Lu’u Lu’u 24

Wucewa Ayam ta fara yi suka sauka a matakalar, suna kai wa k’asa ta sake bud’e wata k’ofar, suna bi ta siririn corridor sai ga su ga al’ummar nan, caaaa sukayi kanta kowa k’ok’arin rumgumarta yake, sa’a d’aya dogarai dake wurin suka dinga taresu suna maidasu baya.
Hannaye ta dinga d’aga musu fuskarta d’auke da murmushi wasu kuma har hannun na ta suke rik’ewa, cikin hakane wani tsoho sosai daya tsufa ya shafi tafin hannunta sai kuma ya sumbaci hannun na shi, fashewa yayi da dariya yana murna da fad’in “Na gode abun bauta, ko yanzu ka d’auki rai na ban da bakin ciki dan jikina da na ta ya had’u.”
Da mamaki jin furucinshi ta kalleshi, sai ta fahimci dayawa dake tab’ata abinda suke yi kenan, a rikice kuma a mugun rud’e ta kallesu ta ja baya cikin murya mai fitar da amon tashin hankali tace” Me kuke yi ne haka? Ya haka kuma?”
Girgiza kai tayi cike da damuwa hawaye na gangaro mata cikin kasalalliyar murya tace “Kun sani jin kunya ganin yanda kuke min abu kamar wata waliyiya, me nake aikatawa daya sha bambam da ku? Me na muku? Wacece ni? Me yasa bakuyi tunanin ni ma mutum ce kamar ku ba? Me ya hanaku fahimtar ni ma ina da irin buk’atocinku na rayuwa, kama daga cin abinci a lokacin buk’atarsa, shan ruwa yayin buk’atarsu, wanka da bacci duka ni ma iya ni, hakazalika idan abincin da na ci ya kai wani mataki na kan buk’aci shiga ban d’aki dan na fesar da marar kyau da kuma anfani a jikina.”
Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tasa hannu ta share hawayenta ta ci gaba da fad’in” Ni ba kowa bace, ya kamata a dakatar da wannan farfagadan da wasu suke son su mulkeku da shi, duk da bansan me ce ce asalin baiwar wad’anda suka gabace ni ba, amma dai nasan an zuzuta abun, dan haka daga yau bana son sake ganin kuna min irin wannan da sunan girmama baiwata ko dan ni zab’abb’iya ce, ni ma mace da namiji suka haifeni sannan aka raine ni kamar yanda aka reneku.”
D’ag musu hannu tayi zata juya ta koma wani namiji ya d’aga muryarsa yace” Hakan na nufin ke ba zab’abb’iya ba ce kenan?”
Juyowa tayi sai kawai ta sauke ido akan shi, cike da fad’uwar gaba ba tare da tunanin zata iya hangoshi a cikin mutanen nan ba yayi saurin sunkuyar da kan shi k’asa, murmushi ta saki tace” E hakane, ni ba zab’abb’iya ba ce, tunda ni dai ban ga wani abu a jikina ko a cikin rayuwata ba daya sha bambam da na ku.”
Wannan tsohon daya tab’a hannunta ne yace” To amma gimbiya ya maganar canjin da zaki kawo mana? Dan na b’ata shekaru da dama ina ciyar da abinci dan kawai ki bayyana ko ‘ya’ya zasu samu rayuwa mai kyau fiye da ta wa, duk da ba k’arfin ciyarwar gareni ba.”
Da mamaki ta kalli tsohon ta gyara tsayuwa tace” Baba yayanka nawa?”
Kai tsaye ya bata amsa da” Bakwai, maza hud’u mata uku, amma duka matan na gidan aurensu.”
Kafeshi tayi da ido tace” Dukansu sunyi karatu?”
A ladabce yace” K’aramar ‘yata ita ce aka haifa shekara biyu bayan haihuwarki, daga lokacin da aka haifeki dukda kinyi b’atan dabo, hakan bai sa na cire rai da samun canji ba, daga lokacin na daina biyan kud’in karatunsu na ce su zauna gida suna kama min sana’ata, dan canji ya kusa zuwa da zasu samu rayuwa mai kyau.”
