Hausa Novels

Lu’u Lu’u 33

*33*

 

Tunda ya gama ya kwanta gefenta ya rumgumeta tsam a jikinshi, a hankalce yake sauraren numfashinta dake sauka a kan k’irjinshi mai d’umin gaske, irin yanda take ta shashek’ar kuka, ga jikinta da yake jin yana d’an sake d’aukar zafi, wanda idan ba zuzutan lamarin yake ba zai iya cewa har rawar d’ari yake jin jikin na ta na yi, hakan yasa shi sake matseta a jikinshi gam tausayinta na k’ara ratsashi, irin yanda ta jure bata masa hargagi ba, ba tayi ihu ba sai fawwalawa Allah komai, dan tunda ta ji an shiga ta tabbatar ya ratsata kawai ta saki jikinta sai hawaye da take.

Hannu ya zura ya k’ara jayo zanin rufar ya rufeta ruf, hannun ya kuma sa wa yana shafa gashinta daya warwatse yana maida mata shi baya, haka suka ci gaba da zama saida ya ji komai na sa a yanzun ya zama daidai, numfashinshi ya fara fita sannu sannu, gumin daya had’a ya tsane a jikinshi sannan ya sake mannata a jikinshi, cikin tausashiyar murya ya furta “Sannu kin ji, sannu, kina jin zafi ne?”

Saida ta sauke wasu numfarfashi a gaggauce sannan ta d’aga masa kai alamar e, sake d’an matseta yayi yace “Zai daina kinji, kiyi hak’uri.”

Cikin muryar kuka da har ta disashe abunda ba’a saba ba tace “Yanzu…ne ka ga…ya dace…ka ban ha…k’uri?”

Murmusawa yayi yace “Ki yi hak’uri na ce, nan gaba idan zan yi zan fara baki hak’uri.”

Kiciniyar tashi ta fara daga jikinshi, amma yanda ta ji ya rik’e gam yasa ta saki wani marayan kuka tana fad’in “Ka yi hak’uri yal’ab’ai, dan Allah karka sake min abun nan da ka yi da zafi sosai…”

Rufe mata baki yayi da tafin hannu yace “Ba yanzu nake nufi ba, sai…”

Yanda take zillewa yasa bai gama fad’a sai kuma yayi saurin fad’in “Wai dakata, me ma ya shigo dake d’akina a wannan daren?”

Fashewa tayi da kuka ta ja zanin rufar ta rufe fuskarta, da sauri ya sauka daga gadon yana fad’in “Shikenan fa, bari na taimaka miki.”

Da sauri ya nufi wajen mab’allin wutar ya kunna, hasken daya had’e d’akin yasa Ayam saurin sake rintse idonta ta dunk’ule cikin zanin, k’arasowa yayi ya jaye darar da niyyar tallabota, rik’e zanin tayi gam cikin masifa tace” Bana so.”

Sakin zanin yayi ya tab’e baki ya juya ya shige ban d’aki, tana jin k’arar ruwa alamar fitowarshi ba yanzu ba ta bud’e fuskarta, abinda ta tambayi kanta shi ne” Ta ya ma zan had’a ido da kai? Mugu azzalumi, sai na sa Pah na ya cire min kan ka.”

Zura k’afafunta tayi k’asa tana rintse ido, jikinta baya mata wani ciwo dan ta saba da motsa jiki, saidai Allah na gani k’asan nan na ta bala’i zugi yake mata kamar ta kama ruwa da barkono, zafi rau wurin ga wani curewa da yayi kamar an k’ulleshi.

Yunk’urwa tayi ta mik’e tsaye kan k’afafunta, juyawa tayi ta lalubi rigarta doguwa da pant d’inta daya jefo k’asa, da sauri ta zura rigar pant d’in kuma tattareshi a hannunta ta rik’e, takawa ta fara yi cikin sand’a har ta bar d’akin ta nufi na mahaifiyarta dan ita take da buk’ata a yanzu a halin da take ciki.

*Tun* fitarta kuma sarki Musail ya fara k’ok’arin cire rigar jikinshi, saukowa tayi daga kan gadon tana fad’in “Kar ma ka fara, ka daina kusanta ta tunda dai kai ba Allah ne a gabanka ba.”

