NOVELSUncategorized
NIDA AMARYATA 5 & 6

5⃣-6⃣
Kallonsu gaba Daya suka maida ga Nihila,wadda ita ko a jikinta,illah ma suburbudar abincinta data ci gaba dayi,banda harara babu abinda Alhaji sani ke aikawa yaran,hakan yasa kowannensu ya gaggauta yin breakfast din,sannan suka mike tare da yiwa mamansu sai sun
dawo,addu’a tayi musu suka fice suna amsawa da ameen.
Kamar kowa jira yakeyi su fita,aka hau rige-rigen magana tsakanin su uku,Amma kafin tasu ta fito ta Nihila ta Riga ta kowa,hakan yasa sukayi shuru,aikuwa sai ji sukayi tace,
“Allah ko baba,dazun Nan abinda kaimin Saida naita Jin kunya,danma dai Aunty hama tace Wai inka tabani Kar inyi maka musu wallahi da cewa zanyi Kai Dan iska ne,Amma fa bakaji bakinka ba sai kamshi yakeyi,Kuma daka….”shut up! Ya fada cikin daga murya,you are very stupid,ya karasa maganar kamar zai maketa,Nihila dako alamar tsoro Bata Nuna ba illa ma kurbar shayinta da takeyi,sabanin Hajiya Hafsa,da duk jikinta ya hau kyarma sanin halin Mai gidan,tana son yin magana Amma tana tsoro ganin yadda mud dinshi ya canza,zuwa ainihin yadda ta sanshi.ji tayi Nihila tace,”Allah baba ka fiya masifa,nifa ko’a gida Naga Aunty hama na fada dariya take bani,Dan sai Inga tayi wani Muni,kamar namijin alade,Kai Kuma fa yanzu baka ganka ba kamar namijin bauna……Tau..tasss…ya dauketa da wasu tagwayen mari,Wanda Saida suka Sata wuntsilowa daga saman kujerar,Bata Gama tantance kanta ba,taji Yana fadin,
“Ke Ni sa’an ubanki ne,Naga alamar bakida tarbiya ko? Dan Kinga na kyaleki? To na daga Miki kafa ne kawai Dan kina matsayin bakuwa,Kuma nayi tunanin ke din irin wadda nake so ce,Ashe sabanin hakan ne,daga yau sai yau,duk ranar Dana Kara ji ko Naga kin Fadi magana Akan wani Abu tsakanina dake,wallahi saina fasa Miki baki…Bai Gama rufe baki ba sai ji yayi katsam a bakinsa,Bai Gama tantancewa ba,yaji ta Kara buga Masa flak’s din shayin dake kan dinning din,wani jiri yaji,yayin daya Fara ganin bibbiyu,a yanayin dayaga tayi tsalle Tayo kansa,in beyi karya ba zai iya cewa ganin ta yayi kamar jackie Chen,ji yayi ta Dane wuyansa tare da sakar Masa gula a dukkan kumatunsa,Wanda yasashi zubewa luuuuu kamar Dan maye, ita ko tamkar ‘yar takwando ta dire kasa.Hankali a tashe Hajiya Hafsa tayi kansa tana Kiran sunanshi,ai kawai sai Jin kukan Nihila tayi a bayanta,Koda ta waiga sai ganinta tayi kwance kasa tanata birgima tare da bare baki tana ihu iyakar iyawarta.Gaba Daya Hajiya ta rasa inda zata Sa ranta,ai itama saita sa kukan tare da shigewa daki kawai ta barsu anan.Tana shiga ta Danna wayar family doctor dinsu ta kira,Yana dauka ta fashe mishi da kuka tana fadin yazo gidan ba lfy!,cikin tashin hankali yace mata gashi Nan zuwa.
Alhaji Daya Zama kamar Dan kwaya,Wanda kukan Nihila ke kokarin dawo dashi hayyacinshi yasa shi dagowa da kyar,duk da jirin dayake ji,Saida yayi kokarin mikewa ya zauna,tare da jingina da jikin kujera.
Lokacin da likita ya karaso da hanzari ya shiga gidan, sakamakon jiyo ihu da yayi,ko masu gadin gidan da sauran ma’aikata abinda ya hanasu zuwa Dan sunada Dan nisa da anihin cikin gidan,Kuma suna kokonton kamar ba daga ciki ihun ke fitowa ba,Dan haka sukayi yi zamansu.
