Mai gilashi ta tarbi Sharifa kuma bata , bata izinin shiga ɗaki ba. Haka kuma babu maraba bare kuma sannu da zuwa. Da yanayin tsinkuwa Sharifa tace Mai gilas an fa samu matsala , dakel ta kalli Sharifa tare da tambayarta meke faruwa ne ? Mu shiga daga ciki cewar ita Sharifa , Mai gilashi tace ba buƙatar sirri a ƙuryar ɗaki , magana dake a fili da ɓoye duk iri ɗaya ne. Da mutum yayi maganar sirri dake gara yaje B B C ya faɗa kila idan anci sa’a a ranar wani bai kamo tashar ba. Faɗi abinda ke tafe dake ko na iya baki shawara. Mai gilashi ni a gwadamin iskanci ne ? A , a , waye ya isa ya nunawa na rigingine hasken farin wata ? Cewar Mai gilashi.  Sharifa tace to ni matar D ‘ K ta zaga , ta faɗamin magana , tayimin gori ta wulaƙantani ta muzantani ta tozartani sannan kuma ta tonamin asiri…….

      Cikin ko in kula tace duk me yayi zafi haka ne ? Zama kusa da ita Sharifa tayi cewa kwana biyu kenan bama waya bama cht kuma bana ganinshi , Mai gilashi tace kila a tunaninta yana wurinki ne ko ? Cikin rashin fahimta Sharifa tace kamar ya ? Riƙe bakinta tayi da sauri tare da cewa rufama kanki asiri kar aji mutuwar sarki bakinki Ade…. Inji Mai gilas.

     Sharifa tace kamar ya haka kuma ? Me zaki ɓoyemin ne bayan kinsan duk karatun iri ɗaya. Mai gilashi tace aini kin daina shawara dani faɗin gaskiya kuma zamanin nan yayi wuya , ina iya faɗa miki kije kiyi ta tallar terere dani , dan girman Allah Mai gilas faɗamin , Mai gilas tace gaskiya Sharifa ni inajin tsoro , dafa Mai gilashi Sharifa tayi tare da cewa idan dai baki faɗamin ba duk yadda tarenmu take tou lallai ƙullu yaci amanar koko , ɗan motsa kanta tayi alamar ta sanar da ita tare da cewa na baki dama kuma nayi miki alƙwari babu wanda zaiji ba wanda zai san anyi.

Mai gilashi tace:• shin bana faɗa miki kina da kishiyoyi ba ? Wanda suke ta harar Dikko a waje ba ? Sharifa tace kin faɗa , shin tunda kike ke Dikko ya taɓa² koda hannunki ne ? Ai bama ya kallo na , tou lallai cikin hijabi kike je mishi zance , Sharifa tace ey wallahi , kina zama kusa dashi ko a , a ? Shiru Sharifa tayi , Mai gilashi tace tou lallai nesa kukeyi da juna ta faɗa tana dariya tare da nuna Sharifa da ɗan yatsa , kallonta Sharifa tayi cewa ai babu ma ta yadda za’ayi ni na zauna kusa dashi , Mai gilashi tace da irin wannan baƙauyar soyayyar zaku cinma nasara har a kai ga matakin aure ? Miƙewa Mai gilashi tayi ta kalli Sharifa sosai sannan tace duk dabbar da tayi kuka tana da dalilin da yasa ta koka , yayin da wasu kan koka lokacin da suke buƙatar abinci , wasu kuma sukanyi kuka yayin da suka ƙoshi ne , kare yakanyi haushi yayin da rigimarshi ta motsa , duk wanda kika gani kwance kila yana rashin lafiya ne ko kuma yana da ƙatotuwar damuwa , haka take ga duk namiji daya tirki ƙarin aure…..