Had’e fuska tayi ta girgiza kai tana ji kamar ta wanka masa mari, saida ta feso zafin dake balbali a zuciyarta kafin ta sake jimk’e wayar nan dake hannunta ta kalli tsohon tace” A hakane kuma kake nema musu canjin rayuwa? Shin ko kasan da ace zan tattara takardun wad’anda sukayi makaranta ne sannan na basu aiki, kasan da ‘yayanka babu wanda zai shiga ciki?”
Cikin jin haushi da fad’a ta kalli dukan mutanen tace” Ire irenshi na wa ke akwai a nan? Wace irin rayuwar jahilci da mutuwar zuciya kukayi a baya? Saboda kawai an ce an haifi zab’abb’iya, shin cikinku akwai wanda zai iya nuna min wani canji guda d’aya tak wanda cikin wanda suka gabaceni suka kawo muku wanda ya tallafi rayuwarku da ta yayanku?”
Kallon tsohon tayi ta d’ora da fad’in” Me aka tab’a canza muku kafin zuwana ni?”
Wulwula ido yayi sai kuma ya girgiza kai yace” E to, zab’abb’e daya gabata wanda daga gareshi muka samu labarin zuwanki, a lokacin muna da k’arancin ruwa, kuma mun kawo kukanmu so ba adadi a wajen sarkinmu, to a lokacin shi ne ya mana rinjiyoyin ruwa wanda a yanzu malaman fada suka mayar da su panpunan zamani.”
Jinjina kai tayi tace” Na ji kun samu ruwa kyauta, bayan shi fa?”
Wata dattijuwa dake gefe ne tace” Wa ya fad’a miki gimbiyarmu? Ai bayan rasuwarshi da wasu shekaru sai iyalenshi suka fara karb’ar kud’in jama’a idan zasu d’ebi ruwa, yanzu haka yara ne birjik a duk gurin birtsatsen nan suna karb’ar kud’i ana d’iban ruwa.”
Wani murmushi tayi tana girgiza kanta kafin tace” Anfani kawai suke da ku suna cika aljihunansu, amma daga yanzu ba zaku sake biyan kud’in ruwa ba, ni zan yi magana da sarkinku wato mahaifina, ku kwantar da hankul…”
Ihun da suka saka da k’arfinsu da tapi na murnar abinda ta fad’a yasa ta dafe kunnuwanta da ta ji ihun har cikin dodon kunnuwanta, addu’a suka dinga mata da fatan alkairi da kirari sanda ta juya tare da rakiyar hadimar nan dogarai kuma suna rik’e mutanen saida suka ga shigewarta an rufe k’ofar kad’ai hayaniyar ta lafa wasu suka fara barin wurin ma.
Suna cikin taka matakalar wayar dake hannunta tayi vibration, da sauri ta duba ta ga lamba ce babu suna, tab’e baki tayi ta bud’e ta kara a kunne, muryar sarki Wudar ce ta ji cikin shauk’i yace “Gimbiyata, fatan kin sauka lafiya?”
Da mamakin jin muryarshi d tunanin kenan shi ya turo mata da wayar? Ganin hadimar nan ta juyo tana kallonta yasa ta mata alama da hannu tace “Ki je kawai ina zuwa.”
Saida ta ga ta juya ta tafi ta sauke ajiyar zuciya tace “Yallab’ai barka.”
Cike da jin k’uruciya da rashin kunya sarki Wudar yace “Ba yallab’ai ba, ki kirani da mijinki.”
Rintse ido tayi ta yatsina fuska kamar ta ga ba-haya tace “Yallab’ai?”
Amsa mata yayi da “E mana, ba kin min alk’awarin aure ba, alk’awari kuma a wurinmu tamkar d’aura auren ne.”
S’an safe gaban goshinta tayi tace “Yallab’ai kana lafiya? Ya d’anka?”
Wani abu ya ji a zuciyarshi saboda tambayar d’anshi da tayi, amma sai ya share yace “Ina lafiya, ke fa?”
Jinjina kai tayi tace “Ina lafiya, nagode.”