Yana shiga falon da Nihila ya Fara cin karo tana birgima.
Subahanallah! Ya furta,tare da karasawa inda take Dan Jin mi aka mata,Yana shirin tabata yaji an tunkudeshi,cike da mamaki ya waiga Dan ganin me wannan karfin halin,ganin Alhaji tsaye akanshi Yana huci,ga bakinsa Daya d’an tasa,yasashi Kara shiga mamakin.
Ji yayi Alhajin na fadin,Kai bakada hankali ne da zaka tabata? Ko an fada maka Nan gidan ‘yan iska ne? Ya fada cikin tsawa,tare da rike kanshi dake barazanar tarwatsewa.tsawar da yayi ne yasa Hajiya fitowa,yayin da ita kanta sarauniyar kukan ta mike tana kallonsa.
Doctor da mamaki ya Kara cika sa, Saiya maida kallonsa ga Hajiya Don neman Karin bayani.
Cike da takaici hajiyar tace, ai dama kayi tafiyarka doctor,tunda naga harya Sami sauki,tunda har yasami zarafin yin fada Dan an taba ‘yar cikinsa wadda yake fadin amaryarsa babu ko kunya.
Shi kanshi doctor ya girgiza da Jin Wai Nihila ce matar Alhajin,duk da jikinta Bai Nuna shekarunta ba,Dan tsab za’a iya Mata aure ta zauna ba Kuma anyi la’akari da cewar yarinya bace,kawai abinda ya daure Masa Kai shine,a shekarun Alhajin,Wanda ya zuwa yanzu ai Bai kamata ace Yana auren kamar wannan ba.Ganin duk sun tsaya suna Masa wasu surutan banza,yasashi cewa doctor ya fice Masa a gida,baya bukatar taimakon.dole doctor ya fice din kamar yadda Mai gidan ya bukata.Hajiya na Shirin yin magana ya dakatar da ita ta hanyar daga Mata hannu,dole taja bakinta tayi shuru.
Itako Nihila ganin Alhaji sani ya tsareta da ido,yasata Kara kwabe fuska,Dan inta tuna Marin daya yi mata,saitaji kamar taita cizonshi,Dan ita tunda suke da Aunty hama Bata taba Koda yimata fada ba,bare Kuma duka,Dan haka tana kallonshi,ta furta wallahi Allah ka isarmin.kallonta duka sukayi, shikuwa Alhaji ya Nuna kanshi da yatsa tare da fadin “Ni kikewa Allah ya Isa?”
“NI bada Kai nake ba,da bangon can nake”,ta fada tana Nuna bayanshi.
Sallamar da akayi ce tasasu fasa maganar da sukayi niyya daga shi har hajiyar.
Da gudu Nihila ta karasa ta rungumeta,tare da fadin, oyoyoo,Aunty hama,shine kikacemin da asuba zakizo kimin wankan Dan in fito Ina kamshi,shine baki zo ba,sai Kuma tafara hawaye,tare da fadin,gashi Nan kin kawoni gidan mugaye sai dukana yakeyi,da yi min fada.
Aunty ham ko Gama ji batayiba ta Kara maimaita kalmar duka?
“Duka fa kikace?
Gyada Kai Nihila tayi,tare da Nuna Mata gefen fuskarta da yayi ja.
Aikuwa take Aunty hama tacire hijabi tare da cin damara,ta Fara fadin Ashe ko yau da bala’i,na rantse da Allah saina Rama Mata,daga auren jiya-jiya ka kamamin ita da duka,duka nawa take,yarinyar da badan ta yaye kanta ba da Ina kyautata zaton da yanzu tana Shan nono,ko an yayeta da ba’a Dade ba,Nan lokacin daka gani kana so ba irin ‘yar murya da bakayi,shine daga ganin an aura maka ita,zaka Fara jibgarta Ani ban San namijin duka bane Kai da mezai Kai ni baka auren hantar ‘ya’ya.wallahi yau saika San ka tabata Dan koka biya Marin da kayi Mata ko Kuma wallahi inta jibagarka kamar an aikoni……
Tabdijam,shin Wai ku tayani kallon Alhaji da Amaryarsa,shin wace iri ya dauko?
Alkalamin khady ✍