KYAWUNA JARAFTA TA 1-END

KYAWUNA JARAFTA TA Page 41 to 50

Kaman an tsikareta wuraren 4 na asuba tafarka da kanta batare da an tadataba, TV dake bangon dakinta ta tsaya chak tana kallo kaman mai tunanin wani abu, dasauri ta yaye bargon data lulluba dashi tasauka daga kan gadon, kunna switch din bangon tayi nan TV da decoder na DSTV duk suka kunna komawa tayi tazauna kan gadon tana sosa idanunta dake cikeda bacci, tadauki remote tashiga neman channels television news, da kyar ta iya ganoshi ta saka da sauri tana gyara zama kaman akwai abinda take shiri ta kalla, ganin ba abinda take nema sukeyi ba yasa tashiga wasu channels din tana skipping amman duka bataci karo da abinda take nema ba yarda remote din tayi akan gado sanan ta tashi tashiga bayi tai duk abinda zatayi sanan tafito dadduma ta shimfida tai nafila sanan tadauki Al Qur’ani tashiga karantawa har aka tada salla hakan yasa tarufe tai salla tana idar wa tai azkar ta tashi sanan tawuce tafito ko kadan batajin dadi, gaban dakin Hajiya tayi knocking tayi sanan tabude kofan ta shiga kan dadduma taga Hajiya zaune tana lazimi, ahankali tace “ina kwana Grandma” murmushi tamata tace “Du’a jiya angaji anyi bacci dawuri, tashi ga wayanki chan na samiki a chaji ina ganinma yacika” dasauri takalli inda ake nuna mata hadadden waya ne a bango dawani irin sauri tafada Jikin Hajiya batasan meyafaru ba kawai saita saki kuka sosai tunda tazo gidan nan she has been so happy, babu mai takura mata ko matsa mata ko kyaranta, ba’a taba bata matarai ba, ba’a hanata zuwa ko’ina, she’s truly happy, jin yanda take kuka yasa grandma ta kankameta itama ahankali tace “I promise you Du’a inhar inada rai adoron kasan nan u will never be sad again, wlh wanan karan ko uban waye kulleshi zanyi akanki, abinda kika going through agidan mahaifinki u will never go through that again kinji, kina tare dani anan har aurenki, I will take care of you, malamin islamiyya da boko ma na saman miki zai dinga zuwa Saturday da Sunday, u will excel kinji, forget komi dayasameki abaya kaddara ce, kyaune Allah yabaki amman hakan bazaisa ki karake rayuwanki a kulle adaki ba dan haka u will learn how to live with ur beauty kinji Du’a dina” gyadamata kai tayi ajikinta ahankali, dagota Grandma tayi takai hannunta kan fuskanta tana share mata hawaye tace “ba’a kuka agidan Hajiya, now tashi kidauki wayanki kije falo ki kwaso kayan shopping dinki ki jera komi a inda yakamata adakinki, idan aikin yamiki yawa ki kira su Razika su tayaki” gyadamata kai tayi ta tashi daga kan jikinta wayan tawuce tadauka tana kallo, iPhone mai kyau 11 pro max Grandma dinta tasai mata ga Sim din MTN aciki, fita tayi daga dakin taje falo ta kwaso kayayyakinta tadawo dakinta, ta shiga jera kayayyakin, harda bags da shoes hadaddu, masu tudu da flat, ga kayan kwalliya, saida tagama tsaf sanan tashiga bayi tayo wanka tafito, shiryawa tayi cikin hadadden abaya again kaman yanda Hajiya tafadi mai ruwan kasa, tai rolling gyalen da kanta dan jiya sauka su Rahima suka koyanata a shagon abaya sunma sai mata pins na kama gyalen tasa pin din, sanan tadauki wayanta tasa a jaka tasaka wani takalmi baki mai dan tudu kadan dayama farin kafanta kyau sosai sanan tafito, a falo taga Hajiya zaune tana shan ruwan bunu kusada ita tazauna tace “grandma bazaki je office yauba” murmushi tamata tace “nariga nai retire, idan kinga naje office ko akwai wani important meeting ne, kokuma naje supervision, tashi kiyi break direba na jiranki zai dinga kaiki yana zuwa ya daukoki kullum, banda latti koni bana tolerating late coming dan tahaka ake discipline na employees, go and eat” tashi tayi tawuce yau tayi breakfast kadan saita shiga kitchen wani karamin roba tadauko mai marfi ta zuba pepper meat aciki duk Hajiya na kallonta sanan ta taho tasa ajaka tana murmushi ganin Hajiya na kallonta, dan hararanta tayi tace “da yanda kikecin nama haka kikecin abinci danaji dadi kura kawai” dariya tayi tarataya jakan a shoulder tace “Grandma Byeeee” Bye Du’a ayi addu’a, gyadamata kai tayi tafice Hajiya na kallonta tundaga kan kafafunta kafanta badai kyau ba ya ilahi, tana ganin zatamai fara sakata sa Safa, mota ta shiga direba yajata zuwa office.Yau tana shiga batai kauyencin datayi jiya awajen kofa ba, glass din na budewa ta shiga ciki, mutane sai kallonta suke maza da mata, saukar da kanta kasa tayi tana tafiya ahankali kafafunta na neman hardewa sabida yanda ake kallonta, dukfa sun tsayar da aikin dasuke kallonta ake, this is the first time data shiga waje kowa ya tsayarda abinda yakeyi yana kallonta, wani irin rawa jikinta yafara kafanta na hardewa daidai tazo stairs tahau kafanta yaturgude baya tayi zata fadi, jitayi antareta ta baya an daura hannaye biyu akan kafadunta murya chan kasa taji ance. “careful” dawani irin sauri tajuyo ta kalleshi, Sharif ne yana sanye cikin suit black yay wani irin kyau, hannayenshi dakekan shoulder dinta ya kalla sanan yajanye su ahankali murya chan kasa yace “sorry about that” sanan yajuya daga inda yake yakalli ma’aikatan su da ganinshi yasa kowa yafara aikin gabanshi kaman da gaske dan kwafa yayi sanan yajuya yakalleta yace “let’s go kinada aiki yau” yay maganan yana gaba ahankali tabiyoshi abaya, Cafeteria dinsu yaje yakarbi cup biyu yajuyo na tea yabata sanan yarike na coffee sukai stairs yana tafiya yace “omg, at this points knees dina sun kusan cirewa kuma duk kece Du’a, mezan fadama future wife dina idan suka cire” dan murmushi kadan tayi tana binshi abaya batare datace komiba hakan yasa yajuyo yakalleta, boye murmushin tayi dan zaro idanu yayi cikeda wasa yace “did u just smile knees dina na aching” ahankali tace “sorry” juyawa yayi yacigaba da tafiya yace “zan gayama future wife dina it’s one gurl called Du’a tasani nake bin stairs zuwa 5th floor fa sabida tana tsoron elevator” murmushi tasakeyi batace komiba har sukakai office dinta, shiga sukayi ta ijiye komi kan table ta tsaya agefe, juyowa yayi ya kalleta yace “me kikeyi abayana sit akan kujeran ki nabaki aikin ki natafi” gyadamai kai tayi tazo ta gabanshi tawuce tazauna kan kujeranta ahankali kaman mai tsoro, wani karamin mini pad yamika mata yace “the CEO sent this, yanaso kiyi zanensu next week idan yashigo aikinsu za’a fara, 5 design na hills, 5 na loafers, 5 different design na croc and unhooked sandals” ganin yanda take kallon pad din yasa yace “it’s a whole lot of work ko, don’t worry take ur time zaki iya kadan yau kiyi sauran gobe” gyadamai kai tayi ahankali hakan yasa yajuya yace “in that case bari natafi” haryakai kofa ta dago kanta ahankali tace “ummmm” juyowa yayida sauri yakalleta yace “da wani abu ne”? gizgiza mai kai tayi tace “thank you, su Rahima gave me the money, Allah amfana Ya Sharif” tunda take maganan harta gama yake kallonta, dauke kai yayi yace “you are welcome” sanan yawuce yafita daga office din.