      Dalili kuwa shine :• duk gero sunanshi gero. Yayin da aka sarrafashi zai tashi daga sunan gero ya koma wani suna na daban , misali , za’a sarrafashi zai zama fura , kunun kanwa , kunun tsamiya , wainar gero , tuwon gero , gumba , farin kunu , kunun zaƙi ke har danbun gero na gani kuma naci shi a bakina…. Amma duk miye silar zamar da duk wannan abubuwan dana lissafo ? Gero ne ! Shine duk aka sarrafa yayi duk abubuwan nan dana faɗa , tou haka take ga duk namijin daya baro gidanshi. Wasu mazajen zasu fito ne cikin soyayya da rashin jin daɗin sunyi nisa da ilayinsu , me yasa sukejin haka ? Kula , soyayya kissa kisisina kwarkwasa iya fira mai daɗi uwa uba kuma kindai gane ba……..? Matansu zasu ɗauke musu tunani su kasance sunayin kewarsu da wa’ancan abubuwan dana lissafo har suje su dawo zuciyarsu da ƙwalwarsu baya barinsu su kalli wasu matan , ko kuma suyi tunanin kowa sai nasu , yana kasuwa ko office amma lissafinshi yana gida , burinshi ya tashi daga kasuwa ya koma dan kasancewa da shi wannan farin cikin dai. Dan haka zasu koma gida cikin farin ciki a taresu da soyayya kuma…….. Kinga namiji ne ba , amma hikimar mace ta juyashi yasa ya zama wani daban..

     Wasu mazan kuma zasu fito gidansu da ɓacin rai. Su fito kasuwa ko wata ma’aikata , idan ogane a wurin aikin abu ƙalilan zakayi ya ɗaga murya , ɓacin ran gida ya shafeka wanda kai bakaji baka kuma gani ba , idan ɗan sanda ko alƙali kila ma idan makuyi sa’a ba yace ku duk ɗin ayi gidan yari daku , tou a fara faɗo mishi karatun da shi kanshi baida lokacin da zai tsaya sauraronku ko yayi lokacin fitar da haƙƙin mai gaskiya  dan haka zaice da mai ƙarar da wanda ake ƙarar duk a haɗaku a kaiku magarƙama. Shima mace ce ta juya mishi lissafi da kuma tunani , mazan haka suke sukan canja ne daga horon da matayensu suka basu , mai tunani ya zama lurasi , lusarin kuma ya zama jarumi. Ya danganta dai da horon da aka bashi daga gida , Sharifa anshe goruba a hannun kuturu ba abu mai wuya bane , tunda har ya ƙetaro iyakar matarshi ya fito sai ki bari matan waje su duma mishi wa² ? Shikenan ke kin haƙuri ? Ki bar musu ? Ke bakya da buƙata ? Sharifa tace ina da… Tou Yusra Jiddah da wata banzar yarinya dana manta sunanta duk kiyi ƙoƙari ki rabasu da Dikko , {{ banzar yarinya da ita Mai gilashi ke nufi itace Sharifa , }} taci gaba da cewa idan kin shirya kin kuma shirya ɗaukar huɗubata bisimillah , tashi sharifa tayi ta matsa kusa da Mai gilas kunneta ta kama tayi mata raɗa bayan sunyi alƙawari da kuma yarjejeniyar amana. Sharifa ta yadda ta kuma ansa , ta yadda da huɗubar *MAI GLASS…* abinda ta faɗa mata zamuji shi idan taje wurin Dikko ne. Dariya Mai gilashi tayi tana kallon Sharifa aka wani tafa , Mai gilas tace haka suke ai mazan iri ɗaya ne , kije ki jaraba. Wannan farashin da zakiyi tukuici sai buƙata ya biya…..

       Bugu:• bugun bala’e sukayi ma Amisty bayan sunyi nasarar cafke banza. Kuma dukan bawai irin na yara ba ko na susar jiki ba. Basu bigeta da wasa ba duka na tashin hankali sukayi mata , dukan da idan dai akayi ma mutum irinshi to sai mutuwa. Tafiya babu dawowa. Tunda sukaji zancen kuɗi sukaje wurin suka kafa tarko , duk wani da zai shiga ko fita a gaban idonsu. In banda wawanci da rashin lissafi kuɗin nan wai suna cikin motar Amisty idan taje wai inda zataje sai ta canja da kuɗin ƙasar tayi hidimominta. Haka sukayi mata duka kamar wanda ya tun kari fadar shugaban ƙasa rungume da bindiga…. Ita kuma bayan ta tabbatar kowa yaje ya kwanta ta sulale dan ta gudu saboda bata yadda kowa ya kwana ɗaki ɗaya da wani ba. Ƙarya tayi musu wai zatayi baƙo shine taga dare yayi zata wani ɓace abunta. Tafa ci ƙaniyarta yadda tunani baya zato. Suka ɗauke motar da kuɗin suka barta nan zube kamar asarar tsakar dare.

