Hausa Novels

Lu’u Lu’u 46

A sanyaye ta amsa da “Lafiya lau, ina wuni.”

A tausashe ya amsa da “Lafiya lau, ya na ji muryarki haka?”

A shagwab’e tace “Ba komai.”

Cike da salo yace “Um um, ban yarda ba, fad’a min me ke faruwa?”

Kamar zata fashe da kuka tace “Na fad’a maka ba komai, kawai da safe zan zo nan.”

D’an zaro ido yayi yace “Ina nan?”

A kumbure tace “Wajenka mana.”

Da mamaki yace “Ayam…kina buk’ata ta a kusa da ke ne?”

Langabe kai tayi tana tunanin ta fad’a masa tilasta ta aka yi? Ko kuma ta fad’a masa asalin abinda take ji? Kamar sub’utar baki tace “E.”

Da sauri sai kuma tace “A’a a’a.”

Yar dariya yayi yana girgiza kai kafin a sanyaye yace “Ayam, bai kamata ki taho ba tare da kin k’arashe aikin dana fara ba.”

Da mamaki a fuskarta tace “Aiki kuma? Wane aiki?”

Ajiyar zuciya ya fara saukewa sannan yace “Da taimakon ubangiji mun yi sa’ar bin dindigin wanda yayi harbin nan bayan an kashe shi shima, da aka bi dindigin wayar mutumin kira na k’arshe daya amsa Bukhatir ne ya kirasa, yanzu haka Bukhatir na hannun hukumarmu kuma ya amsa laifinsa, wanda ya tabbatar mana shida margayiya Zafreen ne suka d’auki nauyin makashin da mak’odan kud’ad’e, gudun kar ya tona musu asiri kuma sai Bukhatir d’in ya kashe shi, dan haka ki k’arasa wannan aikin kafin ki taho.”

Numfashi ta sauke tace” Amma ai ka ce kun kama shi, ita kuma yanzu bata raye, me kuma ya rage da zan yi ni?”

A sauk’ak’e yace” Akwai.”

Ita ma a tausahe yace” Me kenan?”

Cikin nutsuwa yace” Dhurani, wanda shi ne wanda ya taimaka musu wajen gudanar da shirin, sannan shi ya gabatar musu da maharbin sannan ya samarwa da Bukhatir bindigar da bata da lasisi, sannan ki tabbatar kin tsayar da sarkin da zai mulki Khazira, dan barin Khazira ba sarki tamkar barin k’asar Texanda ne babu shugaban k’asa.”

Jim tayi kamar bata jin shi, gaba d’aya jikinta yayi sanyi, a sanyaye tana fito da siraran hawaye tace” U…mad, ina so na kwanta a jikinka,… Damuwa ta min yawa.”

Saida ta share hawayen tace” Please ka bani izinin zuwa da safe gareka, ina neman sassauci.”

Lumshe ido yayi y cije leb’enshi kamar zai yi kuka, aradun Allah mugun abun take taso mishi daga k’asa, wani irin tartsatsi take saka shi yana ji, dama a d’ane yake tun sanda ake shgalin nan saboda yawan tab’ata da yake, yanzu kuma da tayi maganar ta wata irin sigar d’aukar hankali, shi ma kuma ya d’auki maganar da wata sigar d’aukar hankalin, sai abun yake neman fin k’arfin sa.

Shiru yayi ya kasa cewa komai, haka ita ma sai shashek’a da take yi a hankali a hankali, tabbatarwa da tayi ba zai yi magana ba yasa tace “Wa zan d’ora a matsayin sarki? Ni bansan wanda zai iya yin adalci ba, ka zab’a min ?”

Da k’arfin bala’i ya fizgo maganar ta hanyar fad’in “A..da…h.”

A sanyaye baki bud’e ta amsa da “Adah? Sarkin yak’i?”

Jinjina mata kai yayi kamar yana gabanta, sai kuma yace “E, mahaifinki bai da amintacce sama da shi, mai halacci ne da kuma amana.”

Jinjina kai tayi tace “Shikenan, zan gabatar da shi a matsayin sarki Khazira, sarkin k’asar Texanda.”

A hankali yace “Ya yi kyau.”

A ladabce tace “Yallab’ai, zan iya neman wata alfarma?”

Jinjina kai yayi sannan yace “Uhum! Komai na wa na ki ne.”

Murmushi tayi kafin tace “Mah, ina so idan mah ta gama takaba ta dawo Giobarh kusa da ni? Ba na so na sake nesa da ita, ina so ta zauna tare da ni.”

D’an murmushi ya k’ak’aro yace “Buk’atarki ta karb’u, ni ma kuma zan baki mamaki idan kika zo safiyar gobe.”

D fara’a tace “Wane irin mamaki?”

Cikin zolaya yace “Ke wata yarinya, idan na fad’a miki bai zama abun mamaki ba kenan?”

Turo baki tayi tace “Na ji to, amma ni ba yarinya ba ce, tunda ni ma na kusa zama uwa.”

Tana fad’a ta kashe wayar ta aje tana k’yalk’yala dariya, shi ma dariya ya dinga tintsirawa yana girgiza kai ya aje wayar, mik’ewa yayi ya d’auki flask d’in tea ya zuba a kofi sannan ya matsa lemun tsami a ciki ya shanye ya kwanta ruf d ciki dan samun saukin abinda ke damunshi.

 

*Alhamdulillah.*

The post Lu’u Lu’u 46 first appeared on 2gNovels.com.ng.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button