Fizgota yayi ya had’a da jikinshi ya tallabo hab’arta yana kallon k’wayar idonta yace “Ke zaki hanani abinda na yi niyya ne ? Kar fa ki manta ke matata ce.”

Tureshi tayi a jikinta tana fad’in “Ban maka musu ba, amma aure na da kai ya kusa k’arewa.”

Da azama ya tunkareta daga shirin ficewar da take ya sake figo siririn hannunta, a hassale ta juyo har tana fad’awa k’irjinshi, gam gam ya matseta a jikinshi cikin b’acin rai da rad’a kamar a kunne yace” Me yasa ba ki da tunani ne ? Ta ya za ki barta cikin wannan had’arin? Me yasa bata bar nan d’in na kamar yanda…”

Yanda take ta gilma idonta akan fuskarshi ne yasa shi d’auke idonshi yace” Share kawai.”

Da mamaki murya a tausashe tace” Me kake magana a kai? Wacece wai?”

Gashinta ya fizga da k’arfi ya d’aga kanta sama suna sake kallon juna da kyau, had’a bakinshi yayi da na ta ya shiga tsutsa da sauri sauri tare da d’aukarta yana neman direta kan gado, bille bille ta fara tana neman ya sauketa.

*A* lokacin ne Ayam ta saki ihun nan na farkon ganin Umad kafin kuma ta suma, dukansu sun ji hakan yasa Musail sakin Juman ba tare daya shirya ba, dan a zuciyarshi ya ji kamar an yakushe shi da k’arfi, a sukwane ya fita a d’akin saidai bai san ina zai nufa ba, kusan dai a falon nan babu inda bai duba ba amma babu ita, kuma fadawan dake bakin k’ofa sun tabbatar masa ba fita tayi ba, har d’akin Ayam d’in saida ya shiga bata nan, sai kawai ya koma d’akin Juman cikin fad’a yana fad’in “Kin gani ko? Tana ina yanzu? Me ya sameta?”

Kamar wacce ke kallon bak’on abu haka ta kallehi tace “Wai wacece ka ke nuna damuwa a kan…”

A tsawace hankali tashe yace “Ban sani ba, ‘yata na ke miki magna a kai Juman, me ya sameta?”

K’wafa yayi ya juya zai fita tayi saurin rik’o hannunshi, cak ya tsaya ya juyo yna kallonta, kamar zata fashe da kuka ta marairaice tace “Me ya sameta? Wani abu ka shirya a kan ta dama? Shi ya sa tana baccinta a jikina ka korata daga d’akin nan? Musail me ya sa ? Me yasa zaka kashe min yata?”

Fizge hannunshi yayi yace “Ni ban kasheta ba, sake ni.”

Tare k’ofar tayi da sauri tace “Babu inda zaka je Musail, ‘yata fa, wallahi Allah sai ka nemo min yata.”

A harzuk’e dan ya fi ta shiga tashin hankali yace “Kuma daga nan ne zan nemo miki ita d’in?”

Fashewa tayi da kuka ta sulale a bakin k’ofar kamar ranta zai fita, sunkuyawa yayi yace “Juman, ki kauce a hanyar nan na je na duba na ga halin da ‘yata take ciki, idan muna nan kuma wani mummunan abu ya faru da ita fa?”

Da sauri ta tashi tsaye ranta b’ace ta fara kai masa bugu a k’irji tana cewa “Kar ka sake kiranta da ‘yarka, yata ce ni kad’ai Musail, duk abinda ke faruwa ai kai ne mai alhakin k’ullashi.”

Rik’e hannayenta yayi duka biyun ya mannata a k’irjinshi ya tallabe kanta ta baya yana kiran “Shiiiiiiiiii! Ya isa haka, ya isa haka na ji.”

Bata daina fad’in “Bai isa d’in ba, mugu azzalumi, kana so ka kashe ‘yarka ta cikinka da hannunka, wallahi Allah sai ya mana hisabi, ba zan tab’a yafe maka abubuwan da ka min ba, ka rabani da iyayena, ka rabani da masoyi na sannan ka rabani da yata ma yanzu? Me ya rage min yanzu da baka d’aukeshi ba? Fad’a min me ya rage? Rayuwata? To ka d’auka gani gabanka…”

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button