        Har gari ya waye ban samu nayi wani baccin kirki ba , haka kuma na kasa zuwa ɗakinshi , tsoro da fargaba kawai ke damu na , sai zantukan Ashiru dake tayimin luguden san zaman lafiya a zuciyata. Wannan dalili shine ya hanani san zuwa makaranta naji ni kamar wata mara lafiya. Ganin har 1 saura yasa na tafi ɗakinshi a tsorace , da sallama na shiga yana fitowa daga toilet ran nan nashi a haƙe fuskar nan tayi kalar ban tsoro dasa mutum ya shiga cikin yanayin firgicewa , ɗan rakuɓewa nayi cikin rawar murya nace barka da safiya , baimin magana ba bai kuma kalleni ba ya ɗauki wayoyinshi ya nufoni dan fita daga ɗakin….. Cike da tsoro na sake cewa Dikko ina kwana , ke…….. Ya faɗa tare da yankamin wani irin firgitaccen mari saida na juya naje jikin bango dakel na haɗiye yawu lokaci guda zufa ya tsatstsafomin a fuska cikina ya juya yayi wani irin zakuɗa a tsorace na kalleshi , da ɓacin rai ya tambayeni wannan marin meya bayyana miki……? 

       Cikin kuka da marainiyar murya nace har yanzu jikinka da ƙwari , yace to ina nan a yadda nake , ban sauya ba ban kuma tashi a yadda kika sanni ba , dama idan baki manta ba na faɗa miki. Tou yauma na sake maimaitawa idan zaki kiyayi fushina tou ki kiyaye sai ki zauna lafiya , na warke ko ban samu sauƙi ba wannan bai shafeki ba saboda daga matar gida baki kau ba , ya nuna da hannunshi. Rayuwa da ƙaddara abokan juna ne , komai yana da ranar tashi daga aiki kama daga kifin gwangwani har zuwa mu “yan adam , kin gane ba ? Jeki…….. Ya nunamin , tafi ya nunamin hanyar fita , ƙara yawan kukana nayi na taho daga inda nake na shige jikinshi ina cewa na bari Dikko na faɗa maganar ina ɗagowa dan kallon idonshi , sassauta murya yayi yana cewa bakijin magana , iskancin ki kullum gaba yakeyi , wai nine kike faɗa zaki zane ? Haba An mata….? Kayi haƙuri bazan ƙara ba , tou me nayi miki kika ɗaureni bayan ni ba mahaukaci ba. Ko abokin wasanki ne ni ? Ya tambayeni yana ɗagoni daga jikinshi , saida nayi shashshekar kuka nace bana so kana yawon dare ne , sai kuma ki ɗaureni ? Wannan wane irin hukuncin hauka ne ? Ai bana so kana fita na ƙarasa maganar ina komawa jikinshi. Murmushi yayi kaɗan a sakace yace An mata……… Ya ƙarasa maganar yana rumgumeni sosai. Cikin dariya yace wai wane mai bahaggon tunanin ne ya baki wannan shawarar ne ? Ɗagoni yayi kowa yana kallon idon kowa yace sai kawai tace miki idan kika ɗaureni zan daina fita ne ehem. Yayi maganar yana shan idanuwanshi. Suna shanyewa a hankali tare da murza su da salon duniyanci. A kasalance na koma na sake kwanciya , dariya yayi da murya mai kama zuciya ya ɗaukeni yaje ya kwantar dani saman gado , saida ya lulluɓeni ya sumbaceni yace jirani ina dawowa yanxu. Yayi maganar yana fita daga ɗakin……..

     Bayan sati 1.

      Mijin Halimatu dai har yanzu baida lafiya. Jinya har ta kaisu asibiti zugar ƙawayenta kuma babu wanda ya bita sai Hadiza. Da ita ake yini akeyin komai sai dare suke dawowa gida ƙannen shi Abdul in maza suke kwana dashi. Da Halimatu ta tambayi sauran ƙawayenta me yasa basa zuwa cewa sukayi mazajensu basu yadda ba…..