Ranan haka tawuce zane take a E-board dinan, bakaramin burgeshi zanenta Sharif sukayi ba, kafin 4 tagama gabaki daya ma dan she’s so fast da zanen tawuce ta tafi direba yadauketa.

Tana shiga gida tafito tawuce ciki, Razika da Shemau tagani zaune a falo suna kallo TV tabi da kallo ganin film suke kallo yasa tace “ina Grandma” Razika dake kallonta tace “tana sama kaman ta kwanta bata dade da shigowa ba” sama tayi ahankali tabude kofan dakin Hajiya ganinta kan gado tana bacci yasa tawuce dakinta, kaya tacire tawuce bathroom wanka tayo tafito daure da towel tayi gaban wardrobe wani simple short gown tadauka tasaka, jin anyi knocking kofar ta yasa tace “shigo” shigowa Razika tayi dauke da tray na abinci tace “abinci nahado miki nasan kin gaji” wani irin murmushi tayi Razika nada kirki karban tray tayi tace “nagode Razika” gyadamata kai tayi tawuce tafita zama tayi kan gadon ahankali rikeda tray din tana kallon sinasir dake cikin plate, ga lafiyayyen miyan taushe dayaji naman kan Rago, dago kanta tayi sai kawai tacire tray kan jikinta ta ijiye agefe tamike tsaye da sauri switch din TV ta kunna tadau remote takoma kan gado ta zauna, gama booting yayi hakan yasa ta kunna tashar Channels Television News, daidai an nuno wani daga cikin audience ya daga hannu, hoster tace “go ahead” mikewa tsaye yace “My name is Samuel Madina Chris, My question to Mr Asad Abdullahi Kitse is you see we all know you come from a wealthy home/family, so setting up a business starting a company can not be a problem for you cus ur family are buoyant enough to support you with startup capital, mu yanzu that come from not so financially strong family how can we source for start up capital dan bamu da yan uwan dazasu taimaka mana”? 

1 2 3 4 5 6 7Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button