Labarai

Lauyar Data Kare Martabar Manzon Allah S*A*W , A Gaban Kotu Ta Samu Lambar Yabo 

Matashiyar lauyar da ta yi bayani kan dokar “Defense Of Provocation” don kare martabar Manzo Allah S.A.W a jihar Sokoto ta samu lambar yabo ta girmamawa, lauyar ita ce

Babban Basaraken Kudu “Ooni of Ife”, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya karrama Barrisater Aysha Ahmad da lambar yabo a bikin Royal African Young Leadership Forum (RAYLF) Award.,

Aisha wacce a yanzu haka take rike da Daraktan sashen shara’a na hukumar tara kudaden haraji na Kaduna (KADIRS), ta shahara wajen taimakon jama’a da kare hakkin ‘ya’ya mata.

Ta sha samun lambobin yabo da karramawa a lokuta daban-daban a fagen aikinta.

Ko a yan kwanakin nan Barrister Aysha ta samu yabo da addu’oin Alkhairi sosai biyo bayan yadda ta tsaya tsayin daka wajen kare martabar Manzon Allah S*A*W ba tare da shakka ko shayin kowa ba a lokacinda ake tsaka da cece-kuce kan abunda ya faru a Sokoto.

Ooni yace An zabo Aysha ne sakamakon ficen da tayi wajen taimakon al’umma, kwarewar ta wajen aiki, da salon iya jagoranci, da tausayin ya’ya mata da bi masu hakkinsu, kana uwa uba da jajircewar ta da kuma rashin tsoro.

Hoto daga fb

Barrister Aysha ta karbi kambun karramawar ne a dakin taro na Oduduwa Hall dake Obafemi Awolowo University, a ile-Ife.

Rashin tso*ro da sanin makamar aiki yasa Barrista Aysha ta fita tayi bayani akan “Defense of Provocation” wanda ya dauki hankalin duniya musamman malaman addin*i da masoya manzon Allah S*A*W

Wane fata za ku yi mata?

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button