      Har sati ya cinye Yazeed bai zo ba kuma bayayin waya da Jiddah. Shiru kuma har yanzu baiyi maganar turo magabatanshi ba tunda ya tafi waccan ranar sai yau yazo , duk an ɗaɗɗaure mishi jiki da tsumma an sagale hannunshi da igiya an sargafa igiyar a wuyanshi , wai Jiddah ta bashi mamaki shine dan ta tura mishi wata banzar 5million zata turo mishi ɓarayi suzo su kashe shi su ansar mata kuɗinta. Ai ba dole² yasa ta bashi ba , basai ta turo a kasheshi ba , tou ya basu kuɗin ta daina kiranshi kar yayi mata rashin mutunci , shi da ta ganshi duk cikar garin katsina babu ɗan iska kamarshi. Kuka Jidda ta farayi ita wallahi bata tura kowa ba , Yazeed yace ƙarya zaiyi mata ne ? Bafa a wata banzar miliyan biyar inta ya fara riƙe kuɗi ba. Me yasa a lokacin can da bai santa ba ba’aje an dakeshi ba ? Sai akan ita data bashi ne ? Tou ya fasa auren taje tayi da wani.

      Jiddah ta fara wallahi². Yazeed yace shi tama wani daina mishi kukan makirci yasan sharri irin na mata , haka taita bawa Yazeed haƙuri dakel ta shawo kanshi a yadda ya nuna kenan , saida ya sake buɗe fili akayi danbe Jiddah ta tura mishi miliyan biyu tace ta ba malamin ta anayin aiki , dakel Yazeed ya yadda ya anshi biyu , kuma ya tabbatar mata da kuɗin danbe ne ta biya , shi baya wani ra’ayi yana mata yayyafi ne dai dan ta rayu karta mutu. Tayi ma Dikko waya ya ƙaro wasu kuɗin……

     Dady kuwa ya bugu iya bugu a yadda yayi fentin gida da sabbin filawowi , Umar ɗan iska ne kuma baƙin mugu , da Dady yasa aka sauke fentina yace ya bada kuɗin ma’aikata zaiji da komai , ya anshi kuɗi masu yawan gaske a wurin Dady hada na toshiyar baki , Umar kuwa wajen gida kawai yasa aka gyara sauran fenti yaci kasuwa…

    Duk satin nan Mai madubi bataje makaranta ba , naso zuwa gidanta Mai gida D ‘ K ya hanani , makaranta ma shine yake kaini yake kuma ɗaukoni , ga wayar ta idan an kira ba’a samu , sai na haƙura kawai.

       Har yanzu Dikko bai cire wayarshi a jirgi ba , kuma satin nan ya bigeshi bai fita , ko gidansu rabon da yaje tun ranar daya kwantar dani a gado yaje. Kuma ya taho da Papi saboda Nabeela ta tare gidanta. Banje ba , abinda yasa kuma saboda ciki shi yasa ya hanani zuwa.

     Sharifa da Aunty Bilki ganin ana neman a buga musu game over yasa ta samu Dady akan yayi ma Dikko magana yaje wurin Sharifa , ya kama waya ya rufe sati 1 kenan da kusan kwana 2 basa waya kuma basa haɗuwa. Tadaiyi “yar barikinta a gaban mijinta irin tamu ta mata , Dady kuma ya kira Dikko yace duk abinda yake yau yaje ya haɗu da Sharifa. Shi Dady gani yakeyi ita Aunty Bilki tafi Momy mutunci tunda tana san “yan uwanshi har take tunatar dashi akansu.

     Wani irin ihu Dady yayi tare da zubewa ƙasa somamme. Yayyen Hafsa suka rufa mata da duka wanda sune sukayi tsaye wurin nemota. Can abuja suka kamo “yar iska a wata asibiti wai tana jinyar Amisty tana so ta dawo taji ina kuɗi suke ? Shine suka tattaro su dukansu da Amisty da ita Hafsa….. Shine fa kawai ya wani some dan Hafsaf fa kawai ta tabbatar mishi da ɓarayi sun kwashe kuɗi , daga an faɗa mishi shine kawai zai wani zama mataccen bakin maƙabarta………????









*JAMILA MUSA…*

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button